Wani irin shiru take jin gidan tun fitar Hamza, bata gane akwai wutar lantarki ko babu, kasancewar solar da yake gidan, kullum a cikin wuta suke. Bata taba tunanin zata gaji da kallo ba sai yanzun da take da wadattacen lokacin yin shi. Tun karfe goma ta gama bacci, har sharar rashin dalili ta takalarwa kanta, duk da Hamza yayi maganar cewa za'a kawo mai aiki, a cewar shi Anna tayi mishi maganar, yace kuma ta samo musu.
Riga da wando ne a jikinta, sai ta daura farin dankwali, zaka yi tunanin fita zata yi saboda kwalliyar da take. . .