Salma jimm ta yi tana tunanin wannan sako, ba tare data fice daga ciki ba , hakan yasa ta sake ganin shigowar wani sakon . "Kina magana da Hadiza RM, kin gudu daga gidanku to asirinki ya tonu." Salma ta sake karantawa Hadiza kuwa Shahada kawai tai ta tura wannan sako ga Autar marubuta, domin bata da tabbacin Salma ce, sai dai wannan Littafin na Fatima da zarah yake bata yakinin wannan Salma ce , idan kuma ba ita bace hakuri Hadiza zata bata kawai.
Murmushi Salma tai kafin tai mata reply ta ce . "Lallai yarinyar nan ta ya ta gano ni , tabbas. . .