“Idan kika yi addu’a ciwon nan naki zai dinga raguwa.” Kalamansa kawai take tunawa. Goge hawayenta tayi ta ci gaba da tuƙin da bata san inda ta nufa ba. Cusa motar tayi a hanyar daji, sannan ta kashe motar, ta fito ta zagaya bayan motar ta shige. “Ahmad! Ka taimakeni ka tashi kaji? Wallahi baka mutu ba, baka mutu ba Ahmad.” Kayayyakin da ta ɗibo ta ciro ta kunna wutan cikin motar. Duk da hakan bata gani, ta hau hargitsa cikin motar, sai ga tocila, cikin sauri ta ɗauka ta haska. A kafaɗa suka harbe shi, ɗayan harbin kuma a cinya. Rigar jikinsa ta cire, sai ga bullet ɗin tana iya hango shi hakan ya nuna mata bai shiga yadda ya kamata ba.
Ɗan almakashin ta ɗauka ta yi kamar zata kai ta cire, sai kuma ta kasa. Cikin dauriya hannunta na rawa, ta tura almakashin sannan ta zaro. Motsi ta ga ya yi, hakan yasa ta ƙanƙame shi tana dariya me ɗauke da hawaye,
“Nasan baka mutu ba, don Allah ka tashi kaji? Ka tashi mijina gani kusa da kai buɗe idanunka ka gani nice.” Shuru bai sake motsin ba, don haka ta yaga wandonsa, dai-dai inda taga hujin bullet ɗin. Da zarar zata cire sai ta tuna lokacin da yake gyara mata hannunta, da zarar ta ɗan yi ƙara sai ya daina ya rungumeta yana lallashi. Da ƙyar ta iya ciro shi. Sannan tasa auduga ta toshe wurin. Ta rungume shi tana faɗin, “Da zafi ko? Sorry daga wannan shikenan ka ji? Kansa ta ɗora a cinyoyinta, tana karanto addu’a tana tofa masa.
Idan aka ce barci ɓarawo ne yasan wanda yake sacewa, amma ba irin su Meenal ba. Tana nan zaune tana shafa kansa, faɗi take “Zaka ji sauƙi zaka tashi, zamu cigaba da rayuwa tare.” Kuka mai ƙarfi ya ƙara yunƙuro mata. Tana kallon kanta ita ce a zaune a dokan daji daga ita sai Ahmed ɗinta. Mutumin da baya iya barci sai ya tabbatar da ya lallaɓata ta fara yi.
Shafo wuyansa tayi, ta ce “Ka tashi. Idan ka zama gurgu ni zan zama ‘yar jagoranka har inmutu zan kasance a ƙarƙashin bauta maka. Bana son ƙafafunka, bana son komai naka, sai numfashinka. Inganka kana numfashi kaɗai ya isa ya gamsar da ni. Ka tashi zan baka kulawa fiye da kaina, zan soka fiye da irin son da nake yi wa kaina. Kayi numfashi kawai ya gamsar da ni.
Idan kuma mutuwa kayi Ahmad Wallahi ba zan bayar da gawanka ba, zan ɗinga kula da gawanka, har nima in mutu. Ba zan bari Gawanka ta lalace ba. Gangar jikinka zai kasance a ƙarƙashin kulawa ta.”
Surutai take yi babu kai, idan tayi-tayi sai ta rushe da kuka. Hawaye yayi mata kaca-kaca.
Har asuba tayi tana jin ƙarar motoci Meenal bata daina kuka ba. Idanun nan sun kumbura sunyi jajir. Fitowa tayi ta gyara masa kwanciyarsa, sannan ta kama hanya. Wani mai napep ta gani ta roƙe shi ya nuna mata hanyar da zata bi ta kama hanyar Kaduna. Ya nuna mata kawai ta saita hancin motar. Gudu kawai take shararawa, har ta kawo ɗan hanyar da ta kai su gun bafullatani. Cusa kan motar kawai tayi cikin hanyar da bata da tabbas idan mota tana bi.
A kofar bukkan taja burki ta fito da gudu tana bubbuga ƙyauren bukkan. Bafullatani ya fito yana miƙa.
Ganin Meenal yasa ya haɗe rai, “Kun shake zuwa ko? Aradun Allah ba zan baku masauƙi ba, ina sane da duk ishkancin da kuke yi ke da mijinki wanda baya dariya.” Sai yanzu ya kula da irin kukan da Meenal take yi, bayan ya sauke maganarsa, “Ya mutu ko?” Maganar ma ta kasa fita, sai nuna masa mota kawai take yi. Bafullatani ya ƙarasa motar yana leƙe, “Kayyasa! Yarinya me yasha zaki kawo min mushe nan? Ai ya mutu wannan. Bari inkira jauro ya taimaka akaishi ayi mashi Sallah.”
Meenal ta shaƙe shi idanu a warwarje, “Idan ka sake kiran Ahmed ɗina da mushe sai na datse rayuwarka. Ka taimakeni ka bani aron ɗaki zan biyaka ko nawa ne.” Ɗanfillo da ya ji shaƙa, ya hau buɗe haƙora, “To shakeni intaimaka.” Tana sakinsa ya zura da gudun gaske yana haki. “Allah ya ishar min.” Meenal ta zube a ƙasa tana rusa kuka tana roƙon ɗanfillo ya dawo. Da ƙyar dai ya dawo suka fitar da Ahmed zuwa ɗakin da ya taɓa ajiye su.
Abubuwan da suka faru a ɗakin suka dawo mata sabo. Tsurawa inda ya zauna ita tana kwance a jikinsa ido tayi, tana goge hawayenta. Yadda suka kwantar da shi haka yake baya ko motsi. “Ka taimakeni inkai shi asibiti, dole yana buƙatan ƙarin jini. Ahmad yana da rai bai mutu ba.”
Ɗanfillo ya girgiza kai cike da tausayawa, “Bari inshiga daji zankawo magani ba shai Anƙara mashi jini ba.” Gyaɗa kanta kawai tayi ba tare da ta iya cewa uffan ba. Tana nan zaune ta kafe shi da idanu kamar ta kira sunansa ya amsa.
Lado ya dawo hannunsa ɗauke da uban ganye. Meenal ta shafi kan Ahmad ta fito jikinta yana rawa, ta taimakawa Ɗan fillo wajen gyara maganin, aka zuba a tukunya. Ya dubeta ya ce, “Ki zo mu je mu samo iccen da za a dafa magani.” Babu musu ta shiga bin bayansa ƙafafunta babu ko takalmi. Karare suka samo suka dawo.
Bata iya haɗa murhu ba, amma a ranar ta koya. Idan kaji kana cewa baka iya abu ba, bai kama ka bane. Tana nan zaune a gaban maganin ta ƙosa ya tafasa.
Juyewa tayi jikinta na kyarma, suka shigo ɗakin ita da Lado yana ƙoƙarin tayar da kansa, ta share hawayenta ta ce, “Kayi masa a hankali dan Allah.” Lado ya yi banza da ita ya yi ƙoƙarin ganin sai Ahmed yasha maganin, dubansa tayi ta ce,
“Mutumin da baya motsi ta yaya zai iya shan magani?” Lado ya ce, “Kinfi ni gashkiya aradun Allah.” Mayar da shi ya yi ya buɗe inda ciwon yake ya ɗinga tsoma wani tsumma a maganin yana cirewa yana mannawa a wurin da aka harbe shi. Kowani mannawa ɗaya sai jikin Ahmad ya girgiza.
Ko a haka aka barta ta gode Allah. Lado ya nuna mata yadda zata ɗinga yi, ya ce za su je ganin gida ne, amma saboda ita kwana biyu kawai zai yi ya dawo. Babu wata damuwa a tattare da ita, tunda tana tare da Ahmad ɗinta. Ya kuma gaya mata za a ɗinga aiko mata da tuwo a gidan abokinsa.
Shuru tayi ta kafe Lado da idanu har ya ɓacewa ganinta. Hawaye ta sharce tana tunanin kai shi asibiti, amma ta ina zata fara? Waye zai taimaka mata?
Haka Meenal ta wuni da dafa magani tana mannawa a wurin ciwukan. Daga baya dabara ta faɗo mata ta koma sa yatsanta a cikin maganin sai ta sa masa a baki.
Duhu ya fara yi ta ɗauko fitilan da Lado ya bar mata ta kunna. Tagumi tayi ta zuba masa idanu. Wani yaro ya yi Sallama da baƙin tuwonsa ya miƙa mata. Jikinta yana rawa ta ɗinga ci babu ko alamun daɗi. Tana gama ci ta ruga ta amayar da shi saboda ƙarni da yake mata.
Dafe cikinta tayi tana kuka. Haka ta koma kusa da shi ta mayar da kansa cinyoyinta ta ɗaga kanta sama hawaye na bin idanunta. “Allah ka tashi kafaɗun Ahmad.
Kamar daga sama ta ji muryar Lado yana faɗin, “Ke baki da hankali ne? Kina kwana da gawa baki sani ba? Ko baki jin warin da gawan yake yi ne? Ya zama dole kiyi haƙuri ki bada shi ayi masa Sallah.”
Meenal ta gigice iya gigicewa ta miƙe tana jijjiga Ahmad. Da gaske Ahmad warin gawa yake yi, amma Meenal bata ankare ba. Har yanzu da ake maganar nan Meenal bata jin warin gawan da ake faɗa.
Lado yaje ya haɗo jama’a. Meenal tana ji tana gani wasu mata suka rabata da gawan Ahmad. Kuka take yi tana girgiza kai. Ta kasa magana kawai sai hawaye da ke fita daga idanunta babu ƙaƙƙautawa.
Kafin wani lokaci har angama shirya shi tsaf. Lado ya leƙo ya ce taje tayi masa addu’a za a kai shi makwancinsa. Meenal tana ganin kamar wasa, sai da taje gata ga gawan Ahmad a shimfiɗe.
Sunkuyawa tayi takai bakinta tana tofa masa addu’a. Ƙirjinta ta riƙe da ƙarfi tana fitar da numfashi da ƙyar. Duk wanda ya shiga rayuwarta sai ta sa shi a matsala. Da Ahmad bai haɗu da ita ba da yanzu yana rayuwarsa a cikin danginsa.
Tana kallo aka kawo makara aka ɗora shi. Girgiza kai take yi a lokacin da mutane ƙalilan suke yi masa Sallah. Ta riga ta cuci Ahmad da har ta bari mutane ƙalilan suke rakiyarsa. Mutum me jama’a shi ne yau yake kwance mutane ƙalilan suke Sallatan gawansa. Tana durƙushe tana miƙa hannu amma ina. Tana ji tana gani aka rabata da mijinta. Tana ji tana gani aka haƙa rami aka rufe shi.
Lado da dawowarsa kenan daga maƙabarta idanunsa sunyi jazir saboda kuka, “Kinyi asarar mutumin kirki mai son addini kamar mijinki. Allah ya jiƙan Ahmad.” Meenal ta rushe da kuka ta kwanta a cikin ƙasan nan tana birgima. Wani irin tari take yi kamar wacce ake shirin zarewa numfashi. A hankali ta fara rasa dukkan natsuwarta. Rigarsa ta kaiwa duba da aka cire shi a jikinsa duk jini. Abubuwan rayuwarsu ya ɗinga tunowa wanda har ta koma ga Mahaliccinta ba zata taɓa mance su ba. Kullu nafsin za’ikatul maut. Da sannu Dukkan wani rai sai ya ɗanɗani ɗacin mutuwarsa. Haƙiƙa mutuwar Ahmad babban tashin hankali ne ga iyayensa da mutanen gari. Ta yaya zata iya tunkararsu da faɗin ɗan su ya mutu? Wani kuka ya sake ƙwace mata. Girgiza kanta kawai take yi hawaye na sauka da majina.
Tana kallon yadda Lado yake kuka, wanda bai taɓa rayuwa da shi ba kenan sai na kwana ɗaya? Ina ga ita da ke kwana tana tashi da shi?
Anan take ta yanke jiki ta faɗi cikin ƙasan nan bata motsi. Hankalin Lado ya kai matuƙa a tashi. Yana kallon masifu kala-kala. Tsoro ya shige shi kada ayi ta tara masa gawauwaki.
Firgigit! Tayi ta farka daga ɗan barcin da ya kwasheta. Hakan ya sake ruɗata ta shiga shinshinar Ahmad ko zata ji warin gawan da ake faɗi a cikin mafarkinta. Tashi tayi ta sake fita waje a lokacin sha biyun dare. Wuta ta sake kunnawa ta tafasa maganin ta dawo ciki ta ɗinga ɗiga masa a baki. Ganin kamar yana motsi ta ɗaga hannayenta sama tana godiya ga Allah. Sai yanzu ta tuna ashe tun jiya rabonta da Sallah. A gaggauce ta tashi babu ko tsoro ta nufi motar su ta ɗauko dadduma da wata doguwar rigarsa kasancewar yana yawan ajiye tarkacen kayansa a mota ta ɗauko ta dawo tayi Alwala. Da doguwar rigar tayi Sallolinta. Ta jima tana addu’a sannan ta sake komawa ta gasa masa cinyar da hannun. Tana nan zaune da taji zata fara gyangyaɗi sai ta buɗe idanun.
Meenal tasha matuƙar wahala kafin gari ya waye. Amma ita hakan ya fiye mata da ace ta rasa shi gaba ɗaya. Ta amince ta dauwama a hakan indai babu me rabata da Ahmad ɗinta.
Ruwa ta samu ta goge masa jikinsa ta ɗauko farar vest ɗin da ta gani a motar ta sa masa yadda zai ji daɗin jikinsa.
Can daji ta shiga tana tafe ta taka wani abu ya fasa mata ƙafa ta fasa ƙara ta zubar da kararen da ta samo ta zauna tana duba kafafun da jini ya fara zuba. Rintse idanunta tayi, saboda azaba. Tana tunawa da Ahmad ta miƙe tana jin azaban haka ta kwaso kararen ta dawo. Da ƙyar ta iya hura wutan ta zauna tana jiran ya tafasa. Tana ɗingisawa ta shiga ta fara sa masa a baki kamar yadda take yi sannan ta shiga gasa masa cinyar. Motsa ƙafafunsa ya yi sannan ya motsa hannunsa. Tuni ta mance da wani ciwo da ke mata zafi ta kama hannayensa tana dariya hawaye na sauka, “Alhamdulillah Alhamdulillah. Idan na gode maka sai ka ƙara min. Allah na gode maka. Allah ka hanani butulce maka. Allah ka ba mijina lafiya.” Hannunsa ta kama takai wuyanta zuwa bakinta yadda yake yi mata idan yana son ya sanyata cikin fara’a. “Yadda ka faranta min Yayana Allah ya faranta maka.” Bakinsa yake motsawa hakan yasa ta ɗago kansa ta kafa masa ƙoƙon nan a baki. Rabi ya shiga cikinsa rabi ya zube. Hakan yasa ya hau tari. Farin ciki yasa kawai sai dariya take yi ta rasa bakin magana sai dariya.
Duk maganin da yasha ya amayar. Ta kwantar da shi ta samo ruwa ta goge masa jiki ta cire masa vest ɗin ta wanke ta shanya. Ta ɗinga yi masa firfita.
Farin ciki yasa ta ɗinga zubar da hawaye. Macen da bata iya kallonsa sai gashi yau ita ke yi masa komai. Ta rasa me zata bashi ya ci? Tashi tayi bayan ta tsaftace masa jiki ta shiga motarsa tana dube-dube. ‘Yan canji ta gani wanda ‘yan dari dari da dari bibbiyu wanda idan ya siya abu anbashi canji sai ya zube su a wurin.
Kwashewa tayi ta fice. Sai da tayi tafiya mai nisa babu ko takalmi tana tafe tana ɗingisawa. Duk inda ta wuce sai fulanin nan sun bita da kallo. Har ta isa inda ake siyar da rake da lemu mai ɓawo. Ta siya tana tafe tana rintse idanu saboda zafi.
Tana isowa ta kunna wuta ta sake bashi maganin. Sannan ta ɓare lemun tana zuba masa ruwan a baki. Haka ruwan raken idan tasa a bakinta ta taune sai ta hada bakin su wuri guda ta zuba masa ruwan raken.
Tana kallo numfashinsa ya daidaita sai dai bai taɓa bude idanunsa ba.
Ficewa tayi ta samo ganye masu yawa ta tuttura masa a gefe da gefen inda yake kwance gudun kada yawan kwanciyar da yake yi ya yi masa illa. Itama a wani film ta gani.
Meenal kenan a kwana biyu kawai ta sauya kama, ta koma kamar mahaukaciya. Hatta ‘yan yankin sun fita kyan gani. Gari na wayewa tana idar da Sallah zata zauna a gabansa ta gaishe shi sannan ta fara magana kamar mai wa’azi, “Husby mu godewa Allah a duk irin halin da muka tsinci kanmu. Idan muka gode masa sai ya ƙara mana. Ina son ka zama me tawakkali akan dukkan lamuran mu. Ga Meenal ɗinka a gefenka cikin farin cikin kasancewa tare da kai. Idan kowa ya ce baya son Meenal idan har Yayanta yana sonta duk sauran shirme ne. Insha Allahu zaka ji sauƙi zamu yi rayuwa mai daɗi.”
Tana gama kalaman zata sa kuka. Tuwon da ake kawo mata tun tana ci tana amai har ta koma ta haƙura. Ruwan goran da ta ɗauko a motarsa ta buɗe tayi addu’a masu yawa ta tofa a cikin ruwan. Kullum da safe kafin ta bashi lemun zaƙin sai ta fara bashi ruwan addu’o’in. Tana bashi tana shafe masa a fuska. Haka idan dare yayi ƙa’ida ne sai tayi masa addu’a ta tofa masa.
Da daddare tana zaune a bakin murhun kamar ance ta juya taga ƙaton maciji ya fasa kai yana son shiga gurin Ahmad. Girgiza kai tayi, duk yadda take da tsoro a ranar ta nemi tsoron ta rasa. Ƙaton addan Lado ta ɗauka tayi kan macijin nan. Sai da tayi Bismillah sannan ta sara shi biyu. Tana huci, “Waye kai da zaka taɓa min Ahmad?” Da gudu ta shiga gurin Ahmad tana tattaɓa jikinsa. Rungume shi tayi tana magana cikin hawaye, “Ba zan sake barin wani ya cutar min da kai ba. Meyasa baka bari anharbeni ba? Na tabbata da ni aka harfa da ba nan wurin zaka kawo ni ba. Da ka bani kulawa da kanka. Da yanzu ina ɗaki mai AC kana tarairayata. Bansan meyasa na kawo ka nan ba. Ina tsoro Yayana kada inkaika cikin gari su sake biyo mu. Don Allah ka tashi kayi min magana.”
Motsawa ya yi wanda yasa ta dakata da maganar da take yi ta ɗago tana dubansa.