Gabaki daya satin wani irin sama-sama take jinta, kamar wadda take yawo a saman gajimare, ko tafiya takeyi sai ta dinga jinta kamar reshen bishiya saboda nishadin da take ciki. Babu rana daya a cikin satin da ta wuce batare da tayi magana da Hamza ba, yana kiranta, duk da baya mata wata magana da ta shafi wani abu banda Architecture, jiyane kawai ya bukaci sanin inda take karatu. Ta kuma fada mishi, muryar shi wani irin sanyi take mata, duk yanda take a bude. Hausar shi tafi komai burgeta, bawai bai iya bane, akwai yanda yakan fitar da. . .