Bashi ya sami kan shi ba sai wajen karfe goma na daren ranar, wata irin gajiya yakeji har cikin kasusuwan jikin shi. Ko da Fodio yayi mishi tayin zuwa club, kai kawai ya iya girgiza mishi. Yanzun yana shigowa gida, ruwa ya watsa ya sake kaya yana fitowa falon gidan jin cikin shi da ya tattare ya kulle gefe daya saboda yunwar da yakeji. Wata zuciyar na mishi Allah ya kara da bai wuce gidansu ba, da yaci abincin Anna. Tunanin hakan kawai ya kara mishi yunwa. AbdulHafiz kadai ya samu a falon yana zaune kan kujera ya jingina kan shi, idanuwan shi a lumshe da earpiece a kunnuwan shi.
Dan tabashi Hamza yayi dan yasan ko yayi magana ba jin shi zaiyi ba, kunne daya na earpiece din AbdulHafiz ya cire yana kallon Hamza da fadin
“Meye ne?”
Saboda yanda ya takura shi, karatun Qur’ani yake ji cikin muryar Sheikh Abdullahi Abba, da Nabila ce ta koya mishi son qira’ar mutumin, lokutta da dama idan ya zauna shi kadai bayaso tunanin duniya ya dame shi yakan saurara, nutsuwar da take saukar mishi daban take, sam bayason ayi mishi magana a lokaci irin wannan
“Me kaci?”
Hamza ya tambaya, numfashi AbdulHafiz ya sauke, shisa yayo musu take away, wanda zaici yaci, wanda ba zaici ba ya saka a fridge, idan yunwa ta koro wani zai dunduma a microwave din da shi ya siya. Lokutta da yawa yana mamakin yanda zasuyi inda baya nan. Yasan yanzun haka kowa zai dawo da yunwa tunda ya rigasu barin wajen aiki, da tunanin shi din ya nemar musu abinda zasuci
“Ka duba Kitchen”
Ya fadi yana shirin mayar da earpiece din shi
“Me ka siyo? Meye?”
Harara ya watsa ma Hamza
“Karka dameni, kaje ka duba, idan bakaci ka ajiye. Dan Allah ka kyaleni”
Murmushi Hamza yayi, yasan magana ce AbdulHafiz din bayason yi, yana sane shisa yake son saka shi yinta dole
“Uban me kake ji?”
Hamza ya tambaya yana kai hannu ya cire earpiece din da yake hade da wayar AbdulHafiz din, sai dai zarewar da yayi ya saka karatun shiga Pause, numfashi AbdulHafiz ya sake saukewa, ya danna play, karatun na gauraye shirun da dakin yayi, kafin ya kalli Hamza, kallon da yake fassara ‘Sai kuma me?’. ‘Yar dariya Hamzan yayi yana girgiza mishi kai.
“Ustaz AbdulHafiz, yau kuma Ash-Shura ake ji kenan. Allah ya bada lada.”
Earpiece din AbdulHafiz ya mayar, yakan yi mamakin Hamza, babu inda zaka ja a Qur’ani bai cigaba ba, babu kuma inda yake mishi wuyar fahimta, yanda zai zauna yana ja maka ayoyi yana fassarawa, zakace bashi bane idan kuka hadu a wani club din da mace rungume a jikin shi, shisa duk a cikinsu yafi jin haushin lalacewar Hamza, gashi da sanin da zai amfani al’umma ba kan shi kadai ba, sam yabari shaidan yayi galaba a kan shi. Hamza kuwa kitchen ya wuce yana daukar take-away guda daya cikin wanda suke jere a kitchen din, ya bude fridge ya dauko coke ta gwangwani, ya dawo falon ya zauna kasa kan kafet yana budewa, soyayyen danlalin turawa ne, plantain, kwai sai naman kaza.
Sai da ya fara ci tukunna yai tunanin cire wayar shi daga flight mode din daya sakata dan kar wani ya dame shi da kira yana aiki. Duk yinin ranar tun da suka rabu da Hindu ta kara samun waje ta manne a cikin kan shi, zai rantse da Allah har yanzun yanajin yatsun hannunta a cikin nashi. Sai dai a cikin idanuwanta ya karanci bakuntarta a kalar tashi rayuwar, ta waye ta yanayin hirarta da maganganunta, amman ba kalar wayewar shi ba, idanuwanta ba’a bude suke ba, zai kuma ji dadi ya zama na farko daya bude mata su.
‘Ya gajiyar ki, kin ga ban kira ba ko? Sai yanzun na shigo gida ma, abincin zanci, nagaji har cikin kasusuwan jikina Allah.’
Ya tura mata ta text, yana shiga tana biyo shi da amsa,
‘Gajiya tana wajen ka ai, sannu. Sai ka kwanta ka huta.’
Kai ya jinjina yana kurbar coke din shi
‘Sai naji muryarki tukunna.’
Ganin ta dauki mintina bata dawo mishi da amsa ba, ya tabbatar da batasan yanda zata amsa maganar da yayi ba.
‘Ke me kike yanzun?’
Ya bukata, ga mamakin shi ta whatsapp ta mayar mishi da amsa,
‘Na dan yi karatu, ina da test. Ina zaune kawai.’
Amsa ya fara rubuta mata, kafin tunanin kudinta ne zai iya karewa shisa tayi mishi magana ta whatsapp maimakon ta amsa mishi ta text ya fado mishi, sauka yayi daga whatsapp din, AbdulHafiz kance.
‘Sai kayita chatting da yarinya, kasa ta turo maka hotuna ko video, ko kai ka tura mata. Na rana daya ba zakayi tunanin data dinta da kake kararwa ka tura mata da kati ba. Saboda rashin sanin ya kamata.’
Duk shi ya koya musu wannan dabi’ar, Hamza ma ya rigada ya saba, ko ba budurwa ba, in yana tunanin ba wasu kudin kirki gareka ba, zai tura maka kati yace kayi sub da shi. Shisa yaran da kanyi aiki a karkashin shi suke yabawa da yanda bashi da mugunta, hannun shi kuma yake a bude. Yanzun ma bankin shi ya shiga yana tura ma Hindu katin dubu biyar. Kafin ya fita ma yaga sakonta ya shigo ta saman wayar. Budewa yayi yana ganin emoji din mamaki da ta turo mishi.
‘Kai ka turomun da kati ko?’
Kafin ya amsa ta dora da
‘Har dubu biyar, katin dubu biyar. Yayi yawa.’
Murmushi yayi, dan shikam bai dauki katin dubu biyar wani abu ba.
‘Karkiyi ‘dan karatu’. Kiyi da yawa, ina son inga test score din idan kun gama.’
Ya tura maimakon amsa abinda tace, da gaske yake kuma har ran shi, yana son gani, batayi mishi kama da marar kokari ba, tunda take Architecture, amman zaisa ta kara dagewa in har hakan zai yiwu.
‘Kar ka canza maganar nan.’
Wannan karin shiya tura mata emoji din harara.
‘Kar kiyi kamar baki gane bana son maganar ba, zan sauka idan kika sake mun.’
Bayason godiya, shine lokaci daya da yakan tabbatar da yana da kunya. Musamman kan karamin abu kamar katin dubu biyar.
‘Yi hakuri. Nagode sosai sosai.’
Haka kawai yaji ba zai iya hakuri ba, muryarta yake son ji har tsikar jikin shi tashi takeyi. Sauka yayi daga whatsapp din yana kiranta, bugun farko ta dauka, muryarta da ta daki kunnen shi na kara mishi yanayin da yake ji.
“Da gaske jikina ciwo yake.”
Ya sake fadi yana gyara zaman shi, yar dariya ta ji.
“Na cika lalaci ko?”
Ya tambaya, yanaji a jikin shi kai ta girgiza mishi
“Ka gama cin abincin sai ka kwanta.”
Dankalin ya diba yana sakawa a bakin shi ya tauna.
“Bana son magana ina cin abinci, amman gashi na kira ki.”
Yayi maganar da dukkan gaskiyar shi, hakan bai taba faruwa da shi ba, amman yanda yake son jin muryarta, da bai kira ba, abincin ma ba zai ciyu ba. AbdulHafiz da yake zaune ne ya kula da kamar waya Hamzan yake. Hakan yasa karatun da yake ji na karewa, kafin wani ya shigo ya tsayar yana zare earpiece din daga kunnuwan shi hadi da kallon Hamzan da matukar mamaki. Dan yanayin maganganun ya tabbatar mishi da ba Anna bace ba. Kuma yaga abinci yake ci, dan rankwafowa yayi yana kai hannu ya taba fuskar Hamzan daya janye yana fadin.
“Zan kira ‘yan Hisba, lafiya? Ya kake taba mun fuska da daren nan?”
Dariya kawai AbdulHafiz yayi dan yaji lafiyar Hamzan kalau, babu zazzabi a jikin shi, coke din da yake ajiye a gaban shi ya dauka yana shinshina wa yaji ko ba zallar coke bace ba, dan sosai yake mamakin yanda akai Hamza yake magana yana cin abinci, bai damu da harar shi da Hamzan yake yi ba, ko yanda ya fisge gwangwanin coke din yana ajiye cokalin da yake hannun shi cikin abincin hadi da mikewa. Rigar shi AbdulHafiz ya janyo ta baya yana nuna mishi kwanon daya bari.
“Dan Allah AbdulHafiz ka kyaleni, ban gama ba ai, abu zan dauko in dawo.”
Hamzan ya fadi yana dakuna fuska, kitchen ya koma ya bude fridge, akwai section guda daya daga gidan saman, tunda fridge din na tsaye ne da babu mai taba mishi, karamar kwalbar giyar shi ya dauka yana kwancewa, a kitchen din ya tsaya, har lokacin da wayar shi manne a kunnen shi, yanajin Hindu na mishi bayanin tambayar da yayi mata, dan ta gaya mishi akan me test din da za’a yi.
“Dubawa kikeyi ko? Bana son cheaters.”
Dariyar da tayi na saka tsikar jikin shi ta shi, akwai babbar matsala, yai wannan tunanin yana daga kwalbar shi ya sha kusan rabi tukunna ya ajiye.
“Allah ban duba komai ba, inda ka tambaya tun jiya nake karantawa.”
Kai Hamza ya jinjina mata yana sake daga kwalbar ya tuttula ma cikin shi, yanajin yanda jikin shi ya soma daukar dumi na daban, amman yaki dishe wanda muryar Hindu yake haifar mishi. Numfashi ya sauke mai nauyin gaske, yana saka Hindu fadin.
“Gajiya ko? Ka kwanta dan Allah.”
Kai ya jinjina mata.
“Yanzun nan….zamuyi magana da safe?”
Sake ji yayi kamar ta daga mishi kai, kafin tace,
“In shaa Allah. Allah ya hutar da gajiya. Nagode sosai.”
Wayar ya sauke daga kunnen shi batare da yace komai ba, tukunna ya dauki kwalbar yana karasa shanyewa, ya jefa cikin kwandon shara, falon ya koma, yanajin idanuwan AbdulHafiz na bin shi da kallon tuhuma, a karo na farko da yaji dadi AbdulHafiz ne, ba zai taba tambayar shi ba, duk yanda yake so yaji kuwa, in dai bashi ya bude bakin shi yai mishi wani bayani ba, a cewar shi
‘Idan mutum naso kaji abu, zai fada maka da kan shi, lokacin daya shirya, ba saika matsa mishi da tambayoyi ba. Kuma babu kyau jin kwaf.’
Gabaki daya rayuwar AbdulHafiz akan tsarika yake tafiyar da ita. Yau dai Hamza ya godema hakan sosai, saboda baya cikin yanayin da zai iya tsayawa bayani, robar da sauran dankalin yake ciki ya dauka da murfin yana mayarwa kitchen ya rufe ya ajiye. Sannan ya wuce dakin shi. Kayan jikin shi ya canza. Bacci ya kamata ace yayi, kafin ya kira Hindu ya sake rikita kan shi abinda yake da niyyar yi kenan. Amman yanzun kam labari ya sha banban. Akwai yarinyar daya kamata su hadu tun satin daya fita, ya tsaya yana mata yanga. Saboda ba ta wani yi mishi bane ba, balle kuma yanzun da idanuwan shi basa ganin kowa Sai Hindu, baya son kasancewa da kowa sai ita din.
‘Zamu iya haduwa nan da mintina talatin?’
Ya tura mata text din da yana shiga ta dawo mishi da address din inda zai dauketa din. Zai iya karasawa wajen cikin kasa da mintina sha biyar ma, in dai ba ya sami cunkoso a hanya ba. Mukullin mota ya dauka yana fitowa.
“Komai zai iya faruwa da kai a hanyar zuwa din kafin ka karasa, ko idan ka karasa koma ina ne kake shirin zuwa. Zaka iya mutuwa a kowanne lokaci wallahi, tun da sallama takeyi ba”
Hanci Hamza yaja da yake jin kamar wani yaji a cikin hancin nashi da maganganun AbdulHafiz suka haifar mishi, kafin ya juyo ran shi a bace.
“Me yasa kake son shiga rayuwa ta ne haka AbdulHafiz?”
Cikin takaici AbdulHafiz yake kallon shi, ya tsani kalar rayuwar nan daya zabar ma kan shi, ba kadan ba, har kasan zuciyarshi yake jin dacin hakan.
“Na fada maka, mutuwa bata sallama, zata iya daukar ka ko me kakeyi”.
Tsaki Hamza ya ja yana sa AbdulHafiz fadin.
“Karka sake, bana so, karka sake mun tsaki Hamza, karka sake.”
Yana sane yayi, bata mishi rai yake sonyi kamar yanda na shi yake a bace, duk da yasan ko me yasha ba zai sake din ba, baya kure hakurin AbdulHafiz din, ya tabayi sau daya, dakyar suka koma dai-dai. Bai sake ba, baya fata ya sake kuma. Juyawa yayi yana ficewa daga gidan. Yaji dadi da motar AbdulHafiz dince, ya ma manta bai karbi mukullin shi ba. A ciki zai dauki yarinyar, da ita kuma zaije hotel din da yayi niyya. Yasan dai inya dawo sai AbdulHafiz yasa an wanke mishi motar daga cikinta har wajenta, kamar wanda ya kwaso mishi wani mugun abu a jiki.
Baice ba zai daina halayyar da yakeyi ba, amman AbdulHafiz din yakan saka shi jin kamar lokaci zai iya kure mishi a ko da yaushe kafin ya tuba. Bayan shi bama kwana zaiyi ba, yana gama abinda yakeyi zai zare jikin shi, ya fito ya dawo gida, komin dare kuwa, bai taba kwana da wata yarinya a waje daya ba, idan ita bata kama hanya ba, shi zai kama, ko da a cikin hotel dinne, idan bayason komawa gida, zai fita ya sake kama wani dakin daban. Shi bama yason jin mutum a kusa da shi idan har bacci zaiyi, ko da macece kuwa, duk yanda yake son mata, baya iya bacci kusa da daya daga cikin su.
*****
Ranta kal take jin shi tana gama waya da Hamza, duk yau taki sakewa ta fita falo ta zauna. Sai take ganin kamar Anty zata gane ta fita da wani, kamar zata gane Hamza ya rike hannun ta, ko da ta shiga alwalar la’asar bayan ta dawo, sai da ta saka sabulu ta wanke hannunta, ta jima a sujjadarta, cikinta ta dinga neman yafiyar Ubangiji, ko sallar isha’i da tayi hakan ya kasance, bata dago goshinta sai taji kafafuwanta sunyi sanyi. Saboda so take zunuban da take jin nauyinsu su kakkabe su fado. Sai dai zuwa yanzun da suka gama waya da Hamza, ba tunanin zunubanta takeyi ba, tunanin shi takeyi.
Muryar shi na amsa kuwwa a zuciyarta, koya ta juya sai taga fuskar shi a zuciyarta, murmushin rashin dalili takan ji ya kwace mata cike da wani irin shauki, sanin babu wani abin da zata iya tabukawa, yasa ta shiga manhajar Instagram dan ta more kallon hotuna, tana kuma son duba shafin teloline, har yanzun bata gama yanke hukuncin telan da zai mata dinkunan bikinta ba, so takeyi ta sami ko guda ukune, in yaso daga baya saita zabi guda daya. Haka kawai take jin kamar bikin nata ya matso kusa duk da ba’ayi maganar shi ba, zuciyarta bata taba gaya mata karya ba. Gara ta zaba da wuri kafin lokacin ya kure mata tazo tana hanzari a al’amarin.
Tana refreshing shafin tana cin karo da Nabila da ta saka hotuna har guda uku, tsayawa tayi na farkon ya bude. Sai taga AbdulHafiz ne, akan wani doki mai fari da ratsin baki, dokin kan shi koshin da yayi abin kallo ne, yana sanye da kayan sarauta a jikin shi, kan shi nade da farin rawani daya rufe rabin fuskar shi, da alamun murmushi cikin idanuwan shi, daga kasa ta saka caption din.
‘Tafiya dai kwaro, bajimi sai horo, diyan ka basu ruwa. Jikan Shehu mai hidima, Allah ya kare mun kai Dikko na.’
Sauran hotunan biyu takai da sukayi mata kyau matuka. Ita kam ba zasu daina burgeta ba, tana duba comments kuwa sai ga na AbdulHafiz a farko.
‘Gaba ke, baya ke, babu kamar ke Fulani.’
Sai taji kamar fitilar Hamza nason dishewa a ranta. Akwai wani abu tattare da Sarauta da yake burgeta har cikin kasusuwan jikin ta, lokutta da dama takan ji daman ace ita din ta fito daga gidan Sarauta ne. Kasa duba shafikan telolin tayi, ta saka wayar a key tana yin addu’ar bacci, tukunna ta juya hannu tana lumshe idanuwan ta, da fatan Allah ya taimaketa ta samu bacci. Aikam baccin tayi cike da mafarkin Hamza ya zama sarki, ita kuma ta zama Sarauniya, tana gefen shi tsaye ana zuba musu kirari.
Ita kanta da safe da ta tashi sai da dariya ta kamata. Yau saboda tana cikin farin ciki kitchen ta wuce ta fara sharewa, babu ma wanke-wanke, da alama Asma tayi da dare. Doya ta fere ta dora, sannan ta fito ta share falon ta gyara ko ina. Ta koma ta tace doyar, lokacin Asma ta fito itama
“Sannu da aiki. Ni me zan tayaki?”
Kai Hindu ta girgiza mata
“Kije kiyi shirin islamiyya abunki, doya kawai zan soya mana.”
Dan tsaye Asma tayi.
“Ko ki kawo in soya doyar to.”
Dan murmushi Hindu tayi, tana da tabbacin Asma ta gyara musu daki kafin ta fito.
“Asma ki wuce ki kyaleni, kullum ba ke kikeyin aikin ba?”
Dariya kawai Asma tayi tana wucewa ta koma dakin su. Ita aiki bata dauke shi komai ba. Doyar kuwa Hindu ta fara soyawa, ta kunna karatun Qur’ani da take tabi a hankali, Zaid ya shigo kitchen din.
“Me kike soyawa? Ina ci… Yunwa nake ji.”
Dan juyowa tayi ta kalle shi.
“Yaya… Ina kwana. Doya ce fa, amman ban dafa ruwan zafi ba tukunna, bari in duba maka a flask ko akwai saura.”
Kai Zaid ya girgiza mata, tashi yayi cikin shi kamar anyi sata.
“In da miya ki saka mun, idan babu kibani a haka nikam, kyale ruwan zafin nan.”
Plate ta dauka ta dibi doyar ta zuba mishi, tana karasawa ta bude tukunyar miya da take ajiye ta zuba mishi a gefe. Sannan ta mika mishi, ya karba da fadin.
“Nagode sosai.”
Ya fice, duk baudadden halin shi, koya kayi mishi abu sai ya nuna maka yaji dadi. Ko shara ya saka idan kayi, ko da baya kusa ya dawo yagani sai yazo ya sameka yace maka ya gode. Akan ce maza basu cika nuna jin dadin su akan al’amura ba, ita kam ta yarda maza nada banbanci halayya, kowa da yanda na shi yake, dan Zaid kawai yasa ta karyata wannan fadar da mutane kanyi. Ko Anty tana cewa matar shi zata sha wahala da halayen shi da yawa, amman idan ta fahimce su zasu dade basu sami matsala ba, dan shi mutum ne mai saukin kai. Kuma kamar yanda zai nuna maka yaji dadi in kayi mishi abu, haka zai nuna maka baiji dadi ba idan kayi mishi ba dai-dai ba.
Tana karasa soyawa, ta gyara takardar ta rufe kular, dan kar zufa ta koma cikin doyar shisa ta saka takarda a kasa. Tasu ita da Asma ta dauka tana kai musu daki, sannan ta dawo ta duba flask, akwai ruwan zafi, shayinta kawai ta hada, tunda tasan bai dami Asma ba, shisa ma ta saka musu miya a gefe. Tare suka karya yau suna dan taba hira, har suka gama cin doyar. Asma ta dauke plate din da kofin da Hindu tasha shayi ta mayar kitchen, hijabi ta dauka da jakarta tana fadin
“Ni kam na wuce.”
Hindu na amsa ta da
“Kina da kudine a hannun ki?”
Dan yini sukeyi ranakun asabar da lahadi
“Ina da Naira dari.”
Tsaki Hindu taja a fili, dan tasan Asma ba shiga wajen Baba zatayi ba kafin ta wuce din, tana rasa kalarta wasu lokuttan, ko kudine idan ba’a dauka an bata ba, ba zata taba bude bakinta ta tambaya ba.
“Ki mikomun jakata din can, ke ba zaki taba bude baki ki tambaya a baki kudi ba, banza kawai. Uban me zaki siya da Naira dari? Salon ulcer taje ta kamaki a banza.”
Asma dai batace komai ba, murmushi kawai takeyi, ita abubuwa irin haka basa bata mata rai. Jakar ta mika ma Hindu, ta bude tana bata dari biyar. Dan ita ko ranar juma’a sai da Baba ya bata kudi.
“Nagode sosai.”
Asma ta fadi, tana saka Hindun sake jan wani tsakin. Dariya kawai tayi ta fice daga dakin. Hindu kuwa wayarta ta dauko ta duba taga ko Hamza yai mata magana, amman shiru. Tana tunanin ko ta tura mishi sako taji ya tashi lafiya. Ko kuma ta kyale shi, duk da Dimples kance mata.
‘Matan Hausawa na da matsala, sun ma jan aji mummunar fahimta. Su a ganin su jan aji shine namiji ne kawai zai dinga kiranki, idan shi bai miki magana ba ke ba zaki taba mishi magana ba, idan chatting kuke ki dinga amsa shi dai-dai. Kowa fa nasan kulawa, idan bai kira ki ba, ba wani abu bane dan ke kin kira kin duba shi, aji na cikin kama mutuncin ki, karki taba rokon shi wani abu, kisan me kikeyi. Amman ina amfanin bakiyi mishi magana ba, amman yana kira kina makale murya kina fadin sub dina ma ya kare.’
Yar siririyar dariya Hindu tayi yanzun ma, babu yanda za’ayi kai mintina biyar da Dimples bakayi dariya ba. Amman a cikin abinda da yawa kan dauka rashin hankalinta, akwai maganganu masu tarin ma’ana, text tayiwa Hamza.
‘Ka tashi lafiya? Ya gajiyar ka?’
Sannan ta ajiye wayar tana shiga tayi wanka ta fito. Duk da babu inda zataje bai hanata yin kwalliya ba, ta feshe jikinta da turaruka masu karfi tunda tana gida. Doguwar riga ta saka ta material ja da baki daya karbi jikinta, ta sami hula kalar kayan ta saka a kanta tana dan turata baya. Tayi kyau dai-dai ita, sannan ta dauki wayarta tana dorawa kan drawing table dinta, ta dibo kayan zanenta, ta saita takarda, sai da ta saka earpiece a kunnuwanta ta hada da wayar tana sauraren wakokin Ed Sheeran, sannan ta fara zanenta. Jin alamar shigowar sako yasa ta mika hannu ta dauki wayar tana dubawa, Hamza ne.
‘Alhamdulillah. Ke ya kika tashi? Vid call?’
Tana karanta ta zare earpiece din daga kunnenta da sauri, ta tura kujerar da take zaune kai baya tana mikewa, mayafi ta dauka ta nade kanta dashi tana gyara mishi zama. Tukunna ta tura mishi
‘Sure’
Tana komawa manhajar whatsapp, saiga kiran shi ya shigo, kunne daya na earpiece din ta makala tana daga kiran, kyakkyawar fuskar shi na cika screen din wayarta, tana saka ta tunanin yanda mutum zai kasance da kyau haka. Hannu yadan dago mata yana murmushi, a kunyace tace
“Ina kwana”
Maganar da alama ta dade bata kai mishi ba
“Lafiya lau, kin yi kyau.”
Ya furta yana sakata ware idanuwa, dan tasan idan yana waje babu wanda zaice tana da kyau
“Zolaya ko?”
Hakoran shi ta fara gani kafin taji yayi dariya, sai dai kafin tace wani abu taga ya juya yana kokarin ture wani da yake son leqowa, amman sai da ya leqo din.
“Hello, Fodio ne”
Tana kallo Hamza ya kauda fuskar wayar dan taga alamun kujeru, batajin me yake cewa dai, yakai mintina biyu sannan ya dago taga fuskar shi.
“Kiyi hakuri, zakiyita ganin kalar abubuwan nan, abokai na sai hamdala.”
Yar dariya Hindu tayi.
“Bakomai. Ka gaishe da Fodio din.”
Kai ya jinjina mata.
“Zan fita yanzun. Amman zamuyi magana anjima. Ki kula da kanki.”
Ta bude baki tace mishi shima ya kula da kan shi ya kashe kiran, kai kawai ta girgiza tana rubuta maganar ta tura mishi, sannan ta ajiye wayar tana cire mayafin ta cilla kan gado. Zanen ta cigaba da wani nishadi na daban wannan karin.