Karfe 8 suka shirya tsaf domin tafiya, tun a wannan lokacin Salma bata duba wayar taba , tana gama shiryawa ta jefata a cikin jaka , falon suka fito da akwati sun sha abaya ruwan toka iri daya . Aunty Hauwa ta kalli Salma tana cewa. "A'a har Yanzu Farida bata fito ba , kota tafi ne ."? Dariya Salma tai tana cewa. "Ta tafi fa tun dazu." Sannan suka fito , Aunty Hauwa ta tsaya rufe kofa , ita kuma Salma take sanya akwati a cikin Booth, suna gamawa suka shiga , sai aka dau hanya , ni ko nace Allah ya tsare .
Karima kamar hawan jini. . .