UBA MAFI UWA – 1
Tasirin mahaifi a cikin rayuwar ‘ya’yansa
Watakila mai karatu ya ji taken rubutun wani bambarakwai, saboda ba hakan aka saba ji ba. Asalima dai, kishiyar hakan ce ta fi shuhura. Kuma akasari suka fi amincewa da ita. A yau da sahalewar Ubangiji Mabuwayi za mu yi kokarin haska wa mai karatu wasu bangarori da zai fahimci cewa ashe dai uba ba kanwar-lasa ba ne a cikin sha’anin rayuwar kowane mutum. Sawa’un da namiji ne ko mace, kai musamman ma dai ita macen!
An taba maka bayanin inda ka samo kamanninka?
Watakila ba za ka rasa jin dangi suna cewa da kai: “Ai hancinka sak irin na kakanka ne,” ba. Ko ka ji a na cewa: “Wannan katon kan duk a gun kawunsu su ka samo shi.” Amma ba ka taba tsayawa ka yi tunanin to me ya sa hakan take faruwa ba. Misali, a gidanmu nakan ji ana cewa game da Ummu-abiha “Ai wannan hasken da gashin na Mama ne.” “Hancin nan sak irin na Na’ima ne.” “Ai tsayin kafa za ta yi irin na Babanta.” A cikin maganganun ana nuna ta dauko wasu kamanni na mahaifiyar babanta, da wasu daga kanwar mahaifiyarta, wasu daga mahaifin. A lokaci guda kuma ana raja’antar da cewa, ta fi kama da mahaifiyarta! Ko me ya sa hakan ke faruwa?
Bincike ya tabbatar da cewa , kowane dan’adam yakan gadar nau’o’in “hormones” wadanda ke tasiri wurin suffanta halittar jiki da halayya ko dabi’arsa ne daga iyayensa biyu. Wato uba da uwa. Kuma kowannensu yana bayar da kaso daidai da na dayan ne. Wato kaso 23 daga uba, 23 kuma daga uwa. Sai su hadu su samar da 46 da kowane mutum yake da shi. Ashe kenan, idan danka ya gaji guda 23 daga mahaifinsa, a lokaci guda kuma ya gaji irin na kakansa guda 11 da rabi. Kusan 6 kuma daga kakan baban. Duba ga wannan za mu iya saurin fahimta cewa, ba zai zama wani abin al’ajabi ba don da ya yi kamanni da kakansa na biyar ko ma na talatin. Ko Kuma wasu daga ‘yan’uwan mahaifi ko mahaifiyarsa. Saboda dukkansu suna dauke da wani adadi iri daya na kwayoyin halittar. Kodayake, a nan ba wannan ne abin da ya fi damun mu ba. Abin da muka fi son bayyanawa shi ne, mu fahimci cewa tun asali samar da sinadaran da ke da tasiri wurin ginin suffa da dabi’un da, gudunmawa ce daidai wa daida daga Uba da Uwa.
Uba ma yana laulayi!
A wani dogon bincike da masaniya kan dabi’un kananan yara Laverne Antrobus ta jagoranta. Da aka yi wa lakabi da “Biology of Dads”, an nuna abubuwan da suka tabbatar da cewa, iyaye maza ma suna yin laulayin ciki. Wato yayin da matar mutum ta dauki ciki, take fama da laulaye-laulaye. Shi kansa wannan magidancin yakan tsinci kansa cikin yanayi iri-iri, kamar ciwon kai da hajijiya da tashin zuciya da sauransu. Kamar dai yadda mai juna biyu kan ji! Sai dai kawai mu da yake ba cika kula mu ka yi da irin wadannan abubuwan kanana ba, sai mu dauka ba sa faruwa. Amma hakika ko a nan, bayan cin karo da wancan bincike, mun bi diddigin wasu tsirarin magidanta a lokutan da matansu suke da juna-biyu. Sun kuma tabbatar mana da samuwar sauye-sauye masu kama da laulayin a irin lokutan.
Sau da dama, akan sami fadace-fadace a wasu gidajen, yayin da Uwargida ke dauke da juna biyu. Domin kamar yadda take shiga cikin wani yanayi maras dadi, wanda sau da dama ma sai ta ji ranta ya baci. Haka shi ma yakan shiga. Don haka yayin da ta ke cikin damuwa ko ciwon kai da sauran abubuwa da ke hana sukuni, shi ma yakan tsinci kansa a ciki. Don haka abu ne mai sauki a iya bata wa kowannensu rai. Kuma a sami gajen hakuri ko saurin fushi a tare da shi. Yayin da wasu magidantan kuma sukan kara samun fahimtar juna saboda tsintar kawunansu a wani yanayi iri daya.
Abin da dai muke son fito da shi a nan shi ne. Ana dawainiyar rainon ciki da laulayinsa ne tare da uba. Ba wai aikin uwa ne kadai ba. Wuraren da ake raba ayyuka a cikin sha’anin rainon ciki da tarbiyyar yara.
Da ya san mahaifinsa tun yana ciki!
Sau da yawa iyaye maza sukan yi yunkurin magana da jaririn da yake cikin cikin iyalansu, tun kafin a haifo su. Kodayake, a mafi yawan lokaci ana yi ne a matsayin barkwanci. Amma abin da ba mu sani ba, kuma abin mamaki, shi ne dantayin yana amsa waccan magana da mahaifin nasa ke yi masa!
A wannan bincike dai, har wa yau, an nuna, ta hanyar amfani da irin na’urar nan da ake yi wa masu juna biyu scanning. Cewa duk lokacin da Uba ya yi wa dansa magana alhali yana cikin mahaifiyarsa yana amsawa! An kuma haska na’urar kiri-kiri ana gani, inda aka sami wata mai juna biyu da mijinta, aka yi wannan gwajin da su. Inda aka sa mahaifin ya yi wa dantayin magana, ana lura da bugun zuciyarsa, ta cikin na’urar. Yayin da duk kuma uban ya yi wa cikin magana, sai an ga motsin bugun zuciyar dan. Kuma idan uwar ce ta yi wa dantayin magana, sai a ga yana amsawa amma ba kamar yadda yake amsa wa uban ba. Wato yanayin bugun zuciyar nasa yakan fi karfi ne idan mahaifin ya yi fiye da na mahaifiyar. Wani abin sha’awa kuma shi ne, idan wani ne can ya yi maganar, sabanin mahaifan nasa sam ba ya kulawa!
A wannan gabar muna iya fahimtar wani abu mai muhimmancin gaske game da alaka ko dangantakar da ke tsakanin jariri ko jaririya da uba, wanda sam ba ma tunaninsa a baya. Sau da yawa, abin da muke tunani a daidai irin wannan lokaci, jaririn da ke cikin uwa ba shi da wata alaka da kowa bayan mahaifiyarsa da suke a danfare da juna. Amma abin sha’awa, ga shi muna iya fahimta yanzu cewa ashe yana sane da mahaifinsa. Har ma yana amsa maganarsa fiye da ta Mahaifiyar! Hakika irin wannan bincike zai rage mana tunanin da a baya muke yi na tsammanin cewa uba ba shi da wani tasiri a cikin rayuwar jariri kafin haihuwarsa.
Shin uba yana da tasiri yayin nakuda?
Wani gwaji da aka yi a birnin Newcastle, ya tabbatar da cewa da za a bar mutum ya kasance tare da matarsa, a dakin haihuwa, yayin da take nakuda, da ta sami saukin haihuwa kwarai! Yayin da mata da miji suke tare da juna, cikin halin sha’awa ko nuna so da tausayi, akwai wani hormone mai suna oxytocin, da ake wa lakabi da ” love hormone ” da yakan yawaita a jikin matar. Haka a lokacin da mace take cikin nakuda, idan mijinta zai kasance tare da ita. Ya rike ko da hannayenta ne yana yi mata sannu. Nan da nan wannan sinadari na oxytocin zai yawaita a jikin matar. karuwarsa kuma a jikin mace mai nakuda yana taimakawa kwarai wurin saukaka haihuwa. Wato dai fitar yaron ta kasance cikin sauki, kuma cikin gajeren lokaci!
Ashe kenan, uba yana da matukar muhimmanci a cikin sha’anin haihuwa. Watakila ma idan mun ce Uba ma yana nakuda, laifin da muka yi, kadan ne. Musamman ma da yake mun sani cewa a daidai lokacin da take jin zafin nakudar a jikinta, shi ma yana jin nasa zafin ciwon a zuciyarsa.
Amma wani abin lura a nan mai muhimmanci shi ne. Ana so shi maigida ya kasance a nitse, kar ya tashi hankalinsa yayin kasancewar sa da mai nakudar. Wato dai, ba a so ya tashi hankalinsa, ko ma ya munana zato, ya rika tunanin anya kuwa wannan haihuwar za a karke lafiya?
Ala ayyi halin dai, sanin wannan zai sa mu iya fahimtar ashe uba yana da matukar muhimmanci a cikin nakudar da matarsa take yi. Ko ba komai dai, da iyaye maza za su rika tsayawa a kusa da matansu yayin da suke nakuda, matan za su fi samun nutsuwa a zukatansu. Kuma za a rage jiyo kururuwa da zage-zagen “Azzalumi! Mugu! Ka cuce ni!” daga dakunan haihuwa na asibitocinmu.
Abubuwan da su ka kamata mu tattauna a cikin wannan fage, suna da yawan gaske. Tun daga lokacin da jaririn ke cikin mahaifiya, zuwa bayan an haife shi yana yaro, da lokacin da ya fara zama matashi, har ma zuwa lokacin da girma zai fara riskarsa. Ko ka taba tsayawa ka yi tunanin me ya sa uba yake yi wa dansa wasu wasanni masu cike da kasada? Kuma mene amfaninsu ga rayuwar yaron? Shin kana lura da irin shawarwari ko maganganu da fadan da iyaye suke yi wa ‘ya’yansu? Ka lura da maganganun da uba yake yi wa dansa ina suke dosa? Ko kana sane da cewa akwai bambanci ta wasu fannoni muhimmai tsakanin yarinyar da ta girma tare da mahaifinta da kuma wadda ba ta girma da nata ba?