Idan aka ce maka a kasa da wata daya Hindu da Hamza sukai kalar shakuwar da sukayi zaka karyata hakan. Idan basa manne da juna ta waya, suna manne ta chatting, dan ma lokutta da dama karatu yake tayata yi, amman ko zane takeyi, maimakon ta saka waka ko karatu yanda takanyi wani lokacin, sai suyi waya. Ko aiki yake yakanyi mata text. Sai dai kamar yanda tagani tun a haduwar su ta farko, yana da rigima, sosai yana da rigima fiye da yanda take tunani. Zuwa yanzun Hauwa kadai tasan suna tare da Hamzan, batason ta cika yawan magana akan shi din, tunda bawai yace yana sonta bane ko wani abu.
Ko kadan bata wasa da addu’a kan hakan ya kasance. Dan har ranta take jin Hamzan. A lokacin kuma sau uku kadai suka hadu, zai wuce hidima ne sai ya biyo makaranta yaganta, ko mintina biyar baya cikawa, saboda yace mata sosai aiki ya rincabe musu. Yaune dai sukayi dashi zaizo har gida ya ganta. Dan ta ma sanarma da Anty, ta kuma gaya mata baya tashi aiki da wuri, ba zai samu zuwa da yamma ba. Ita kanta wani sama-sama take jinta, duk da yana kokarin kiranta video call, ba kamar tana ganin shi ba, yayi mata alkawarin ana idar da Magriba, zai bata awa biyu cikakku
“Ina so in ganki”
Shine abinda ya furta mata
“Da gaske ina so in ganki, Video call din nan baya mun”
Dariya kawai tayi, sai gashi kuma ya samar musu lokaci. Yau kam kwalliya tayi sosai, tana saka Abaya, a harabar gidan ta same shi a tsaye jikin motar shi. Jikin shi sanye da shadda sai maiqo takeyi, fara kal da ita, sai hular shi da takalmin kafar shi ruwan toka, yayi mata kyau kamar ta sace shi ta boye kar wata ta kallar mata shi. Murmushi yayi mata
“Sannu da zuwa”
Ta furta tana ajiye mishi kujerar data dauko, ta rabasu da yake guda biyune a hade, itama ta ajiye daya a gefe.
“Ina zuwa”
Cewar Hindu tana komawa, a bangaren Mama ta tsaya tana shiga kitchen ta dauko mishi ruwa roba daya, sai coke da tagani a ciki, batasan waya zuba ba. Ta dai dauki guda daya ta sami plate mai kyau, sannan ta koma. Plate din ta ajiye a kasa, tana dora ruwan da coke din a kai.
“Ga ruwa”
Hannu Hamza ya kai yana daukar coke din dan lemon shine
“Ke dai ki sha ruwan, nikam na dauki coke”
Yai maganar yana bude robar yakai bakin shi ya kurba
“Kin san yanda nayi kewar ki kuwa?”
Sadda kanta kasa tayi a kunyace, tana jin dadi idan yace yayi kewarta, sai taji kamar tana da wani muhimmanci mai girma a wajen shi
“Nima nayi kewar ka ai”
Ta tsinci kanta da furtawa, tana saka shi girgiza mata kai
“Da kinyi kewata da kin kalleni, tunda kika fito idanuwanki suke a kasa”
Dariya ta danyi, ba kallon shi bane batason yi, kunya take ji, yayi mata kyau na gaske, idan bai sani ba.
“Hindu…”
Ya kira can kasan makoshi, saboda ganinta ya birkita mishi lissafi gabaki daya. Ba karamin kokari yayi ba wajen kokawa da zuciyar shi ganin bai rungumeta a cikin harabar gidan su ba. Yanzun ma kokari yakeyi na ganin bai kamo ko da hannunta da take ta wasa da wayarta da shi bane ya rike a cikin na shi. A hankali ta dago kai tana sauke idanuwanta cikin na shi, amman yanayin da take gani a cikin su ya sakata sauke nata babu shiri. Numfashi ya sauke yana runtsa idanuwan shi hadi da bude su a kanta
“Me yasa duk wanda yai miki magana sai kin amsa shi a Instagram?”
Ya tambaya da wani yanayi a muryar shi yana kuma tsareta da idanuwan shi, tambayar tayi mata bazata, Hamza kuma amsarta yake jira, har ranshi yake jin wani irin kishin yaga garadan banzan nan suna mata magana. Bayaso sam, ba wai soyayya suke ko wani abun ba, amman yanajin tashi ce shi kadai, har kuma ranar da zai daina jin hakan, bayason kowanne namiji a kusa dashi, shisa sam bayabin mace sau biyu, saboda ba zai taba iya rabata da wani ba, yanada wannan kishin, ballantana kuma Hindu da ta sami waje tayi kane-kane a rayuwar shi.
“Haka kawai”
Ta amsa dan batasan me ya kamata tace mishi ba
“Bana so, bana so kina magana da su”
Ya furta cike da ikon da ya bata mamaki, a gefe daya kuma yana mata dadi, dan ya daga mata burin da take da shi a kan shi, a cikin muryar shi take son karantar kamar kishi yake son nunawa. Dan murmushi tayi
“Ki kalle ni Hindu… Da gaske nakeyi bana so, ki daina magana da su”
Kai ta jinjina mishi, ya sauke numfashi, kafin yace
“Nagode…”
Hadi da mika mata hannun shi, bataga komai da take rike dashi ba sai wayarta, dan daga mishi wayar tayi cike da alamar tambaya, ya jinjina mata kai, daga mukulli ta cire sannan ta mika mishi, Instagram dinta ya shiga yana goge hoton da ta saka jiya, baka ganin komai sai fuskarta da hular da take kanta, ta saka da caption din ‘Work, work, work’. Sai dai alamun bacci da gajiyar da take cike da idanuwanta yasa tayi mishi wani irin kyau kamar ya lasheta. Tarin mazan da suke kasan comment section dinta yasa ya tabbatar shi kadai yaga tayi kyan ba.
Hindu kuwa tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, dan Hamza ya wuce Mijin Novel, duk yanda take hasaso mazajen, shi yana nuna mata kyawun shine kawai yayi dai-dai da nasu, amman ya fisu rikici da baudadden halayya. Kawai shi ba miskili bane, ba kuma shuru-shuru bane. Yana magana sosai sosai, duk wani hoto da bayason wasu kartin banza suna gani, suna kalle mishi ita suna hadiyar miyau yabi ya goge. Tukunna ya mika mata wayar da fadin
“Bana so, bansan me yasa kike yawan saka hotunan ki ba”
Duba Instagram din tayi taga ya goge mata hotuna masu yawan gaske
“Duk ka cire mun hotuna, wasu fa bani da su a wayar yanzun”
Hindu ta fadi kamar zatayi kuka, akwai hotunan da ta dora ne ko da zata rasa wayar. Kafadu yadan daga mata yana hade fuska. Akan ta yake mamakin kan shi sosai, bai taba daukar wayar ko da cikin abokan shi ya goge musu wani abu ba, amman ikon da yakeji akan Hindu mai girma ne
“Ki dinga turo mun kafin ki saka, kowanne wawa zai bude bakin shi yayi magana kinyi kyau. Bana so”
Kallon shi tayi tana sauke numfashi, tama rasa abinda ya kamata tace mishi
“Kina jina kikayi shiru”
Ya sake fadi, kai ta iya daga mishi kawai, dan lamarin ne take ganin yafi karfinta.
“Thank you”
Ya furta yana kai hannun shi ya dan murza goshin shi, kafin ya sauke shi yana kamo na Hindu da zuciyarta tayi wani irin tsalle kamar zata faso kirjinta ta fito, kar wani ya fito yagan su, ko wani ya shigo yagan su
“Na cika rigima ko?”
Ya fadi yana lankwasa yatsun hannunta hadi da sake budesu ya hada cikin nashi ya dumtsa, kafin ya sauke idanuwan shi cikin nata da yake ganin bayanannen tsoro a cikin su, kome tayi kara birkita mishi lissafi takeyi
“Haka zakiyi ta hakuri dani”
Ya fadi muryar shi can kasan makoshi. Hannunta take son zamewa daga cikin nashi, so take tace ya sakar mata hannu kar wani ya fito, amman sam ta kasa. Bakinta yayi mata wani irin nauyi, kuma kallon da yake mata batajin zata iya tabuka wani abin kirki, da kan shi ya sakar mata hannu bayan yadan dumtsa shi, hadi da sauke numfashi yana mikewa, da idanuwa Hindu ta bishi, motar ya bude ya mike hannu yana dauko agogon daya siya wajen Mansura. A status dinta yaga ta dora, yayi mishi kyau sosai. Bata tsare shi da tambayar wa zai bama ba, dan tasan halin shi da kyauta.
Dawowa yayi ya zauna, yana jin dadin samun wani dalilin da zai rike hannunta. Agogon ya fara kwancewa sannan ya kama hannunta yana dago shi, ya daura mata agogon, sai yaga hannun yayi mishi kyau. Yana ganin agogon ya hango shi cikin hannunta. Itama dago da hannun tayi, zuciyarta ta shiga wani yanayi da ba zata iya misaltawa ba
“Nagode…”
Ta furta a hankali, kai kawai Hamza ya iya daga mata, yanajin dadin sallar isha’i da yaji an fara kira
“An kira sallah”
Ya furta yana saka Hindu ware mishi idanuwa kafin ta shagwabe fuska
“Tafiya zakayi ko?”
Ta bukata tanajin kewar shi na danneta tun kafin ya tafin
“Ki kasheni kawai, Ki kasheni”
Ya fadi cikin yaran fulatanci yana sakata dakuna mishi fuska cike da rashin fahimta
“Zan dawo ai, in kina da lokaci gobe zanzo muje muci abincin rana tare”
Kai ta jinjina mishi, a cikin kanta tana tunanin lakcocin da take dasu goben. Hamza daya mike yana katse mata tunanin da takeyi
“Da gaske tafiya zakayi ko?”
Tai maganar cikin muryar da ta saka shi son sumbatarta, amman hannunta ya rike ta fara zare mishi idanuwa kamar yana zare mata rai, zai dauke shi lokaci mai tsayi kafin yazo wannan matakin, lokacin da bayajin yana da hakurin jiran shi, saboda yanda komai tayi yake kara kwadaita mishi ita.
“Hindu so kike ki hanani tafiya ko?”
Yar dariya tayi tana girgiza mishi kai
“Zan ganki gobe In shaa Allah”
Mikewa tayi itama, kawai saiya tsinci kan shi da sake kamo hannunta, yana share tsoron da yake gani a cikin idanuwanta, hannun yakai yana goga shi akan fuskar shi, kafin ya sumbaci cikin tafin hannunta
“Bye…”
Ya iya furtawa yana sakar mata hannun da taji yayi wani irin nauyi. Harya shiga mota ta kasa cewa komai, tana kallo yayi baya da motar shi yana fita daga gidan, juyawa tayi, duk da bataji alamar akwai wani a bayanta ba. Sai take jin kamar anga abinda tayi, kamar wani yaga hannunta a fuskar Hamza, zuciyarta cike fal da tsoro ta samu ta dauki kujerun ta hade su waje daya. Anan tabar su ta dauki plate din da ruwan da bai shaba ta shige gida, zuwa kitchen din Mama tayi ta ajiye mata plate, ta mayar da ruwan mazaunin shi. Sannan ta wuce bangaren su tana sakun Khadee a zaune
“Shikuma menene laifin shi? Gajere ne? Ko katon hanci?”
Khadee ta tambaya cike da zolaya, zagayawa Hindu tayi ta zauna kan kujera, bata cikin yanayin da zata biyewa tsokanar Khadee din, yanayinta yasa Khadee fadin
“Lafiya? Me ya faru?”
Kallon Khadee tayi da wani irin yanayi a fuskarta tace
“Ina son shi Khadee…”
Ware idanuwa Khadee tayi, ita kanta Hindu mamakin kalaman takeyi, amman daga zuciyarta suka fito, mikewa tayi
“Ke dai ki mun addu’a. Allah ya tabbatar mun”
Khadee da kallon mamaki take bin Hindu harta shige daki tana barinta a wajen, da tunanin ko dai wani dan wasan fim dinne Allah ya jeho Najeriya suka hadu da Hindun.
*****
A gidan su ya kwana, duk da bai shiga da wuri ba sai wajen sha daya na dare. Yanzun kuma karfe tara harya gama shirin shi, ya fito falo yana samun Anna da Auta a zaune
“Hamma na ganka rannan… Kai da wata ta wajen Byblos… Mantawa nayi in fada maka”
Wani kallo ya watsa mata
“Uban ki kike a wajen? Kuma baki iya gaisuwa ba?”
Yar dariya Auta tayi
“Ina kwana… Allah da gaske na ganka. Ni Anna ta aikeni ai ranar, kafin inje in maka magana harka shiga mota”
Numfashi Hamza ya sauke, yana jin idanuwan Anna a kan shi, amman yaki kallon ta, sai da tace
“Wacece ita?”
Dan kallon Anna yayi
“Ni banma tuna ranar bafa Ann, bazai wuce abokan aiki ba”
Ya fadi yana ganin yanda Anna bata yarda ba, amman ba zata fada mishi hakan bane kawai.
“Ko ita ce? Ban ga fuskarta ba sosai”
Auta tace tana saka Hamza watsa mata wani irin kallo da yasa ta fadin
“Allah ya baka hakuri. Ni shirin makaranta zanyi daman”
Ta karasa maganar tana tashi tabar dakin. Da idanuwa dai Anna take bin shi
“Ban san sau nawa zanyi maka magana kan nutsuwa waje daya ba, kana da aiki me kyau. Na rasa abinda kake jira”
Dakuna fuska Hamza yayi yana turo labban shi
“Ni zan fita wajen aiki”
Yai maganar yana nufar hanyar kofa, inda yaci karo da Appa dayai wa magana cikin harshen fulatanci, Appan na tambayar yanayin aikin Hamzan, shikuma yana amsa shi
“Maganar aure nayi mishi shine zai fita yabar mun gidan”
Dan juyawa Hamza yayi
“Anna mana”
Ya furta, yana wuce Appa ya fice daga gidan dan karma su hadu su biyun suna mishi maganar aure. Bai hango shi a wannan kejin ba dan nan kusa, babu wanda zai kulla mishi yarinyar mutane ya rasa yanda zaiyi da ita, haka kawai a takura shi a hana shi sakewa. Kullum dole ka koma waje daya ka dinga kwana, ba zai kwana a waje yanda yaga dama ba, saboda yayi aure. Bai shiryama wannan matsatsin rayuwar ba, kuma bai gama ginin shi ba, shine uzurin da yake amfani dashi wajen sakawa Anna tana saurara mishi da maganar auren.
Yana fita daga gidan ya tsinci kan shi da kiran wayar Hindu, ko muryarta yaji. Ga mamakin shi, kashewa yaji tayi, sai ga text tayi mishi
“Ina aji”
Tana sake turo wani
“Sha biyu da rabi zan fito, zan kiraka”
Titi ya kalla, kafin yadan kalli wayar shi yana fara rubutu
“Ok. Zan zo sai mu fita lokacin”
Ya tura mata, tukunna ya nufi hanyar da zata kaishi gidan Fodio. Yana karasawa ya samu suna karyawa, waje ya samu ya zauna shima yana cin dankalin da kwai, hannu yakai zai dauki kofin yoghurt da yake gaban AbdulHafiz ya doke mishi hannu
“Wallahi nayi brush”
Hamza ya fadi, yana saka Fodio da Arafat kwashewa da dariya
“Brush shine abinda zai tsarkake maka bakin ka?”
AbdulHafiz ya bukata yana daukar kofin shi ya rike a hannu, tuntuni ya gaya musu ya daina hada irin wannan abubuwan da su, ya siyo kofina daban yana kaiwa dakin shi
“To ni ina ma naje?”
Hamza ya tambaya yana dorawa da
“Dan Allah kabani in kurba”
Fodio ne ya sakeyin dariya, fadan AbdulHafiz din da Hamza baya gajiyawa wajen saka shi nishadi
“Karbi…”
Arafat ya fadi yana mika mishi kofin da yake hannun shi, lekawa Hamza yayi
“Kai ni bana shan tea dalla”
Bude baki Arafat yayi cike da mamaki, kafin ya jinjina kai yana furta
“Laifina ne da nayi maka tayi”
Banza Hamza yayi yana kyale shi, Yoghurt din ce ranshi ya biya
“Ido guba AbdulHafiz, ba kyau wallahi”
Ko inda yake AbdulHafiz bai kalla ba, yasan ba bashi zaiyi ba, saida yasha fiye da rabi tukunna ya tura ma Hamza kofin yana fadin
“Dan Allah Arafat ka tashi, yanzun yaushe zamu shiga Kano har mu gama mu sake kamo hanya? Bafa naso mu kwana”
Kofin shayin Arafat ya daga yana shanye na ciki, hadi da maida numfashi kafin ya mike
“Ba zaka bar mutum abinci ya narke mishi ba. Kaya fa kawai zan sake”
Harar shi AbdulHafiz yayi
“Daka wuce ai da yanzun ka sake kayan… Ka zauna mayar mun da magana”
Wucewar Arafat din yayi kuwa.
“Ko in shirya mu tafi tare?”
Fodio ya tambaya yana daga hannun shi ya kare fuskar shi
“Hararata yake ko?”
Ya tambayi Hamza daya daga mishi kai yana dariya
“Wanne wulakanci ne wannan? Sai ka tashi ai”
Da sauri Fodio ya mike yana wucewa daki dan ya watsa ruwa, idanuwan shi AbdulHafiz ya tsayar kan Hamza
“Kai ba zakaje ba?”
Kai Hamza ya girgiza mishi, ai yaji suna maganar zuwan tun jiya da rana, ya riga ya saka ma ran shi ganin Hindu yau. Ko ya bisu tunaninta damun shi zaiyi, gara dai yaganta din
“Kuje abinku”
Dan kallon shi AbdulHafiz yayi, yasan Hamza baya wuce tayin yawo, ko marar muhimmanci, balle kuma yanzun da aikine zai kaisu, kuma su dukan su, dan zasu biya su dauki Abdallah. Shi kadai zasu bari, yasan akwai dalilin da yasa ba zaije din ba
“Ka shiga uku AbdulHafiz, ka tambayeni dalili mana, nasan kana so ka tambaya, ina jin idanuwanka na mun rami a bayan kaina…”
Hamza yai maganar da wani yanayi tattare da muryar shi. Shiru AbdulHafiz din yayi, idan Hamzan na so yaji zai gaya mishi, ba zai fara saka hancin shi cikin abinda bai shafe shi ba
“Nabila na da aiki”
Hamza ya fadi yana saka AbdulHafiz fadin
“Jibi yanda kake kiran sunanta gatsau dan Allah”
Dariya Hamzan yayi
“Kana jina ashe, kayi banza ka kyaleni”
Shirun AbdulHafiz ya sakeyi mishi, har su Fodio suka fito suka wuce, Hamza yana karasa cinyewa nan ya tsallake yana barin kwanonin, zai tabbatar sanda zasu dawo baya gidan, ballanta AbdulHafiz ya sauke mishi fadan ba zai iya gyara waje ba. Kwalabe biyu ya dauka na vodka, duk da yasan yayi safiya ya bulbula ma cikin shi abu mai karfi haka, sai dai ita kadai ce zata taimaki yanayin da yake ciki, rabin kwalba yasha yana jin kan shi ya fara nauyi, hakura yayi ya kwanta, sai da ya saita alarm din wayar shi zuwa sha biyu da rabi, tukunna ya kwanta, yana lumshe idanuwan shi yabar baccin da yake son daukar shi yin aikin shi.
*****
Karamin tsaki yake ja a mota, yana tuqi kamar zai tashi sama, kwata-kwata baiji karar alarm din wayar ba, sai bayan ya tashi wajen daya da kwata, sannan ya kula wayar a silent take gabaki daya. Yaga Hindu ta kira shi har sau biyu, ruwa ya watsa a gaggauce yana sake kaya ya fita. A hanya ya tsaya ya siya mata shawarma da kaji, sai lemuka, yasan ko yaushe in dai tana makaranta to zaiji tana tare da Hauwa, shisa yayi ledoji biyu. Yana shiga makarantar ya samu waje yayi parking, tukunna ya kira wayarta, bugun farko ta dauka
“Dan Allah karkice komai, kiyi hakuri, wallahi bacci nayi, wayar kuma tana silent, ki fito ina wajen parking din motoci…”
Hamza ya fadi muryar shi cike da ban hakuri, batace komai ba, shima wayar ya sauke yana jin babu dadi, saba alkawari ba sabon shi bane ba, balle shi yace ta jira shi zaizo. Ji yayi an kwankwasa motar, hakan yasa shi mika hannu ya bude mata, kai ta leqo tana mishi murmushin daya kasa mayar mata
“Kiyi hakuri…”
Ya furta kamar zai mata kuka, dariyar ta sakeyi tana shiga motar ta zauna.
“Ki rufo kofar akwai rana”
Hamza ya fadi, dan baima kashe motar ba, saboda AC din. Batayi musu ba ta rufo mishi murfin, sai take jinta wani iri saboda gilasan gabaki daya a rufe suke, kuma motocin duk da take ganin shi dasu tinted ne.
“Ya kike?”
Ya fadi yana yawata idanuwan shi akanta, yana ganin gajiyar da take fuskarta, yasan kuma karatune, ga ranar da ake kwallawa. Haka kawai yaji bayason ta koma cikin zafi
“Alhamdulillah…. Da baka zo bama”
Idanuwan shi ya kafe ta dasu
“Baki so ganina ba kenan?”
Da sauri ta girgiza mishi kai
“Aa wallahi, ba haka nake nufi ba, da kayi baccin ka dai”
Ledojin da suke ajiye a gefen shi ya dauko yana mika mata
“Bansan ko kunci wani abu ba, ke da Hauwa… Bari kar in rike miki sauran lokacin cin abincin”
Murmushi tayi, suna ma masallaci ita da Hauwa din, sanda ya kiratane suke tunanin zuwa suci abinci, dukkan su a gajiye suke. Hannu ta saka ta karbi ledojin tana fadin
“Mungode sosai”
Kai ya jinjina mata, yana kwance seatbelt din da yake daure a jikin shi, kafin tayi wani kwakkwaran motsi ya gyara zaman shi, bata san me ya faru ba, ba zatace ga yanda akayi ba, sai jinta tayi gabaki daya a jikin shi ya rungumeta hadi da fadin
“Yau nayi laifi, dan Allah kiyi hakuri”
Duka da rungumar da sakinta bai wuce minti daya ba, amman wani zazzabi taji ya saukar mata, da kan shi Hamza ya bude bangaren shi ya fita, ya zagaya yana bude mata nata bangaren, kafafuwanta ta janyo dakyar tana dire su a kasa tukunna ta fita daga motar.
“Ki kula da kanki dan Allah”
Ya furta, kai kawai ta iya daga mishi, tana jin kamshin turarukan shi da suka manne mata, dakyar take daga kafafunta tana takawa ta nufi hanyar da zata kaita masallacin da take tunanin shiga saboda zunubin da takeji a jikinta. Hamza kuwa daya koma motar yana rufe murfin, kan shi ya hada da abin tuqin yana maida numfashi, baisa ya akayi ba shima, kawai ji yayi idan bai riketa ba komai zai iya faruwa, yanajin bugun da zuciyar shi takeyi a cikin kirjin shi, numfashi kawai yake mayarwa kamar wanda yayi gudu.
Baisan abinda yake damun shi ba, yasan yanda yake akan mata, amman abinda yakeji akan Hindu yayi yawan da ya fara bashi tsoro, yakai mintina goma anan zaune cikin motar, kafin ya iya tashin motar, yana juyata ya fita, a bakin gate din ya tsaya yana ba masu gadin dan katin shigar da suka bashi, hadi da dubu biyu, yaja gilashin motar shi, bai damu da godiyar da suke ta faman yi mishi ba, da fatan sauka lafiya. Garama wannan, dan yana bukatar shi a halin da yake ciki.