Duniyar tayi mishi tsaye waje daya, kallo daya za kai mishi kasan baya cikin kwanciyar hankali, damuwar da take tare da zuciyar shi shimfide take kan fuskar shi.
"Me yake damun ka?"
AbdulHafiz ya tambaye shi, kai kawai ya iya girgiza mishi yana fadin
"Babu komai."
Ya kuma ji dadin yanda bai matsa mishi da tambaya ba, saboda bashi da wata amsa tsayayya da zai iya baiwa AbdulHafiz din. A watanni biyun nan cikin Hindu ba karamin wahala yake bata ba, bata kwana biyu ba'a kara mata ruwa ba. Gara cikin satin nan yaga ta fara warware wa, watannin. . .