Ahmad ya mike da sauri ya rasa ma me zai yi, yana da tabbacin ko kafin a kawo mata audugan mata kayanta za su gama lalacewa. Rigarsa ya cire sannan ya ciro farar vest din jikinsa ya mika mata. Karba kawai tayi a lokacin da aka zo a mayar da ita.
Ahmed yana da bukatar yin wani abu tun kafin lokaci ya kure masa. Bai bar wurin ba, sai da D.p.o din ya yi masa alkawarin zai sa a dubata, kai tsaye Hotel ya nufa ya kama, sannan ya samu ya dan watsa ruwa, yana ji a zuciyarsa, Meenal zata yi kwanan wulakanci.
Shigar kananan kaya ya yi ya fice zuwa gidan su Meenal.
Alhaji Sudais ya dubi Zubaida kanwar Ahmad ya ce ta je ta kira masa Ahmad. Zubaida ta dubi mahaifinta ta ce, “Abba ai dazu Hajiya ta ce masa idan ya shigo gidan nan Allah ya isa ba ta yafe ba.” Abba ya tashi a firgice yana duban Hajiya Zaliha,
“Kin kori Ahmad daga gidan nan?
Alhamdulillahi. Ahmad shi kadai kika Haifa, shi kadai ya rage maki, ni kuwa ina da ‘ya’ya har biyar kin ga kuwa ke kike da asara ba ni ba. Domin rayuwar ɗanki yana cikin hatsari. Ina tayaki murna.”
Abba ya rintse idanunsa yana jin zuciyarsa tana azalzalarsa, yana mamakin lokacin da ta sauya halayyarta. Alhaji Sammani ya shigo falon a fusace, “Yaya danka Ahmad ya ci mutuncina, idan ‘yar uwarsa tana da wannan halayyar sai ya fada a idanun duniya?”
Abba ya dube shi a tsanake, “Sammani naga kamar ka raina ni. Ka kiyayi kanka bana son shashancin banza. Waye ya jawo Ahmad ya fada halayyarta din idan ba kai ba? Akan karamin abu kun jawo matsala ta zama babba. Don Allah ku barni inji da abin da ke damuna bana son wani ya sake kawo min zancen nan.” Abba ya rufe idanunsa kawai yana tunanin zaman Ahmad a waje babban hatsari ne
Haka kawai Ahmad ya sauya tunanin zuwa gidan su Meenal ya kama hanyar mashayar nan. Yana nan zaune idanunsa suka hasko masa Halima, da wani babban mutum, suna zaune suna ciye-ciye. Ahmad ya zare idanunsa yana sake duban Halima.
Idan bai yi karba Halima tana ɗaya daga cikin mutanen Meenal da yake yabawa da halin su. Mikewa ya yi zumbur yana son a yau ba sai gobe ba, yasan wace ce matarsa Meenal, meyasa duk wa’innan matsalolin suke tunkarar Meenal ne? Garin saurin ya tashi ya buge kwalba, hakan yasa ya durkusa domin ya dauka. Hannun mace ya gani itama ta kai hannunta. Dagowa ya yi yana son ganin wacece? “Meenal! Ya furta a zuciyarsa da karfi.
Ji ya yi gabansa ya fadi, ta yaya Meenal din da ke cikin Cell zata bayyana anan wurin? Ya gigice da yawa, sai dubanta yake yi yana son dole sai idanunsa sun gaya masa gizo suke masa ba Meenal ba ce. Amma hakan ya gagara a zahiri Meenal yake gani.” Mikewar da tayi ne yasa shi karantar wani abu a cikin mintunan da ba za su wuce biyu ba. Kafin ya sami karfin halin yin Magana ya ji muryar Halima tana kwala kira, “Meenal!”
Hakan yasa dan abinda ya fara karanta sake subuce masa. Halima ce ta karaso wurin tana aikin dariya,
“An gaya maka ban ganka bane? A tunaninka Meenal ɗinka aka aura ko? To kayi kuskure, ka auri Meenal jabu, ta asalin kuwa tana tare da mu. Muna da irin Meenal babu adadi, muna iya watsa ta a duk lokacin da muka so. Asalin Meenal tana hannun mu a daure, cikin wahalar rayuwa. Uwarta ma da ta haifeta bata isa ta gane wacece asalin Meenal dinta ba. Tunda tasha kwana daki daya da jabun, amma bata sani ba.”
Dr. Bakori ya tattaro dukkan wata natsuwarsa ya watsa hankalinsa abisa fuskar wacce aka kira da Meenal. Kirjinta kadai ya isa ya gamsar da shi wannan ba Meenal ba ce, to idan ba Meenal ba ce a gabansa wacece? Akwai yanayin da Meenal take shiga da zarar ya yabi namiji, har gobe tana nan da wannan halin, don haka ya gyara tsayuwarsa,
“Koma wacece na aura bai dameni ba, nidai nasan Meenal na aura. Idan kuma ke ce asalin Meenal din babu shakka zan kyale wancan intsaya maki, don ki tabbatar da mu maza masu adalci ne.” Dariya ce ɗauke da fuskar wannan Meenal din, tabbas ba Meenal dinsa ba ce, domin bai taɓa ganin dariya a fuskar Meenal ba. Da gaske Meenal dinsa ta tsani maza tsana me tsanani, har yau ɗin nan da ya ziyarceta babu alamun zata rangwanta irin tsanar da ke tsakaninta da namiji.
Abu na karshe da ya rage masa, shi ne ya kama hannun wannan Meenal din. Hannunta ya kama ya murde, tayi kara. Sakinta ya yi tare da girgiza kansa, “Idan Meenal akwai jabu babu makawa wannan ce jabun.”
Bai sake furta komai ba ya bar wurin tare da kiran lambar D.p.o din yana tambayarsa Meenal tana nan? Sai da yasa aka sake zuwa domin tabbatarwa, a zaune aka sameta tayi tagumi, har yanzu hawayen basu daina zuba daga idanunta ba.
A yau dinnan ba sai gobe ba, zai je gun mahaifiyar Meenal sai ta gaya masa abin da ke faruwa. Ta yaya za a sami wata Meenal din? Bayan ga Meenal can a cikin Cell? Wannan karon aguje yake tukin motar da alamun ganganci a tare da shi. Tun bayan da Maigadin ya bude masa gate ya yi parking, bai sake yin birki ba, sai a tsakiyar falon Umma.
Dole ya lalubo natsuwarsa sannan ya iya yiwa Umma maganar da ta kawo shi,
“Umma ba Meenal ce tayi kisan nan ba. Umma ba zan matsa nan da can ba, sai nasan wacece Meenal. Lokacin ɓoye ɓoye ya kare tunda dai a yanzu matata ce, ruwana ne inboye aibunta, haka ruwana ne in tona mata asiri. Umma wacece ‘yarki Meenal?”
Umma ta girgiza kai cikin matsanancin kuka, ita kanta ta gama yanke hukuncin sanar da Dr. Bakori wacece matarsa Meenal. Ya zama dole a yanzu yasan wacece ya aura.
“To idan kuma ya kasa jurewa ya sakar maki ‘ya fa? Idan Dr. Bakori ya gujeku a duniya babu sauran me sake tausayinku.” Ji tayi gabanta ya fadi, ta yi saurin shanye abin da take shirin sanar da shi. Girgiza kansa ya yi kamar ya shiga zuciyarta,
“Na auri Meenal ne saboda bana son insan wacece ita infasa aurenta.
A yanzu ko da Meenal ta kasance ita ke aikata dukkan kisan da ake zarginta da aikatawa, ba zan taba gudunta ba. A shirye nake da na ƙarar da duk wani abu da na mallaka saboda infarantawa Meenal. Ki taimakeni ki fitar dani daga cikin ruɗani ki gaya min wacece matata Meenal?”
Hankalin Umma ya kwanta, ta kuma tabbatar da Dr. Bakori zai aikata dukkan abin da ya fada tunda har zai iya auren Meenal a dai-dai lokacin da hukuma suke zarginta da aikata laifin kisan kai.
A hankali ta dago ta goge hawayen da suka sake zubo mata, bata kaunar dalilin da zai sa ta tuna baya, ba ta kaunar dalilin da zai sa ta gayawa wasu bakar kaddararta. Sai dai ya zama dole yau ta bude abin da Meenal take hana kowa tono shi. Ta fara Magana kamar haka:
“Kafin aje ko ina ba ni ba ce mahaifiyar Meenal!” Dr. Bakori da ya ji wani irin abu ya gilma masa da karfin tsiya ya mike yana duban Hajiya Salma baki a bude. Idan har ta haka sanin Meenal zai kasance masa zai fi kyau ya hakura da neman sanin Meenal.
Girgiza kansa yake yi, da ke barazanar tsinkewa daga jikinsa. Umma ta sharce hawayenta,
“Idan har zaka dinga tsorata da irin wa’innan kalaman, babu shakka kunnuwanka ba za su jure sanin wacece Meenal ba, haka zalika kowacce kalma zata iya tarwatsa tunaninka, daga farkonta har zuwa karshenta. Dole ka koyi juriya ya yin sanin matarka. Haka zalika har yau da nake baka labarin nan Meenal bata san cewa bani ba ce mahaifiyarta ba. Idan Meenal tasan hakikanin abubuwan da ke faruwa, zata iya rataye kanta ta mutu gaba daya.
Dr. Bakori ya hadiye wani abu me daci da ya taso masa, ya koma ya zauna, ba tare da ya iya furta komai ba. Hakan yasa Umma ta cigaba da maganarta,
“Mahaifiyar Meenal ba musulma ba ce, haka kuma ta fito ne daga Jihar Gombe. Na hadu da ita a cikin B.U.K dake Kano. Dakinmu daya da ita. Hakan yasa mana wata irin shakuwa da juna. Baban Alheri wani pastor ne me tsattsauran ra’ayi, hakan yasa Alheri ta zama mace me tsananin kamun kai, da gujewa abinda zai bata mata karatu. Kullum zaka ganta dauke da Bible dinta. Mutane da yawa sunyi mamakin yadda akayi ina ‘yar gidan malamai kuma na shaku da Alheri haka.
Alheri tana da kyau sosai, haka kuma bata kula maza. A irin lokacin ne Munnir dan sarkin Gombe ya kyalla idanu ya ganta. Duk hanyar da zai bi ya bi don ta kula shi abin yaci tura.
Dan haka ya kafa mata tarko, mun fita siyayya yasa aka sato ta. A cikin dakinsa ya yi mata fyade.”
Dr. Bakori ya rintse ido yana jin tamkar yana wurin wannan abubuwan suke faruwa. Umma ta goge hawayenta ta cigaba da Magana, “Wannan hali da Munnir yasa Alheri a ciki yasa ta fita hayyacinta, kullum cikin kuka take yi, ta daina zuwa daukar karatu.
Rana na biyu ta fito da kyar ya sake sawa aka sace ta. Munnir ya daure Alheri ya dinga aikata duk abinda ya gadama da ita.
Sai da ya zamana bata ko iya tafiya. Haka ta daina ci ta daina Magana, kullum sai dai kaga tana hawaye. Dole ta tattara ta koma garin su, sai dai kafin ta tafi daga ni har ita muka yi musayar adireshi, duk da dama can tasan gidanmu.
Da komawarta tayi ta ciwo aka rasa meke damunta, binciken farko aka gano tana dauke da ciki. Tayi kuka kamar ranta zai fita, haka mahaifinta ya koreta daga gidan. Ta ki tafiya tana rokonsa, don haka ya gindaya mata dokar dole taje a zubar da cikin nan tun kafin mutanensa su ankare da cikin. A lokacin Alheri ta gaya masu babu abinda take so a duniyarta kamar cikin jikinta. Mahaifinta ya kama ta ya daure a cikin wani daki, kullum da kalar azabar da yake gana mata. Amma zuciyar Alheri ta riga ta kekashe akan son da take yiwa cikinta.
A cikin irin azaban da take sha ne, mahaifiyarta ta kwance ta, ta bata Gold dinta me tsada ta ce ta siyar ta ja jari ta fice daga garin idan ba haka ba, mahaifinta zai iya kasheta. Tana kuka ta fice daga gidan, kai tsaye Kano ta nufo. Da isarta ta kai Gold din aka siyar ta nemeni a lokacin ina gidanmu. Ina ganinta hankalina ya tashi, ta gaya min dukkan abinda ke faruwa, ni na hada ta da wanda ya samo mata dan karamin gida ta siya. Anan ta fara rayuwarta da cikinta.
Nima a wannan lokacin na sami miji nayi aurena. Don haka haduwar mu da Alheri ya yi wahala.
Cikin ikon Allah Alheri ta haihu, da kanta ta zabawa Meenal sunan musulunci, wanda Allah ne kadai yasan dalilinta. Ta dauki kaunar duniyar nan ta dora akan Meenal. Da ita take fita sana’ar siyar da kosai a kasuwa, tun kafin ta cika sati biyu da haihuwarta. Tun Alheri suna iya samun abincin da za su ci, har dan jarin ya karye.
Ta koma tana aikatau a wani gida, suka nuna mata basu son tana zuwa da yarinya, dole ta dinga ajiye Meenal ita kadai a gida. Ranar da ta dawo ta sami Meenal din kwance cikin kasa gini da ya fado ya zubo mata. Ta gigice tayi ta kuka tana rokon a taimaketa ‘yarta ta mutu, amma babu wanda ya tausaya mata. Haka tana rungume da yarinyar da ba ta motsi tana rizgar kuka.
Daukar yarinyar tayi tasa a baya ta bi titi tana nuna masa yarinyar da bata motsi tana fadin a taimaketa. Karshe sai aka koma yi mata kallon mahaukaciya. Hakan yasa ta hakura ta dawo bakin asibiti tana kuka har aka samu wata baiwar Allah ta ce a duba ta ita zata biya kudin.
Da kyar aka samo numfashin Meenal.
Duk wanda yasan Alheri a baya idan ya dubeta a yanzu da wahala ya shaidata. Gininsu da ya zube hakannan suke kwana a ciki. Idan dare ya yi ita ke samo tsummokara ta boye Meenal a ciki ita kuma ta kwanta cikin sanyi. Da ruwan sama yazo sai hankalin Alheri ya kara tashi, saboda babu inda za su fake. Hakan yasa rana guda ta share wuri ta fara ɗiban kasan da ya zube da sauran bulo din, ta gina dakin awaki, ta dibo abubuwan da zata rufe duk ta rufe, sannan ta dibo kayan shimfidansu suna kwanciya a ciki.
Idan dare ya yi sai ta dauko wani langa-langa ta rufe su. Haka take zama bata iya barci tana tsoron kada sauro ya ciji Meenal kada tayi zazzabi dan bata da kudin maganin sauro bare akai ga kudin zuwa asibiti.
Makocin su, ko alama bashi da imani daga shi har matarsa. Ranar da yunwa ta isheta ne ta leka gidan makocinta akaro na farko tana rokon su abinci, budar bakinsa sai ce mata ya yi, yaga ta gina kejin awaki idan ta yarda zata dinga zuba masa awaki suna kwana a ciki to zai dinga bata abinda zata ci. Ba tare da dogon tunani ba, tace ta amince zata dinga kwana da awakin.”
Umma tana kawowa nan ta dinga shessheka. Jikin Dr. Bakori ya gama yin sanyi. Ko a haka aka bar rayuwar Meenal dole ta zama abar tausayi. Yana son jin ta yadda mutum dan adam zai kwana guri guda da dabba. Umma ta ci gaba da magana muryarta tana rawa,
“Awakan da Malam Adamu ya hada Alheri da su sun fi karfin dakin da ta gina take kwana da ‘yarta, sai ya zamana tana rabewa a gefe tana barin awakin anan. A wannan lokacin Meenal ta soma wayo domin tana cikin shekara guda a cikin adadin shekarunta a wancan lokacin. Abin damuwar abincin da ake baiwa Alheri, bai taka kara ya karye ba, idan tuwo za a bata, sai ya kasance garin da aka samo daga kasan inji ne aka tuke mata. Haka zata baiwa Meenal. Watarana barci ya kwashe ta, hakan yasa awakin nan suka tattake Meenal, tana ta ihu amma alheri ba ta ji ba. Kamar a mafarki take jin kukan Meenal, don haka ta bude ido ta daga yarinyar. Itama sai ta kama kuka. Haka ta dinga rarrashin yarinyar amma bata daina kuka ba. Gari na wayewa ta leka ta gayawa Malam Adamu abinda ya faru, babu amsa me daɗi haka ba a taimaka mata ankai ‘yarta anduba hannun ba.
Da kanta ta dinga daure mata hannun tana gasa mata da ruwan zafi. Abinda ba ta sani ba, idan ta ajiye Meenal zata dan fita nema masu wani abun, sai Meenal ta taka taje dakin awakin nan ta ci kashin awakin. Da zarar ta ji yunwa dama kashin awaki take zuwa ta ci. Kafin wani lokaci cikin yarinya ya haye, sai zawo. Alheri tayi kuka tayi kuka ta gode Allah. Haka ta ding aba yarinyar kanwa, tunda babu kudin zuwa Asibiti.
Haka suka kawo wa awakin su ragowar tuwo da yaran suka ci suka bari, suka hada masu da dussa, saboda kada Alheri ta ci. Ta faki idanunsu ta dibi tuwon nan a cikin dussa ta wanke ta dama masu hakannan babu suga suka sha.
Haka rayuwar ta cigaba da tafiyar masu har Meenal ta shiga shekaru uku a duniya, a lokacin bakinta ya bude, haka sai ta faki idon uwar ta shige gidan Malam Adamu. Da kuka take fitowa hakan yasa Alheri ta dauketa tana kuka tana gaya mata ta daina zuwa ko ina basu da kowa sai Allah. Watarana Meenal ta kama hanya ta shiga gidan Saude, a lokacin Saude tana cikin fushi, don haka ta dinga aunawa Meenal zagi tana fadin ita ta tsani dan shege yana shigar mata gida, bacin rai da rashin imani yasa ta dauki Meenal ta tsoma a ruwan zafi ta cillota waje.
Aranar Alheri tayi kuka, kamar ranta zai fita.
Da kanta ta kwaye mata ciwon tana wanke mata. Haka zalika ta mayar masu da awakin su ta koma kwana daga ita sai ‘yarta me kuna. A maimakon ciwon Meenal ya yi sauki sai abin ya sake rincabewa.
Gashi ko zanin rufuwa basu da shi. Hakan yasa Alheri tabar unguwarsu ta tafi wani unguwa taga anyi shanya ta saci zani tana ninyar guduwa aka yi mata ihun barauniya.
Anan aka rufeta da duka, da kyar wani mutum ya dakatar da dukan yana tambayar me ta sata? Da aka gaya masa ya girgiza kansa kawai yah au mutanen da fada. Ya dauki kudi ya ba ta kai tsaye ta koma gida, bata damu da wahalan da tasha ba ta dauki ‘yarta ta kaita Chemist aka wanke kunan aka bata magani.
Ranar da ta tashi babu lafiya, ko hannunta ba ta iya dagawa saboda azabar ciwo. Meenal din tana gefenta tana aikin kuka. Tana ji tana gani ba ta da ikon taimakon ‘yarta bare har ta sama mata abin da za su ci. ‘Yar tana kuka uwar tana daga kwance hawaye na bin fuskarta. Da kukan Meenal ya yi yawa, kawai Alheri ta rungumeta a kirjinta tana buga bayanta dan babu abin da zata iya yi mata.
A haka suka kwana cikin halin yunwa a cikin wannan kejin awakin. Rana na biyu ne cikin dare Alherin ta lallaba ta shiga gidan Saude ta leka kichin dinta ta kankare kanzon shinkafa tana lallabawa zata fita, Saude da ta fito bayi tana kallon ikon Allah ta rike ta tamau, ta kwarara ihu tana fadin ta kama barauniya.
Mutane da yawa suka fito kowa yana fadin a fito da ita kawai su kona ta. Wata mata ta ce me ta satar maki? Babu kunya ta ce kanzon shinkafa ta satar mata. Daga me jan tsaki sai me juyawa kawai yana tafiya, matar nan ta dubi Saude ta ce, mata taji tsoron Allah, kanzon nan zubarwa za su yi. Saude ta ce aikuwa da ta bawa mazinaciya abincinta ai gara ta zubar. Ta kwace kanzon ta watsar tana harararta. Alheri ta durkusa bisa guiwowinta tana kuka tana rokon Saude da ta taimaka mata ‘yarta zata iya mutuwa saboda yunwa.
Amma fir Saude ta hana. Haka ta ja jikinta ta fice ta dauki Meenal ta rungume tana kuka.”
Umma ta sharce hawayen fuskarta tana duban Dr. Bakori ta ce,
“A gaskiya Doctor kafin a sami uwa irin Alheri za a dade. Alheri ta bar dukkan gatanta saboda Meenal, Alheri ta fuskanci jarabawa iri-iri a dalilin Meenal. A wannan daren wata mata ta yi sallama kofar dakin awakin nan ta mika mata abinci. Duk da irin yunwar da ke azalzalar Alheri hakan bai sa ta damu da cikinta ba, har sai da taga Meenal ta ture kwanon alamun ta koshi. Duk da haka sai ta ajiye mata akan gobe zata dumama mata ta samu ta ci.