Kofar dakin ya ji an tura a hankali. Idanunshi da suka canja launin kamanninsu ya dago ya sauke su a fuskar Fatima da ta fara takowa. Zuciyarshi yake jin tana sassauta zafin da ta dauka a lokacin, ya koma kujerar da ke bayan teburinshi ya zauna, yana kara kallon fuskarta.
“Abbi ina kwana? Ashe ka dawo? Yanzu Uncle Zahra ke cewa shi ya dauko ka daga airport jiya wai.”
Murmushi mai wahala ya sufce a lebenshi. Ya kalle ta cike da kulawa, tausayinta, da tsantsar kaunar natsuwar da Allah Ya zuba a kanta. Mikewa ya yi a saman kafafunshi ya mika mata hannuwanshi. Gabanshi ta karasa tana kama hannunshi kafun ya zaunar da ita a kujerar da ke gefenshi yana fadin
“Na dawo gida lokacin kun yi bacci Fatima. Na tashi yau kuma ba ku kai ga tashi ba. Shine na shigo in dan yi karatu kafun anjima in kara duba ku. Ina Aisha? Ya makaranta? Ana maida hankali sosai?”
“Na fahimta Abbi.”
Ta fada cike da murmushi a fuskarta ta na ci gaba
“Na san dama akwai abun da ya sa bamu ganka tun jiyan ba. Makaranta Alhamdulillah, Aisha na baro ta tana wanka. Yanzu Mummy ta kira mu wai..”
Shiru ta yi, kamar ba ta son sanar da shi abun da take son fada, Capt. Anwar ya matse hannunta da ke cikin nashi yana fadin
“Wai me? Ki fada mun na ji.”
“Wai za ta zo ta tafi da mu mu yi hutu da su.”
Idanunshi ya lullube. Bacin ran da ya bar zuciyarshi ya kara dawowa. Bai san me Zubaida ke so da shi a wannan duniyar ba. Bai yi tunanin bayan duk ababen da suka faru za ta kara nuna fuskarta a gaban yaranshi ba, sai dai bai yi mamaki ba. Domin kuwa duk mutumen da zai iya aikata abun da ta aikata, ba abun mamaki ba ne dan ya rasa kunya a gaba daya rayuwarshi ma.
“Ba zan hana ku magana da mahaifiyarku ba Fatima, kin sani. Ba zan damu ba ko da za ta shigo cikin gidana ta gana da ku. Amma in bar ku kuje Kaduna ku zauna da ita na kwana guda?”
Kanshi ya girgiza yana jin abun kamar wani sa6o kafun ya karasa da fadin
“Ba zan taba yi muku alkawarin nan ba…”
“Abbi na gane komai Wallahi. Na san ba ka yi hakan dan ka bata mana ba. Sai dai Aisha, Abbi. Aisha ta dora ranta a kan Mummy fiye da duk yadda zan kwatanta.”
Numfashi ya zuka ya fesar da shi. Ya kalle ta a hankali yana fadin
“Dole ta saba da rashinta, Fatima. Dole ta yarda da kaddarar da ta fado rayuwarmu, dole kuma ta anshi duk ababen da za su tunkare mu a yanzu. Ba zan boye miki ba, da ni da Zubaida ba za mu taba kara zama tare a matsayin family ba.”
Wani irin shiru ne ya ziyarci dakin karatun, Fatima da dan karamin tunaninta ta kasa gano abun da ya kawo canji a cikin kauna irin wadda mahaifinta ke yi wa Mummynsu. Tana tuna lokacin da ta barsu tare da Abbinsu, tana tuna kwanakin da suka shafe suna jinyar rashinta su dukansu, sai dai bayan wannan, ba ta san menene dalilin da ya sa Mummy ta barsu ba. Ba ta san me yasa Abbi ya dauki fushi mai tsauri a kanta ba.
“Tashi mu je mu ci abinci. Fita zan yi nima akwai aiki da zan yi.”
“Abbi ban san me zan ce ma Mummy ba. Aisha ma ban san me zan fada mata ba.”
“Ki fadawa Zubaida maganar da muka gama yi yanzu. Ki bar Aisha da ni, zan fahimtar da ita in sha Allah.”
Kanta Fatima ta girgiza tana yarda da shi. Ta mike a hankali suka fito falon inda suka tarda Zahra zaune da wayarshi a hannu yana duba shafinshi na Instagram.
“Barka da kwana Yaya.”
Zahra ya fada yana gyara zama a cikin kujerar da yake zaune. Kallonshi Anwar ya yi yana fadin
“Ya kamata ace ka koyi gaisuwar kirki zuwa yanzu Zahra. Ka tashi lafiya?”
Dariya ta sufcewa Zahra yana fadin
“Kasan gaisuwar manya Yaya, idan na ce Ina kwana kaman ban baka girmanka ba.”
Kanshi Anwar ya girgiza yana murmushin takaici. Tunda suka taso bai taba jin Zahra ya canja gaisuwarshi ba. Ko da General zai gaida kuwa.
A bangaren tebirin cin abinci Nuriyya ce tare da Mamma suna jera musu abun da za su karya da shi. A saman fuskokinsu Anwaar ya sauke kallonshi yana tunanin yadda kaddararsu ta juya, ta dawo da shi da kannenshi zama a karkashin rufin kwano guda.
“Abbiiii!”
Aisha da ta fito daga dakinsu da gudu ta fada tana makale kafafuwanshi.
“Good morning Abbi. I missed you.”
Murmushi ya saki cike da kaunarta bayyane a fuskarshi. Zubaida ta so ta bata mishi yara da aron al’adun da ba na malam bahaushe ba. Tarbiyyar ce ke bibiyar Aisha har yau bata iya gaisheshi da yarensu ba. Kumatunta ya kama yana fadin
“Ina kwana ake cewa Aisha. Sau nawa zan sanar da ke?”
Alamar O ta yi da bakinta, ta saka hannunta ta rufe shi kafun ta saki dariya tana fadin
“I’m sorry Abbi. Ba zan kara ba.”
Dariya suka saka gaba dayansu da suke sauraren diramarsu. Capt. Sarari ya seta kallonshi a fuskarta yana fadin
“Na yi kewarku sosai Ummina.”
“Yaya ina kwana?”
Nuriyya ta fada tana sauke kallonta a fuskarshi.
“Noorie rikicin duniya. Ya aiki ya kokari?”
Dariya ta saki tana fadin
“Rikici ai sai su Aisha kuma. Mun yi kewarka kawai dai.”
“Nayi kewarku sosai nima. Ina nufin da yawa fa. Musamman ma Mammata. Ina kwana?”
Ya fada yana fadada murmushinshi tare da sauke kallonshi a fuskar Mamma da ke dauke da murmushi a fuskarta.
“Ka tashi lafiya?”
Ta fada tana karantar yanayinshi, tana kallon yadda yake kokarin boye tashin hankalin da ya samu kanshi.
Kallonta yake shima, ya saki murmushin da bai kai zuciyarshi ba yana fadin
“Lafiya lau Mamma. Na yi kewar girkinki.”
“Ka zauna ka ci har ka barshi. Abun da ka fi so na girka yau.”
“Na gode Mamma”
Ya fada yana jan kujerarshi yana zaunawa. Kanshin masar farar shinkafar da aka bude ne ya sauka a hancinshi. Lafiyayyen farfesun kan ragon da za a hada masar da shi ya sanya Anwaar jin yunwa sosai a dai dai lokacin, ya kalli Mamma da murmushi yana yaba tsarin girkin tun bai kai ga sanya shi a bakinshi ba.
A tsakiya Fatima da Aisha suka saka shi. Uncle Zahra ya zauna a kujerar gefen Aisha, Nuriyya ta zauna a ta gefen Fatima, mamma kuma ta zauna a kujerar da ke fuskantarshi. Da Bismillah suka fara cin abincin ba tare da kowannensu ya kara magana ba.
***
Gaba daya yinin ranar a daburce ta ida shi, tana lura da yadda Bamanga Jafaru ke jifarta da kallonshi mai bata labarin “Na gode da wulakancin ki” sai dai yadda take jin zuciyarta a cunkushe, ba ta damu da shi ba ko sauke kallonta a kanshi.
Karfe takwas saura na dare Ruqayya ta fito daga National Assembly, a gajiye sosai, dan tunda aka rantsar da su ba su taba irin wannan zaman mai wahala da cin rai ba. Gardama, da korafe-korafen aiyukan da suke gabatarwa. A yanayi irin wannan ta fara fahimtar inda siyasar Najeriya ta sa gaba. Ta fara gane yadda ba a dauki tunanin mace wani abu mai muhimmanci ba. Yadda ake tauye mata da tauye musu yancinsu. A zatonta abun ya tsaya a gidajen aurensu ne, amma a yanzu da ta shigo cikin majalissa, taga yadda tauye yancin mata ya samo asali tun daga demokradiyar kasar ne.
Cikin takaici ta girgiza kanta, tana tuna kalaman speaker a kan aiyukan da ta gabatar lokacin da ya kalle ta yana fadin wai a matsayinta na mace ta ya zata iya gane aiyukan da mutanenta suke bukata?
Sosai da sosai zuciyarta ta sosu da kalaminshi, musamman lokacin da ya kara da fadin bai ga dalilin da zai kawo mata siyasa ba. Idan kuma har akwai wani dalili, to bai wuce musu na tara kudin da za su sayi gwalagwalan da za su saka a wuya da kunnensu.
Murmushi mai wahala ta saki tana jin zafin kalaminshi, tana tuna yadda sauran matan majalissar suka dinga kokarin kare kansu, a nata bangaren magana a wurin da babu ilimi tamkar asarar kalami ne, dan haka ta kara shigewa cikin kujerarta a lokacin, a kasan zuciyarta tana tabbatarwa kanta tabbas sai ta shayar da shi mamakin da zai tabbatar mishi cewa mace ce ginshikin rayuwar ko wane dan Adam. Idan ma ya manta, ita za ta tunatar da shi cewa mace ce ta dauki cikinshi na wata tara, ita ce ta yi nakudarshi, ta kuma taimakawa zuwanshi doron duniyar da yake yi wa mata kallon wanda ba su san ina suka sa gabansu ba.
Har suka shigo harabar gidan, bata daina jin zafin da zuciyarta ke yi mata ba. Fuskar Hammad tare da Marwa da ta gani, ya tunatar da ita Labiba Baba Buhari da ke zaune a gidan tana jiranta. Sai kuma lokacin ta tuno da abun da ya taimaki bacin ranta, ta fito ta fara takawa inda yaran ke tsaye.
“Sannu da zuwa Ammi.”
Hammad ya fada yana ansar dogon fayil din da take rungume da shi, ya anshi jakarta yana ci gaba
“Ammi fuskanki ya nuna gajiya sosai. Kaman ma baki ci abinci ba, idanunki ya rame shima.”
Dariyar yadda yake magana take yi tana fadin
“Ba za ka gane ba Hammad.”
Ta karasa tana fadada murmushinta tare da dora hannunta a kafadarshi suna takawa, hakan ya zame mata tamkar al’adarta, tana samun kanta a cikin wani irin yanayi a duk lokacin da ya zo tarbarta, suka fara takawa yayin da ta dora hannunta a kafadarshi. Sosai yake tuna mata Usman, domin a lokuta da dama a haka suke tafiya idan suka taso daga makarantar allo.
“Ka ga baki ko? Naga har kun saba da Marwa ma.”
Cikin falon Ummi suka karasa, ya zauna a gefenta yana fadin
“Na ga Aunt Labiba, Ammi. Ta ce ban yi kama da ke ba ko kadan. Sai dai wai lokacin da kina kaman shekarata kema baki da jiki ko kadan.”
Dariya Ruqayya ta saki tana fadin
“Labiba Baba Buhari! Zan yi maganinta kuwa.”
“Ta ce ma tana da hotunanku lokacin da kuke makaranta za ta gwada mun na ga.”
“Hammad!”
Ta fada tana dariya tana ci gaba
“Ba za ka ga hotunan nan ba kuwa.”
Ta mike tana tambayar
“Ina Ummi? Yunwa sosai nike ji. Ko kun ci abinci kun manta da ni?”
“Ammi ina son inga hotunan fa.”
“Hammad!”
Ta kira shi cike da sautin kashedi a muryarta. Ya kalle ta tare da murmushi yana mikewa suna karasawa dakin Ummi da sallamarsu.
“Ummita.”
Ruqayya ta fada tana zaunawa a gefenta tare da dora kanta a kafadarta tana ci gaba
“Ummi ya karfin jiki? Ina bakin namu? Kun ci abinci kuwa?”
“Da alama gajiyar ta yau ba irin ta kullun ce ba. Na ga kina nema ki karasa ni tun lokacina bai ida zuwa ba.”
“Ummi mana..”
Ta fada suna dariya har ma da Hammad. Ummi ta kalli yadda ta yi saurin mikewa tana fadin
“Jikina fa ya warware, yanzu ko da Muhammadu zan iya dambatawa.”
“Ummi ba dai ni Muhammadun kike nufi ba?”
Hammad ya fada yana fara nade hannun long sleeve rigar da ke jikinshi yana ci gaba
“Idan kuma ni kike nufi a shirye nike mu fara dambatawan.”
“Kai tafi can Dallah, idan kai ne ai daukarka zanyi in tika da kasa baka ma sani ba.”
Dariya Ruqayya take yi sosai tana kallon yadda suke diramarsu. Hammad yayi saurin karasowa gefen Ummin yana fadin
“Ban san kin san wani Muhammadu ba bayan ni Ummi. Dan haka yanzu zaki tashi mu gwada karfi.”
Mikewa Ummi tayi tana dungure mishi kai tana fadin
“Kalle shi kaman wanda zai yi wani abun arziki. Mutumen da ko yar kwallon nan ta zamani da samari suke bugawa bai iya ba. Mu je ka ci abinci kafun ka fadi a nan.”
Fuskarshi ya yamutsa yana kallon Ummi yana fadin
“Kullun dai maganar kenan. Ni kwallo ba wurin kukana ba ne ba. Na fi son in zauna tare da ku Ummi. Ko kun fara gajiya da ni?”
Hannunshi Ummi ta kama tana fadin
“Wace ni in gaji da kai Muhammaduna. Ai kai ke taya ni zaman gidan nan nima. Ban san ya zan yi idan ka tafi jami’a ba.”
Kallonsu Ruqayya take yi lokacin da suka juya baya suka fara takawa. Idan har akwai irin wannan yanayin a duniyarsu, me za ta yi da wani wanda wata kila zai shigo ya rusa musu jin dadin da a yanzu rayuwarsu ta ginu da shi? Wasu mixed emotions ne suka fara yi mata sallama a kasan zuciya. Ta mike bayan ta cire Jilbaab din jikinta ta karasa bangaren baki domin kiran su Labiba su ci abinci tare.
A hankali Ruqayya ta tura kofar dakin. Kanta ta fara lekawa kafun ta isar da gangar jikinta. Tabbunan da ta bari a fuskar Labiba suna nan, sai shacin yatsun da ya fara bajewa wanda wata kila ta dalilin wankan da ta yi ne.
Murmushi suka sakan ma juna mai kunshe da labaran da suka cunkushe zukatansu. Ta zauna a kujerar gefenta kafun ta mika hannu ta dauki Ahmad da ke hannun Labiba.
“Kinga sai yanzu na dawo? Ban yi zaton zan dade da yawa ba haka. Ga Ahmad da Marwa na ga kaman suna bukatar kaya, da kun je ko da Hammad ne an samo abubuwan da suke bukata.”
Murmushi kadai ne abun da ya iya fita daga bakin Labiba. Zuciyarta a cunkushe take, haka ma kwakwalwarta. Abubuwan da suke bukata a yanzu ba sune ba damuwarta. Kauda fuskarta tayi, a hankali tana fadin
“Ahmad bai da lafiya Ruqayya.”
Kallon yaron da ke hannunta Ruqayya ta yi, tana lura da yadda bashi da walwala ta yara masu shekaru kusan ukku a rayuwarsu. Ta maida kallonta ga Labiba tana tambayar
“Shekararshi nawa? Me ya same shi?”
“Next month zai yi shekara ukku. Watanni shidda da suka wuce aka gano yana da matsala a zuciyarshi.”
“Ya Allah!”
Ruqayya ta fada tana tallabe yaron a jikinta. Ba ta bukatar tambayarta dalilin da ya hana su zuwa asibiti. Ba ta bukatar sanin ko yana kan wani magani a lokacin. Yanayin Labiba da yanayin da yaran ke ciki, ya bata ansar duka tambayoyinta. Zuciyarta a hankali take budewa da wasu irin al’amurra. Ba ta san me ya kamata ta fara yi ba, amma dukkansu suna jin zafin da zukatansu ke hurawa a jikinsu. Dukansu suna jin yadda suke tausayawa Ahmad, dan karamin yaron da bai san komai ba a rayuwarshi, mikewa Ruqayya ta yi tana fadin
“Mu je mu ci abinci. Akwai maganganun da nike son mu yi da yawa.”
Babu wanda ya kara magana cikinsu har suka fito zuwa teburin da suka tar da Hammad da Ummi. Zuciyoyinsu babu dadi, haka suka zauna suka fara cin tuwon shinkafa da miyar danyar kubewar da ta wadatu da man shanu na kirki. Sai da suka gama, Hammad da Marwa suka kwashe kwanukan kafun Ruqayya ta samu damar ganawa da Labiba.
A falonta da ke kallon na Ummi suka karasa, a tare suke kallon wurin ita da Labiba. Rayuwa da kalar sauyin da ta zo musu da shi, shine abun da suke jinjinawa a kasan zukatansu. Shiru mai nisa ya ratsa tsakaninsu kafun Ruqayya ta kauda shirun da fadin
“Ina kika shiga Labiba? Ya akai rayuwa ta dawo mana haka?”
Tamkar abun da zuciyarta take jira kenan. Tamkar fami aka yi mata a raunikan da ta samu a duka gabban jikinta. Kamar wadda ta dade tana yawon neman wanda zata labartawa tarihin rayuwarta. Haka take jin idanunta na kullewa ganinta. Haka rayuwa ta fara daukarta, tana yawo da ita a sararin samaniya, tamkar wadda aka cimimiye, haka ta ji an dauke ta, an wurga ta shekaru goma sha da suka wuce a rayuwarta.