Skip to content
Part 20 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Na sadaukar da labarin nan agun duk wata ‘ya mace mai biyayyan aure. Mai daukar aure ibada hanyar shiga Aljannah.
Da isowarsu suka sami jami’an tsaro da motar asibiti suna jiran su. Meenal ya duba cikin sanyin jiki, hakan yasa ta aika masa da murmushi. A cikin mota tana langwabe a jikinsa, ta dube shi ta ce, “Insha Allahu matsalolin mu sun kusa zuwa karshe. Kuma muna isowa lafiyarka za’a fara dubawa kafin aje kan kowa.”

Shafo kanta ya yi ya ce, “Yau ina son inkwanta kusa da matata, tana bani labari me daɗi. Na jima ban sami irin kulawan nan ba, bai kamata ina zuwa in tafi asibiti su kwantar da ni ba.” Shuru tayi bata ce komai ba.
Masauƙi suka fara isowa, wanda yasa Meenal nuna tsantsar farin cikinta da wurin da suka sauka, musamman da taga akwai kayan wasanni da motsa jiki. Suna shiga ta ruga da gudu ta ɗauki ƙwallo, sai kawai abinda ya faru ya dawo mata, sai gani take yi kamar za’a a sake harbin Ahmad, ta fasa ƙara, tare da rintse ido.

“Meenal zo nan.” Abinda ya iya gaya mata kenan. Tana zuwa ya haɗeta da ƙirjinsa, yana maimaita mata karatun da idan hadda ce ya kamata ace ta gama haddacewa. Hure masa idanu tayi, zararan giransa suka rufe tare da idanunsa luf. A hankali ta furta, “Kana da kyau mijina. A cikin mazaje miliyan bana jin za a sami namiji mai kyawunka. Kyan hali, kyan zuciya.” A hankali ta ƙarashe maganar kamar mai tsoron wani ya ji, “Tausayi shi ya zama jigon zamanka gwarzon jarumi. Zan yi ta amfani da kalaman bakina har su ƙare ina yabon kyawawan halayyarka mijina.”

Hawaye suka kwararo daga idanunta, tana tuna shi ne mutum na farko da ya fara sawa ta daina tsanar maza. Ada tana tunanin duk halayyarsu guda ce. Sai gashi Allah ya nuna mata ikonsa, ya nuna mata ya halicci bayinsa, a mutane masu halayya mabambanta. Kamar yadda zanen tafukan hannayenmu ba iri ɗaya bane, kowa da irin nasa.
Idanu ya zuba mata ba tare da ya iya furta komai ba. Baya son ya gaya mata hutun kwana ɗaya kawai zai yi sannan ya shiga aikin mutumin da har yanzu bai san ko waye shi ba. Duk da Peter ya yi ta masa naci a fara duba ƙafafunsa, tukunna kafin shiga aikin, ya nuna masu babu komai zai iya indai suna gefensa. Haka ya so ayi aikin tare da Meenal, kasancewar bata fara shan maganinta da wuri ba yasa za a ɗan jinkirta.

Yana daga kwance duk inda tabi sai ya zura mata idanu. Har ta kammala kwalliyarta. Falo ta koma ta ɗiban masa kayan marmari, ta dawo kusa da shi.

“Tashi inbaka kayan marmari.” Lumshe idanu ya yi ba tare da yunƙura ba. A hankali ta gutsiri ayaban, sannan ta kwanto ta manna masa a bakin. Shuru suka yi cikin wani yanayi mai wahalar fassarawa. Daga ita har shi jikinsu rawa yake yi.

Yana gab da amsar haƙƙinsa, wani tunani ya dakatar shi. Ita kanta ta gama tsorata jikinta sai rawa yake yi, jin shurun yasa ta ɗago tana dubansa. Riƙe cikinsa ya yi da ƙarfi yana ajiyar numfashi.
Bata san lokacin da ta wartsake ba, ta ɗago idanunsa da suka sauya launi zuwa ja, ta kafe shi da idanu. Kafin wani lokaci ta fara tsiyayar hawaye. Tallabo shi tayi tana dubansa cikin damuwa, “Husband! Dama saboda ni kake ciwon ciki? Dama ina da maganin damuwarka? Na daɗe ina tunanin me yake saka ciwon nan? Na jima ina tuhumar kaina, sai gashi yau na ganewa idanuna. Allah zai kama ni da laifin cutar da kai. Ka gaya min dalilin kasa karɓar haƙƙinka tsawon wani lokaci kana fama da matsala.”

Yau yasan Meenal ba zata taɓa jin lallashi ba, don haka dabara ta ƙare masa. Kawai ya zuba mata idanu. “Ina magana kayi banza da ni ko?” Miƙewa ta yi fuu ta fice ta bar ɗakin. Rana ta farko a duniyarta da ta yi fushi da mijinta. Rana ta farko da take jin damuwar matakin da ta ɗauka.

Yau bashi da ninyar lallashinta, don haka ya lumshe ido da ninyar ya yi barci amma abu ya gagara. Ba zai taɓa iya barci da lafiyarsa babu Meenal a kusa ba. Haɗe kanta tayi da guiwa tana kukan tausayin mijinta. Shi kullum damuwarsa shi ne ya faranta mata. Garin faranta ranta yana son ya cuci kansa. A hankali ya lallaɓa da sandarsa ya iso inda take, “Waye ya gaya maki mata tana iya fushi da mijinta? Kina son kisha duka ko? Oya tashi ki koma gadon nan tun kafin in bubbuge ɗan bakin nan, mai iya zaro zance.”

Maganganunsa sun sanyata dariya, musamman yadda ya yi maganar cikin sigar lallashi.

Goge hawayen tayi zata yi magana, yasa dogon yatsansa yana zagaye laɓɓanta. “Zo mu je muyi hira ki bani labari. Amma banda shagwaɓa.” Buɗe fararen haƙoranta tayi alamun dariya, sannan suka koma kan luntsumemen gadon su, me tsananin taushi. Sun lume a cikin gadon kowanne da irin tunanin da yake. “Meyasa ka fasa auren Salma da Khadija?”

Tambayar tazo masa a wani iri, a lokacin da bai taɓa zata ba. Hannunsa ya tura a ƙasan mararta yana shafawa a hankali. Riƙe hannun tayi tana ƙyalƙyaltar dariya. Har abada Ahmad ba zai taɓa gajiya da kallon dariyar matarsa ba. Idan zata dauwama a haka, shi kuma zai dauwama yana dubanta, ba tare da ya gaji ba, haka zai dauwama a cikin farin ciki mara yankewa.

“Na fasa auren Salma, a lokacin da saura awa ɗaya a ɗaura auren, ina gidansu saƙo ya shigo min ta whatsapp ina buɗewa, naga Salma da wani mutum da kowa yasan sana’arsa bin maza da mata ta baya ne, sannan ga ƙarin bayani nan, a cikin takardar da ya ɗauki Salma ya kaita ayi mata aiki ta bayanta. Abubuwa dai, haka ga Video ɗin Salma nan a Asibiti ana dubata. Kaina ya kulle na shiga tashin hankali Meenal, na rasa ta yadda zan fara. Abin mamaki ina shigowa gidan, sai na ga Salma da mutumin nan suna magana ƙasa-ƙasa. Daga gani a ruɗe take, daga baya ta ɗinga leƙe, haka ta fice ba tare da kowa ya sani ba, ta same shi, bansan me suka yi ba, sai gata ta dawo. Tana ganina ta hau kame-kame nace daga ina take kawai ta ɗinga yi min ƙarya. Har ta koma cikin ƙawayenta ban san abin yi ba, sai da naga lokaci yana ƙurewa sannan na sanar da fasa aurenta.”
Meenal ta zaro idanu a matuƙar firgice. Abin ya tsorata ta, da wani ya bata labari ba zata yarda ba, saboda irin sanin da tayi wa Salma. Tura hannunsa ya yi a kanta yana sosawa yana lumshe idanu, kafin ya cigaba,

“Ita kuma Khadija na ɗauke ta mun je asibiti ana gobe ɗaurin aure, aka yi mana General check up da yake asibitin mu ne, ban sami result ba, sai da ana kusan minti arba’in a ɗaura aure aka tabbatar min da tana da h.i.v, haka a lokacin ne abokin mu yake tabbatar min da Khadija bin maza take yi a ɓoye. Meenal naga jarabawa kala-kala kuma na karɓe su da hannu bibbiyu. Khadija da Salma sun bani mamaki. Ke kuma da na fara tsanarki, sai na ɗinga bin duk wasu abubuwanki, anan idanuna suka nuna min ke a lokacin da kike watsar da giya, haka kike shafawa a jikinki don kawai a ce kin sha.

Meenal nayi matuƙar shan wahala wajen kokawa da zuciyata dole sai ta tsaneki. Shiyasa aka ce ba a saka Hijabi bane zaka sami ta ƙwarai.”

Meenal ta yi shuru can ya ce mata, “Haka daga baya na gane ba ke nake gani a wasu wuraren ba, fuska aka saka.”

Girgiza kai tayi, “Hon Munnir ne zai gaya maka fuska aka saka, kuma ba haka abin yake ba. Sau tari ni ɗin ce dai kake gani. Babu wata mace da aka taɓa sakawa fuska ta, da sannu zaka fahimci yadda lamarin yake.”

Dr. Bakori ya yi murmushi, kawai ya ɗauki maganarta tamkar shirme, ya ƙi ya mayar da hankali akan zancenta, da zai mayar da hankali da ya ɗauki wannan ‘yar maganar nata ya buɗa ta ta zama babban labari. Da zai fahimci Meenal da barcin da ke ƙoƙarin kwasarsa, bai sami muhallin zama a cikin zuciyarsa ba.
Meenal tana kallonsa barci ya kwashe shi, yana ajiye numfashinsa a natse. Addu’a ta tofa masa tayi ƙoƙarin ta janye jikinta, hakan bai samu ba, domin gaba ɗaya ya kanannayeta. Tuni ta lula cikin wata duniya mai nisan gaske. Da Dr. Bakori zai buɗe idanu zai kuma yi mata magana, babu shakka da yaga abin mamaki da idanunsa.

Da sassafe, tana barci ya rubuta mata 'yar takarda ya fice kai tsaye motar asibitin suka ja shi. 

A ƙalla sai da Dakta Bakori da sauran abokan aikinsa, suka share awa shida, suna abu ɗaya. Don haka suna kammalawa kowa ya fito da fatan samun nasara a wannan aiki.

Sai dai yana zare safar hannu, ya duba da kyau, Meenal ce sanye da doguwar riga baƙa, tayi matuƙar yin kyau. A ganinsa wahalar da yasha ne, ya sa take yi masa gizo, sai ya sake ware idanunsa. Ko tantama babu Meenal ce. Cikin sauri ya riƙe sandarsa ya nufi inda ya ganta. Sauri take yi abinta har ta fice daga Asibitin. Hakan yasa ya cewa Driver yazo ya mayar da shi gida.

A zaune ya sameta taci kuka idanun nan sun kumbura saboda kuka. Tana ganin shi tayi sauri ta rungume shi, “Husby ka tafi ka barni.” Dubanta kawai yake yi da mamaki, “Yanzu naga wata a doguwar riga a Asibitin mu kamanninku ya ɓaci, ina zaton ma ke ce.”

Sake rungume shi tayi tana sakin ajiyar zuciya. Babu alamun zata yi masa magana, “Baby me kika ci?” Kafaɗa ta noƙe, “Ni ba zan ci komai ba, tunda ka tafi ka barni ina barci.” Shafa kanta ya yi suka zauna a kujera ɗaya, “Sorry gani nan kusa da ke ai na dawo. Bani labarin irin kukan da kika yi.” Dariya ta saki tana sake shinshinarsa, “Kukana bai dameka ba, sai ma labari zan baka na irin kukan da nayi ko?”

Shafa cikinta ya yi, “Kin ga yadda rashin cin abinci ya sa cikin ki ya shige ko? Oya tashi ki ɗauko abincin da aka kawo inbaki da kaina.” Babu musu ta tashi ta zubo abincin. Idan ya bata cokali ɗaya, idan zai ƙara mata sai ta tura Cokalin zuwa bakinsa. “Husby kana warin asibiti.”

Murmushi ya yi, “To muje ki haɗa min ruwan wanka.” Babu musu ta haɗa masa ruwan wankan, ta tsaya tana jiransa ya fito. Ƙafarsa kaɗai ke hana shi aiwatar mata da wasu abubuwa, amma yana addu’ar aikin da za’ayi masa ya zama ansami nasara.

Cikin ikon Allah akayi masa aikinsa, haka ya hana a raba shi da Meenal ɗinsa. Haka ya na da tabbacin a yanzu idan ya warke zai iya takawa, cikin ikon Allah, kafaɗarsa baya jin irin abinda yake ji kwanakin baya. Meenal ta rungume shi, ta ce, “Ka kula da kanka zanje inkarɓo maka Apple ɗin yanzu zan dawo.” Kai kawai ya gyaɗa mata, ya mayar da kansa ya rufe idanu.
Ƙamshin turaren Meenal ya ji, wanda rabonta da turaren tun kafin ya aureta. Mamaki yasa ya ware idanunsa.

Ta windon ya hangota, tana magana da wani Doctor. Idan bai yi ƙarya ba Doctor ɗin har dafa kafaɗarta ya yi yana bayani. Ya Rufe idanunsa, yasan ba kayan nan Meenal tasa ba, yana da tabbacin idanunsa suna yi masa gizo, yana duban wata a matsayin Meenal. Idan ba Meenal ba ce wacece? Meke shirin faruwa ne?

Ya sake rintse idanun, yana ji ana shafa fuskarsa. Ya buɗe su fes akan Meenal ɗauke da Apple. Miƙa masa tayi tana murmushi. Ya ɗan girgiza kansa yana lumshe idanunsa. Tuni Apple ɗin ya fice masa a rai. Kansa ya hau ciwo. Baya son yin magana don haka ya cigaba da lumshe idanunsa.

To fa meke shirin faruwa ne? Ku biyo ni ni ‘yar mutan Borno dan jin yadda zata kaya.

<< Meenal 19Meenal 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×