Skip to content
Part 5 of 5 in the Series Matar Bahaushe by Lubbatu Maitafsir

Katsina, Nigeria

June, 1994

A gaban makarantar sakandiren yan mata ta kimiyya da fasaha (Science and Technical) da ke karamar hukumar Sandamu Baba Ado direba ya gyara tsayuwar motarshi. Yan mata biyun da ya fara cin karo da su ya bai wa sallahun nemo mishi Labiba Baba Buhari, kafun ya koma bayan motar ya tsaya yana ta faman kallon yadda dalibai ke tururuwar fitowa da akwatinansu. Wasu na shiga motocin hayar da suka zagaye gaban makarantar, wasu kuma suna shiga motocin gidan da aka zo daukarsu, da yawa kuma suna takawa, wanda ba shi da masaniyar inda suka sa gaba.

“Alhamdulillah.”

Labiba ta fada a lokacin da ta mika jarabawar larabcin da suka gama zanawa. Ta fito daga ajin tana jin yadda zuciyarta ke budewa da farin ciki da annashuwar sake ganin fuskar Abbanta.

A hanya ta ci karo da yan mata biyun da suka sanar mata sakon baba direba, ta karasa da sauri ta dauki kayanta da suke gefe ajje, a lokaci guda tana waige-waigen ta inda kawarta, wadda ta zame mata yar uwa tun daga lokaci na farko da kafarta ta tako cikin makarantar Sandamu za ta iya bullowa, amma ba ta hange ta ba.

A hankali ta fara takawa, jefi-jefi suna bankwana da sauran daliban da take cin karo da su, domin kuwa jarabawar kammala aji ukku ce suka gama zanawa, haka kuma da yawa daga cikinsu ba za su dawo makarantar ba.

Har ta iso gaban motar mahaifinta suka gaisa da Baba direba, ba ta ga ko da mai kama da Ruqayya ba. Kawar da ta zame mata yar uwar da bata taba samu ba a duniyarta. Kasancewar a lokacin haihuwarta mahaifiyarta Sauda balarabiyar kasar Sudan ta ansa kiran mahalicci. Ba ta da wani yaya ko kuma kani ko kanwarta. Haka suke rayuwa ita da Daadah mahaifiyar Abbanta, da kuma Abbanta wanda shekaru goma sha ukku ke nan da rasuwar Sauda amma bai kara ko kallon mace da sunan soyayya ba. Haka Daadah ta yi fadanta ta gaji, har lokacin da ta ansa kiran mahaliccinta shekara guda kenan.

Farin cikin da Labiba ke ciki take jin yana dakushewa. Domin kuwa ta kasa gane hali irin na Ruqayya Manaaf. A karshen ko wanne zangon karatu, ta san yadda suke kai ruwa rana kafun ta yarda su kaita garinsu, kafun su dauki hanyar nasu garin. A can gaba da makarantar ta hange ta a tsaye tamkar wadda take tunanin wani abu. A hankali ta taka zuwa inda take tsaye, sai dai babu alamar ta san da zuwanta. Hakan ya sanya Labiba dora hannunta a kafadar Ruqayya, wadda ta juyo a firgice tana fadin

“Kin bani tsoro Labee.”

Dariya ta saki tana kama hannunta tare da fadin

“Ki zo mu tafi ga Baba direba can yana jiranmu.”

Kamar yadda Labiba ta yi tsammani, wannan karon ma sai da Ruqayya ta fara kawo mata kabli da ba’adi. Sai dai ba ta bi ta kan uzurinta ba, ta kama akwatinta suka karasa wurin motar suka saka shi a baya, kafun suka shiga suka dauki hanyar Zangon-Daura.

A kofar gidan su Ruqayya Manaaf suka yi sallama cike da kewar junansu, wanda ya jaza musu zubar hawaye. Alkawarin sake ganawa suka yi wa juna, kafun Labiba ta shiga mota suka dauki hanyar Katsina ta Dikko dakin kara.

Murmushinta a lokacin da suka shigo garin Katsina kara budewa yake yi. Zuciya da idanunta na azalzalarta da son sauke kallonta a fuskar Abbanta. A hankali ta jingine kanta jikin kujerar motar, tana tuna yadda rayuwarsu ke tafiya cike da kauna, kulawa, da tattalin da mahaifinta yake bata tun bayan rasuwar Umminta. Rabon da ta ga Engr. Baba Buhari Sulaiman, tuna ranar da ya maida ta makaranta a wannan zangon karatun. Baba direba ne ke yawan kai mata ziyara tare da bata sakon da Abbanta ya bada a kai. Ba ta kawo komai a kasan zuciyarta ba, domin kuwa ta san yadda Abbanta ke da hidindimun da suka sha mishi kanshi. Sai dai a yanzu da suka tsaya a gaban kofar gidansu da ke kofar marusa, ta ga yadda aka canja fasalin gida, aka kara gyara shi. Ta fito da gudu cike da nuna farin cikinta, sai dai bata ga Abbanta a kofar dakinshi ba kamar ko da yaushe da yake tsayawa jiranta.

A hankali ta sassauta gudun da take yi, ta tsaya a saman kafafunta tana jin yadda zuciyarta ke dokawa. Ba dai Abbanta ba shi da lafiya ba? Jikinta a salube, zuciyarta tana dokawa da dukkan karfinta ta fara takawa a hankali. Hannunta Labiba ta sa ta bude labulen da yayi sutura wa dakinshi, a hankali ta fara yawata kallonta, idanunta suka fada a fuskar wata kakkaurar bakar mace, doguwa, mai murjajjen jikin da ya fi yanayi da na cikakkakun matan Hausawa.

“Ina Abbana?”

Ta tambaya tana bin fuskar matar da ta kafe ta da nata idanuwan da kallo mai cike da ma’anonin da Labiba ba ta san ya zata yi musu fassara ba.

Tsayuwarta Hajiya Ladi ta gyara, tana kallon ikon Allah tare da rashin tarbiyya a wurin diyar mijinta. Tana tabbatar da maganganun mutane da ake sheda mata cewar Engr. Buhari Sulaiman ya gama sangarta ‘yarshi guda daya tilo. Ya lalata tarbiyyarta, bata ganin kan kowa da gashi idan ba shine ba.

A yau kam ta ga zahiri. Ta ga labaran da aka dinga bata a gaban fuskarta. Sai dai bata shigo gidan dan Labiba ta ga lagonta ba. A shirye ta zo, da niyyar kauda aljannun da suke yawo a kan yar karamar yarinyar mai shegiyar fitsarar tsiya.

“Ke kuma haka aka koya miki gaisuwa? Ko baki ganni ba ne da zaki tsaya nan kina tsare ni da tambayar ina Abbanki?”

Bakinta Labiba ta ji ya kulle, ta nemi miyau da kyar, ta hadiya ya jika mata makoshinta da ya gama bushewa. Ta bude kallonta a fuskar matar, a dai dai lokacin kuma ta fara bata tsoro. Hannunta bai saki labulen dakin ba ta fara ja da baya kafun ta sake shi ta koma da gudun tsiya, sosai zuciyarta ke harbawa, dan a zatonta, batan kai ne ya kawo ta gidan da ba nasu ba.

A soron kofar gidan ta ji ta fada jikin mutum, ta dago cike da tsoro mai hade da tashin hankali ta sauke kallonta a fuskar Abbanta.

“Abba?”

Ta fada cike da shakku a sautin muryarta. Ya kama hannunta yana murmushi tare da jan kumatunta yana fadin

“Ina kike shirin zuwa da irin gudun nan? Kin girma fa yanzu Labiba. Ya kamata ki natsu.”

Abban nata ne dai ba wani ba ne ba. Ta kara kallon inda suke tsaye, soron gidansu ne ba batan kai tayi ba kamar yadda ta zata. Sai dai matar da ta gani a cikin gidan, a kuma dakin Abbanta, tun da ta zo duniya ba ta taba ganinta ba. Ba dai…? Kanta ta girgiza hawaye ya sauka a kuncinta kafun ta sanya hannunta ta kankame Abbanta, shima haka ya zagaye hannayenshi yana rike ta. Yana jin kewar ‘yar tashi sosai tana bi mishi zuciya. Yana tunanin yadda za su kare idan ya bata labarin ababen da suka faru bayan bata nan.

“Mu je ki natsu ki huta Labiba. Akwai magana da zamu yi da ke.”

Ta san za a rina dama. Ta san akwai maganganu da yawa a bakin Abbanta. Sai dai ko kadan ba ta so ta yarda da zargin da zuciyarta take jifarta da shi. Ba ta son aminta da duk ababen da suke yawata mata a kasan zuciya.

A tare suka shigo gidan da sallama a labban Abbanta, matar da ta gani dazu ta ansa mishi, wannan karon da wadataccen murmushi a fuskarta, ta yi saurin karasowa gabansu tana fadin

“Yar Abba kin gano Abban naki ko?”

Yanayin yadda ta yi wa Labiba magana a wannan karon cike yake da kulawa da kaunar da ta tabbata ba ta karasa kasan zuciyarta ba. Ta kalle ta tana mamakin anya matar da ta gani dazu ce kuwa? Wadda ta yi mata magana cike da kiyayya da kyama?

Murmushin karfin hali ya sufce a fuskarta. A hankali ta ce

“Ina kwana.”

“Lafiya lau Labiba. Ya makaranta? Mu je ga dakinki can an gyara ki huta ki ci abinci. Na san kin sha gajiya dai.”

Mamaki ne ya kashe duk wata lakkar da ke kafafun Labiba a lokacin. Ta dago tana kallon fuskar Engr. Buhari Sulaiman tana ganin yadda yake binsu da kallon murmushi mai hade da kauna. Ba dai matarshi ba ce ba? A wannan karon ta karasa tambayar a kasan ranta. Amma ta kasa furtawa, ta bi bayan Hajiya Ladi da ta doshi hanyar dakin da Daadah ta zauna kafun ta rasu. Labiba na kallonta ta ga ta tura dakin ta bude, kafun ta juyo tana aika mata irin kallon da ta fara gani a fuskarta tana fadin

“Ga dakinki nan.”

Idanunta ta kyafta, tana mamakin hali irin na wannan mata kafun ta ce

“Ba nan ba ne dakina. Wannan dakin Daadah ne.”

Murmushi Hajiya Ladi ta saki, ta matso daf da Labiba tana fadin

“Daga yau wannan ne dakinki. Domin kuwa tsohon dakinki, Rafi’ah ta riga ta maye gurbinshi.”

“Rafi’ah?”

Ta dandana sunan a saman harshenta amma bata gano mai mallakar sunan ba. Ta kalle ta cike da neman karin bayani, kafun bakinta ya motsa Hajiya Ladi ta ci gaba da cewa

“Na ji labarinki tun ban dora idanuwana a fuskarki ba. Na ji labarin rashin da’a da tarbiyyarki. Ni Hajiya Ladi dai dai nike da ke karamin kwari. Idan kika nemi rena ni kuma, wallahi zaman gidan nan sai ya zame miki tamkar a gidan bursuna.”

Tana gama fadar haka ta juya, ta bar Labiba cike da tunani da tashin hankali. Rayuwarsu mai cike da tarihin da suka gina a gidan ita da mahaifinta ta fara dawowa cikin kanta. Kauna da salon kulawar da Engr. Baba Buhari yake bata, ba ta san ya zasu kare ba a yanzu da ya auro macen da bata dace da shi da rayuwarsu ba. A hankali take jin saukar hawaye a saman kuncinta, ta sanya hannunta ta shafe shi, kafun ta yaye labulen dakin Daadah ta tura kanta a hankali.

<< Matar Bahaushe 4

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.