Baba Laure ce zaune tsakar gida tana yi wa Salma kitso, zanen hausa take rangada mata a kanta mai matukar kyau, gefe guda kuma ga Fatima can tana iza wuta Aliyuu ne ya shigo yana yin sallama, murmushi ya jefawa mahaifiyarshi da cewa. "Babata ta kaina." Kana idanunsa suka kai kan Salma idanunta sama kamar shi take kallo, sai dai bata iya ganin komai. Shagala ya yi da kallon Salma irin yadda wannan kitso yayi matukar fito da kyawunta "Allah ya yi halitta, kodai kyan wannan yarinyar ne yasa akai mata wannan sihiri." Abin da Aliyuu yake fad'a ke. . .