Skip to content
Part 17 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

“Husby! Husby!! Ka zo ka gyara min hannun ya warware. Wayyo ni Husby kazo ko inyi maka kuka.” Dube-dube take yi bata ganshi ba. Sai wani ƙaton abu kamar mage ta fasa ihu tayi hanyar waje, ya ɗauketa cak yana juyi da ita.

“Babyn Husby me tsoro. Happy Birthday to you. Umma ta kirani ta ce yau ‘yarta ta ƙara girma da ƙatuwa amma har yanzu ‘yar baby ce ƙarama.”

Meenal ta zaro idanu, “Husby shine zaka kawo min abin tsoro a matsayin Birthday Gift ɗina? Ni Wallahi ba zan yarda ba.” Da gudu take bin shi hakan yasa suka fara ƙoƙarin zagaye falon. Dai-dai da Sallamar Maman Anwar da mijinta sai wata mai ɗaukar hoto. Kowa sai ya hau ce mata happy birthday. Daɗi da farin ciki suka yi mata yawa kawai sai ta nufi mijinta ta rungume shi, “Thank you Husband.”

Da hannu ya nuna mata ‘yar babyn me kama da mage, “Kin ga Gift ɗin da mijinki ya kawo maki. Yi maza ki ɗauka ki zo ki godewa mijinki.” Duk da tana tsoron magen hakan bai hana ta tunkararsa ba. Tana ɗaukewa ta ware idanu. Wani ƙaton Cake ne me tambarin Heart. Anyi masa ado me kyau da ɗaukar idanu. A gefensa kuma wata sarƙa ce da ɗankunne da zobe masu matukar kyau na Gold. Sai ɗaukar idanu suke.

Dawowa tayi ta rungume shi sai hawaye. Ɗan yatsansa ya sanya ya ɗauke hawayen.

Maman Anwar ta ce, “Oh Walh gani nake yi yanzu babu soyayya sai zaman haƙuri. Ashe ba haka abin yake ba? Ita dai ta dace Walh.” Nuhu yana jinta ya yi banza da ita.

Ahmed ya jawo hannunta har zuwa gaban Cake ɗin. Anyi rubutu kamar haka AHNAL sunan ya burgeta ta zaro idanu ta juyo tana fuskantarsa, “Wow Husby sunana da sunanka aka haɗa? Ana nufin Ah..” Kasa faɗin sunan tayi kasancewar bata taba kira ba, ta rufe fuskarta da tafukan hannunta. Hannayensa yasa ya bude mata idanun yana kallonta, “Meenal. Bude idanunki ki karasa. Kira sunana yau ko sau daya ne zai gamsar da ni. Duk hanyar da zan bi don inga kin kirani da Ahmed abin ya faskara. Yau ina hada ki da Allah ki kira sunana, zaki sa ni a cikin farin ciki mara yankewa.”

Meenal ta bude idanunta a hankali ta ce, “Ah… Ah…” Girgiza kanta tayi rufe idanun hawaye suka biyo baya ta yi magana me kama da rad’a
“I Can’t. “

Girgiza kai ya yi ya dauki dankunnen ya makala mata ya dauki abin hannun ya makala mata, har zuwa sarka da zobe. Sun yi mata kyau sosai. Haka babu kwalliya a fuskarta akayi ta daukar hotunan. Dama ita Meenal bata kwalliya. Ahmad ya yanko Cake din ya sa mata abaki ta ciro ragowan na bakinta ta sa masa.

Haka suka yi ta daukar hotuna har da su Maman Anwar. Sai yamma likis suka tafi. Meenal ta tasa Cake dinnan a gabanta tana ci suna hira. Mamakin shan zakin yarinyar kawai yake yi. Baya son ta kula ya mayar da hankalinsa akanta dan yasan sai ta cusa masa Cake din ko baya so.

Kamar ta shiga zuciyarsa kawai ta mike da Cake din kato a hannunta ta nufo bakinsa. Rike ciki ya yi ya ce “Wash!” A rude ta zubar da Cake din ta tallabo fuskarsa. Kashe mata ido ya yi yana murmushi. Ta turo bakinta, “Kana son tsokana ta ko? To zo muje muyi wasan buya.” Ware idanunsa ya yi, “Meenal ke da zaki ce inzo mu je mu kwanta tunda mun gaji?”

Noke kafada tayi, “Ni dai a’a kawai ka zo mu je.” Rigimar Meenal yana damunsa. Dole ya tashi yana biye mata. Ita kullum kawai ayi ta wasa. Ga dare ya yi kuma ruwan sama ake shekawa. Kafin ya ankare ta fice waje da gudu bayan ta sami nasarar daukar ball. Yarinyar bata tsoron dare sam!

Kwala mata kira yake yi amma ina.. A matukar tsorace ya mara mata baya yana fadin, “Meenal! Meenal!!” Shuru babu kowa sai karar ruwan sama. Juye-juye yake yi yana faman nemanta. Gabansa yana fadi da karfi. “Meenal!” Ya sake kwada mata kira.

Daga can wajen wani bishiya ta ce, “Na’am Husby zo ka ganni anan.” Cikin sauri ya karasa inda take, amma sai ta hau guje-guje. Tana cikin nishadi fiye da tunaninsa. Kamo ta ya yi ya dauke ta ya kafe ta da idanu ruwan yana sauka akan su. “Ina son ki Meenal. Ina son komai naki. Kiyi min alkawari kome rintsi kina tare da ni.”

Hannayenta tasa da suke digan ruwa ta shafi tattausan gashin kansa har zuwa sajen fuskarsa. “Nayi alkawari duk rintsi ina tare da kai. Ka yafe min bata maka da nayi ba zan sake yi maka ko da musu ba.” Ta cigaba da shafar fuskarsa, “Sauke ni inyi tafiya da kafafuna.”

Sauketa ya yi, har sun kusa shiga daki ya juyo ya hango Ball din a can ta sake shi. “Meenal zo nan ki dauko ball din can.” Langwabewa tayi, “Wash kafafuna kaje ka dauko.” Idanu ya zaro, “Wa ya ce ki kai shi wurin? Ki wuce ki je ki dauka tun kafin inzane maki jiki.”

Tana tafiya tana tsalle-tsallenta. Yau ya ci burin zai karbi hakkinsa, ba zai yarda da ya kashe kansa ba. Duk da baya son karya alkawarinsa amma yau sha’awar Meenal ta kai shi matsayin da ba zai iya jurewa ba. Kullum da sabon salon da take yi masa na sabon soyayya.

Kamar ance ya daga kansa ya hango wani mutum fuskarsa a rufe ya saita Meenal da bindiga. Hankalinsa ya yi masifar tashi. Dawo da kallonsa ya yi ga Meenal da take ta tsalle-tsalle sunkuyawa tayi da nufin daukar kwallon. Dr. Bakori ya kwala mata kira bai san lokacin da ya isa gareta ba gaba daya ya mayar da ita bayansa. A lokacin aka ci nasarar harbinsa har sau biyu. Jini ya fallatso mata a fuska.

Meenal ta daga kai ta dubi inda ta ji karar harbin tuni mai harbin ya bi ta kansa. Gidan akwai tazara sosai tsakanin su da Gate shiyasa ba kasafai zaka yi abu aji ba. Haka Dr Bakori shi ya mayar da masu gadin can gate kawai.

Meenal tayi mutuwar tsaye jinin Ahmed ta dinga shafowa a fuskarta. “Ahmaddd!!!!” Bata san lokacin da ta kwala masa kira da karfin gaske ba.

Fuskarsa ta tallabo jikinta na rawa, da kyar ya iya hada kalmomi ya gaya mata, “Meenal ki bar gidan nan. Ki cewa Hajiya su yafe min. Idan baki bar gidan nan ba za su kasheki.”

Kalmar shahada ya dinga nanatawa har ya cika. Meenal tana nan zaune ita ba matacciya ba ita ba rayayya ba. Ankashe Ahmad dinta a gabanta?

Wani irin marayan kuka ta ji ya taho mata. Ta dinga taba wuyansa tana girgizawa. Wani karfi ta ji ya zo mata ta mike tayi cikin gidan da gudu, ta kwaso wasu abubuwa ta zuba a mota. Ta sake dawowa yana nan kwance cikin jini. Sai yanzu ta sake fahimtar Ahmad dinta ne a kwance cikin jini. Kuka ta fasa me karfi tana jijjiga shi, “Ka tashi!” Bakinta na rawa take shafan jinin jikinsa tana nuna shi. Gaba daya dabara ta kare mata. Tunda take ganin tashin hankali da idanunta bata taba ganin irin na yau ba. Da gudu ta kama hanyar gate tana numfarfashi. Usman Mai gadi ta ci karo da shi tun kafin ta isa gate din, take faɗin, “Sun kashe shi.” Abinda kawai ta iya furtawa kenan ta rushe da wani irin kuka. Shi kansa ya ruɗe sai tambayarta yake su wa?

Da hannu kawai take nuna masa hanyar. Ta tashi ta kuma kwasawa da gudu ta nufi Ahmad. Usman da yaga danyen aikin nan ya sa hannu akai. Hadiye kukan tayi ta ce, “Ka taimaka ka sa min shi a mota zan kai shi asibiti.”

Taɓa shi ya yi ya ce “Hajiya ai ya rasu. Kuma ya za ayi ki iya tuki.” A rude take dan haka ta dinga shafo jinin jikin Ahmed tana girgiza kai, “A mota zaka sa min shi zan iya a mota eh a mota.”

Usman ya taimaka mata aka sanya Ahmad a bayan motarsa Meenal babu ko takalmi ta tayar da motar a matukar rude. Wani irin tuki take yi na ganganci. Bata san hanyar Abuja ba, ga dare ya yi gashi ana ta ruwan sama. Sai zagaye titunan take yi bata san inda zata je ba. Kauyen da suka kwana ya fado mata a rai sai dai kuma ba zata iya saita kanta a hanyar komawa Kaduna ba. Parking tayi ta rusa kuka me karfi. Fitowa tayi daga motar tana rusa kuka.

Wasu ‘yan iska suka yo kanta suka rike ta suna son yi mata fyad’e. Gudu take yi suna binta. Har tayi nisa ta tuna Ahmad dinta ne a cikin mota. Dawowa tayi ta tsaya masu kawai tana kuka. Wani katon sanda ta gani hakan yasa ta zaro kawai tayi kansu kamar mahaukaciya. Tuni suka bace suna yi mata kallon sabuwar hauka ce. Cikin motar ta koma ta sake tayar da motar tana surutai ita kadai, “Husband kada ka damu kaji? You will be ok. Zan samu wuri ingyara ka mu cigaba da rayuwarmu.” Tana maganar tana kuka.

Idan abin ya ciyo ta ta bugi sitiyarin motar da karfi ta ce, “Alhamdulillah Alhamdulillah. Allah na gode maka da wannan jarabawa. Ni musulma ce me cikakken imani. Ni ba kowa ba ce. Allah na gode maka a yadda kayo ni. Ahmad ka tashi kaji sunanka a bakina.”

Kuka me karfi ya kwace mata ta taka birki da karfi sakamakon wani babban mota da saura kiris ta buga masa. Sai dai tana kaucewa babban motar ta bugawa wata karama. Gaban motar ta sami matsala amma sai ta koma baya ta kauce kawai ta cigaba da diban gudu a titi tana fadin, ” Alhamdulillah. Ahmad dina nasan kana cikin koshin lafiya. Idan ka mutu nasan kana Aljannah.”

Tari me karfi ya taho mata hade da wani gudan jini. Goge bakinta tayi da jini ya gama batawa tana girgiza kai, “Jininka na gani da idanuna? Sun kashe ka. Jinin Ahmad dina? Mijina Ahmad jininsa a jikina jininsa a fuskata jininsa…” Kirjinta ta rike da karfi tana karanto addu’ar da duk ta zo bakinta. Haka bakinta bai fasa godewa Allah ba da irin iftila’in da take gani tun samun cikinta.

A can gidan kuwa tana fita ‘yan daban da mahaifinta ya aiko suka sake dawowa domin kashe Meenal tunda sun kashe Ahmad din. Don cewa akayi kada a barsu da rai. Suna dawowa duban duniyar nan sun yi babu Meenal babu gawan Ahmad. Wannan lamari ya tashi hankalin Hon Munnir kwarai da gaske.
Maman Anwar ta ɗora waya a kunne tana wayar ƙarya, “Eh Wallahi baki ga soyayya ba, kamar indiyawa. Ni mamakin da nake yi dama ana soyayya irin haka?

Namiji ya yi ta rawan jiki da mace ko a gaban waye? A’a kinsan wasu mazan hotiho ne, basu iya komai ba sai latsa waya, da iya ɗaure fuska kamar wa’inda akayiwa mutuwa, sai dare ya yi kiji ana lalubanki ana kwance zane.” Kashe wayar tayi ta bugi cinyoyinta, “Kai Wallahi da sake. Nuhu dole fa mu sauya irin wannan rayuwar tamu, dan muma mu mori ƙuruciyar mu.
Abubuwan matarsa sun fara bashi tsoro, ya santa da sa ido, amma bai san abin ya yi nisa haka ba. “Nuhu kai tsaye? Ko baki kula a cikin salon soyayyarsu har roƙonta mijin keyi akan ta kira sunansa ba? Har hawaye ta fitar saboda ba zata iya kiran sunan ba.” Sosa kanta tayi, ita kanta abin ya bata sha’awa. Sai dai kuma ita tana da wahalar kuka ne. Halin su ɗaya da ƙawarta Bingel, da wahala ka ga hawayen su.

Matsowa tayi kusa da shi tana ɗan sosa kai, “To nikam Baban Anwar, ko irin wasannin nan mu ɗinga yi mana, na guje-guje.” dubanta ya yi kamar kayan wanki, ya murɗe fuska, “Kin ga Yahanasu ki kiyayeni. Bana son shirman banza!

Tun da can baki san da guje-gujen ba sai yanzu? Kuma a hakan ake guje-guje? Ai sai mace tana ƙamshi ne, tana sanya kayan da za su burgeka. Haka ita mace ita tasan yadda take yiwa mijinta har ya ji ta burge shi zai iya biyewa shirmanta. Ita mace a gaban mijinta zamowa take yi wawuya bata san ma me take yi ba. Amma ke shegen wayonki yaushe zai barki?”

Kwanciya ya yi a doguwar kujera yana jin baƙin cikin Maman Anwar a zuciyarsa. Ita kuwa wasannin nan sun burgeta. Tunaninta kawai ta ƙirƙiri Birthday ƙila itama ta samo kansa ta wannan hanyar. Wanka tayi tasa wani riga da siket da ta siyo a gwanjo tun wani zuwa da tayi gidan Bingel suka shiga ‘yan gwanjo. Idan ba zata manta ba Bingel da kanta ta samo mata burgujejen siket ɗin ta ce zai yi mata kyau. Ko wankewa bata yi ba, ta zura a jikinta, tasa turare mai tsananin ƙarfi da hawa kai, ita a dole yau sai ta zama Meenal.
Yana kwance ya ji takun abu da gudu, hakan yasa ya ɗago kai a tsorace yana son ganin menene haka? Maman Anwar ya gani, abin har ya so ya bashi dariya. Yadda ta zaune shi, sai da ya rintse idanunsa. Warin gwanjon da turaren suka buge shi, har maƙogoro. A fusace ya miƙe, kamar zai rufe ta da duka, “Amma dai Maman Anwar kinsha wani abu ne ko? Meyasa kike haka ne? Ke ni na fi sonki a yadda kike da, don Allah kada ki ce zaki ɗauko kwaikwayo ki jawo min ciwon kai.”

Miƙewa ya yi, abin nan ya yi mata ciwo ƙwarai. Komawa ɗakin tayi ta dubi kanta a madubi, ta liliyo wani ashar, “Kan ubancan! Ni Bingel zata wulaƙanta? Wannan wani irin siket ne haka? Ko dai gatse tayi min ni kuma na ɗauka da gaske take?” Shuru tayi ta sake fitowa tana kallon ƙirjin mijinta babu ko alamun gashin nan da maza ke bari me kyau.

“Baban Anwar ni sai inyi ta jin takaicin ko ɗan gashin nan na ƙirji baka da shi. Kwantancen sajen ma babu, bare gashin kai insami abin wasa da shi.” Taɓe bakinsa ya yi, “Zaki ji da shi ai. Ki sauya tsari wannan tsarin naki bai bani sha’awa ba bai kuma birgeni ba.”
Shuru ta yi can ta ce, “Jibi Birthday ɗina.” Harara ya sakar mata ya cigaba da danna wayarsa.

Sallama suka ji, ya tashi ya buɗe. Abinda Usman ya gaya masa ya rikita shi fiye da tunaninsa. A gigice yake yi wa Usman faɗa, “Baka da hankali ne zaka barta ta fita? Meyasa baka kirani ba? Yanzu ina ta je da Ahmed ɗin? Innalillahi wa inna ilaihirraji un.” Ita kanta Maman Anwar ta gigice. Usman kawai yasa kai ya fice domin fara duba asibitoci.

<< Meenal 16Meenal 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×