Skip to content
Part 3 of 5 in the Series Matar Bahaushe by Lubbatu Maitafsir

Duk yadda take jin kafuwar idanunshi a komai na jikin halittarta, bai hana ta ci gaba da takawa ta samu ta wuri ta zauna ba. Bayan amsa sallamarta da Capt. Sarari ya samu karfin halin yi, babu wanda ya kara magana dukkansu. A karo na farko bakunansu suka motsa a tare, a lokaci guda kuma suka kara kullewa ko wannensu na bai wa dan uwanshi damar ci gaba.

Ajiyar zuciya Ruqayya ta sauke, kafun ta kalle shi tana fadin

“Ba wai ina son saka ka a jerin mutanen da suka maida rayuwata haka ba ne ba. Ba kuma ina son nuna maka rashin muhimmanci ba ne ba.

Uzurina nike son ka karba Capt. Anwar, ka gane abun da kake nema daga gare ni ba wanda zai taba samuwa ne ba.”

Ba yau ya fara jin kalaman nan nata ba. Ba wannan ne karo na farko da suke bar mishi tabo a tsakanin zuciyarshi ba, sai dai a wannan karon ya ga gaskiyar maganar tata a idanuwanta. Ya kuma tabbata da wuya idan akwai wani abun da zai iya hada tsakanin ita da shi.

Duk da ababen da yake kallo a daidai lokacin, Capt. Sarari bai yi kasa a gwiwa ba, zamanshi ya gyara yana fadin

“Ba ke kadai ba ce mai dauke da tabo na jinsin mutane. Ba ke kadai ba ce mutanen duniya suka taba koyawa hankali. Sanin da nayi na rayuwata ba za ta taba cika ba tare da taimakon jinsin mace ba shine abun da ya zaunar da ni a nan a yanzu. Haka kema taki rayuwar Ruqayya. Dukkanmu muna bukatar juna saboda hakan shine abun da Allah Ya tsara a duniyarmu. Ki bani dama mana, da ni da su Aysha muna bukatarki a rayuwarmu sosai.”

Murmushi ta saki tana kauda fuskarta. Ba wai bata da tausayi bane, ko kuma yadda wasu mazan ke tunanin babu zuciya a tsakanin kirjinta ba. Babu confusion a cikin rayuwarta illa tarin darussan da ba za su taba barin kwanyarta ba. Dan haka bata bukatar ya cakuda tashi rayuwar da tunanin ita ce kadai macen da yake bukata a duniyarshi.

“A cikin fahimtarka da tawa akwai banbanci ban musa maka ba. Haka a cikin tunanin da kake yi da wanda ni nake yi ban hango abun da kake hangowa a tsakaninmu ba. Ina rokonka da girman Allah ka manta da kudurinka a kaina, ka manta da duk wata alaka da kake tunanin za ta iya hada mu. Ka bari mu ci gaba da rayuwa tamkar komai bai taba shiga tsakaninmu ba.”

Idanunshi ya kauda daga kallon fuskarta. Yana jin yadda wani bangare na zuciyarshi yake sarewa a kanta, sai dai wani bangaren na gaya mishi tana bukatar lokaci, dan haka a hankali ya ce

“Alakar da nike tunanin ta kullu tsakaninmu ba nine na kulla ta a kasan zuciyata ba, dan haka ni kaina ban san ranar da ciwonta zai daina bibiyata ba. Sai dai kamar yadda kika bukata, zan yi kokarin nisanta kaina da ke. Amma duk lokacin da kika kara ganina ki tabbatar ba nine na kawo kaina ba, abun da ke cikin zuciyata ne ya dawo da ni, a wannan lokacin kuma babu wani abu da zai kara raba ni da ke Ruqayya Manaaf.”

Bata dauki maganganunshi da wani tasiri ba domin a tunaninta burga ce irinta mazajen da suke son cimma burinsu, nuna isa ce irin ta maza da suka saba nunawa a gaban mataye, dan haka hankalinta a kwance ta kalle shi tana fadin

“Ka kwatanta mantawa da ni, ina tabbatar maka ba za ka kara marmarin sake ganawa da ni ba zuwa gaba. Na gode da dukkan komai Capt. Anwar.”

Murmushi mai ciwo ya sufce a tsakanin lebenshi, Ruqayya Manaaf tana wasa da ikon Allah a kan bayinshi ya ke tunani, ya mike a tsakanin tsawonshi da ya kere nata yana cusa hannayenshi a aljihunshi kafun ya ce

“Lokaci ne kawai zai tabbatar mana da haka, so, ka da ki yi gaggawar yanke hukunci a kan abun da baki sani ba.”

Mikewa ta yi itama, ta kalle shi da nata murmushin tana fadin

“Ba zan taba gardama da lokaci ba, dan shine abun da ya dawo da ni macen da nike a yanzu.”

Kanshi ya jinjina yana yarda da maganarta. Sai da ya fara takawa kafun ya kalle ta ya ce

“Ba zan ce sai yaushe ba, amma zan ce sai lokacin da lokaci ya bamu aron lokaci. Na barki lafiya Hon. Dangambo.”

“Ka gaishe da Fatima da Aysha Capt. Anwar. Dan ban san me zan ce a game da lokacin da kake bukatar ya ara maka lokaci ba.”

Dariya yayi mai ciwo har hakoranshi suna fitowa. Tana kallon yadda bai ce komai ba ya juya yana zaro wayar shi a aljihunshi na wando kafun ya bude kofar falon ya wuce, tare da bacewa a idanuwanta.

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, sosai take fatan wannan ya kasance karonsu na karshe ita da shi. Ya barta ta dumfari abubuwan da suka sha gabanta a lokacin. Dakin Ummi ta karasa, a zaune ta same ta da casbaharta a hannu tana sanye da hijabinta tana azhkar. Daf da kafafuwanta Ruqayya ta karasa tare da cire jilbab din jikinta ta mike ta kwanta a gefenta, a cikin duk wata wahala da zata samu kanta a rayuwa gefen Hajiya Maryama ne kawai take iya nuna ta, a gefenta ne take samun kulawa, a gefenta ne take jin komai na dawowa cikin kanta har ma ta samu damar samun mafitarshi a ko da yaushe.

“Ummi ya gida? Ya karfin jiki? Kin ci abinci kuwa?”

A tare ta jera mata tambayoyin tare da mikewa zaune tana fara matsa mata kafarta. Dariya bakar dattijuwar mai shekaru hamsin da ukku a duniya ta saki a hankali. Kallonta ta yi, tana tausayin yadda duniya ta maida ta. A hankali ta ce

“Gida alhamdulillah. Jiki ma da sauki sosai, kuma na ci abinci na sha magani. Dan na san shine tambayarki ta gaba.”

“Ummi!”

Ruqayya ta fada tana dariyar da ta bayyana hakoranta farare. Kafun a hankali ta ji hannun Hajiya Maryama ya rike nata, ta dago ta sauke kallonta a fuskarta. Itama kallon nata take yi, sai dai wannan karon cike da kulawa, tausayawa, da  son tunatar da ita ababen da take jin kamar Ruqayya din ta manta. A hankali ta ce

“Ba ki tunanin lokaci yayi da zaki bude zuciyar ki, ki bata dama ta anshi tayin da Anwaar ya zo mata da shi?”

Idanunta Ruqayya ta lullube, yanayin fuskar Ummin ya tabbatar mata da maganar da take son yi mata kenan, dan haka ta gyara zamanta a hankali tana fadin

“Ban san ta ya zan fara hakan ba Ummi. Ina nufin babu hakan a zuciyata Ko kadan, gaskiya na fada tsakanina da Allah na. A halin yanzu idan kika dauke ku, Ina nufin ke da Hammad, bani da wani sauran burin da ya wuce mun samun ci gaba a siyasata. Kubutar da Faruq, da kuma neman Usman a duk duniyar da ya shiga. Matsawar Allah Ya cika mun burikan nan nawa, wallahi Ummi ba ni da sauran wani abu da nike nema a duniyata..”

“Ba naki maganarki ne ba Ruqayya. Ba kuma na manta tabon da rayuwa ta bar miki ba. So nike ki fahimci cewar ba za ki iya canja tsarin da Allah Ya shimfida a tsakanin bayinShi ba. Ki gane cewar jinsin mace da namiji, babu wanda zai iya yi ba tare da taimakon dan uwanshi ba.”

Murmushi Ruqayya ta saki mai cike da ma’anonin da ta bar wa zuciyarta saninsu. Ta matse hannun Ummi da ke cikin nata tana fadin

“Ban yi musu a kan hakan ba Ummi. Ina kuma ganin yadda mutane da yawa suka yarda da hakan, har ma suka aminta da shi. Sai dai a tawa rayuwar ban san ta ya zan fara yarda da hakan ba. Ban san ta ya zan kara aminta da wani da namiji ba bayan tabbunan da jinsinshi ya bar mini a kasan zuciya..”

Muryarta ta karye a dai dai wannan lokacin. Bakin tarihin da bata kaunar tuna shi ya yi mata kyakkyawan duka a saman zuciya, rashin tabbas na mazajen da ta fi kusanci da su a duniya ya dawo mata sabo, yana fifita mata ciwukan da suka bar wa rayuwarta wanda ba ta da tabbas na ranar da za su warke idan mai zuwa ce.

“Ba zan daina yi miki addu’a ba Ruqayya. Ba zan yi kasa a gwiwa wurin nusar da ke kan abun da ya dace ba. Sai dai ba zan so ganin irin yanayin nan a fuskarki a ko da yaushe ba.”

Murmushi ta saki, wanda ya zame mata tamkar halitta, domin kuwa a cikin farin ciki da bakin ciki murmushin ne abun da ke yawan wanzuwa a fuskarta. Ta mike ta dauki jilbab dinta da ke gefe tana fadin

“Ummi kin mantar da ni zan gana da lauyan Farouq bayan maghribar nan. Sannan ina da taro da shuwagabannin kungiyoyin mata na katsina state da karfe takwas na anjima, gashi na dawo gidan ma ban samu na huta ba.”

Kallonta Hajiya Maryama take tana ganin yadda take son kaucewa maganar da suke yi, ta girgiza kanta cike da sabawa da halayen nan na Ruqayya tana fadin

“Maghribar ai bata karasa ba, kina da lokacin hutawa, sai dai zan fi ganewa idan kika ce Ummi ki adana maganganunki dan ba za su taba ba yin tasiri a kaina.”

“Ummi mana.”

Ta fada tana saka dariya tare da juyawa ta bude kofar dakin tana ci gaba

“Allah ba haka nike nufi ba.”

Murmushi kawai Ummi ta yi tana jinjina kanta, ba ta sauke kallonta a kan Ruqayya din ba har zuwa lokacin da ta bude kofar dakin ta wuce, kafun ta maida ta ta rufe ta.

<< Matar Bahaushe 2Matar Bahaushe 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.