Skip to content
Part 19 of 33 in the Series Mijin Novel by Lubna Sufyan

“Hello”

Ta furta muryarta can kasan makoshi, kallo daya zakaiwa fuskarta ka fahimci yanda take cikin damuwar da tun jiya kowa yake dauka jimamin rabuwa da gida ne.

“An daura, Hindu an daura.”

Hamza ya fadi daga dayan bangaren, runtsa idanuwanta tayi tana bude su, hadi da sauke wani irin numfashi, tun dazun take kallon agogo tana jiran karfe goma tayi, tana jiran taji canjin da marubuta kan fadi duk idan an daura auren ka, sai dai shiru, bata ji komai ba, bata ji a jikinta cewa an daura ba, da bai kirata ba sai dai idan taga dawowar wani daga cikin mazan gidan, yanzun ne dai muryar shi da tsantsar dokin da yake ciki yasa zuciyarta wani irin zirga-zirga a cikin kirjinta. Amman a kasan wannan akwai wani ciwo da ya ki fitar mata tun jiya.

“Okay…”

Ta furta, tana jin hayaniya daga dayan bangaren kafin ta sauke wayar daga kunnenta tana katse kiran ta ajiyeta kan mudubi.

“Ke anata neman ki, kin karya?”

Biebee data leko dakin ta bukata, dan su sun tafi wata hidimar, kai Hindu ta girgiza mata.

“Sugar bana jin yunwa wallahi.”

Cewar Hindun kamar yanda takan kira Biebee wani lokaci, dan kallonta Biebee ta yi.

“Zaki zauna ulcer ta kamaki, aure fa akayi miki ba wani mugun abu ba, is not like ba zaki dinga zuwa gida ba.”

Murmushin karfin hali kawai Hindu ta iya yiwa Biebee din, tana tsintar kanta da kasa furta komai.

“Ni dai zan hado miki tea.”

Ta karasa maganar tana juyawa, numfashi Hindu ta sauke, tana saka hannu ta gyara zaman dankwalin da yake nade a kanta, ba wata kwalliya bace mai nauyi a kan fuskarta, amman tayi kyau matuka, ba kunshin hannunta ba, yanayinta kawai idan ka kalla zaka gane itace amaryar, taji dadin kasancewar ita kadai a cikin dakin. Biebee batafi mintina biyar ba ta sake dawowa, wannan karin tana shigowa har cikin dakin, ta mika ma Hindu kofin shayin data hada shi da kauri sosai yanda zai rike mata ciki. Sannan ta fice daga dakin, kofin Hindu ta daga takai bakinta ta kurba a hankali, sai taji idanuwanta sun cika taf da hawaye.

“Oh shit…”

Sune kalman farko da Hamza ya furta a daren jiya da misalin karfe tara da rabi na dare, bayan ya daga video call din da tayi mishi da alama babu shiri, bai kuma yi nufin ya daga ba, abin yazo mishi a shammace, yanda take ganin yanayin hoton na rawa, da alama so yake yi ya kashe, amman a rikice yake.

“Ka sallameni dare na yi.”

Ta sake jin muryar yarinyar da ko idanuwanta ta rufe tun jiyan tana sake dawo mata, kafin Hamza ya kashe video call din yana ta maimaita.

“Oh shit.”

Abinda ya taso yai tsaye bayan zuciyarta har yanzun tana jin shi, yaki fitowa, kuma yaki wucewa, hotunan kwalliyar da akayi mata ne da ta tura mishi taga bai ce komai ba, kuma tun da yamma basu kara magana ba, shisa ta kira shi video call din, dan tayi kewar shi a yinin ranar ba kadan ba, tana kuma da tabbacin ba bacci yake yi ba, har yanzun tana dana sanin kiran shi da tayi. Yafi mintina talatin tsakani kafin ya kira wayarta, zuwa lokacin hawaye ma ta neme su ta rasa, harabar gidan ta fita dan ta samu sararin yin video call din da shi, jikinta babu inda baya rawa lokacin da ta kara wayar a kunnenta.

“Bansan me zance miki ba.”

Ya furta daga dayan bangaren yana ba hawayen da take ta nema damar zubowa.

“Ran daren aurenmu? Hamza ranar daren aurenmu? Me ka ke nema? Me yake damunka da ba zaka iya jira ba? Awanni nawa suka rage mana? Me yasa za kai mun haka?”

Tana jin yanda yake sauke numfashi.

“Bansan me zance ba.”

Ya sake furtawa.

“Karka kara cemun bakasan me zaka ce ba, wallahi karka kara.”

Ta yi maganar a masife.

“Idan nace miki bazan iya jira bane zaki yarda?”

Numfashinta taji yana mata barazana, Hamza so yake yi ya kasheta taga alama, inda wani yace mata wata rana kirjinta zai yi kamar an dora dutse haka ba zata yarda ba, amman yau har wuta take ji kamar tana ci a cikin shi saboda zogin da yake mata.

“Bazan iya jira ba Hindu, in ba mutuwa kike so inyi ba.”

Bakinta ta bude tana neman iska ko zata samu tayi numfashi, kafin da kyar ta iya cewa,

“Kai zaka kasheni Hamza, so ka ke yi ka kasheni.”

Tana jin numfashin daya sauke.

“Karki karamun abinda nake ji, dan Allah yau kawai, yau kawai ki kyaleni. Awanni kadan ya rage mana kamar yanda ki ka ce, ki kyaleni inyi abinda zan samawa kaina sauki kafin su cika.”

Ya karasa maganar yana kashe wayar, saukewa tayi daga kunnenta, wasu hawaye masu dumi na zubar mata lokacin da take danna wayar tana kiran shi, bata saka a kunne ba sai da taga ya daga.

“Babe.”

Ya kira da wani irin yanayi a muryar shi.

“Wanne bangare na ki kyaleni ne baki gane ba?”

Hannu tasa ta goge fuskarta.

“Baka isa ba, wallahi kayi kadan kaimun abinda kai mun sannan kace in kyaleka.”

Ta karfi da yaji Hamza ya koya mata masifa, duk da bawai bata fada bane ba, na yanzun ne yafi na da, bala’in shi yasa bata shakkar gaya mishi magana lokutta irin haka.

“Idan baki kyaleni ba ya zakiyi dani? Na zaba miki abinda yafi sauki ne amman kina so ki karama kanki ciwon kai.”

Dariya tayi da bata da alaka da nishadi sam, zuwa yanzun bata jin akwai wani abu, ko wata magana da zai fada ta bata mamaki sam.

“Babu yanda zanyi da kai, amman bata mun ran da kayi sai Allah ya saka mun.”

Ta furta muryarta na rawa, bata jira mai za ice ba saboda kukan da take ji yana neman kwace mata, ta kashe wayar. Kan cinyarta ta dora tana hade kanta da gwiwa wani irin hawaye masu dumi na zubo mata, kamar yanda ta hada shi da Allah yanzun, haka zata ci gaba da hada shi da Allah har saiya canza, tana da yaki nin zai canza, ba za izo mata da sauki ba, amman zata jure, zata yi wannan jahadin, zata canza shi. Idan tana gidan shi hakan zaifi saurin faruwa, zata tabbatar da ita kadai ta ishe shi, saboda zatayi mishi duk wani abu da yake so.

Kiran shi ne ya shigo, sai da taja hanci, tana sake goge fuskarta, tukunna ta dago kai, tana daukar wayar da ta yanke, ajiyar zuciya kawai take saukewa, sake kira ya yi, ta daga ta kara a kunnenta.

“Ni zaki hada da Allah? Hindu ni zaki hada da Allah? Tashin hankali ki ke nema dani ko?”

Dafe kanta tayi tana furta.

“Kai! Kai jama’a, oh Allah na.”

Saboda batasan me kuma yake so tayi ba, batasan ina yake so ta tsoma ranta ba, shi ya yi mata laifi, amman yana neman yafita rigima akan abin, zuciyarta ciwo takeyi, bai san ya bata hakuri ko zataji san yi ba, dan lallashi ma bata samu ba, amman shi yake so ya fita hayaniya.

“Me ki ke nufi?”

Kai take girgizawa.

“Babu komai, Hamza babu abinda na ke nufi, sai da safe.”

Har ranta wayar tayi niyyar kashewa, bata da karfin biye mishi, abinda take ji kawai ya isheta.

“Babban kuskuren da zakiyi ki kashemun waya, wallahi karki kashe mun waya Hindu?”

Wasu hawayen ta ji sun sake zubo mata, kasha din shi na zauna mata.

“Ya ka ke so inyi? Me kake nema dani? Baka tausayina ne? Baka san me nake ji ba ko?”

Tayi maganar muryarta na karyewa, tana jin ya yi shiru, kafin cikin sanyin murya ya ce,

“Ke ce ba kya tausayina saboda bakisan halin da nake ciki ba, da kinsan me nake ji a daren yau da baki nemi hadani da Allah ba, kamar zunuban da nake dauka da kaina basu min yawa ba, shine ki ke son karamun wani.”

Kara karya mata zuciya yake, balle cikin yanayin da ya yi maganar kamar shima zai yi mata kuka.

“Ko dan kin fini saurin kuka? Shisa duk abinda zai faru ni ne mai laifi?”

Bata san me zata ce ba.

“Ki bani hakuri, kin bata mun rai bayan banajin dadi, Babe ki bani hakuri.”

Numfashi Hindu ta sauke.

“Kayi hakuri.”

Ta tsinci kanta da furtawa ko wayar zata zo karshe, numfashi mai nauyi ya sauke mata cikin kunne.

“Ya wuce, ina son ki, kinsan haka ko?”

Kai kawai ta daga, kafin tace wani abu ya riga ta.

“Sai da safe, ki kulamun da kanki.”

Yana kashe wayar kamar shikenan, kamar idan abinda ya ke ikirarin tayi mishi ya wuce a wajen shi itama abinda ya yi mata ya wuce a wajen ta, kamar yarinyar da yabi yau laifinta ne shisa baiga dalilin da zai bata hakuri ba, ta kai awa daya a zaune a wajen, sai da taga bayan ciwon zuciya, zazzabin ciwon sauro na gab da kamata tukunna ta tashi ta shiga cikin gida, baccin kirki ma bata samu ba, dan duk yanda zata rufe idanuwanta sai taga Hamza da wasu matan. Haka ta tashi safiyar yau komai bayayi mata dadi, shisa bata ma neme shi ba, shima din daya kira tsintar kanta tayi da rashin son yin magana da shi.

Hawayen da take ji suna shirin zubo mata ta kai dan yatsa tana sharewa. Kukan zai jira, nan da yan wasu awanni zata yi mai dalili, dan da wuri za’a kaisu. Tea dinta ta kara kurba, tun da yan uwan Baba dana Anty, harda ma wasu cikin na Mama suka je jere suka dawo suke maganar gidanta, kujeru saiti biyu Baba yai mata, Hamza ma yaso subar maganar kayan dakin, ta dai fada mishi Baba ba zai taba bari ba, amman taji suna cewa dakunan suna da yawa, ko falo guda hudu ne a cikin gidan, a biyu kawai suka yi jere, sauran ma duk an kawo kayan daki suna lullube a cikin ledoji ko bude su ba’ayi ba.

Kowa maganar gidan yake yi, har ranta wannan ya yi mata dadi, gidan da take mafarki ne, ko a hoto Hamza bai taba nuna mata ba, basu ma tabayin maganar gida da shi ba har saida aka zo maganar yin jere tukunna. Ance gidan Khadee ma babu laifi, duk da karamine, daki biyu, amman a iya karfin shi, yayi kokari matuka, ko ina yasha tayal. Khadee dinma da kanta sai da tazo cikin murna tana fadin.

“Ke banza kinga yanda ake maganar gidanki? Ance ya hadu wallahi, kina zuwa kiyumun video.”

Murmushi kawai tayi, Hamza ya rage mata walwalar da ya kamata ace tanayi, ya kamata ace tana tunanin dinner dinta da za’ayi karfe takwas na ranar. Amman zuciyarta ciwo take yi mata, da kyar ta samu ta karasa shanye shayin, tana barin kofin nan kan mudubi, ta mike ta karasa kan gado ta sami waje tayi zamanta, tana kallon yanda Aunties dinta suke shigowa sunata tsokanarta da fadin,

“Yarinya zuwa sha biyu zamu tattaraki mu kai ki.”

Da sun fadi haka sai taji zuciyarta tayi wani irin tsalle, ba’a fadi wannan fargabar da tashin hankali na tunanin barin gida ba a littafi, kwanciya tayi jin alamar zazzabin tashin hankali da ya ke shirin rufeta.

*****

Bai taba gajiya da daukar hoto ba sai yau, babbar rigar da take jikin shi ta ishe shi, yana fitowa daga motar da tayi parking cikin gidan Fodio ya fara cire babbar rigar jikin shi, yana cire hular ya rike hannu ya taka zuwa bakin kofar da zata shigar dashi gidan, yana jira AbdulHafiz da mukullin yake a hannun shi ya karaso yazo yana bude gidan. Shigewa Hamza ya yi hadi dayin sallama, ya jefe babbar rigar akan kujera ya samu waje ya zauna. Tun karfe goma aka daura aure, amman azahar ma a hanya suka tsaya suka yi, sai yanzun ne suke shigowa gida. Ko karin kirki bai tsaya ya yi da safe ba, tun jiya yake jin shi a hargitse.

Daya motsa sai ya yi kamar wasu sarkoki ne suke biye da shi suna jiran lokaci ya cika su daure shi waje daya, zuciyar shi taki aminta da cewar auren shine aka daura, badan sarkokin da yake ji sun dabaibaye shi ba, zai dauka ko mafarki yake yi, da suka fito daga wajen daurin auren ma, yana kula da kallon da Fodio yake yi mishi, kamar shima yana mamakin yanda akayi Hamza yai wannan wautar, yanda ya yarda ya daukar ma kanshi gagarumin nauyi kamar aure. Har a kasusuwan jikin shi yake ji bai shirya ba, shine abinda yasa shi sulalewa ya fice daga gidan jiya ya nemi yarinyar da Hindu bata tashi kiran shi video call ba sai da suna tare.

Ba kuma zaice ya akai ya dangwalo wayar ya amsa video call din ba, ga kan shi da yake ji da nauyi sosai tamkar an dora dutse, giya ta fara dira cikin shi a safiyar yau, sai shayin daya kurba da kyar, kamar kayoyi ne a cikin shi ko wasu itace haka yake ji. Ana fadin,

“Amin”

Sai da yaji wani abu ya tsirga mishi har zuciya yana sa hanjin cikin shi kullewa waje daya. Shikenan an daura, shikenan an mishi katanga da abubuwa da yawa a rayuwar shi, abubuwan da bai shirya bankwana dasu a yan wasu shekaru masu zuwa ba, yanzun ma mikewa ya yi yana nufar kitchen. AC din dakin bata hana zufa tsatsafo mishi a goshi ba, yana shiga kitchen din fridge ya nufa ya bude, giyar ta gwangwani ya dauka ya bude yana dagawa ya kwankwada, sanda ya sauke gwangwanin yasha fiye da rabi, numfashi ya ke mayarwa kamar wanda ya yi gudu.

Yasa hannu ya balle maballin rigar shi guda biyu, dan yanajin kamar sun taimaka wajen shake mishi wuya suna barazana da kaikawo na iskar numfashin shi. Motsin da yaji sai da ya zabura, juyawa ya yi yaga AbdulHafiz da yake kallon shi, gwangwanin ya daga yana karasa shanye abinda yake ciki, saida ya matsa shi da hannun shi tukunna ya jefa cikin kwandon shara, yana kallon AbdulHafiz din ya saka hannu a cikin aljihun shi ya zaro wata farar takarda yar karama yana karasowa ya ajiye mishi akan kantar kitchen din, ya mika hannu ya bude fridge din ya dauki ruwa yana ficewa.

Idanuwan shi Hamza ya runtsa yana bude su akan yar takardar da take dauke da rubutun da akayi da pensir.

“Isra’i:32”

Runtsa idanuwan shi Hamza ya karayi, fassarar ayar na yawo a cikin su.

“KADA KU KUSANCI ZINA, DOMIN ITA ALFASHA CE KUMA TAFARKI NE MUMMUNA”

Bude idanuwan shi ya yi yana ganin rubutun da yake kasan na farkon.

“Nur:02”

Wannan karin numfashi Hamza ya ja mai nauyi yana fitarwa.

“MAZINACIYA DA MAZINACI, TO KUYI BULALA GA KOWANNE DAYA DAGA GARE SU, BULALA DARI. KUMA KADA TAUSAYI YA KAMAKU GAME DA SU A CIKIN ADDININ ALLAH IDAN KUN KASANCE KUNA YIN IMANI DA ALLAH DA RANAR LAHIRA. KUMA WANI YANKIN JAMA’A DAGA MUMINAI, SU HALARCI AZABAR SU”

Ya kai mintina biyar yana kara jin shi a hargitse, tun jiya AbdulHafiz yake mishi wannan abin, yana kara hargitsa mishi lissafi, ya manta ranar karshe da yaji zunuban shi na bin shi kamar zasu kayar da shi sai bayan yarinyar jiya. Daga ayoyin da suka yi magana akan hukuncin zina, sai kuma wanda suka yi magana akan muninta da yanda take ragargaza imani tare da ayyuka. Yau tunda safe ya ajiye mishi ayar da tayi magana kan a jefe wanda ya yi zina da aure.

Yana da tabbacin da yawa AbdulHafiz din ya samo ya rubuta yana ajiye mishi duk wadda hannun shi ya kai ya dauko. Baiyi magana ba, bai ce mishi komai ba, saboda bashi da abin fada, tunatarwa ce AbdulHafiz ya ke yi mishi, kuma daga ranar daya fara bin mata ya riga da ya hango barin hakan duk ranar da aka daura mishi aure, saboda bai shiryama daukar wannan gagarumin zunubin ba, da kan shi dai baya jin yana da karfin daukar hukuncin zina da aure, a lokaci daya kuma yanzun shaidan na kallon shi a gefe, yana saka shi tunanin yanda zai kare gabaki daya rayuwar shi da mace daya tal.

Tunda aka furta Amin din data kulle shi karkashin inuwa daya da Hindu ya kiraya ta amsa shi da.

“Okay.”

Ta kashe sai ya kara jin duk wani zumudi da yake ya fita kan shi, tsoro da firgici sun maye gurbin shi, ga AbdulHafiz da bai taimaka wajen samun nutsuwar shi ba, asalima so yake ya karasa firgitar da shi. Da kyar ya iya dafa bango ya fito daga falon, ya samu Abdallah ya dawo, tunda shi gidan su Hamzan ya wuce, Anna ta kira su zo su karbi abinci, har ya fara zuzzuba musu, waje Hamza ya samu ya zauna. Yanajin hirar da suke kamar zasu tashi dakin, amman sam hankalin shi ba’a kansu yake ba, abincin kawai yake kaiwa bakin shi yana hadiyewa badan yana gane dadin shi ba.

AbdulHafiz ne ya mika mishi robar ruwan daya dauka da sauri yana budewa ya sha, sai lokacin ya ji abincin da yake ta hadiya ya karasa cikin shi inda ya zauna da wani irin yanayi.

“Ka ajiye idan ka koshi.”

AbdulHafiz din ya fadi da harshen fulatanci, yana saka Hamza dagowa ya kalle shi.

“Kamar ka damu da lafiyata.”

Ya amsa yana ci gaba da hadiye abincin shi, ya yi niyyar ajiyewa, maganar da AbdulHafiz din ya yi ne ta saka shi karasa cinye abincin da ya ke cikin plate din, aikam ji yake kamar zai mutu saboda cikar da cikin shi ya yi, ga shinkafar tayi mishi tsai-tsaye. Ajiye plate din ya yi yana mikewa.

“Ina zaka je?”

Arafat ya bukata.

“In da ka aike ni.”

Hamza ya amsa shi yana tsallake Fodio ya wuce kitchen, gwangwanye hudu ya diba na giyar shi yana dawowa ya wuce daki, ya doko kofar kamar zai karyata, yana saka Arafat runtse idanuwan shi da karar.

“Ni kadai ne ko yanayin Hamza da gaske ya canza tun da aka daura auren nan?”

Arafat ya tambaya yana kallon su.

“Kai mun alfarma daya Arafat, da kaji na fara maganar aure, ka kamani, ka girgizani, idan banji ba, ka daukeni ka tsoma kaina a bokitin ruwa, kayi komai daya kamata, amman ka duba abokantakar mu, karka barni inyi kuskuren da Hamza ya yi.”

Dariya Abdallah ya yi yana kallon Fodio.

“Auren nan fa dadi gare shi, ka koma gida a gajiye ka samu wadda zata yi maka sannu ma da dadi, koya aka bata maka rai a waje in ka koma gida yaranka zasuyi wani abin da dole saiya sakayi dariya.”

Zuciyar shi Fodio ya dafe yana girgiza kai.

“Abdallah ina magana da wanda zasu fahimta, gaba ki daya rayuwar ka akan iyali ta kare, duk zaman da zaka yi maganarka kenan.”

Murmushi Abdallah ya yi yana ajiye plate din abincin shi, dan ba wani mai yawa yaci ba, zai koma gida suci, baya son ya cika cikin shi. Fodio ba zai taba fahimtar yanda aure yake ba, in zai kwana yana mishi bayani, kuma yasan rayuwar gidansu Fodio din ta taimaka sosai wajen saka mi shi kokwanton nan.

“AbdulHafiz ba zaka ce wani abu ba?”

Abdallah ya tambaya, AbdulHafiz din na girgiza mi shi kai.

“Bazan bata baki na akan Fodio ba, zan mishi addu’a da maganganun.”

Ya karasa yana mikewa shima, gara ya watsa ruwa ya canza kaya, yanzun zasu kara fita daukar yan kai amare, inya dawo saiya duba Hamza, ba shi da kalaman da zai yi amfani dasu ne, har ran shi yake jin kamar akwai kuskure a auren nan da Hamza ya yi, saboda ta kowacce fuska yau Hamza ya nuna sam bai shirya daukar nauyin daya dorama kan shi ba.

<< Mijin Novel 18Mijin Novel 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×