"Tom ka ce tana zuwa." Ummanta ta bawa yaron amsa , sannan ya fice "Tashi ki je ." Cewar Ummanta Hadiza babu musu ta tashi da sauri ta fara shiryawa, wata abayarta tasa ruwan toka , sannan ta baza turare aka fita . Cikin taku mai kyau ta fita waje ta hangi wani dogon saurayi fari kalar hutu, ya jingina jikin bakar motarshi yana danna waya . Kamar kamshin turaren Hadiza ne ya dakeshi, ya juyo yana kallonta tare da cire gilashi. Ganin taki karasowa inda yake , hakan yasa ya taka cikin taku na girma ya tsaya a gabanta . "Assalamualaiki ma'abociyar kyau da kasaita. . .