"Jama'a anan muka kawo karshen wannan Littafin namu mai suna Fatima da zarah. Na wannan shahararriyar marubuciya Autar marubuta." Umman Salma ke nan dake sauraran redio. Nan ita ma Karima tana zaune tana bude WhatsApp take sauraran wannan gidan redio, daidai lokacin da yake cewa. "In sha Allahu gobe misalin karfe 4 na yamma zamu kasance tare da wannan marubuciya a wannan gidan mai albarka." "Ga duk masu son turo sako zasu iya fara turowa tun yanzu a wannan number kamar haka."... Sai ga Hadiza ta shigo Firgita Karima ta yi ganin Shigowar Hadiza, domin kullum Karima bata barin. . .