Bayan Alhaji Yusuf ya tafi Salma ta mike ta shige daki ta cigaba da kuka , duk yadda Umar yayi domin ya rarrasheta taki , domin tasan idan ta koma gidan Alaji Yusuf burinta na zama marubuciya tabbas sai dai mafarki. Haka tai ta kuka tana sunbatu kala-kala har akai kiran sallar isha'i Ko abinci bata iya ci ba ta shige daki ta rufe , mahaifiyarta abin yana damunta sai dai babu yadda zata yi , domin komai wuya tafi son Salma a kusa da ita .
Anan cikin gidan Alaji Yusuf kuwa . Karima ce zaune sai had'a gumi take rike da. . .