Tunda ya shiga gida, kayan jikin shi kawai ya sake yana saka wando iya gwiwa sai wata riga mai dogon hannu hadi da hula ruwan madara. Yaja hular yana dorata saman kan shi, tukunna ya dauki wayar shi, earpiece ya duba ya hada a jikin wayar, ya makala ma kunnuwan shi batare daya kunna komai ba, magana ce bayaso yayi da kowa, kuma akwai aikin da bayaso ya kwanar mishi, da ba zai fita falon ba. Yana karasawa ya dauki system din shi daga kan tebirin da take yana jan cajar da take hade da system din ya koma kama. . .