Skip to content

Martabarmu | Babi Na Uku

5
(3)

<< Previous

1986, Kano

Yaron da yake rike a hannunta take kallo, yaran da duka satin shi biyar a duniya, wasu hawaye masu dumi na tarar mata cikin idanuwa. Amman zuwa yau tasan cewa kukan nan babu wani amfani da zai musu, kukan ba zai dawo mata da kaninta ba, ba zai canza kaddarar yaron da yake hannunta ta Maraici a satika biyu bayan haihuwar shi ba. Ba zatace tashin hankali bakonta bane ba, tasan shi a lokacin da ta raya Yayya, ta kuma san shi a lokacin da Ahmadi ya hadata da Maryama da ta zame mata Karfen kafa (Rufaida Omar). Tana kuma cikin shi har yanzun da Maryama ta ajiye kwai a cikin gidan Ahmadi, dan duk lokacin da zata ga giccinta ko kukan yaran nata Haris, sai taji wani abu ya tsirga mata.

Kwance take a daki tun bayan da tayi sallar asuba satika biyu kenan da suka wuce, haka kawai jikinta yai wani irin sanyi, ba shida alaka kuma da fadan da sukayi da Ahmadi tasani, kishinta a duk ranar da yake dakin Maryama daban da abinda takeji yanzun. Ko daya shigo ya dubata ma da safe inda yake bata kalla ba, ballantana ta amsa dukkan tambayoyin da yakeyi mata. Tana jin shi harya fice, dakyar ta iya tashi ta watsa ruwa, Rayyan ma tayi mishi wankan. Gobe ko jibi take da niyyar yaye shi, a karo na farko da har zatayi yaye batare da wani cikin ba.

Zatayi karya idan tace abin baya damunta, bata da kowa da yake fahimtar ta duk dangi, daga Gwaggo Bare sai Khadi. Yayyanta mata da suke ciki daya data gwada fada musu damuwar ta zancen su kusan kala dayane

“Kiyi hakuri da kaddarar ki Maimuna, kowa da kika gani ba son kishiyar nan yakeyi ba, ki cire wasu zarge-zarge daga ranki tunda mijin ki na son ki”

Shisa ta koyi kame bakinta a gabansu, son da suke ikirarin Ahmadi nayi matane dalilin komai, sunki fahimtar soyayyar nan tashi da yake matace yake rabawa da Maryama. Soyayyar da aka ga yana mata ce ta tsone idanuwan su Maryama harta shigo mata gidan miji. Yanzun kuma soyayyar da suka kasa nasarar dakushewa gabaki daya a zuciyar shice dalilin da take zargin suna son hana mata cigaba da ajiye yara a gidan Ahmadi. Ko da ta tambaye shi tana so taje gidan Gwaggo Bare a lokacin bai hanata ba, tana zuwa da kukanta ta shiga gidan, tana saka Gwaggon yin fatali da rariyar hannunta da take tankaden garin dawa tana mikewa ta tarbeta

“Na shiga ukku ni jikanyar Munzali… Maimuna lafiya?”

Cewar Gwaggo bayan ta taimaka mata ta kwance goyon Rayyan ta sabashi a nata bayan ta daure da zani. Kai Maimuna take jijjigawa kukan da takeyi yana kara yawaita

“Gwaggo har yanzun shiru, ban taba wata shidda cikakku ina shayarwa babu wani cikin a jikina ba. Ina tsoron ko Maryama ta shafemun mahaifa…”

Salati Gwaggo takeyi tana karawa

“Anya su Maryama basu kwashe kayan su daga gaban Ma’aiki ba? Ina mutanen nan suke so sukai haqqi? Wato gaje gidan gabaki daya sukeyi shisa ake so a hanaki haihuwa. Wallahi bokan Karime yayi karya…”

Bata bar gidan Gwaggo ba saida ta tabbatar mata da taji labarin wani Gwani da yafi Malaminta kwarewa, dan shi sha yanzun magani yanzun ne. Yasan ilimin taurari fiye da misali, zataje wajen shi ya buga musu kasa ya fayyace musu abinda yake faruwa. Koyayane har gida zatazo tayi mata bayani, sai a san yanda za’ayi. An kuma tabbatar mata da cewa da gaske daurin mahaifa akayi mata, cikin kogon maciji aka binne asirin, ranar yini tayi kuka kamar ranta zai fita, sanda Ahmadi ya dawo duka fuskarta a kumbure take, shine musababbin fadansu, tambayarta da yayi ko lafiya ta kuma amsa shi da

“Rabona da lafiya tun kafin na yayibo mana Maryama, tun kafin ka bata damar da zatayi amfani da ita wajen kassarani”

Tana ganin tashin hankalin da yake cikin idanuwan shi kafin ya karasa cikin dakin sosai yana tsugunnawa kusa da ita

“Wani abin tayi miki? Da na fita tayi miki wani abinne?”

Ahmadi yake tambaya, wannan karon cikin idanuwa Maimuna take kallon shi

“Baka mamakin yanda har yanzun bani da shigar ciki? Ko ka bace lissafin watannin Rayyan?”

Cike da rashin fahimta Ahmadi yake kallonta, bawai ya bata lissafin watannin Rayyan bane ba, amman bai kawo komai a ranshi game da batun ciki da Maimuna bata samu ba. Yasan haihuwa nufin Allah ne, kuma ya banbanta lokacin samuwarta a tsakanin mutane. Watakila wannan karin abin ya canza matane shisa.

“Ba cikin wata na sha takwas yake ba? Satin daya wuce inajin kike mun zancen yaye shi.”

Kai Maimuna ta jinjina mishi.

“Kana sane kenan, baka dai mamakin yanda akayi bani da wani cikinne kawai.”

Numfashi Ahmadi ya sauke.

“Haihuwa nufin Allah ne Maimuna, ba lallai duka tazo miki iri daya ba.”

Kai take girgiza mishi, taso ya fahimceta ba saita mishi gwari-gwari ba

“Ina tsoron ko an mun wani abune, ko an shafe mun mahaifa n….”

Ahmadi bai bari ta karasa ba ya katse ta da,

“Subhanallahi… Maimuna… Wanne irin zancene wannan? Yaushe kika fara yarda da irin abubuwan nan? Me ya shiga kanki? Waye zai miki wani abu?”

Idanuwanta cike da hawaye ta ce.

“Wa kasan zaimun wani abu banda Maryama? Yanda suka mallakeka suka shigo gidan nan shine suke neman duk wata hanya da zasu nisantani da kai.”

Ta karashe maganar cikin zafin zuciya da kunar rai, tana saka Ahmadi yin duk wani salati da zaizo bakin shi.

“Allah ya kare mun ke ya shiga tsakanin ki da kowaye yake son juyar miki da tunani haka. Maimuna dan girman Allah ki natsu kiyi amfani da hankalin ki kan zantukan da ake gaya miki”

A tausashe yake maganar, kawai yanayin yanda yakeyi dinne ya kara tunzura zuciyarta.

“Baka damu ba shisa ba zaka fahimceni ba, tunda ita ta fara tara maka yara….ta fara fitowa tsakar gida tana daga mun kafada zata fara lissafin yawan yara dani….”

Mikewa kawai Ahmadi yayi

“Allah ya shiryeki ya yaye miki abinda ya shiga kanki. Saikin gyara lamurran ki wallahi”

Yake fadi yana ficewa daga dakin, bayason tsayawa yaji maganganunta balle harya biye mata suyi fadan da idan basuyi ba yaga alama batajin dadi. Haka ta kwana ko wadattacen bacci bata samu ba saboda kunar zuci. A haka kuma ta wuni tanajin ta sama-sama. Su Khalifa ma na dawowa gidan daga makaranta, kadasu tayi gidan Yaya Ayuba, har abinci saci acan dan bata samu karfin dora tukunya ba. Bata kara mamaki ba sai da Ahmadi ya shigo gidan ko la’asar batayi ba, tasan ba girkinta bane ba, shisa ta kara mamakin ganin ya fado dakin nata

“Maimuna…”

Ya kira da wani irin yanayi a muryar shi da yasa gabanta yin mummunar faduwa, tana kuma mikewa daga kishingidar da tayi, tunda tasa Rayyan ya kwanta yayi bacci itama take nan gefen shi. Ganin yanda yake kallonta yasa ta mikewa tsaye gabaki daya

“Lafiya? Me ya faru?”

Ta tambaya, so yake ya bude bakin shi ya gaya mata rasuwar dan uwan da yasan duk a cikin  gidan su tafi shakuwa da shi, tsiran su ba wani mai yawa bane ba, duka shekaru biyu ya bata, kuma shi kadai ne take ji har kasan ranta duk a cikin yaran matar Baban nata da taki jinin ta bude idanuwanta tagani. Amman kowa yasan Maimuna yasan Audu, ko kasuwa yaje tsarabarta daban take da ta sauran mutanen gidan. Badume daya koma da zama bayan auren shi bai yanke zumuncin da yake tsakanin su ba, duk juma’ar duniya yana shigowa, kuma kowa yasan dan ita kadai yakanyi hakan, har gida yake zuwa ya dubata ya kai mata yan tsarabun da ya siyo.

Kusancin su mai girmane, shisa aka rasa mai zuwa ya fada mata gobarar da ta afka musu tun a daren jiya, gobarar da tai sanadin rayuwar Audu, matar shi da yaran shi biyu, cikin ikon Allah tana barin Bilal, jaririn da satin shi uku da haihuwa. Lamarin da ya girgiza kauyen Badume da kewayenta, domin Audu mutum ne mai karamci da sanin ya kamata, tun zaman shi babu wanda zaice ga ranar da yaga fuskar shi ba dauke da murmushi ba. Mutum ne da yake samun shaidar arziki ko da baya waje. Ahmadi aka samu har wajen aiki, suna ganin kamar zai fi mata sauki idan taji daga bakin shi, shikuma yana juyayin yanda ba zata taba manta a bakin shi taji wannan lamarin ba.

Da bakin shi ya fada mata zancen auren shi da Maryama, zancen da ya birkita mishi Maimunar shi ta yanda har yanzun bata dawo dai-dai ba, shi din mutum ne mai rauni, sam ba zai iya fada mata wannan zancen ba. Asalima yana ganinta yaji idanuwan shi sun ciko da kwalla, kwallar rashin Audu da ba ita kadai zataji shi ba, kwallar tausayin matar tashi da halin da yasan zata shiga. Bai iya komai ba sai hade dan sauran tazarar dake tsakanin su yana rikota jikin shi, zuwa lokacin harta fara kuka tun kafin ma tasan meya faru, jikinta ya gama bata koma menene ya faru ba abu bane me kyau.

Ko ina jikinta bari yakeyi

“Me ya faru? Ahmadi waya rasu? Ko Baba ne?”

Take tambaya tana dagowa daga jikin shi, kai ya girgiza mata yana kokarin danne kwallar dake son zubo mishi. Dakyar ya iya cewa

“Ki dauko mayafin ki…”

Batayi musu ba, dan ko ina jikinta bari yake, mayafin ta dauko tana rike dashi a hannunta ta fice daga dakin, tama manta da Rayyan da yake kwance a cikin dakin, takalman ma, daya nata, dayan na Ahmadi daya cire a bakin kofar ta saka. Saida ya fito daga dakin ya kalleta cike da tausayawa, nata takalmin ya tsugunna ya dauka yana tura mata, kula tayi ta zare nashi, ta saka nata. Sannan ya dago yana saka takalman a kafar shi. Maryama da ta fito goye da Haris ya kalla, da idanuwan shi yai mata nuni da bangaren Maimunar, ganin har tayi hanyar waje

“Rayyan yana bacci…”

Ya furta a hankali, itama da alama hankalinta a tashe yake

“Me yake faruwa?”

Dan lekawa yayi bai hango alamar Maimuna ba, hakan yasa shi fadin

“Audune Allah yayi mishi rasuwa, sunyi gobara jiya da dare, kamar da iyalin duka…”

Yanda Maryama ta dafe kirji tana sakin wani salati daya fito da kuka yasa Ahmadi wucewa yabi bayan Maimuna, ta yanki hanya kuwa sai sauri takeyi. Kunya ya cire ya ajiye gefe yana karasawa da sauri ya kama hannunta ya rike. Ko da suka isa gidan ma bai saketa ba saida ya karasa da ita har cikin gidan. Inda ta samu tashin hankalin da bata taba tsammani ba, tayi suma ranar yakai hudu tana farfadowa ana gaya mata labari kala daya. Tun da dare data samu natsuwar da zata iya mikewa taje ta karbi Bilal da sai kuka yake a hannun Yayar Audu din wato Talatu.

“Da kin barshi kin ji da kanki kawai Maimuna, ko tsayuwar kirki bakya iyawa…”

Talatu ta karasa cikin kuka. Wata mata da Maimuna ba zatace kowacce ba a lokacin ta karbe zancen da fadin

“Shima yaron zafin maraici ne yake taba shi, duk wanda suke shayarwa an gwada bashi mama fur yaki karba…”

Hannu kawai Maimuna ta saka tana daukar Bilal batare da tace musu komai ba ta fice daga dakin. Waje ta samu a tsakar gidan tana zama da yaron a hannunta, tanajin kamar duk duniya shi kadai ne alakar data rage mata a tsakaninta da Audu, kamar babu jinin shi a jikinta, kallon Bilal take, kaunar yaron na ratsa duk wani sassa na jikinta, tana tuna yanda ko ranar suna shi satika uku da suka wuce harda ita ake tsokanar Audu da yaran sak shiya biyo, duk ya kwace ma Jummai matar shi kamanni da yaran nasu, kunya irin ta Audu murmushi kawai yayi ya fice daga gidan.

Da tasan duk bankwana sukeyi da ta bishi sun dan zanta, da ta bishi ko yan mintina ta kara samu a tare da shi. Amman ina, ko ganin karshe da tayi mishi juma’ar data gabata basu wani dade ba, ruwa kawai yasha

“Nayi yamma Maimuna, idan Allah ya bamu aron rayuwa a gidanki zanci abincin rana juma’a mai zuwa”

Ta tuna kalaman shi, da suka saka hawaye masu zafi zubo mata. Tana kara rike Bilal a jikinta, wani irin zazzabine ya rufeta da tasan kaduwa da firgicine suka saukar mata da shi. Ance an gwada bashi mama yaki karba, ita kam gwadawa tayi yanzun, kamar Bilal yasan kalar kusancin da yake tsakanin ta da Audu ya kuwa karba, kafin wani lokaci yayi luf a jikinta. Aikam hakan ba karamin kara rikita kowa yayi a gidan ba, haka akaita koke-koke ana zantukan zumuncin da yake tsakanin Maimuna da Margayin. Ba ayi bakwai ba kuwa sai da ya zamana babu mai gwada karbar Bilal daga hannun Maimuna, masu tunanin cewa ma zasu rike shi basu furta zancen ba, dan ta nuna abune da ba zai yiwu ba.

Rayyan ma da Maryama ta biyota dashi, kamar yasan wani abu mai girma ya faru, baiko gwada zai sha Mama ba, larabar tazo musu da sauyi mai girma gabaki dayan su. Tayi rashi babba, ta kuma karbi amanar da take tunanin babu wanda ya cancanci a yarda da yai rikonta sai ita, ta karbi Bilal da Ahmadi ya nuna goyon bayan shi dari bisa dari a kai. Ko bai auri Maimuna ba, shi din mai rike jinin Audu ne, akwai wannan kusancin a tsakanin su. Shisa har yanzun da take rike da Bilal, rashin Audu yake kara tabata

“In shaa Allah in dai ina numfashi ba za kai maraici ba….babu wanda zai kalleka ya kiraka maraya”

Ta furta a fili tana share kwalla, sosai take kallon yaron, yanda duk akance tana kama da Audu, yanda har ranar sunan Bilal da ake ma Audu tsiya aka dawo kanta bayan fitar shi cewa ai itama Bilal din kamanninta ne, yau sak Audu take gani a fuskar yaron, dogon hancin nan nashi, idanuwan shi da kowa kan tanka har akayi zaton baki zai kama su, komai na Audu take gani a tattare da Bilal. Rayyan da yake baccine ya farka ya rarrafo yana karasowa inda take zaune. Hakan yasa ta share kwallar da ta zubo mata.

Hannun shi Rayyan ya mika ya kama na Bilal din

“Kaga kanin da ka samu ko Rayyan?”

Maimuna ta fadi, tana kallon yanda kamar Bilal ne yaji maganar da tayi ba Rayyan ba, dan shi ya sa dan karamin hannun shi yana rike yatsan Rayyan din, haka kawai yanayin yasa zuciyar Maimuna wani irin dokawa da karfi, a lokaci daya kaddara na budewa yaran shafin da a dogon tunanin Maimuna bata hango musu ba.

1991, Kano

“Rayyan…”

Maimuna da duka yaran suke kira Ayya ta kira tana sakawa Shamsu riga a jikin shi.

“Rayyan…”

Ta sake kira, saboda taga giccin shi, shirin makaranta takeyi musu. Suzo su dauki safa kafin Ahmadi ya shigo ya samu basu shirya ba ya dora laifin a kanta. Dan akan makarantar yaran daga boko har islamiyya bayason wasa sam. Wani lokacin idan tayi mitar fadan daya koya sai yace zama da itane, ita ta koya mishi fada.

“Wallahi Rayyan na fito sai na dake ka.”

Ayya tai maganar ranta a bace, tana balle maballin rigar da take jikin Shamsu

“Ayya kina kiran Rayyan ne? Yana wajen Abbu.”

Bilal ya fadi, dago kai Ayya tayi

“Kai ne ka wuce daman?”

Kai ya jinjina mata yana saka murmushi kwace mata. Shekaru biyar kenan, a cikin shekarun tana da abubuwa da yawa da zatayi godiya domin su, ciki harda karin yara biyu da Allah ya bata, Rukayya sai Shamsu da take goyo yanzun. Duk yanda a fakaice bayan shekaru biyu da shigowar Bilal rayuwarta ta samu cikin Rukayya, Ahmadi nata kokarin tunatar da ita kan yanda yake fada mata komai na Allah ne, duk ta daga hankalinta akan rashin haihuwa, yanzun gashi nan komai da lokaci yayi Allah ya bata.

“Hmm…”

Kawai ta iya furtawa, ita kadai tasan wahalar da tasha kafin ta samu cikin Rukayya, duk kalar tsoronta saida Khadi ta rakata wajen Malam Mainasara, kuma zata gode Allah da ya bata wannan damar

“Bakin aljani ne aka saka ya shafar miki mahaifa. Aikine akayi babba gaskiya”

Rubutu ya bata na kwana uku, daya a barbada gishiri, daya a barbada sikari, dayan a saka lemon tsami. Sai wani tsinke kwakwa daya karya wajen gida takwas yana samun leda ya daure a ciki, yace idan ta dawo da tsinken za’a gwada aga idan rubutun yayi aiki ko akasin hakan. Zatayi karya idan tace bata dawo da shakku a zuciyarta ba, saboda maganar shi na cewa har yaranta Maryama take son cutarwa. Amman a tsayin shekarun nan ta yarda Maryama zatayi komai dan ta cutar da ita, dan yanzun takan biye mata idan ta takaleta, da wahala ta fadama Maryaman magana daya bata rama ba.

Ta alaqanta hakan da yara uku duk maza da Maryama take gani ras a gabanta, Haris, Jabir, sai kuma Naadir. Shisa take daddaga mata kai har haka, ko da gadone ta fita a cikin gidan yanzun, tunda ita mazan ta biyu, sai mace guda daya. Duk yanda take jin cewar Bilal nata ne, duk kuma rashin banbancin da Ahmadi yake nunawa tsakanin Bilal da yaran shi ba zata hada shi a cikin magadan Ahmadi ba. Tasan wannan har kasan ranta. Akwai shakuwa mai karfi tsakanin su Khalifa da yan uwan su, zata jinjinawa Ahmadi ta wannan fannin.

Tun tana nesa-nesa da ganin yaranta bangaren Maryama har ta fara saduda, na rana daya bata taba ganin Maryama tayi kokarin cutar dasu ba, a fuska ma bata nuna wannan alamar ba, duk da Gwaggo kance mata

“Mugu bashida kammani, wanda yake kusa da kai yafi samun damar cutar ka Maimuna, kiyi kaffa-kaffa da yaranki”

Tana kuma iya kokarinta, tunda har yanzun da wahalar gaske Maryama ta basu abu su karba, ko menene kuwa. Itama Maryama tun abin na damunta harya daina, bata kuma fasa gwada basu duk abinda suka samu tana baiwa nata yaran ko tana ci ba. A ganinta dai ta fita hakkin su tunda ta basu, zabinsu ne karba ko kin karba. Gara ma Bilal da ta rasa kalar yaron, tunda take sau hudu hannunta ya taba kaiwa jikin shi da sunan duka, shima akan Maryama ne, indai yana son abu ta bashi saiya karba yaci, duka dukan da tayi mishi har wani zazzabi tayi, zata rantse tafi shi jin zafin dukan.

Tana son yaranta, tana son yaranta fiye da tunanin mai tunani, amman daban take jin Bilal, har a ranta daban take jin shi, bayan kauna akwai tausayin maraicin yaron da yake manne a zuciyarta. Gashi da manyance na ban namaki, kuma duk yafi shakuwa da ita a cikin yaran, zaka gansu suna tsakar gida suna wasa, amman yafi zabar zama a kusa da ita akan ya shiga cikin yan uwan shi suyi wasa. Ko kwance take shiru tana tunanin duniya sai Bilal ya shigo ya hana mata wannan tunanin, da shirmen shi da hirar shi takan ji sauki a ranta.

Tana jinjina yanda Malam Mainasara yace Maryama zata iya cutar da su Khalifa, a karo na farko da take kyautata zaton ta akan Maryama

“Idan baki tashi tsaye ba, sai ta sabauta miki yara, so take babban danta ya gaje komai na gidan, yafi kowa a zuciyar mijin ku”

A kasan shakkun da takeyi akan maganar akwai tunani barkatai da ya jefa kwakwalwar ta, lokuttan da takan ga kowanne yaro zaune a kasa, amman Haris nakan cinyar Ahmadi, ko wasu lokuttan da zai baiwa kowa abu, sai taga ya diba cikin nashi ya karawa Haris, sosai zuciyarta ta cika da tsoron tabbacin maganar Malam Mainasara. Amman zata gwada shi taga idan aikin shi yana ci kafin ta yarda da bugun kasar da yayi mata. Dan harta gaji da wannan tarkacen Malaman na Khadi da Gwaggo, kowanne a cikin su fadar yanda ayyukan Malaman yake, sai a kanta ne hakan yake zama daban, sai a kanta ne aikin bayaci tunda ga Maryama nan daram a gidan Ahmadi, har dinki takeyi da a cewar Ahmadi ai daman tun a gida tanayin abinta.

Gidan nasu kullum cikin mutane yake da sukan kawo dinkuna ko kuma suzo karba, dan dinkinne yasa Maryama harta datsa mata magana kwanaki

“Ina da ayyuka da yawa a gabana, ina da hidindimu Maimuna, ki daina tunanin ina da lokacin yi miki wani abu. Wallahi banda wannan lokacin, gidane dai yanzun na fara zama a cikin, saiki bari idan Allah ya tsara zan rigaki kwanta dama sai kiga an fitar miki da gawata daga gidan nan”

Maganganun sun mata zafi kuwa, sun kuma sakata tunanin fara sana’a itama, amman ta rasa, ta dai yiwa Ahmadi magana, yace zai tayata tunani, watakila ko takalma ne sai ya dinga kawo mata, ko ta tara kudade ta bayar sai ya saka mata a shagon shi ana juyawa, duk ribar saiya kawo mata abinta. Ko babu komai a ganin Maimuna zata samu wadatattun kudin da zataci gaba da naimarwa kanta da yaranta taimako wajen kariya daga sharrin masu sharri. Yanda Malam Mainasara yace tayi da rubutun haka tayi kuwa, sai dai tayi sa’a Ahmadi ya hanata fita da ranar komawar ta zagayo.

Sai da akayi wajen kwanaki takwas tsakani sannan ta sami dalilin da tayi amfani dashi wajen fitar. Mamaki ta dingayi tana karawa, saboda karyayyun tsinkayen da Malam Mainasara ya batane ya juye cikin wani farin kyalle ya nannade, ya jujjuya a gaban idanuwansu ita da Khadi, ana bude kyallen saiga tsinke mike kyam kamar ba’a karya shi ba

“Ma shaa Allah, aiki yayi yanda ake so. An samu damar karya sihirin”

Farin ciki fal ranta, farin cikin da batayi wasu dakika tanayi ba, tsoro ya maye gurbin shi, jin Khadi tace

“Saura raba soyayyar Haris da Ahmadi Malam, ya za’ayi da yaron?”

Zungurinta Maimuna tayi cikin tashin hankali, Khadin na zabga mata harara, taga alamar ko kadan Maimuna ba zatayi hankali ba har yanzun. Har wani abin tausayine a batun daya shafi kishiya

“Ni dai kar ayi mishi wani abu, idan sihirine a warware abin ya kaunace shi dai-dai da sauran yaran”

Maimuna ta fadi cikin rawar murya, ba jan yaran take a jikinta ba sam, bata dai tsangwamar su, idan sun zo bangarenta su zauna, idan abincine suka samu su Khalifa naci sukan ci dasu, suyi wasan su. Amman Haris har rawar jiki yaron yakeyi idan ta saka shi ya miko mata abu, ko kuma Ahmadi ya aiko shi bangarenta, da gudun shi yakan shigo. Harda murmushin nan da duk idan yayi sai taga kamar Ahmadi. Batasan kome takeji akan su Haris kauna bace, tafi alakanta shi da shakuwa da kuma shiga rai irin wanda yara suke dashi, wani garin magani ya dauka ya bata

“A ruwa zaki dan barbada yasha, shikenan”

Karba dai tayi kawai badan zuciyarta ta aminta ba, haka ta dawo gida tana jinta kamar marar lafiya. Duk shigowar dasu Haris din sukayi ranar ta kasa ko da mikewa balle ta barbada maganin ta san yanda zatayi ta bashi. A haka Ahmadi ya shigo ya sameta, yaran suka tarye shi da gudun su suna fadin

“Abbu sannu da dawowa”

Kamar yanda suke kiran Ahmadi da shi, Maryama kuma Mami. Amman duk a cikin yaran Haris ya zabi ya dauka, sai ta bishi da kallo, bataso yanda ya tabbatar mata da zancen Malam Mainasara ba, sam bata zaci Maryama na da zuciyar wannan muguntar ba. Ita kam ba zata saka ido Ahmadi ya dinga nuna bambanci a tsakanin yaran ba.

“Duk yaran baka ga kowa ba sai Haris kenan?”

Ta bukata, tsareta Ahmadi yai da idanuwa, duk rashin kunyarta tana bala’in shakkar shi, yanzun ma tsintar kanta tayi da sauke nata idanuwan. Saida ya sallami yaran ya basu alawa da biskit din daya siyo musu tsaraba, suka fice daga dakin, sannan ya kara kallon ta

“Me yake shiga kanki ne wani lokaci?”

Kallon shi tayi itama

“Ni babu abinda ya shiga kaina, amman kana nuna bambanci tsakanin yaran. Inma Haris kafi so bai kamata kana nunawa karara ba, ko ni zuciyata bata sosu ba, yara ai suna gani, kuma yaro baya mantuwa”

Numfashi Ahmadi ya sauke, Allah ne shaida yana kaunar yaran shi, idan ma akwai wanda yakeji daban a cikin su Zubaida ce. Kaunar da yake ma yarinyar daban take, sai yake jin kamar tafi kowa bukatar kaunar shi, dan kasancewarta mace, ko kallon su yake yana hasaso yanda rayuwa zata kasance musu, sai ya dinga ganin su Khalifa sunyi aure da iyalinsu suna zuwa duba shi badan suna bukatar shi ba, dan kyautatawa kawai, amman yakan hango Zubaida har karshen rayuwar su tana bukatar kulawar shi, kuma ba zataji kamar ta girmi taimako daga wajen shi ba.

Haris na da kwalafaci, a iya zaman da yake da yaran shi yana kula da dabi’un su, Haris na cikin yaran da suke yunwar kulawa, ko yanayin shi ka gani yanda yake so yayi komai dan ya faranta maka ko zaka kula shi ya isa ka fahimta, ba bambanci yake nunawa ba, kaunar su yake nuna musu dai-dai bukatar su, amman idan yai kokarin fahimtar da Maimuna zata sauya zancen shi zuwa wani abin. Shisa ya sake zancen gabaki daya

“Yaya Ayuba kemun maganar kara bude wani shago, ina jin zan mishi zancen zaki kawo wani abu ko yaduka ne a siyo a juya miki….”

Kai kawai ta iya jinjinawa, ta kula da maganar Haris ne bayaso ayi. Shisa ta kyale shi, washegari kuwa da safe saiga yaran sun shigo dakinta, tana hada shayi. Zuciyarta na rawa ta sami kofi ta shiga kitchen, anan ta kwanto maganin da yake nade cikin karbun zaninta, sai take ganin kamar Ahmadi zai fito ya ganta, barbadawa tayi a kofi tana saurin zuba ruwan shayi a ciki, dan shekawa tayi, ko bai shanye ba inta samu ya kurba hakan ma ya isa. Tana shiga daki ta ajiye kofin a kasa ta nufi inda Bilal yake rike da cokali mai yatsu da batasan inda ya dauko shi ba karya cake ido ko wani waje. Kama shi tayi ta karbe cokalin, kallonta yakeyi da ido kawai tunda da wahalar gaske kaji kukan shi.

Tana juyowa taga kofin shayin da ta ajiye a hannun Rayyan, ya kuma daga ya kafa bakin shi

“Rayyan….”

Ta kira cikin tashin hankali, kafin ta karasa ta karbe kofin harya shanye. Dago shi tayi gabaki daya ta rikice

“Na shiga uku ni Maimuna…. Na shiga uku, Rayyan….”

Take furtawa tana tale bakin shi kamar hakan zai dawo da abinda yasha, kafin ta saka hannu tana taba fuskar shi, goshin shi da wuyan shi, har hannu tasa cikin rigar shi taji ko ya fara alamun zazzabi, bata taba tsorata irin haka ba, sauke shi tayi kasa dan sai buntsurewa yake yi tana tsugunnawa itama

“Dan ubanka ka tsaya kafin in kwada maka mari”

Ta fadi jikinta ko ina na bari da tashin hankali, dai-dai shigowar Ahmadi

“Lafiya? Me ya faru? Me ya same shi?”

Ya jero mata tambayoyin ganin yanda take a rikice

“Kamar wani abu naga yakai bakin shi, kafin inzo harya hadiye”

Ta furta muryarta na rawa, dana sani ne yai mata rumfa, saboda tashin hankalin da take ciki na rashin sanin mai maganin zaiyi tunda a kan idanuwanta taga karfin aiki irin na Malami Mainasara.

“Bakwajin magana wallahi, na rasa me yasa kuke ajiye kananun abubuwa da yaran nan zasu iya dauka su hadiye….”

Ahmadi ya karasa maganar yana daukar Rayyan da a lokacin duka shekarun shi basu karasa hudu ba

“Me ka ci Rayyan? Fadamun kaji?”

Kai Rayyan din ya girgiza mishi alamar shi baici komai ba. Babu dabar da Ahmadi bai mishi ba, amman yace shi shayi kawai yasha. Barin shi yayi tunda zai fita aiki, yace ma Maimuna din da taga ko zazzabi ya fara ta dauke shi ta kai shi asibiti, kudi ya dauka ya bata, duk da yakan ba kowaccen su kudi su ajiye tsaron laluri koda wani abu na gaggawa zai taso shi yana wajen aiki. Yinin ranar Rayyan wasan shi yake kamar komai bai faru ba, itace ta wuni ta kuma kwana da zazzabi.

Har alkawari tayi na cewa in dai komai bai sami Rayyan ba, har abada ta daina bin Malamai zata cigaba da addu’a tana shan karya tambaya dai da kaikayi koma kan mashekiya, babu kalar addu’a da alkawurran da bata dingayi ba. Daga wannan zazzabin da takeyine ya juye mata laulayi mai zafin gaske. Ta sha wahala matuka, cikin da ta samu kuma na kara daga kimar aikin Malam Mainasara a idanuwanta. Bata yaye Rukayya ba kuma ta sami cikin Shamsu, kamar yanda tayi a haihuwar Khalifa da Zubaida, harma da Rayyan. Duk yanda Khadi taso su koma wajen Malam Mainasara kiyawa tayi, dan ta tsorata da lamarin shi akan Haris, batasan meye ya bata ba har Rayyan yasha, tsoro kuma ya hana ta furtawa kowa zancen, har aminiyar tata Khadi.

A cikin shekarun biyar din nan, a gaban idanuwanta Rayyan, Bilal da sauran yaran suke girma, amman na Rayyan da Bilal ba ita kadai yake baiwa mamaki ba, har mutanen da duk zasu gansu. Kowa zancen yanda suke tasowa kamar yan biyu yakeyi, duk da akwai banbancin shekara daya da watanni har shida a tsakanin su. Amman hatta tsayin su dayane, dan hasken fata kawai Rayyan yafi Bilal, dan shi Rayyan farine tas-tas, Ahmadi ne yakan kaisu aski, hatta da askin iri daya akeyi musu. Kowa yan biyunta yake kira, idan baka sani ba ba zaka taba cewa ba yan biyu bane, ita kanta Maimuna bata gyarawa mutane in sun fadi.

Balle kuma duk a cikin yaran Rayyan ake cewa yafi kowa kyau tunda shi yake kama da ita, shisa kamannin shi da Bilal ya baci, ko ita in ta gefen idanuwa suka gitta ko tana daga daki taji muryoyin su bata gane wanene a cikin su, balle duk kayan da Ahmadi zai siya iri daya yake siyarwa Bilal da Rayyan din.

“Ka dauki jakar ka?”

Ta tambayi Bilal din

“Hamma ya daukar muna…”

Ahmadi bai yarda da wani bai girmi wani da wasu shekaru ba, ko wata daya wani ya baka a cikin gidan saika bashi girman shi, kuma idan ya saka abu sai kayi. Da yake kaunar da take tsakanin shi da yaran mai girma ce, kowa bayason abinda Abbu zai mishi fada ko yayi fushi.

“Allah ya tsare, ka kula da Hamman ka kaji ko?”

Cewar Maimuna, duk da tasan Rayyan ne ya kamata ya kula da Bilal din, sai dai rigimar Rayyan a yan shekarun shi har mamaki take ba Maimuna, ga taurin kai kamar mutanen farko, idan abu yakeyi ko kashe shi zatayi saiya koma ya karasa, yanzun ma Ahmadi ya hana mata dukan shi, a cewar shi zai kangare. Taci gaba da mishi addu’a kawai. Amman ko yaran gidan Yaya Ayuba suka shigo, har wanda suka girmi Rayyan basa shiga gonar shi, duka yake musu, ga rikicin shi baya rabuwa, in ana fada dashi in bashi ya hakura ba, haduwa goma in kukayi sai ya kara cakumarka, abinda Maimuna ta kula dashi yan watannin nan, Bilal ne kawai zai shiga tsakani in ana fada da Rayyan din ya hakura.

Wani lokacin in Bilal yaita janye shi sai fadan ya koma kan Bilal din, tana kuma kula da yaron baya taba daga hannu da sunan ya rama duk wani duka da Rayyan din zai mishi, sai dai in karewa zaiyi, har sai yaga zuciyar shi tayi sanyi tukunna zaka ji yace mishi

“Ka daina fada Hamma, Ayya bata so, Abbu ma bayaso, nima bana so, ka daina”

Amman idan ba Bilal ba babu wanda ya isa ya taba fadan Rayyan cikin dadin rai, yana kuka yana zillewa zata samu ta rufe shi a daki. Amman ko kowa ya manta inya fito saiyaci gaba. Har kuka tayi shekaranjiya akan taurin kan Rayyan, sai take ganin kamar abinda yasha ne yake saka shi wannan abubuwan, kamar tana da laifi a kaddarar Rayyan, kuka takeyi har a sujjada tana rokon idan wani laifin ne ma Allah ya jarabceta ta wani fanni bata kan yaranta ba, kishi da Maryama ba tasan yanda zata bari ba, amman bin Malamai ta hakura dashi, duk da yanzun tana jin kamar ta aiki Khadi a buga mata kasa akan Rayyan, amman tana tsoron a gano mata abinda zai kara daga mata hankali.

Har waje ta fito taga Ahmadi ya tattara kan yaran

“Ayya sai mun dawo”

Haris ya fadi da murmushin da baka raba fuskar yaran dashi, sai ta tsinci kanta da mayar mishi da murmushin

“Allah ya tsare, ku kula da kyau, ayi karatu kuma”

Kai ya jinjina, ya juya kenan sukai karo da Rayyan, da kafin wani yai motsi ya dauke Haris din da mari yana saka Ahmadi karasowa ya tallafe mishi kai

“Rayyan… Bana hanaka dukan yayyanka ba? Haris din ba Hamman ka bane ba? Ka bashi hakuri yanzun nan”

Kallon Ahmadi din Rayyan yayi kamar zaice wani abu, sai kuma ya fasa yana kama hanya ya nufi waje, Bilal na rufa mishi baya da saurin shi. Numfashi Ahmadi ya sauke

“Allah ka tausasa mun zafin zuciyar yaron nan. Allah ka tausasamun shi, kai kabani, Allah ka bani ikon sauke amana”

Yake fadi a cikin ranshi,kwatankwacin addu’ar da yakanyi wa duka yaran duk lokacin da zasuyi wani abu ba dai-dai ba, musamman Rayyan da bayason yawan dukan shi saboda kalar yaran ta fita daban duk a cikin yaran. Haris da yake tsaye ya sadda kan shi kasa Ahmadi ya kamo

“Haris saika dinga hakuri da kanin naka kaji ko?”

Murmushi Haris yayi mishi

“Ni na buge shi Abbu, bangani ba amman”

Kai kawai Ahmadi ya jinjina, yana kama hannun Haris din, ya juyo ya kalli Maimuna da fuskarta take dauke da ban hakuri kan halayen Rayyan din, murmushin karfin gwiwa yayi mata

“A dawo lafiya, ka kula da kanka.”

Ya furta a hankali

“Kema haka” Ya fadi suna ficewa, daki ta koma tana sauke numfashi. Da tunanin halayen Rayyan manne a zuciyarta.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×