Skip to content
Part 1 of 5 in the Series Matakan Nasarar Iyali by Hamza Dawaki

GINSHIKAN RIKON AURE

Ginshikan rikon aure ba daga zabin ango ko amarya ba ne.

Daya daga cikin abubuwan mamaki na mutanen wannan lokaci shi ne, sun yarda cewa, auren mutanen dauri ya fi inganci da karko a kan na yanzu, amma ba su yarda da tsari ko hanyoyin da suke bi wurin tabbatar da irin wancan aure mai danko ba! Tamkar dai ka ce, mutum ya yarda yana tare da wani ciwo, amma in an ba shi maganin da ya tabbatar zai warkar masa da ciwon sai ya ce wannan na bakaken fata ne, shi sai na Turai yake sha. Tare kuma da cewa ga na Turan a gabansa yana ta faman sha ba alamun sauki. Watakila ba abin da zai hana a kira wannan dabi’a da ragon azanci.

Kafin mu luluka da nisa, bari in ajiye mana wani katon waigi, wanda ba na so mai karatu ya manta shi har zuwa karshen wannan takarda. Imam Malik (Rahimahullah) ya rawaito cewa manyan tabi’ai Qasim ibn Muhammad da Saalim ibn Abdullahi da Sulaimanu ibn Yasaar (Allah Ya yarda da su) sun kasance suna cewa, Iyaye za su iya aurar da ƴaƴansu (ƴan mata) ba tare da neman izininsu ba. (wato ba tare da dole sai an ba su zaɓi cewa wane za a ba su, sun yarda ko ba su yarda ba). Kuma wannan ya zame musu dolensu su zauna da mazajen.

Kar ka bari tunaninka ya tafi zuwa kan abin da yake faruwa a wannan zamani, na kurarin ƴanci da wayewa. Tsayar da shi ya tafi a kan doron hankali da shari’a. Idan ka yi haka, ina sa ran wannan magana za ta iya ba ka damar fahimtar a kalla abu daya, muhimmi. Shi aure, kacokan manya ne suke kulla shi, idan har ana so ya dore kuma ya yi kyau. Domin manya su suka san ainishin ma mene ne aure. Amma duk kaifin hankalin yaro ko yarinya da tarin iliminsu tabbas ba za su taba gane hakikanin yadda zaman aure yake ba, har sai sun shiga cikinsa. Wannan yana daga manyan dalilan da suka sa magabata suke zabar wa yayansu abokan aure, maimakon bari su zabi wanda kawai zuciyarsu ta kayatu da shi.

Za kuma ka yi saurin yarda da hakan, idan ka dubi nassin da suka yi dogaro da shi. Wanda yake nuni da cewa. “Budurwa ana neman izininta ne, amma bazawara ita ke da mallakin kanta.” Wato ita ana ba ta dama ta zabi wanda duk ta ga zai dace da ita. Idan har za ka iya cewa a ranka, “Me ya sa aka bar ita bazawara ta zabi abokin rayuwa da kanta?” Watakila kuma hankalinka zai ba ka amsa shigen haka. “Watakila saboda ita ta girma, ta taba dandana duniyar auren, ta ji yadda take.” Wato ba wai irin shigar da budurwa za ta yi mata kawai da magagin soyayya da ruduwa ba.

Amma duk da haka, bi ni, mu ci gaba da tafiya, ko sauran hujjoji za su gamsar da kai, idan wannan ta gaza.

Idan mun so koma ga waccan turba tasu, za mu taras cewa, akwai ta’adodi kyawawa da dama da iyayen suke amfani da su. Wadanda kuma ko yanzu in da za mu iya koyi tabbas zamantakewar auren ‘ya’yanmu sai ta inganta. Misali, daga muhimman abubuwan da suka fi damuwa da shi a wancan lokaci, shi ne mutum, wato wanda ko wadda za a aura din. Shin wane ne shi? Nagarta da nasabarsa da dangogin wadannan. Sabanin yanzu da muka fi damuwa da me mutum ya mallaka ko wane mukami ne da shi?!

Me ya sa aka fi damuwa da asali da nagarta?

Ko ka taba tsayawa ka saurari tattaunawar da waliyan ango da amarya suke yi da kyau, yayin da ake daura aure? Idan amsarka “E” ce, to na tabbata ka taba ji waliyin angon yana cewa na amaryar “Muna neman iri.” Ko da kuwa ban ja ka da nisa ba, kana iya fahimtar cewa wancan irin da ake magana ba komai ba ne face mutum.  Abubuwa biyu suna da muhimmanci matuka game da duba asali da nagartar wadanda za a hada dangantaka ta aure da su: Na farko iyaye ko dangin da za ka kai ‘ya ko danka cikinsu. Na biyu kuma zuriya ko ‘ya’yan da ake sa ran za a iya haifa a cikin wannan aure.

1. Iyaye da dangin da za a kai mutum ciki

Yana daga cikin manyan abubuwan da suke samar da tasgaro a zamantakewar aure, kuma suke kara yawan hauhawar sakin aure da ake ta faman kuka da shi a yau, zare iyaye daga cikin harkokin tafiyar da zaman aure. Watakila wayewa ta zamani da ta wadace mu ce ta sa muke ganin iyaye ba su da wata rawar takawa a cikin zaman aurenmu. Shi ya sa kuma su ma ganin yadda muka nuna mun fi su iyawa suka hakura, su ka ja baya su ka bi mu da ido. Tare kuma da cewa zare hannun nasu daga ciki ba karamar matsala yake haifarwa ba.

A al’adance, a da, idan aka yi wa yarinya aure, aka kai ta gidan miji, ba a tahowa a bar ta haka sasakai, musamman idan tana da dan nisa da gidan iyayenta, sai an sami wani dattijo a unguwar an yi mata uba da shi. Wannan mutumin kuma yakan riki abin da muhimmanci ne, ba tare da da cewa ba shi da dangin iya ko na baba da yarinyar. Duk wata matsala da ta taso daga wannan gida, shi ne zai yi ruwa da tsaki wurin ganin an kawo karshenta. Kamar yadda zai yi a gidan tasa ‘yar, ko ma fiye.  Sau da dama kuma shi da kansa ne zai rika ziyartar gidan yana lura da yanayi da magangannsu. A matsayinsa na kwararre da ya dade a fannin. Kuma yana ganin wata alamar matsala zai ba su shawara ko nasiha mafi dacewa.

A addinance, wannan al’ada ta sa ido ko bibiyar halin da ‘ya’yan mutum suke ciki, bayan sun yi aure ta sami asali daga managartan magabata. Misali, kakan Annabawa Annabi Ibrahim (A.S) ya kasance yakan ziyarci gidan dansa, har ma ya tambayi yanayin da suke ciki. Haka Fiyayyen halitta, Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yakan ziyarci gidan Sayyidina Usman Ibn Affan da na Sayyidina Aliyu Ibn Abu Talib, Allah Ya qara musu yarda. Don haka hakan ya kasance wata sunna abar koyi.

Wannan ziyara ba wai kuma magabata suna yin ta don kawai a gaisa, a tambayi lafiyar juna ba ne. Wani abu da zai ba ka sha’awa da dattawan surukai, in suka je gidan ‘ya’yansu, sukan tambayi surikar (wato ‘yar da dansu ya auro) maimakon nasu ‘ya’yan. Saboda daya daga cikin manyan dalilansu na ziyarar, shi ne suna daraja ‘ya’yan da aka ba su amana. Dama kuma burin ganin nasu ‘ya’yan ba su cutar da na kowa ba. Sabanin surukan zamani da kowa dansa kawai ya sani.

Kyakkyawan misali

Sayyidina Amr Ibn As ya kasance yana ziyarar gidan dansa Abudullahi Ibn Amr (Allah Ya kara musu yarda) yayin da ya yi aure. Idan ya je kuma, yakan tambayi matar game da mijin nata. Sai baiwar Allahn ta yabi angon game da yawan ibadarsa, amma a ciki tana sakaya wata magana da take nuna da cewa ba ya hada shimfida da ita. Saboda kasancewarsa mutum mai yawan azumi da rana, kuma mai yawan salla da dare. Yayin da suriki nagari ya ji wannan batu, shi da kansa ya tafi ya sanar da Annabi sallallahu alaihi wa sallam, don a dauki matakin kwato wa surikar tasa hakki.

Wannan kadai ya isa ya nuna mana cewa, lallai nagarta da asali suna da matukar muhimmanci a cikin inganta zamantakewar aure. Wadanda kuma ana samun su ne a wurin surukai da dangi nagari. 

2. ‘Ya’yan da za a iya samarwa a dalilin aure

Abu na biyu, shi ne ‘ya’yan da za a iya samarwa a wannan aure. Ko a kimayyance an tabbatar da cewa kowane da yakan gadar rabin kwayoyin halittarsa (genes) daga mahaifiyarsa, rabin kuma daga mahinfi. Wannan yana nuni da cewa duk lokacin da ka hada zuriya da wasu mutane, to danka zai iya samun wasu dabi’u na iyaye ko kakannin wannan dangi. Domin ita jijiya tana kowa ne ga ainishin biyarta.

Kammalawa

Idan har Allah Ya taimake ka, ka karanta wannan takarda har karshe da budaddiyar zuciya, ina sa ran kai ma za ka iya yarda cewa shi fa aure da muke magana, rikon sa ba wai na ango da amarya ba ne kadai. Wata igiya ce da mutane da dama suke rike da ita. A mataki na farko, su iyaye, sannan a tsakiya, wadanda ake gani rike da ita dumu-dumu, su ango da amaryar. Yayin da daga can karshe kuma, su ma ‘ya’yan da aka haifa a cikin wannan auren suke da katafariyar rawa wurin rikon igiyar auren. A cikin wannan rukunai uku, duk inda aka samu rauni daga rukuni daya, to babu shakka wannan igiyar za ta iya tsinkewa.

Idan kuwa haka ne, to tabbas ya kamata mu yi hakuri, musamman na zabar aboki ko abokiyar rayuwa, mu bar manya su nuna mana yadda ake bude fagen da bisimillah. Domin fagensu ne, wanda su suka san shi. Allah Ya sa mu dace.

Matakan Nasarar Iyali 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×