Bauchi
Karfe 11:20 Salma ta farka a bacci , sannan ta karewa dakin da take ciki kallo, kana ta mike ta fita tsakar gida, koda ta fita mai gidan da matarshi suna zaune suna ta hira Salma ta durkusa gabansu tana cewa. "Ina kwanan ku , kuyi hakuri ."
Murmushi mijin ya yi , kana ya ce. "Aa karki damu, Fatima ki dauko mata abinci ta karya ." Ta mike kamar yadda ya ce . Ta kawowa Salma doya da kwai sai kunu a cikin kofi "Na gode ." Salma ta fad'a bayan ta aje mata a gabanta "Ammma baiwar Allah kinga jikin ki babu. . .