Lokacin da Alaji Yusuf ya karaso, babu wani labari dai na Salma, nan suka zauna suna tunanin mafita da yadda za a bullowa lamarin. "Da dai an sanar da 'yan sanda ko."? Inji Umma Alaji Yusuf ya ce ."Yanzu yarinyar nan bana tunanin 'bata tayi ko sace ta akai , to mu sanar da yan sanda mu ce musu me ." Malam Aminu ya ce ."Haka ne ." Umma ta sake fad'in."Sanin gaibu ai sai Allah duk bamu da tabbacin meke faruwa da Salma ko ."
A lokacin Zainab ta rado sallama tana turo kai , ganinsu jigum wasu a tsaye yasa taji. . .