Bayan Salma sun gama wannan tattaunawar, har abinci suka samu suka ci, sukai sallah, sannan suka hau mota. Ganin Aunty Hauwa ta murza kan mota sun jiya yasa Salma cewa. "Aunty wannan titin ai bazai kai mu Tarauni ba ." Aunty Hauwa ta kalleta tana cewa. "Eh zamu je station ne , sun kira mu , domin an taho da Hadiza daga sokkoto." Salma ta aje numfashi mai nauyi , Aunty Hauwa ta cigaba da tafiya. Nan kuwa hankalin mutane duk ya tashi, ko aure ba a daura ba an tafi da Amarya har Jahar Kano, hakan yasa ango da zugarshi suka bisu , jingum. . .