Suna shiga ciki , sabuwar yar aikin Aunty Hauwa dake zaune falo tana kallo, ta sake rissinawa tana cewa. "Sannu da zuwa Aunty." Aunty Hauwa ta kalleta tare da zama a kujera tana cewa."yawwa sannu Farida, fatan kin dorawa Salma ruwan wankan da nace ." Cikin girmamawa Faridan ta ce ."Na dora Aunty, har abinci ma an gama ." Ta ce "yawwa." Salma tai murmushi sannan ta nemi guri ta zauna , yayin da Farida take shigewa ciki . Ajiyar zuciya mai zafi Salma ta sauke ."Aunty wannan gidan ya yi kyau sosai." Ta fad'a tana duban koina Aunty Hauwa ita ma ta. . .