Salma tana d'ago kai ta ganta , da sauri ta mike tsaye tana jaa da baya . Idanun Fatima jajir tamkar wacce ta fita a hayyacinta . "Wato kin zo gidana , ki hanani farin ciki, kin yi cuta an miki magana, an sa miki jinin mijina, mahaifiyarshi tana yabonki a gabana, ya sai miki waya , abin da ya rage ki aure shi kooh."
Salma da matukar tashin hankali take ja da baya tana cewa. "Wallahi Aunty Fatima ba haka bane , babu komai tsakaninmu saii.." Dakatar da ita tai tana d'aga wukar kamar zata caka mata "Kafin na yarga biyar , ki kwashe. . .