Duk yadda take jin kafuwar idanunshi a komai na jikin halittarta, bai hana ta ci gaba da takawa ta samu ta wuri ta zauna ba. Bayan amsa sallamarta da Capt. Sarari ya samu karfin halin yi, babu wanda ya kara magana dukkansu. A karo na farko bakunansu suka motsa a tare, a lokaci guda kuma suka kara kullewa ko wannensu na bai wa dan uwanshi damar ci gaba.
Ajiyar zuciya Ruqayya ta sauke, kafun ta kalle shi tana fadin
"Ba wai ina son saka ka a jerin mutanen da suka maida rayuwata haka ba ne ba. Ba kuma ina son. . .