Akwai tarin kalubale a cikin kowacce rayuwa. Akwai nasarori akwai kuma akasinsa. Haka zalika a cikin wannan duniyar akwai mutanen kirki akwai kuma na banza. Kamar yadda al’umma take cike da mutane kala-kala. Ga harsuna mabambanta. Haka zalika a cikin zuciyoyi akwai wacce tana cikin farin ciki, wata kuma gani take yi ba za ta taba yin farin ciki ba, har ta koma ga mahaliccinta.
A wannan yanayi matashiya Meenal take jin kamar ta yi bankwana da abin da ake kira farin ciki. Duk da yanayin garin na yau, cike yake da sassanyar iska ma’abociyar sanyaya zukatan masoya. Kai hatta dattije suna cikin annashuwa a cikin irin wannan yanayi. Said ai kuma a wurin Meenal sabanin hakanne a cikin zuciyarta. Domin ji take yi tamkar an yi gobara ne a cikinta.
Cikin wani yanayi take zaune a daya daga cikin jerin kujerun da suke jere a farfajiyar gidan. Idanunta masu tsananin kyau, wadanda hawaye ke kwance a cikin su. A yanayin da take fitar da maganganun bakinta kadai idan ka dubeta zaka fahimci tana cikin tsananin damuwa. Ta dubi kawarta Halima da suke hira kamar abin arziki. A lokaci guda kuma ta rikide tamkar mayunwaciyar zakanya, a sakamakon yadda Halima ta karkatar da hirarsu zuwa batun auren Salma da ake shirin yi, kuma take ganin gara su dage suma su yi auren nan.
Maganganun da take yi masu zafi ne, sai dai kuma cikin sanyi take yi mata maganar kamar wacce aka tursasa.
“Aure? Me ya sa zan yi aure? Me nake nema a duniya na rasa? Ina da kuɗi, ina da ilmi, ina da kyau. Yayata ta haifa min yarinya mai kyau da natsuwa. Ina tare da iyayena. Don Allah ki gaya min ƙawata me zan nema agun namiji har ya kai ni ga aurensa? In auri namiji ya yi min kishiya? In auri namiji ya taka ni? Ko kuwa in auri namiji ya sa min ciwon zuciya? Don Allah gaya min dalilin da zai sa in ji sha’awar aure har in aikata hakan?” Namiji ya kashe min rayuwata gaba ɗaya.”
Meenal da ta sauke maganarta cikin wata irin natsuwa, tare da dafe kanta tana yamutsa fuska. Kafin ƙawarta Halima ta sami bakin magana, ta ɗora da cewa, “Ba zan taɓa yin soyayya ba, ba zan kuma taɓa yin aure ba har in koma ga Allah. Ina fatan ba za ki tambayeni dalilin hakan ba?”
Meenal ta rufe maganar ta hanyar ɗorawa Halima zancen da ya sa bakinta sake sarƙewa. Har kullum tana mamaki idan Meenal tana wasu maganganun kamar mai jinnu.
Ganin irin kallon da Halima take yi mata ya sa ta aika mata da murmushi kawai ta miƙe. Kafin tasan abin yi har ta shige ɗakinta ta rufe da ɗan makulli.
Tana shiga ɗakin ta rushe da matsananciyar kuka, ta dafe ƙirjinta da ke yi mata suya. Tari mai ƙarfi ta ɗinga yi, kafin kace me? Sai jini ta baki ta hanci. Duk da haka bata daina tarin ba. Hankalin Halima ya tashi gashi ta rufe ƙofarta. Cikin sauri ta koma sasan mahaifiyar Meenal tana gaya mata halin da ake ciki. Kafin abinda bai wuce minti biyar ba, hankula sun tashi a gidan. Da ƙyar mai gadin su ya iya ɓalla ƙofar.
Ko kafin a kaita mota har ta sume. Hajiya Salma ta dinga kuka kamar ranta zai fita. Ita dai Halima sai abin ya dinga bata mamaki. Me ya sami Meenal bayan yanzu ta gama yi mata murmushi?.
Bayan likitoci sun karɓeta ne mahaifiyar Meenal ta dubi Halima ido jajir ta ce, “Halima idan kina son zumuncin ku da Meenal ya ɗore kada ki sake yi mata zancen aure! Duka-duka shekarun Meenal, ashirin a duniya, ina ganin bata yi girman da za a dinga kawo mata zancen saurayi ba bare kuma aure. Haka Meenal, bata da wata ƙawa,, kema ɗin ta amince maki ne saboda wani dalili nata. Zan baki shawara ta ƙarshe, kada ki yarda ki saki jiki da Meenal domin bata ƙawance! A kowani irin lokaci zaki iya neman ƙawancen ku ki rasa.”
Umma tana gama jawabinta ta fice daga wurin ta bar Halima baki a buɗe. Ita dai ta shiga duhu, tana buƙatan ƙarin bayani, sai dai kuma agun wa? Me yasa suke jifanta da irin wadannan kalaman?
Jim kaɗan bayan shawo kan Meenal tana kwance idanunta a rufe hawaye ke bin gefen fuskarta. Umma da Halima suna zaune a gefenta. Umma tana yi mata nasiha cikin natsuwa.
Wani ƙamshi ne ya ci nasarar shiga ƙofofin hancinta, lokaci guda zafi da ƙuncin da take ji ya sauya zuwa wani irin sanyi. Kai tsaye ta fassara hakan da son ƙamshi da Allah ya ɗora mata.
A.A Bakori matashin likita mai natsuwa da girman kai. Haka mutum ne mai zafi da rashin son wargi. Dogo ne mai ɗauke da faffaɗan ƙirji. Fari ne tas! Kallo ɗaya zaka yi masa ka fahimci tsantsar bafullatani ne. Su kansu nasis ɗin da ke biye da shi a tsorace suke, duk da suna jin daɗin aiki da shi matuƙa.
Kallo ɗaya ya yi mata ya gama tantance kamanninta. Cikin girmamawa ya gaida Umma, hakan yasa Meenal buɗe idanunta. Suna haɗa idanu dukkan su suka yi saurin kawar da kai. Haɗa rai ya yi sosai yana dubanta,
“An kawo ki Asibitin nan yafi a ƙirga akan matsala ɗaya. Hajiya yarinyar nan mutuwa take buƙata, ina ganin da kun daina wahalar da kanku wajen kawo ta asibiti. Allah ya ƙara sauki.”
Da idanu ta raka shi har ya juya ya bar ɗakin. A zuciyarta ta ce, “Namiji dai har abada ba zai canza ba. Babu tausayi sai baƙar magana. Ka shiga cikin jerin irin mazan da na tsana. Idan ka sake gaya min wata kalma wacce zata sa min damuwa babu shakka sai na fasa maka kai.”
Halima da Umma suka kwana da Meenal. Don haka cikin tsakiyar dare, Dr A.A Bakori ne tsaye akan Meenal yana dubata. Wannan ƙa’idarsa ce duk dare sai ya je ya duba marasa lafiyansa. Ya yi mamakin ganin Meenal a cikin dogon tunani wanda har ya kama hannunta yana duba ƙarin ruwan, amma bata sani ba. Sai da ta ji zafin irin riƙon da ya yi mata ne kafin ta ɗan waiwayo. Kafe juna suka yi da ido, wanda dukkansu sun rasa dalilin kallon. A lokaci guda kowannan su ya kawar da kansa.
“Ki bi duniya a sannu, kin ɗauketa da zafi, Don haka zata yi ta ƙona ki. Ke yarinya ce ƙarama bai kamata kina jawowa iyayenki matsala ba. Mahaifiyarki bata huta ba, na tabbata mahaifinki ma yana can cikin damuwa.”
Dubansa tayi cikin sauri, sannan ta fizge hannunta, “Da ina da dama da nace idan likita namiji ya sake kusanto inda nake ban yafe ba. Akan kada insake musayar magana da kai, zan dage wajen cire duk wani abin da zai iya kawo min matsalar da za a kawo ni nan.”
Yamutsa fuska ya yi kamar ya fahimci abin da take nufi. Shareta ya yi, ba tare da ya sake duban inda take ba ya kammala abin da zai yi ya fice. Meenal ta bi shi da kallon mamaki. Bata taɓa ganin namijin da ya haɗu da ita bai nuna yana sonta ba sai yau, bata taɓa ganin namijin da bai yaudareta ba ta hanyar nuna mata damuwarta tana damunsa ba sai yau. Shima kenan yana sahun mugayen da nasu muguntar ta shaharar da baya iya ɓoyewa.
Nan da nan ta fara jin zuciyarta tana tafasa. A hankali ta ke karanto addu’a har ta fara jin natsuwa tana shigarta.
Dr. Bakori yana komawa Office kalaman Meenal suka dinga dukansa. Ƙoƙari yake yi dole sai ya share lamarin yarinyar, amma kuma tayi amfani da kalaman da ya zama dole ya ji menene?
Ta ina? Ɗayar zuciyar tayi saurin ankarar da shi. A karo na barkatai yake sake jin tsanar yarinyar. Fayel ɗinta yake ta kallo yana nanata sunan da ya gani a rubuce, Meenal S. Ya kasa gane me S ɗin yake nufi, kuma meyasa babu cikakken sunan? Cire tunanin ya yi a zuciyarsa, haka kuma ya ci alwashin ya gama duba yarinyar.
Har aka sallame su bata sake sa Dr. Bakori a idanunta ba. Hakan ba ƙaramin dadi ya yi mata ba.
Zaune take agurin bikin Salma tana ta faman latsa wayarta ba tare da ta dubi ko da mutum ɗaya ba. Ƙawayen kowa ya fita harkarta, don kowa ya san halinta agun girman kai. Ɗagowa tayi tana duban yadda Salma ke rawar kai, tana zumuɗi. Murmushi ta yi ta ce, “Idan namiji ne sai ya mayar da murmushin nan naki kuka, idan namiji ne sai ya sa kin fito duniya kina kurma ihu. Insha Allahu babu ni babu soyayya.”
Ƙarfe biyu agogon ya buga, hakan yake nuni da saura minti talatin kacal! Salma ta zama amarya. Tayi matuƙar kyau a cikin shigarta ta leshi sai ƙamshi ke tashi a jikinta. A karo na farko da Salma ta ɗan burgeta. A zuciyarta take yi mata fatan dacewa da abokin rayuwa.
Wata magana ta gilma kamar wucewar iska mai ƙarfi. “Anti Salma! Anti Salma!! Ki zo ga su Baba cike a falo da Uncle Ahmad ya ce wai ya fasa aurenki.”
A firgice Salma ta miƙe tana me dafa ƙirji. Ya fasa aurena? Meyasa zai yi min haka?” A gigice tayi falon da gudu cikin rashin natsuwa. Meenal ce mace ta biyu da ta rufa mata baya cikin wani irin gigita. Don haka sauran ƙawayen ma da suka sha anko suka mara masu baya.
A tsakiyar falon Salma ta zube a gaban Ahmad da ke tsaye. Allah kaɗai yasan me suke tattaunawa. “Don Allah Uncle A, ka taimakeni kada ka rusa min farin ciki, Don Allah ka aureni ko da bayan kwana biyu ne ka sake ni. Zaka sa inkasa shiga jama’a, zaka sa duniya ta sami abin gulma akaina, a maimakon tausayawa.”
Meenal ce ta ratso, sai muryarta ake ji da ƙarfi cikin tashin hankali, “Salma har yaushe kika yi lalacewar da zaki durƙusawa shashashan namiji wanda bai san ciwon kansa ba? Wannan kaɗan kenan daga cikin hallayar maza. Idan ya gane ya ci galaba wajen sa maki ciwon zuciya abu na gaba da zai nema agurinki to rayuwarki ce. Kai kuma ka je zaka haɗu da abinda kayi mata mafiyinsa. Haka ka kwantar da hankalinka zaka haifa za a rama mata. Idan kana tunanin ka ci galaba ne akanta kayi kaɗan Wallahi. Mugu azzalumi. Tunda ka kasa gane darajar ‘ya mace babu shakka mahaifiyarka ma ba kowa ba ce agurinka fa ce…”
Bata kai ga ƙarasawa ba yasa hannu ya ɗauketa da mari har sau biyu.
Duk abin da ake yi sai yanzu suka haɗa idanu, a lokacin da take dafe da kuncinta. Tsoro da firgici ya shige su. Ba kowa bane face Dr. A.A Bakori. Kusan ma ya fi ta shiga ruɗu. Ran Meenal yana wani irin tafarfasa ta ce, “Naso ace kwana zaka yi kana marina, da ka mari zuciyar Salma a rana mafi mahimmanci a cikin rayuwarta. Ban yi mamaki ba zaka yi fiye da hakan ma.”
Meenal ta sa hannu ta ci kwalar fararen kayansa idanun nan sun koma kamar jan gauta, “Ka fito ka gayawa duniya dalilin fasa aurenta tun kafin a cigaba da yi mata sharri! Ka fito ka gayawa duniya kai mayaudari ne kayi amfani da yaudara ka cuceta.”
Tuni tarin nan nata ya sarƙe ta, ta dinga yi. Ahmad ya riƙo dukka hannayenta yana dubanta. Gaba ɗaya sai kallo ya koma kansu. Salma kuwa rusan kuka take yi kamar ranta zai fita. Jinin yana fara fita daga bakinta, ya shimfiɗar da ita. Hannunta da ta riƙe nasa da ƙarfi yabi da kallo. A hankali ya zame ya kafe kyakkyawan fuskarta da kallo. A karo na farko da ya ji damuwarta a ransa. Haka a karo na farko da yaga mara lafiya cikin buƙatar taimakon gaggawa da ya gagara taimaka mata. Jiki babu ƙwari yasa kai zai fice. Har ya kai bakin ƙofa ya sake waiwayota ya ɗan kalleta yana ji a jikinsa yayi mata kallon ƙarshe, Don ba za su sake haɗuwa ba. Girgiza kai kawai ya yi ya fice abinsa. Babu wanda ya iya furta komai har sai da aka tabbatar ya tafi kafin kowa ya buɗe baki ya fara magana. Ita kuwa Salma ta zama ƙaramar mahaukaciya. A ya yin da ‘yan uwan Salma suka ɗauki Meenal zuwa Asibiti.
Masha Allah. Ku zo mu hadu mu karanta rikitaccen littafina domin mu zakulo amsoshinmu a ciki. Ina tare da ku tun daga farkon labarin nan har izuwa karshe. Zamu tattauna akan wannan labari, zamu tattauna a karkashin comment, zamu yi hira zamu tattauna akan wannan littafi. Ku ajiye ra’ayoyinku insha Allahu muna tare
Wai chakwakiya kenan Allah yatashi kafada meenal
😂😂😂😂