Skip to content
Part 12 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Sai dai karfen nasara a tsakiyar daji ta lalace masa. Ga yamma tayi sosai. Gashi da kudi a cikin motar. Fitowa yayi da kudin a hannunsa ya kamo hannunta suka shiga cikin dan hanyar da suke hange kamar da gidaje. A kofar wata bukka suka yi sallama. Wani bafullatani ya fito suka gaisa da fillanci domin da alamun baya jin hausa. Dr. Bakori yayi masa bayanin lalacewar motarsa. Fulanin nan ya ce sai dai su shiga wata bukka da ya nuna masa gobe sai a shiga gari a nemo masa mai gyara. Babu musu ya yi masa godiya suka shiga ciki. Babu komai sai tabarma. Dr. Bakori ya saki ajiyar zuciya ya yi Hamdala.

Meenal ta takure gefe guda shima yana zaune a gefensa. Bafullatanin mai kirki ya kawo masu fura da nono. Hannu yasa ya dawo da Meenal kirjinsa ya dago fuskarta suna duban juna. Rufe idanun tayi ta rasa lokacin da soyayyar Bakori ya shigeta da har yake shirin yi mata illa. Har yanzu karyata zuciyarta take yi. Bai taba cewa yana sonta ba, da alama tausayinta kawai yake ji kamar yadda ya fada. Ina maganar sakinta da zai yi? Lumshe idanun ta sake yi a lokacin da taji tattausar hannunsa a bisa cinyarta.

Gabanta ne ya fadi da karfi. Har kullum mamakin irin soyayyar Dr. Bakori take yi, mutumin da baya dariya baya kallon mace bare ta burge shi haka masifaffe. Bata taba tunanin zai iya yin soyayya ba. Magana yake a natse “Kada ki damu da inda muka tsinci kanmu, wannan ma wani ilimi ne. Ki tashi muje muyi Sallah.”

Sunkuyar da kanta tayi kawai ba tare da ta iya furta komai ba.

Muryar Danfulani yasa duk suka dube shi. Bafillatani yana ganin su ya ware ido yana tambayar ko bata da lafiya ne? Dr. Bakori ya saki murmushinsa ya ce ‘Eh jiri take gani shiyasa na riketa kada ta fad’i.” Bafullatani ya gyada kansa ya ce, “A tsaye take da zaka ce zata fad’i kamar wata bishiya?” Bakori ya sake yin murmushi kawai ba tare da sake furta komai ba.

Buta suka ajiye mata suka nufi dan karamin Massalacin da aka kewaye da duwatsu. Yana fita taje ta kama ruwa a bayan wurin da suka dan kewaye, ta yi alwalan ta dawo ciki, kasancewar al’adarta kwana daya kawai ya yi ya koma. Ta jima zaune akan dadduma ta daga hannayenta sama tana kuka. Addu’arta wannan karon yafi karkata akan mahaifiyarta.

Ajiyar zuciya tayi dole masifar tayi mata yawa. Anhaifeta ba ta hanyar aure ba, haka dangin mahaifiyarta sun kasance kiristocin da ake ji da su a fannin addinin su. Kuka sosai take yi tana jin zafin mahaifinta a ranta, domin kuwa shine silar komai.

Tana nan zaune barci mara dadi ya dauketa. Bai shigo dakin ba, sai da ya yi isha’i ya kuma zagaya ya siya masu nama. Bafillatani yana ta jin dadi, don rabonsa da nama, tun wani zuwa da maidakinsa tazo ta siya masu na dari biyu.

Kasancewar Allah ya yi shi da danbanzan mako.

Zuba mata idanu ya yi yana kare mata kallo. Bai so za su kwana a irin wannan wurin ba, amma kuma idan ya tuna da zai sake samun ilimi sai ya ji natsuwa sosai. Wayarsa babu network bare ya kira yaji abinda ke faruwa a garin Kano. Yana nan zaune bai tashe ta ba, Bafullatani ya kawo masu garwashi saboda sanyin da ake dokawa. Godiya ya yi masa ya cigaba da zuba mata idanu, ya rasa yadda zai yi mata.

Rigarsa ya cire tunda tana da kauri, ya jawota gaba daya jikinsa, ya rufeta. Shi kuma a hankali dumin jikinta yana ratsa shi. Wani saƙo ya aika mata, wanda yasa kamar a mafarki take jin wani abu a cikin jikinta, don haka cikin magagi tasa hannu ta rungume shi tsam. Wani yanayi suka afka mai wahalar fasaltawa. Bafullatani ya ɗan leko,

“Asshalamu alaikum.” Dr. Bakori bai dago ba, amma kuma ya dakata da abinda yake yi, musamman da Bafullatanin nan ya haske su da fitilar hannunsa, da ya kawo masu yana ta aikin washe hakora. Kamar daga sama Ahmed ya ji ya ce, “Ku dai kun huta abinku kuna ta ishkanci.

Tun da kuka zo nake kula da ku kuna shikin sha’awar juna. Hala baku shaba yi bane?” Dr. Bakori ya dago yana kallonsa, mutumin da ya ce masa baya jin hausa? Meenal kuwa da tuni ta farka, saboda kunya bata san lokacin da ta sake makalewa Dr. Bakori ba, tana jin wani irin kunyar mutumin da bata taba gani ba, sai a yau. Ahmed ya daure fuskarsa kamar bai taba dariya ba, “Ka ajiye abinda ka kawo ka tafi kawai.”

Danfulani yaso ya sake furta wani abu, amma kuma ganin babu fuska yasa ya ajiye ya juya. Ahmed ya rungumeta ya ce, “Sorry na tasheki ko? Yi barcinki ba zan sake taba ki ba.” Da asuba gaba daya jikinsa ya yi tsami domin kuwa a zaune ya kwana Meenal tana jikinsa. Tashinta ya yi ya ajiye mata ruwa, yaje ya tashi bafullatani suka wuce Masallaci.

Suna hanyar dawowa bafullatanin me suna Lado ya dube shi, “Ni gashkiya na ƙosha ku tafi, kun dameni.”

Ahmed bai dube shi ba ya ce, “Haba ai ba a kosawa bako ya tafi. Me muka yi maka?”
“Da farko dai ku ‘yan ishka ne, kuna shawa ina yawan kwadayin matata. Na biyu kuma, ni bana shon zuwa Masallaci da ashuba idan ina barci. Shaboda shon zuciya, ka tashe ni, ina borcina me dadi. Aradun Allah ku zo ku tafi bazan iya ba.”

Ahmad ya yi banza da shi kawai ya cigaba da tafiyarsa. A tunaninsa dan fillo wasa yake yi, sai ya faki idanunsa, ya wuce ya hau mota sai gashi ya dawo da bakanike. Ahmed ya dube shi bai ce komai ba, suka gangara gurin motar, aka duba aka gyara. Ya ce bari ya kwaso kaya yazo ya sallame shi. Lado ya tokare sandarsa yana tsaye har suka fito, tana rungume a kirjinsa, ya ce “Allah shi raka taki gona. Itama shegiya tana jin dadin abun.” Ahmad ya ciro dubu dari ya mika wa Lado, a matsayin tukuicinsa na taimakonsa da ya yi.

Ya kuma ce garin ya yi masa kyau zai dawo ya gina katon masallaci, zai kuma siya fili ya yi gininsa wurin ya burge shi.” Lado ya jefa sandarsa sama, ya yi kirari ya ce, da fillanci, “Kyautar nan naka sai nayi shekara ina ci basu kare ba. Gaskiya naji dadi na gode. Duk da haka ku tafi sai matata ta dawo sai ku dawo domin dayan abun kudi basu siyan shi.”

Ahmad dai bai ce masa komai ba, suka wuce abin su. Har gareji ya kai mutumin sannan aka sake duba motar, ya biya shi hakkinsa, suka kama hanya.

A wani katafaren gida suka sauka, bayan maigadin ya bude masa gidan. Kakkarfar ajiyar zuciya ya saki “Inna fatan Allah yasa karshen matsalar kenan.”

Akwai ma’aikata a gidan hakan yasa zuciyar Meenal ta gaya mata akwai mutane a gidan. musamman yadda taga akwai bangarori daban daban. A falo tayi wa kanta mazauni, tana karewa tsaruwan falon kallo.
Rufe idanunta tayi ita kanta tana fatan wannan ya zama karshen matsalarta.
Nuni ya yi mata da daki, ya fice daga gidan.

Shi kansa dakin ya tsaru sosai. Wanka ta yi ta gasa jikinta da ya yi mata nauyi, sannan ta bude akwatinta ta ciro doguwar riga. Haka Meenal take Allah ya dora mata son dogayen riguna da kananan kaya. Sai dai ba zata iya sa kananan kaya a gaban Dr. Bakori ba. Turare ta goga kadan, tunda bata zo da humrar ta ba.

Tuni barci mai nauyi ya yi awon gaba da ita. Ji tayi ana hura mata iska a fuska. a hankali ta bude idanunta ta dora a kyakkyawar fuskarsa. Allah ya yi halittarsa akan Dr. Bakori. Hannunta ya lalubo yana murzawa a hankali. Haka ya dora fuskarsa a bisa nata, ya hada hancin su wuri guda. “Zo muje ki karya sai ki koma barcin ki.”

Ba zata iya tashi ba, dan haka ta mayar da idanun ta rufe. Bude bargon ya yi gaba daya ya kamo hannunta. Tana mikewa jiri ya nemi kwasarta ya yi saurin dawo da ita kirjinsa. Dan karamin dankwalin da ke kanta ya zame, sai ga gashinta baki sidik, ya bayyana.

Shuru ya yi ya tabbatar da ya dawo hayyacinsa sannan ya kamo ta suka wuce falo, inda ya zube abin karyawar da yaje ya yo order. A hankali yake ciyar da ita har ta koshi sannan shima ya fara ci. Hakan ya tuna mata da labarin da aka bata akan mahaifiyarta, sai ta bata abincin idan ta koshi ne take sawa a cikinta, wataran ma haka take hakura ta bar mata ragowar ko zata nema anjima. Hawaye ta ji suna zubowa daga idanunta, cikin dabara ta dauke su ba tare da ta bari ya gani ba.

Duk abubuwan nan da Dr. Bakori yake yi mata ta kasa sakin jiki da shi, tasan dole watarana sai halin su na maza ya bayyana a jikinsa.

“Zo muje mu kwanta.” Babu musu ta biyo shi suka kwanta akan lafiyayyan gadon. A natse yake mata magana, “Wannan gidana ne, akwai matar abokina a wancan bangaren da na basu suna zama. Zamu dan zauna anan zuwa komai ya lafa.” Wayarsa da ke kara ya dauka tare da mikewa zaune, alamun girmamawa. “Lafiya lau Abba, yanzu haka ina Abuja. Komai yana tafiya dai-dai.” Abban ya godewa Allah, ya ce a gaida Meenal.

Yana son kiran mahaifiyarsa, amma kuma maganganunta suna yi masa yawa, suna sake tsorata shi. A yanzu mahaifiyarsa ce kadai damuwarsa. Yana son ta janye tsinuwarta kafin ya iya tunkarar gidan mahaifinsa. Lokaci guda bacin rai ya bayyana karara a fuskarsa. Kura masa idanu tayi, ta rasa ta yadda za ayi ta iya bashi hakuri. Cikin sanyin muryarta ta ce, “Kayi hakuri. Baka yin kyau da fushi.”

Ajiyar zuciya ya yi ya kamo hannunta, “Ba fushi nake yi ba Meenal.” A hankali yake wasa da hannunta kamar bai san abinda yake yi mata ba, hannunsa ya akan wuyar rigarta kasancewar wuyar rigar mai fadi ce, hakan yasa yake dan yi mata waiwayi. A sanyaye ta dago tana dubansa, sai taga ya kurawa wani wuri ido, hakan yasa ta sunkuyar da kanta, ta lumshe idanun. Tsoro da firgici suka shigeta a lokacin da zuciyarta take gaya mata inda hannunsa zai je, amma kuma ba hakan ke nuna mata hannunsa ba zai iya kai inda ya nufa ba. Jikinta yana rawa tasa dayan hannunta ta rike hannunsa, idanunta a rintse.

Cire hannun ya yi ya rungumeta tsam ya raɗa mata, “Sarkin tsoro.”

Lallaɓata yake yi, domin bai mance alkawarin da ya dauka ba, ba zai taba kusantar Meenal ba, har sai ya daidaita ta, da kowa nata. Har sai ya ga tana zaune a cikin ‘yan uwanta suna dariya.

Duk ranar da yaga wannan ranar babu shakka a ranar zai karbi hakkinsa. Baya son Meenal ta fara samun zuri’a bayan rayuwarta bata gama daidaita ba. Bandaki ya shiga yana jin ciwon mara fiye da tunaninsa, yana jin idan bai kwanta da matarsa ba zai iya samun matsala. Dan haka kawai ya sakarwa kansa ruwa yana jin saukar ruwan, amma kuma shi kadai yasan halin da yake ciki. Jallabiyarsa ya sa ya fice ya nufi Frij ya dauki lemon tsami ya matse a kofi ya shanye. Sai a lokacin ya sami natsuwa, domin Ahmed bashi daga cikin irin mazan da wasa yake gamsar da su.

Yana nan zaune a falon idanunsa a rufe ta fito kanta a kasa. “Me nayi maka? Ai banyi maka musu ba.” Ya kura mata idanu yana dubanta, zai so su dinga nesanta juna, gudun afkawarsa cikin matsala. Ya yi alkawarin abu mai matukar wahala. Baya son ya karya alkawarin nan. Kamar zai kamo ta sai kuma ya janye hannunsa, “Baki yi min komai ba, ni ne dai kamar bani da lafiya.”

Yadda yaga ta rude abin ya bashi mamaki. Gashi dai karara a idanunta har yanzu tana dauke da shakkan maza, daga ciki har da shi, amma kuma ya rasa dalilin da yasa ta damu da lamarinsa. Girgiza kai ya yi yarinyar ta cika shagwaba da alamun sai ya yi da gaske.

“Ba wani ciwo bane naji sauki. Kaina ke dan sara min.” A hankali ta matso kusa da shi tasa hannu ta kama kan, hakan yasa ya kurawa labbanta idanu, suna walkiya cikin man baki, da alama bata jima da gogawa ba. Indai yarinyar zata kusanto shi sai ya rasa dukkan natsuwarsa.

“Ya Salam! Yarinyar nan zata zama ajalina.” Cikin sauri ya sake nufar Frij din ya ciro lemon tsami. Idanunsa sun kada sun koma jajir. Ba zata iya magana ba, amma idanunta shi suke kallo cikin wani irin kasala. Tana son tambayarsa me Lemon tsamin yake yi? Amma ta kasa. Tana kallonsa har ya gama sha, sannan ya mike ba tare da ya dubi inda take ba, ya fice daga gidan. Maman Anwar ce tayi Sallama kofar dakin, tun kafin a bata izinin shiga ta turo kofar ta shigo. Meenal tayi saurin gyara kanta ta dauki dankwali ta rufe kanta da yake a yamutse. Maman Anwar ta kafeta da idanu, sai kuma ta kawar da kai, “Tunda ke baki shigo ba, mu bari mu zo mu gaishe ki. Naga maigidan agun mijina shiyasa nace bari inshigo. Sunana Yahanasu, ana kirana Maman Anwar, ina da yaro Anwar, haka muke zaune a cikin gidan nan.”

Meenal ta jima tana tattara natsuwarta, hakan yasa Maman Anwar take ganin kamar tsabar ji da kai ne yasa ta ki yi mata magana. Meenal tayi magana cikin sanyi, “sunana Meenal.” Maman Anwar ta gyada kai kawai tana dubanta. Shurun ya yi yawa, haka Maman Anwar taki tafiya, tana zargin wani abu, don haka ta zauna tana son ta tabbatar. Shuru-Shuru Dr. Bakori yaki dawowa, haka itama shugaban masu son ganin kwaf taki tafiya. Ita kuma bata iya hira ba, bare tayi mata.

Kwankwasa kofa akayi Meenal ta mike taje ta bude. Hancinta ya dan ja, “Baki ganni ba, baki yi cigiyata ba ko?” Langwabewa tayi, “To ai hankalina ya tashi da ban ganka ba, taba wuyana kaji zafi.” Ya kai hannu wuyan, kamar shokin ya ja shi ya yi saurin cire hannunsa yana fadin “Wai Wai yau dole inyiwa wata allura kada zazzabi ya kwantar min da ita.”

Dariya tayi sosai, hakan yasa ya lalace da kallonta, sau biyu kenan tun saninsa da ita da yaga dariya a bisa fuskarta. Yaji dadin wannan dariyar fiye da komai. Yana rungume da ita suka shigo. Ganin Maman Anwar ya dan saki fara’a “Ashe har yanzu kina nan? Lallai kin kyauta sosai.”

Maman Anwar ta saki yake ta mike tana duban yadda Meenal tayi kwanciyarta a kirjinsa, “Wallahi kuwa Doctor yanzu nake shirin tafiya sai ga dawowarka. Na gaisheku ni zan wuce.”

Duban Meenal ya yi da take kirjinsa kamar mage, “Baby wannan ce makociyarki da nake baki labari. Kin ga kin sami kawa kenan ko?”
Meenal ta tabe baki ita dai hakannan hankalinta bai kwanta da Maman Anwar ba.

Haka Maman Anwar ta fice tana cizon yatsa.
Daga shigarta gida ta sami Mijinta Baban Anwar yana kwance yana mamakin yadda taje ta zauna bayan tasan yana gida, a tsaye ta rike kugunta tana dubansa,

“A gaskiya Baban Anwar ba zan boye maka ba, sam baka iya soyayya ba. Haba kalli abokinka yadda yake tarairayar matarsa agabana. Idanunsa kadai zaka kalla ka ga zallar sonta. Ana magana ana wani kashe murya, kai kuwa kullum kana kwance da gajeren wando kana chatting.”

Dubanta ya yi da mamaki sannan ya yi murmushi, “Kai amma sun burgeni. Ita kuma matar ya tayi”

Zama ta yi tana kumbura hanci, “Matar nan yana dawowa ta kwanta a kirjinsa tana zuba masa kalamai da shagwaba. Shi kuma duk ya lalace a tarairayarta, har yana cewa zai yi mata allura saboda kawai tace tayi zazzabi da ya fita ya barta.”

Ajiye wayarsa ya yi ya ce, “Da kyau! Idan mace tana lallaba mijinta, sakamakon da take samu kenan na kulawarsa.

Ta yaya za ki zo tsakiyar kaina kina magana a tsaye kamar kina magana da sa’anki kiyi tunanin samun kulawana? Kowani namiji yana son kulawa yana kuma son shagwaba. Ita kanta shagwabar kala-kala ce ba kowacce take burge namiji ba, akwai wacce zaki yi ya ji kamar ya shake ki don bakin ciki.

Daga nan sai ki fara fita kina cewa ai mijinki ya tsani shagwaba, bayan baki san ta yadda zaki yi ta bane. Don Allah matsa min akaina.”
Tashi tayi tana zumburo baki, “Oho dai kawai baka iya soyayyya ba Malam.”

“Eh ban iya ba, alhakinki ne ki koya min, tun bana yi watarana sai kiga nayi. Shugaban masoya.”
Ya fada mata da gatse.

Shikuwa Dr. Bakori cijewa ya yi ya kasa taba ta. Ita kanta tana kula da sauyawarsa, amma sai bata kawo komai a ranta ba. Dubansa tayi a hankali take magana kamar tana jin tsoron wani ya ji, “Asiyo kayayyakin girki indora mana.” Girgiza kansa ya yi yana jin wani irin ciwon kai, “A’a Meenal ina son ki huta. Duk abinda zai sa ki sauya bana sonsa.

Kullum Maigadi zai dinga kawo abinci daga Shagalinku Restaurant. Allah ya yi maki albarka, yasa ki gama da duniya lafiya.”

Meenal ta sunkuyar da kanta shuru, hakan yasa ya yi tunanin zata iya fara kuka, don haka ya ce, “Meenal zo ki yi min tausa a kafafuna, suna yi min zafi.”

Cikin sauri ta nufi kafafun tana ja, kamar wacce take yi masa susa. Wani irin kasala ya rufe shi, yana lullumshe idanu. Karar wayarsa yasa ya dan ware idanunsa, sannan ya dauka, yana me daidaita natsuwarsa, “Doctor baka sake nemana ba, ko har ka mance da kowa?” Ahmed ya dan sosa kansa, a lokaci daya ya dan ji nauyinsa a matsayinsa na surukinsa.

“Ya ayyukan da komai? Bakori ya sauya maganar zuwa gaisuwa. Murmushin mugunta Hon Munnir ya yi ya ce, “Komai lafiya, sai dai Alhaji Munnir bai mutu ba yana nan a raye. Yanzu haka kai ake nema duk da ya hana a baza maganar a media, amma ina tabbatar maka ‘yan sanda suna nemanka ido rufe. Ina fatan idan ankama ka ba zaka ambaci sunana ba? Dama miliyan Hamsin dinnan na diba ne na baka idan Alhaji Khalid ya mutu, ni kuma sai incika sauran ka baiwa matarka Meenal. Ka ga aiki ya koma baya kenan.”

Hon Munnir ya karashe maganar, yana murmushi, shi kadai yasan mugun nufin da ke zuciyarsa, shi kadai yasan sirrin da ake yi masa kallon wawa.

<< Meenal 12Meenal 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.