Meenal ta saki ajiyar zuciya a falon ta dubi mijinta da kulawa, "Wai kuwa kayi magana da su Hajiyarka?"
Bai dubeta ba ya bata amsa, "Duk halin da nake ciki su Hajiya da Abba sun sani. Ina magana da su haka suna magana da ni. Abu ɗaya ya rage min shi ne inje in kai masu ke. Akwai abubuwan da nake son su kammala ne.
Shuru tayi bata sake cewa komai ba. Kore shurun ya yi yana mata magana cikin damuwa.
“Meenal ina ganinki bibbiyu a idanuna. Kina juya min wata Meenal ɗin ba Meenal ɗina ba. Me ke shirin. . .
I would love to read your stories