Skip to content
Part 5 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Ahmad da ya yi nisa a cikin tunani ya rasa meke masa dadi. Abubuwa rututu suna damun kwakwalwarsa. Yana bukatar samun hutu. Don haka ne da sassafe ya wuce gida ba tare da ya sake waiwayar Meenal ba. Haka itama da safen tasa rigima sai an sallameta.

Kwance take a jikin Umma tana yi mata tsifan kai, sai lumshe idanu take yi. “Ummana ciwon mara yana damuna da yawa ko zaki kaini asibiti ne?” Umman ta shafi kanta, “Tashi mu je Meenal kada ciwon ya yi tsanani.” Babu musu ta tashi suka shirya suka kama hanyar Asibitin su Dr. Bakori. Ta ji dad’i da bashi zai duba ta ba. Bayan gwaje-gwaje Doctor ya fara yi masu bayani, “Hajiya irin ciwon cikin ‘yarki ko tasha magani sai dai ya lafa mata, amma da zarar tayi aure insha Allahu zata rabu da ciwon gaba daya. Don haka a bisa shawara ki aurar da ita.” Meenal ta mike tana yi masa wani irin kallo, “Waye zai yi auren? Kai Allah shi kyauta. Namiji dai sunansa kenan namiji. To mun gode da shawara.” Da sauri ta fice daga Office din har tana bangaje mutum. Fizgota yayi da nufin ya wanke ta da mari, don shi baya daukar raini kwata-kwata. Ganin ita ce ya sauke hannunsa, wanda tuni ta rufe fuskarta saboda tsoro. Abu daya ya hana shi marin ta saboda baya son tana cigaba da dangata maza a masu hali iri daya.
“Kina da ciwon hauka ko?”

Hawaye suka zubo mata ta hau girgiza kai, “Tabbas namiji ne ajalina. Ka kashe ni mana ka huta.” Sakinta ya yi ta fice da gudu. Office din ya karasa ya gaida Umma yana dubanta, “Umma meke damun Meenal ne?”

Doctor ya kora masa bayani, duk akayi shuru aka rasa me iya magana. Daga baya ya kore shurun da cewa, ” Ya kamata Meenal ta ajiye akidarta ta fuskanci rayuwa. Ba zai yuwu idan namiji daya ya aikata kuskure ace dukka mazan haka suke ba. Ina son insan menene kaddarar Meenal? Me maza suka yi mata?” Mikewa Umma tayi wanda tuni hawaye suka jika mata gaban hijabi, “Meenal bata son ana tunawa da rayuwarta. Meenal ta roki duk wani wanda yasan kaddararta da kada ya soma ya gayawa wasu. Da ba haka ba da na gaya maka dalilan Meenal na tsanar maza na tabbata sai ka taya ta tsanar su.

Yana kallo har Umma ta bacewa ganinsa. Shuru ya yi kamar me son gano wata matsalar sai kuma ya mike ya fice.

Yau kwanansa biyu ko sunan Meenal baya kaunar zuciyarsa ta tuna masa. Kokari yake yi dole sai ya mance da ita.

Meenal ce kwance a gadonta sai juyi take yi. Wayarta ta ciro ta had’a sim din da ta cire da dadewa. Tana bude wayar ta ji shigowan sako. “Da zaki hakura ki daina bincike da kin huta. Rayuwarki a doron kasa kamar barazana ce ga tawa rayuwar. Dole zaki mutu Meenal. Zaki mutu…”

Toshe bakinta tayi hawaye suna sake zuba daga idanunta. Ita kanta tasan rayuwarta ba me tsawo ba ce. Bata son mahaifiyarta tasan wannan abubuwan da ke faruwa domin barinta ta sani tamkar wargaza dukkan farin cikinta ne. Tana son mahaifiyarta fiye da kowa. Tana son sanin mutumin nan, ita kanta tana son haduwa da mutumin da take son ko ya kasheta ko kuma ita ta kashe shi. Alkawari tayi indai tana rayuwa sai ta kashe rayuka biyu.

Mi’kewa tayi ta nufi inda take boye wukar ta. Cikin minti goma sha biyar ta sauya shigarta zuwa baqaqen kaya.
Jin bugun kofa yasa tayi saurin sauya shigar ta boye kayan. Umma ce ta shigo tana dubanta, “Meenal ya naga kamar kinyi kuka? Babu wani abu ko?” Girgiza kai kawai tayi tana lumshe idanu, “Umma barci nake ji sai da safe.” Shuru Umma tayi kamar ba zata fita ba, sai kuma ta jawo mata kofar ta fice. Cikin gaggawa ta mayar da kayan ta fice. Mai keke napep din yana jiranta suka nausa titi.

Dr. Bakori yana zaune ya kasa taba komai da abokinsa ya kawo masu, saboda gani yake kamar komai giya ce a gurin. Kamshin turarenta da take yawan amfani da shi ya tona mata asiri. Sai dai kamar yadda ya shaki kamshinta haka yake agurinta. Shuru tayi tana waige hakan yasa ya dukar da kansa. Jikinta ya bata Dr. Bakori yana wurin nan. Idan kuwa yana nan zai iya kawo mata cikas. Sosai take ware idanu tana nemansa, amma bata ga ko me kama da shi ba. Hakan yasa ta nemi wuri ta zauna. Wukar ta fitar tana kallo. A lokacin Dr. Bakori ya dago idanunsa yana duban wukar da ke hannun Meenal. A zahiri ya yi matukar firgita. Bai taba tunanin ko allura Meenal zata iya rikewa ba, bare har akai ga wuka. Yadda take juya wukar ya nuna masa karara Meenal rayuwar wani take nema.

Mi’kewa tayi bayan ta boye, sannan ta kama hanyar wani lungu. Mi’kewa ya yi yana kokarin bin bayanta. Sai dai ko sama ko kasa ya duba ta bai ganta ba. Yana fitowa yana waige-waige ya fara jin ana guje-guje ankashe wani mutum. Ya kara firgita da yaji sunan Alhaji Tasi’u a matsayin mutumin da aka kashe a mashaya. Alhaji Tasi’u fitacce ne kuma dan kasuwa ne, da duniya take yi masa kallon me mutunci. Sai ga gawansa a yashe a mashaya. Dr. Bakori yana da tabbacin Meenal bata yi nisa da wurin nan ba. Kuma babu ko tantama ita tayi wannan kisan. Fitowa ya yi bakin titin da sauri. Yana kallonta jikinta duk jini ta shige napep ta bar wurin.

Dr. Bakori da ya ji wani irin jiri mai karfi ya kwashe shi, ya yi saurin dafa motar da ke kusa da shi yana Salati. “Meenal kisa? Meenal zaki iya kashe rai?” Innalillahi kawai yake maimaitawa. Rayuwar Meenal tana cikin hatsari. Ta zabi kashe kuruciyarta ta hanyar da ba zata taba bullewa da ita ba.
A daddafe ya bar wurin. Kafin wani lokaci kafafen yada labarai sun shiga yada mutuwar babban mutum Alhaji Tasi’u. Haka ‘yan sanda suna can suna bincike akan wanda ya yi wannan barnar. Gaba daya Dr. Bakori ya sauya, ya daina magana ya daina kula kowa.

Sanye yake da jallabiya fara sol, sai ya koma sak balarabensa. Masallaci yake son zuwa Hajiya ta tsaida shi, “Ahmad meke damunka ne? Meke saka zama haka? Ko kana da matsala ce?” Girgiza kansa ya yi yana kirkiro murmushi wanda ke kara kawata fuskarsa, “Hajiyata bani da wata damuwa. Yanayin aikin ne kawai babu dadi.” Bata matsa masa ba ta kyale shi ya wuce.

A motarsa yake tafe shuru kamar wanda yake fama da wata lalura. Ta unguwarsu Meenal ya biyo, hakan yasa ya had’u da jama’a masu yawa. Mamaki ya hana shi sakat duban kowa yake yi cike da mamaki. Gabansa kuwa fad’i yake yi da karfi.

Har kofar gidan ya karasa. “Bawan Allah lafiya na ganku da yawa haka?” Dr. Bakori ya yi tambayar da bai san lokacin da ta fito masa ba. Kai tsaye aka bashi amsa da Meenal ce Allah ya yi mata rasuwa.

Kansa ya ji ya yi masa wani irin nauyi. Da karfin Addu’a ya kwato kansa da ke barazanar tsinkewa daga jikinsa. “MEENAL! Kai ban yarda ba.” Ya Kashe motar ya kutsa cikin gidan. Babu shakka Meenal ta rasu. Har gaban Umma ya karaso da ke zaune rike da carbi idanun nan sun kumbura. “Umma ina gawan Meenal?” Anti Rufaida ta nuna masa wani daki. Ya mi’kewa da nufin ya karasa gun gawar. Kawarta Farida da Halima suka sha gabansa cikin kuka, “Me zaka yi wa gawanta? Ta bar wasiyya kafin ta rasu kada a sake abar wani namiji ya bude gawarta idan ba Sallah za ayi mata ba.” Duban su yake yi daya bayan daya. Da za su san bakin cikin da ke zuciyarsa da ba su dakatar da shi akan abinda yake shirin yi ba. Sai dai yana jin ko mahaifiyar Meenal bata isa ta hana shi ganin gawarta ba. Idanu jajir ya ke dubansu. Tsoronsa yasa suka dan ja baya kawai ya shige.

Allahu akbar! Rai bakon duniya. Gaba daya kamanninta sun sauya. Audiga ce manne a cikin hancinta. Dr. Bakori ya rufe ta tare da rintse idanunsa, yana jin kirjinsa yana masa wani irin nauyi. Babu shakka Meenal wata jigo ce a cikin rayuwarsa. MEENAL ta kasance yarinyar da tun dora idanunsa akanta yake jin wani abu game da ita. MEENAL ta mutu ta bar shi da rayuwa mara dadi. Ya tabbata shima babu jimawa zai bi bayanta. Ya mi’ke kamar zautacce ya fice daga gidan ba tare da ya yi wa kowa magana ba. Ya rasa dalilin da yasa jikinsa ke bashi Meenal dinsa ba zata taba tafiya ta bar shi ba. Yana da tabbacin Meenal ce duk wani jin dadin rayuwarsa.

Shi kansa bai san yadda akayi ya kawo kansa gida ba, shi dai ya tsinci kansa a tsugunne a gaban Hajiya yana ce mata, “Hajiya Meenal ta mutu. Shi kenan sai wata Meenal din amma ba wannan ba.” Hajiya ta gaza fahimtarsa don haka ta kira Alhaji Sudais tana gaya masa Ahmad ya haukace ya yi gamo da Aljana. Dole ya ja bakinsa ya yi shuru. Qur’ani yake son ya ce a kawo masa amma bakinsa ya gaza furta komai.

Kwanan Ahmed biyar bai san inda kansa yake ba. Duk wani abu da aka san magani ne da ya danganci Aljanu babu wanda ba ayi masa ba, amma shuru. A ranar da ya cika sati guda ne ya tashi da kansa ya koma bakin aiki.

Sai dai babu magana a tsakaninsa da kowa. Hatta iyayensa baya sakin jiki da su. Ya koma asalin Ahmad dinsa na da. Daga manya har kanana basu iya matsowa kusa da shi.

A cikin wani daki mai tsananin duhu, Meenal ce a zaune andaureta da igiya. Gaba daya ta gama fita hayyacinta. Da bawa yana da ikon ganin dakin nan mai tsananin duhu babu shakka da Meenal ta zama mace ta farko da zaka fara zubar mata da hawaye. Tun da aka kawo ta wannan wurin bata sa komai a bakinta ba. Dakin aka bude wanda haske ya cika mata idanu.

Wani mutum me cikar zati ya shigo da kattai a kalla za su kai su biyar. Wanda ya fi kowa muni a cikin su ya fizgo kan Meenal. Mutumin nan ya ce, “Kada ka tsinka mata gashi sassauta rikon don Allah.” Babu musu ya sassauta irin rikon da ya yi mata. “Meenal sunan ki ko ‘yan mata? Kina da taurin kai. Kin ga yanzu na raba ki da kowa. Babu wanda yasan kina raye. Yadda kika so ki wargaza min shiri na hakan bai yuwu ba. Zaki cigaba da rayuwa a cikin kaskanci. Anan wurin zaki yi kashi anan zaki yi fitsari. Anan wurin zaki karasa rayuwarki. Gara ki mutu inmikawa angulu namanki su cinye. Na tura a kashe Alhaji Tasi’u saboda inɗaureki, amma sai kika tsallake. Na tura wani yana turo maki saƙon wasiƙa, anan ma sai kika kashe wayar. Yanzu zan yi maganinki.” Kallonsa kawai take yi, taso kwarai da bakinta zai iya magana da ta furta masa ko da kalma daya zuwa biyu. Ta fi tausayin mahaifiyarta akan kanta. Tasan duk inda mahaifiyarta take bata cikin natsuwarta. Tasan yayarta Rufaida tana cikin halin kuka da tashin hankali. Ina ma zata iya samun waya da ta sanar masu su kwantar da hankalin su ba ‘yar su Meenal suka rufe ba. Hon Munnir ya dubi agogon hannunsa yana murmushi, “Yanzu ina da meeting ne zuwa anjima zan sake dawowa ko bankwana mu yi. Idan na tabbatar baki doron kasa zan fi samun sukuni inyi abubuwana, cikin kwanciyar hankali. Amma kafin nan sai kin isa ga Alhaji Khalid kin kashe min shi a hannayenki

Duk mutanen da suke kawo min mishkila ke zan tura kiyi amfani da kyanki ki rude su ki kashe min su kafin nima inkashe ki. Sai na gama azabtar da ke daga baya kuma ingyaraki dan kiyi kyan gani. Yanzu za a kawo maki farar shinkafa babu magi bare gishiri dole ki ci. Ruwan wanke-wanke zaki cigaba da sha har na tsawon sati biyu.

Ruf! Suka fice suka rufeta. Wayyo me nayi a duniyar nan maza ke wahalar da ni? Hon Munnir ba zan taba yafe maka ba. Na tsaneka. Ya Allah ka taimake ni ka kawo min dauki. Kuka take yi me ratsa zuciya. So take ta mutu ko zata huta. Kanta ta rinka bugawa a karfe tana rokon mutuwarta. Haka ta gaji ta kwantar da kanta. Kafin wani lokaci ta sume anan wurin.

“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un.” A firgice ya tashi daga mummunan mafarkin da ya yi akan Meenal. Meyasa kullum sai ya ganta a cikin mafarkinsa tana kuka tana rokonsa ya taimaka mata? Me ke shirin faruwa ne? Jikinsa yana bashi Meenal tana raye. Macen da ya gani a matsayin gawa ba Meenal ba ce. Ya zama dole ya ziyarci gidan mahaifiyar Meenal domin ya ji ta yadda akayi Meenal ta rasu.

Shigar kananan kaya ya yi, duk da ya rame hakan bai hana kayan yi masa kyau ba. A natse ya shiga motarsa ya kama hanyar gidan Umma. A zaune ya sameta a falon fuskar nan kamar an’kona. Sai yau ya kare mata kallo. Fuskarta ba dai-dai take ba, kamar ta taba konewa ko dai wani abu. Sunkuyar da kanta tayi tana sake zubda hawaye. “Doctor ka ga gidana ya koma babu kowa ko? Meenal ta tafi ta barni. Dama nasan ba zai barta da rai ba. Meenal tana kokarin boye min matsalar da take ciki amma ni na san komai.”

Dr. Bakori da ya shiga duhu sosai ya dubi Hajiya Salma da kulawa ya ce, “Umma su waye za su kashe ta? Kuma ya akayi Meenal ta mutu ko Asibiti ba a kaita ba?”

Kokarin dakatar da hawayen take yi, amma abin ya ci tura. Cikin kuka ta ce, “Daga zazzabi na tafi na barta. Dawowar da zanyi da safe naga har ta rasu jikinta duk ya sauya. Meyasa Meenal zata tafi ta barni?”

Dr. Bakori ya dan dai-daita natsuwarsa yana dubanta, “Umma su waye suka kashe ta? Me tayi masu?” Kuka Umma take yi kamar yau akayi mata mutuwar. Girgiza kai kawai take yi tana sake jin damuwa fiye da kullum. “Allah ya jikanki Meenal. Kin tafi kin barni a cikin tashin hankali. Na sani ba zan taba samun yarinya me sadaukarwa kamar yadda na sameki ba. Kin juri gwagwarmaya ashe ba zaki sami farin cikin da nake yi maki fata ba. Ki jirani Meenal ina tafe insha Allahu.”

Shi kansa yasan ba zai taba samun kanta ba, bare har ya sami abinda yake son samu. Tausayinta ya rufe dukkanin ilahirin jikinsa. A sanyaye ya fice daga gidan ba tare da yasan takamaiman inda zai je ba.

Da shigowarsa falo Abbansa ya dube shi da kulawa, “Ahmad kana sane da zuwa duba Alhaji Khalid ko? Kasan baya kaunar wani likita ya duba shi sai kai? Don haka nake son a sati mai zuwa ka gama kintsawa zaka wuce Sokoto ka duba shi.” Baya son tafiyar nan, ya tsani iyayi irin na Alhaji Khalid da har zai bar kasar nan amma ya kasa zuwa a duba shi, har sai ya taso shi a gari mai nisa dan kawai ya nunawa duniya shi me kudi ne. Tabbas darajar mahaifinsa yake ci da ba haka ba babu abinda zai sanya yaje duba lafiyarsa. Da kulawa ya amsawa mahaifinsa ba don ya kai zuciyarsa ba.

Cikin kazantarta take kwana tana tashi. Meenal ‘yar gayu mai ji da kamshi, yau ita ce a cikin wurin da ko karen gidan su ba zata taba bari a sanya shi a wurin ba. Gaba daya tayi baƙi ta rame. Da ace ana sabawa da wahala da Meenal ta share hawayenta ta kira wannan sabuwar rayuwa da sabo. Yau din ma farar shinkafa ce aka ajiye mata da ruwan wanke-wanke. Hawaye masu zafi suka zubo mata. “MAHAIFINA KE WAHALAR DA NI? Ya Allah kasa mafarki nake yi. Allah kasa wannan mutumin ba mutumin da nake duba a matsayin wanda ya wanzar da samuwata a doron duniya bane. Allah kasa Ummana ta karyata faruwan hakan.”

Idan ya kasance mahaifinta ya zama dole ko sau daya ne tak! Ya ji tausayinta a ransa. Amma ya tabbatar mata bai taba jin tausayinta ko da sau daya ne a rayuwarsa ba.

<< Meenal 4Meenal 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.