Skip to content
Part 7 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Da idanu ta raka shi har ya fice daga ɗakin. Shuru ta yi ta kwantar da kanta a jikin filon ba tare da ta sake yin kwakkwarar motsi ba.

Dawowa ya yi hannunsa ɗauke da ruwan tea ya dire a gabanta, “Tashi kisha ruwan tea din ko kadan ne.” A hankali ta yunkura. Hannunta ba zai iya rike cokalin ba, dole ya dinga ɗiba yana sa mata a baki. Mamaki yake yi yadda Meenal ta tsaya ya taimaka mata. Da alamu dai ta cire shi daga jinsin maza tana kokarin maida shi jinsin da tafi kauna wato mata. Dole Dr. Bakori yana da buƙatar yin dogon nazari kafin ya iya aiwatar da duk wani aikinsa. Yana son kiran mahaifinsa, amma hankalinsa bai kwanta da ya yi waya da layinsa ba. Ya tabbata duk inda Hon Munnir yake a shirye yake akansa. Zai iya yin komai don ya gano irin shirin da yake kokarin yi. Meenal ce damuwarsa, yafi buƙatar ya tseratar da ita fiye da kansa.

“Ina jin fitsari.” Kalman da ya iya tsinta kenan daga bakin Meenal. A dan firgice ya juyo yana dubanta. Ta yaya zai iya taimaka mata har tayi fitsari? Ba zai iya ba. Mi’kewa ya yi yana duban agogo har biyun dare ya gota. “Meenal ban san yadda zan yi maki ki yi fitsari ba. Wannan aikin yafi karfina.” Idanunta suka kawo kwalla.
“Ka kalli kanka a matsayin mace ‘yar uwata ka kaini inyi fitsarin nan. Da ace ina yi maka kallon namiji babu shakka da ban zauna wuri guda da kai ba.

A tsanake yake kallonta. Sai dai wannan karon kallon mahaukaciya zalla yake yi mata. Yana ji a ransa ko bindiga za a ɗora masa a kirji ba zai iya aikata abinda Meenal take buƙata ba. Ficewa ya yi daga dakin, bai jima ba ya dawo tare da ma’aikaciya ya nuna mata abinda yake son tayi masa. Shi kuma ya fice ya gyara zamansa a farfajiyar wurin da babu wasu mutane.

Idanu ya zubawa abinda ya gifta ta gabansa kamar walkiya yana mamakin wace ce haka? Ba karamin sani kayiwa Meenal ba, da har zaka iya tantance ta da macen da ta wuce cikin bakaken shiga a yanzu. Ji ya yi gabansa ya fad’i. Tsoron kada a cutar da Meenal ya shige shi. To wace ce take irin shigar Meenal? Anya babu wata wacce tasan sirrin Meenal da take son aikata wani laifi ta dora laifin akan Meenal?

Tashi ya yi ya nufi dakinsa. Meenal ya samu har tayi barci. Mamaki ya kara kama shi, ta yaya yanzu yanzu daga fitarsa har Meenal tayi barci? Kuma har tayi nisa a cikin barcin. Lekawa ya yi ko ina, sannan ya dawo ya rufe kofar. Tun kafin ya yi dogon bincike ya fahimci irin maganin barcin da aka shaƙa mata. Murmushi ya yi yana sake dubanta, “Meenal kina cikin matsala. Mutanen da suke nemanki suna da yawa. Allah yasa kada ki sa ni a cikin matsala.”

Ya kasa barci yana zaune yana gadinta, har aka kira Sallar asuba. Ba zai iya tafiya masallaci ya barta anan ba, dan gani yake yi da zarar ya tafi ba zai dawo ya sameta da rai ba.

Zuciyarsa tana gaya masa hanyoyi da yawa da ya kamata yabi domin cirewa Meenal tunanin maza dukka iri daya ne. Haka ya fi gazgata dayan zuciyarsa akan dole Meenal ta amince ta aure shi, saboda jikinsa yana bashi zai yi rayuwa me tsawo tsakaninsa da Meenal, idan kuwa ya cigaba da zama da ita a hakan bayan bata kasance muharrramarsa ba, za su sami matsala ta fuskar shaidan. Ya gama shirinsa tsaf zai bar garin zuwa Kano zai je wani wuri ya boye Meenal tukun kafin ya sake sabon shiri.

Yana fitowa yaga babu kowa a Hotel din sai wasu jami’an tsaro. Da mamaki ya karasa suka gaisa anan ake yi masa bayanin anyi kisa ne shi kadai ya rage a cikin Hotel din a rufe shi har sai ankammala bincike.

Kai tsaye tunaninsa ya dawo kan macen da ya gani a daren jiya. Haka kuma abinda aka shakawa Meenal ya nuna ko waye yayi kisan nan babu ko tantama yana da alaka da Meenal.

Duban jami’an tsaron ya yi ya ce masu shima yana tare da matarsa ne bata da lafiya yanzu za su wuce. Meenal da kanta ta dingisa suka fice kowa da irin tunanin da ke cinsa. Sun yi nisa a cikin tafiyar wayar Dr. Bakori ta hau kara, babu bata lokaci ya dauka tare da bude muryar wayar gaba daya. Hon Munnir yake magana cikin isa, “Ina zaka je da Meenal?”

Tambayar ta bashi haushi amma sai ya dake, ” Zan kaita babban asibiti a duba ta da kyau domin ina da buƙatar ta.”

“Ya maganar kashe Alhaji Khalid?”

“Ina da buƙatar nazari kafin aiwatar da aikin nan. Haka kuma ina ganin abar min Meenal kawai ta isheni kudin ayyukana.”

Alhaji Munnir ya saki malalacin murmushi, “Barin yarinyar nan a raye tamkar lokacin wargaza zaman duniya ta ce ta zo. Barin yarinyar nan a raye barazana ce ga sarautar da nake shirin karba a garin Gombe. Haka zalika barazana ce me girma a idon duniya. Idan zaka kashe min ita a yanzu ka hada da Alhaji Khalid ni sai na cire danginku daga cikin talauci.”

Dr. Bakori ya sha mur kamar bai taba dariya ba a duniyarsa, “Kana da gadara Hon Munnir. Ni kuma bana mu’amala da mutum me gadara. Ka gaya min iya adadin abinda kake son mallaka min, ni nayi maka alkawarin zan mallaka maka mafiyinsu zuwa anjima da yamma. Idan kana takama da kudi babu ko shakka mun fi ka arziki. Ni ina yin aikina ne saboda taimakon rayuka ba don neman kudi ba. Zai fi kyau ka dinga gyara kalamanka, kasan hanyar da zaka biyo min domin sauke kowacce kalma d’aya.

Kana fitar da kalaman a cikin garaje, don hakane suke cin karo da juna wajen kawo maka matsala. A yayin furta su.

Kit! Dr. Bakori ya tsinke wayar ba tare da ya dubi gefen da Meenal take ba.

“Meenal rayuwarki tana cikin hatsari. Zai fi kyau ki natsu ki saki jiki da ni ki gaya min komai, kila akwai hanyar da zan iya taimaka maki har burinki ya cika akan maza.”

Shuru Meenal tayi kamar ba zata yi magana ba. A karo na farko da zuciyarta ta amince da wani d’a namiji kuma zata iya bude baki ta fad’i alkhairinsa a gaban kowa. Sai dai har yanzu babu sha’awar yin hulda da wani namiji a cikin zuciyarta. Indai zai taimaka mata da gaske ta cimma burinta akan Hon Munnir a shirye take da ta amincewa duk abin da zai buƙata.

“Zaki aureni?” Tambayar ta zo mata a bazata, haka shima fitar tambayar ta zo masa a sama, ba kamar yadda yaso ya jera tambayar ba. Yasan abu ne me matukar wahala tayi masa kallon Rahama, kasancewar bai san ta yadda zai lallasheta har ta gane me yake nufi ba. Ci gaba ya yi da magana ba tare da ya dubeta ba, “Ba aurenki zan yi dan ina sonki ba a’a kamar yadda babu tsarin namiji a rayuwarki haka nima rayuwata babu wurin ajiye wata ‘ya mace. Zan aureki ne in taimaka maki har burinki ya cika muna gamawa sai in sake ki ki ci gaba da rayuwarki babu namiji a kusa. Aiki zai haɗa ni da ke zamu kwana daki daya, a tsarin addininmu haramun ne, haka kamar lalura irin wannan da ya kama sai na taɓa ki, shima babu kyau. Duk da ni likita ne na taba mata kala-kala, amma ke kin fita daban Meenal.”

Ya sauke maganar a hankali tare da kafe ta da idanu. A hankali ya janye idanun ya mayar da hankali a bisa titi. Maganganun Dr. Bakori gaskiya ce, amma ba ta jin zata iya amince masa. Don haka tayi banza da shi kawai ta ci gaba da duban gefen hanya. Shi kansa bai damu ba, babban burinsa ya ƙarasa gida gun mahaifiyar Meenal domin ya ji abubuwan da yake son ji.

A can wani kauye da ke hanyar Kano ya je ya ajiyeta a gidan wata tsohuwa me yawan fara’a. Sai bayan sun gaisa ne ya dubi tsohuwar, “Sunanta Meenal. Iyatu ina son ki rike min ita da kyau zuwa ranar da zan waiwayeta. Amana ce a gareni.” Kuɗi ya mikawa tsohuwar ya mike da nufin tafiya. A karo na babu adadi idanunsu ya harde da na juna. Idan bai yi ƙarya ba hawaye ya gani kwance a cikin kwayar idanunta kamar me son furta wani abu. A hankali ya ƙaraso daf da ita ta yadda suke iya jin hucin juna. A karo na farko da ta ji wani irin kasala me tsananin shiga jiki ya rufe ta. Hannu yasa ya ɗago habarta, idanunsu ya sake haduwa. Rintse idanun tayi da karfi gabanta yana wani irin faɗuwa.

“Allah kaɗai shi ne gatanki Meenal. Zan tafi ki kula da kanki.”

Tana tsaye ya fice daga ɗakin ya ƙarasa gurin Iyatu domin yi mata Sallama. Tana kallo ya ɓacewa ganinta, tana kallo ya yi mata nisa, tana kallo ya barta a gidan da babu danginta.

Dr. Bakori yana wuce wa ya tattara dukkan farin cikin Meenal ya tafi da shi. Cikin abin da bai wuce minti biyu ba, fara’ar fuskar Iyatu ya ɓace ɓat! Kamar ba ita ba ce take ta aikin bude baki. Meenal tana tsaye shuru, ta ji an fizgota, hakan yasa ta ɗan yi kara, saboda ciwon ta. “Ke mu nan gidan ba ayi mana shagwaba, maza ki zo ki share gidan nan, sannan ki zo muje mu ci kasuwan dare.”

Meenal ta lashi labbanta da suka bushe, wannan ba komai ba ne a cikin irin matsalolin rayuwarta. Zuciyarta ta riga ta bushe. Karbar tsintsiyar ta yi tana ɗingisawa ta kama shara. Yadda ta rike tsintsiyar ya fusata Iyatu ta kwace tsintsiyar ta murde hannun. Kara ta saki me karfi, wanda ya yi dai-dai da dauke numfashinta.

Duk da yana sane da Iyatu zata kula da Meenal, hankalinsa ya gaza kwanciya a inda ya barta. Ba shi da sauran lokaci da zai ba ta. Da isarsa gida ya sami mahaifinsa a ɗaki shi kaɗai ya kora masa dukkan abubuwan da suke faruwa. Alhaji Sudais ya tabbatar da dansa ya fada cikin hatsari. Duban Ahmad din ya yi yaga babu alamun damuwa a tare da shi, kawai ya girgiza kai,

“Hon Munnir shi ne wanda ake sa ran zai karbi sarautar Gombe, da zarar babu mahaifinsa. Menene alaƙarsa da yarinyar? Meyasa kuma yake son kashe babban amininsa Alhaji Khalid?” Dr. Bakori ya saki ajiyar zuciya,

“Shi ne abin tambaya Abba. Amma kada hakan ya dameka, ni zan iya da shi. Ina son kuma ka bani izinin in auri Meenal in kawo maka ita a matsayin suruka, don na tabbata aurenta ne kadai zai sa ta janye tsanar da take gwada wa akan namiji. Ina son Meenal ta gane ba dukka mazan ne suka hadu suka zama iri daya ba. Daga karshe na tsinci kaina a cikin tausayin rayuwar Meenal.” Alhaji Sudais ya girgiza kai, “Ta bani tausayi Ahmad. Na amince ka aureta domin ceto rayuwarta. Sannan ina son kabi komai a hankali. Anjima zan kira Alhaji Khalid zan gaya masa jikinka ya matsa sai da ka dawo. Kafin mu samo mafitan yadda zamu biyowa lamarin.”

Har kullum Dr. Bakori yana jinjinawa mahaifinsa, ya fita daban a cikin sauran jama’a.
Komawa d’akinsa ya yi, sai dai barci ya gagare shi. Yana rufe idanunsa yake cin karo da Meenal tana kuka. Ya rasa dalilin da gabansa ke fad’iwa da zarar ya tuna da halin da take ciki.

Da misalin karfe goma na safe ya fito cikin shirinsa na zuwa Office, wanda a zahiri gidan su Meenal zai je. Duk yadda Hajiyarsa ta so ya tsaya ya karya abin ya gagara, dole ta bishi da addu’a.

ya jima tsaye a kofar gidan yana neman ta hanyar da zai iya yiwa mahaifiyarta bayani, sannan ya yi sallama. Hajiya Salma da Baba Sani ne zaune a katon falon, da alamu faɗa yake yi mata idan ka kalli yadda idanunta ke tsiyayan hawaye.

Bayan sun gaisa ne ɗakin ya dauki shuru, daga bisani Dr. Bakori ya dubi Baba Sani ya ce,

“Na zo neman auren ‘yar ku ce Meenal.” Gaba daya sai aka hau kallon kallo. Umma ta dube shi sosai, “Ana auren matacciya ne? Ko kuwa wata Meenal din garemu? Haba Doctor ya zaka kawo min rudani?” Mikewa ya yi tsaye yana tunanin ta yadda zai warware mata komai. A hankali ya sauke idanunsa akan Baba Sani da yake dubansa, cike da mamaki. “Baba ‘yarku bata mutu ba tana raye. Wani Hon Munnir yasa aka sace ta, ya sauya maku ita da gawa.”

A zabure suka tashi tare da maimaita sunan Munnir! Umma ta fasa kuka tana neman fita hayyacinta. Dr Bakori ya girgiza mata kai, “A’a yanzu ba lokacin kuka bane. Ina son ingaya maku dukkan abinda ya faru. Ina son bayan na gama bayanin nan zan dawo maku da ita ku daura min aure da ita a cikin satin da zamu shiga.”

Babu me kwakkwarar motsi, har sai da Dr. Bakori ya dire bayaninsa akan Meenal. Hatta Baba Sani da yake namiji sai da rayuwar Meenal ya bashi tausayi har ya zubar da hawaye. “Ka taimakeni ka dawo wa ‘yata da farin cikin da ta rasa tun tana cikin cikina. Hon Munnir da gaske yake yi idan Meenal tana raye ba zai taba samun abinda yake so ba.”

Baba Sani ya mike yana zagaya falon, “Yanzu har rashin imanin Munnir ya kai haka? Allah da saninka komai ke faruwa, ka kawo mana karshen matsalar nan.”

Dr. Bakori bai bar gidan ba, sai da Baba Sani ya amince zai karbi bakuncin ‘yan uwan mahaifinsa, da nufin mika sadaki.

Tun kafin ya iso gida har mahaifinsa ya isar da bayani akan auren Ahmed. Mutane da yawa daga cikin family din ba su dauki abin da mahimmanci ba, domin sun san babu yadda za ayi abun ya yuwu. Ita kuwa Umman Meenal kwana tayi tana gayawa Allah kukanta. Haka gani take yi kamar karya ce ba Meenal ba ce. Kai tsaye Umma ta daga waya ta kira Halima ta kwashe komai ta gaya mata. Cikin firgici Haliman ke tambayar Umma a wani gari Meenal take yanzu?

Umma ta bata amsa da itama bata sani ba, amma tabbas zuwa gobe za a dawo da ita. Haka ta kira ‘yar uwar Meenal Rufaida ta gaya mata komai. Wannan abin al’ajabi ya gaza barin kowa ya rintsa.

Tun bayan da Meenal ta farfado ta ganta a yashe a kofar dakin iyatu, ga dare ya tsala gashi tana jin fitsari kafafunta sun rike sosai. Tunawa tayi da lokacin da take jin fitsari Dr. Bakori ya samo wacce ta taimaka mata. Hawaye ke kwance a cikin idanunta a kokarinta na hana su zuba. Dumi ta ji a jikinta hakan ke tabbatar mata da ta saki fitsarin a jikinta. Gyarawa tayi tana son ta kwanta, sai dai kaikayin fitsarin da tayi ya dameta, ga sanyi da ya shige ta sosai. Bata san me tayi wa matar nan ba, ta zabi hanyar nan a matsayin hanyar gallaza mata.

Wani cinnaka ne yakai mata cizo ta sosa wurin tana jin zafin har tsakiyar kanta. A haka barcin wahala ya kwasheta, jikin nan duk alamun cizon sauro da kwari. Da asuba Iyatu ta fito tana dubanta, “Au dama suman iskanci ne kika tashi da kanki? To maza jeki ki gyara min daki, zuwa anjima mu je kasuwa.” Da kyar Meenal ta yunkura tana shiga dakin idanunta suka hasko mata fiya-fiya da ke kan windo. Tabbas tana son ta mutu, tana son ta takaitawa mutanen da suka tsaneta wahala. A hankali ta bude Fiya-fiyan ta daga kanta tana kaiwa bakinta ta fashe da kuka me tsuma zuciya. Tana jin saukan fiya-fiyan a cikinta, ta saki ajiyar zuciya me karfi.

A hankali cikin ya dinga juyawa tana jin yana murdewea, tabbas tasan karshenta tazo. Babu nadama ko ɗaya a tare da ita, ta kosa ta daina fahimtar komai dake cikin duniyar.
Shigowar Iyatu kenan taga Meenal a kwance cikin kumfa, tana ta mimmikewa. Iyatu ta zaro ido tana duba kwalban da ke kusa da ita. Da gudu tayi waje tana kwarma ihu a taimaketa yarinya ta kashe kanta.

Shigowarsa kenan yake jin sumbatun iyatu. Shi kansa bai san lokacin da ya shigo gidan ba. Tana ganinsa ta sake gigicewa, “Wallahi ba ni na kasheta ba, fiya-fiya tasha ta kashe kanta.” Dakin ya shiga ya karasa kanta tana kwance tana shure-shure. Tallabo kanta ya yi yana duban yadda kumfar ke fita,

“Meenal! Meenal!!” Hakan ba zai yi masa ba, ya dauketa cak cikin matukar sanyin jiki ya fice da ita. Kallon Iyatu ya yi kallo ne me cike da zargi, kawai yasa ta a mota ya fice daga unguwar da gudun gaske. Babban Asibiti ya nufa da ita. cikin ikon Allah aka karbeta likitoci suka dukufa akanta. Yana nan tsaye a harabar Asibitin shuru, kamar me son tuna wani abu.

Wayarsa ce ta yi kara kawai ya dauka ba tare da ya damu da sanin waye ba, “Dr, Bakori baka isa ka ci amanata ba. Kana tunanin har zaka cimma burinka na auren Meenal? Ina tabbatar maka sai dai ka auri gawa. Kuma ya zamar maka dole ka kashe min ALhaji Khalid kamar yadda ka amsa min da farko. Bana son intabaka ne shiyasa na sa maka idanu, da ba haka ba, da sai naga gatanka,”

Dr. Bakori bashi da karfin halin furta komai, baya jin a yadda yake din nan ko dukansa aka zo ana yi zai iya kare kansa. Meenal ta rugurguza masa komai.

Doctor din ya same shi, suka wuce Office yana yi masa bayanin Meenal tana nan lafiya, sun samu sun taro gubar da tasha. Dr Bakori ya yi ajiyar zuciya, ya fice daga asibitin. Kayayyaki yaje ya siyo ya dawo ya tunkari dakin. Idonta biyu ta kurawa saman dakin ido. Ji ya yi kamar ya dauketa da mari, saboda bacin rai. Ita kanta ta kasa hada idanu da shi.

“Da kin mutu yau me kika tanada domin fadawa Ubangijinki? Nayi takaicin bata lokacina agurin da bai kamata ba. Na ajiye aikina saboda ke, na shiga hatsarurruka saboda ke, na shiga inda bai dace ba saboda ke, duk ki rasa sakamakon da zaki yi min sai ta hanyar shan guba? Banyi mamakin abinda kika aikata ba, idan nayi la’akari da rashin hankalinki. Daga yanzu ba zan sake taimaka maki ba, zan barki kiyi duk abinda kika gadama.”

Kawar da kanta tayi tana Magana can ciki, “Na rasa me taimaka min nayi fitsari a cikin kayana, ina zaune a duniyar ba tare da na bautawa Ubangijina ba. Tun abincin da ka bani ban sake samun abinci ci ba, na kwana a waje a cikin cinnaka, na sume babu wanda ya taimaka min.

Bana jin dadin zaman duniyar. Ina shan wahala, kaina yana min ciwo cikina yana min ciwo bani da lafiya bani da lafiya.” Haka ta dinga maimaitawa hawaye suna tsiyaya daga idanunta. Dr. Bakori ya tsaya kawai yana kallonta, tausayinta yake ji ko kuwa sonta ne ya haifar da wani irin tausayi me ratsa jiki? Da gaske Bakori yana da bukatar zubar da hawaye indai zai yuwu, domin rage radadin da ke cinsa a zuciya. Jikinsa a sanyaye ya karaso kusa da gadon ya dora hannu a goshinta. Shuru tayi kamar bata motsi, “Meenal me kika yi mata ta azabtar min da ke? Kiyi hakuri laifina ne, daga yau b azan sake amincewa da kowa ya rike min ke ba.Da ga yanzu da kaina zan tsaya ina kula da ke.”

Alluran da suka ajiye ya dauka duk ya dudduba har yaga wanda ya kamata ya zuba mata a cikin ruwan. Yana nan zaune har barci ya sake kwasarta.

Kwanan Meenal biyu ya hana kowa ganinta, har sai da ta murmure sannan ya dauketa ya kaita gun Ummanta. Meenal ta fito tana takawa a hankali, tana ganin Ummanta ta rungumeta gaba daya ba kuka suke yi ba, hawaye suke fitarwa me tsananin dumi.

“Umma inashan wahala. Umma namiji ya mayar da rayuwarmu abin kyama, abin gudu, abin tausayi. Umma ina shan wahala.”
Umman ta kasa yin Magana sai shafa bayanta kawai take yi. Dr. Bakori ya juya kawai ya fice daga gidan.

<< Meenal 6Meenal 8 >>

1 thought on “Meenal 7”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.