Tunda Salma tai alwalar magariba ta shiga daki ta kulle, duk da cewa tunda Anas ya tafi raka Aunty Hauwa bata sake jin motsinsa ba Wajen karfe 8 taji ana kwankwasa mata kofa . "Waye ."? Suwaiba dake tsaye kofar dakin ta ce .
"Ni ce nan hajjiya ce take kiranki a falo." Salma ta ce . "Tom gani nan ." Ta tashi tasa hijabiinta kana ta fita zuwa falon , tana zaune ta harde a kujera, ganin wannan yanayi yasa Salma ta durkusa a kasa tana cewa. "Gani hajjiya.
D'ago kai ta yi , sannan ta ce . "Ki tattare kayanki a wannan daren kibar gidan. . .