Ran shi in yayi dubu a bace yake, shisa ko sallama baiyi ba ya shiga gidan Fodio. Shi ya hadu da mutumin da zaiwa zane a Office yau, suna karasa magana kan shi tsaye nan yayo. Shi kan shi yaga kokarin da yayi har yai magana da mutumin batare da an samu wata matsala ba.
“Ina ta kiran ka baka daga ba”
Arafat da yake tsaye ya furta, kallon shi Hamza yayi yana daga girar shi batare da yace komai ba, tunda baisan neman me Arafat din yake mishi ba. In dan client din sune, ya rigada ya gama magana da shi
“Fodio ne daman…”
Arafat din ya fadi muryar shi na rawa, hakan yasa Hamza cewa
“Me ya faru? Me ya sami Fodio din?”
Kai Arafat ya girgiza
“Nima ban sani ba, tun jiya wajen karfe biyu na dare ya kirani naje na dauko shi, ko motar shi bansan ina ya kai ba, ya kulle kan shi a daki, duk yau fa bai fito ba”
Da mamaki a fuskar Hamza yake kallon Arafat din, baice komai ba ya nufi hanyar dakin Fodio din, Arafat na bin bayan shi. Kwankwasawa ya fara yi
“Fodio…”
Ya kira yana cigaba da dukan kofar, dai-dai lokacin da AbdulHafiz ya karaso hadi dayin sallama yana dorawa da,
“Yanzun nake ganin text din ka Arafat, me yake faruwa ne? Me ya sami Fodio din?”
Kafin Arafat ya amsa, Hamza ya riga shi da fadin,
“Da mun san me ya same shi ba zaka ganmu anan tsaye ba.”
Sosai AbdulHafiz din yake kallon Hamza, yayi watanni yana ganin yanayin da yake shimfide a cikin idanuwan shi yanzun, abu kadan yaje bata mishi rai, duk da ba hakuri gare shi ba tun da can, amman na yanzun ya wuce misali, yasan Hamza, ya san shi kamar yunwar cikin shi, yau neman taimako yakeyi, yana kokarin boye damuwar shi a bayan bacin rai.
“Ko me yake damun ka ya jira.”
AbdulHafiz ya furta, yana karasawa ya kwankwasa dakin.
“Fodio bamu da duk rana, ka bude kofar nan, nasan kana ciki, kana jinmu kuma, idan waje kake so duk mu baka, ka bude ka fada mana sai mu tafi…”
Shirun dai ne amsar da suka samu.
“Idan na sake kwankwasawa zan dauka wani abu ya sameka, zan karya kofar in shigo Fodio…”
Wani shirun ya sake ziyartar wajen, kafin suji alamar motsi, ana murza mukulli, tukunna Fodio ya bude dakin, kallo daya zakayi mishi kasan baya tare da nutsuwa ko kadan, ga idanuwan shi sun canza launi, sun rine sunyi wani irin ja.
“Me yasa ba zaku kyaleni ba?”
Arafat ne ya fara wucewa cikin dakin, kafin Hamza yabi bayan shi, runtsa idanuwan shi Fodio yayi yana wani irin sauke numfashi, takawa yayi da nufin fita daga dakin, AbdulHafiz da yake bakin kofar ya hankada shi yana mayar da shi ciki, shima ya shiga, sannan ya tura kofar yana jingina bayan shi a jiki.
“What the fuck? Meye haka wai? Naji… Ku fita ina bukatar ku bani waje, kun ganni ai, babu abinda ya sameni, bana son magana ne da kowa.”
Fodio ya fadi muryar shi a dakushe.
“Baka san magana da kowa, tunda ka bude kofar kai kadai kake surutu Fodio.”
Arafat daya sami waje gefen gadon dakin ya zauna ya fadi, AbdulHafiz na dan daga kafadun shi cikin yarda da maganar Atafat din yana kallon Fodio, kafin ya zame takalman kafar shi yana shiga cikin dakin sosai shima. Kallon su Fodio yakeyi, sosai yake kallon su, Hamza na zaune ya saka hannuwan shi ya dafe fuskar shi. Arafat ya hau saman gadon sosai yana jingina bayan shi da bango hadi da mike kafafuwannshi, sai AbdulHafiz da yake zaune shima, ya dora kafar shi daya akan dayar.
Ya san su, ba tun yanzun ba, kamar yanda yace bayason magana da su, ba zasu ce mishi komai ba, in zasu wuni zaune a dakin, ko a tsakanin su ba zasuyi hira ba, amman ba zasu taba barin shi ya zauna shi kadai ba a yanayin da suka gan shi. Tsikar jikin shi yaji ta tashi, kafin tsoron da ganin su yasa ya tafi ya dawo mishi yana cika mishi zuciya taf, idanuwan shi ya runtse yana jin shi a hotel din, yana jin kamar yana tsakiyar mata suna cashewa a hall din da aka kama dan gudanar da bikin cikar shekara na abokin shi da karatu ya hada su, shi kan shi kuma ya shigo Kaduna ne musamman saboda taron bikin.
Zai iya cewa, kafin su Hamza, Ashir ne abokin da yake da shi, kuma abokin shi tilo da suke waya, suka san gidajen juna a garin Kano. Kuma har su Hamza sun san Ashir din, dan in ya shigo Kaduna suna haduwa duk a gaggaisa, har fita sukanyi tare. Idan yana hasaso wani lokaci da zai tuba ya daina rayuwar da yakeyi, yakan yi zaton kowanne mutum na duniya mai irin halayen shi ma yana da wannan tunanin, amman banda Ashir. Ko maganar akayi mishi tunda lalacewar da gidansu sukaga yayi ne yasa su yi mishi aure ko zai kintsu, maganar shi daya ce,
“Mai rabon shiryuwa fa zai shiryu, kana zaune in kana da rabo, ba sai ka wani wahalar da kanka ba, ku barni inyi shagalina.”
Ashir na rayuwa kamar an mishi alkawarin shekaru masu tsayi, yana rayuwa kamar yana da tabbacin me goben shi zata haifar. Haka daren jiya ya kasance musu. Ko Fodio bai fita daga gida ba sai karfe sha daya da rabi na dare, tunda ance musu shagalin har asuba zai kai, kuma haka suka cigaba da rallewa bayan an yanka cake, misalin karfe daya da rabi na dare, da shi da Ashir sun saka wata yarinya a tsakiya suna tiqa rawa ta rashin mutunci, Ashir din na mishi alamu da ya ganar mishi yanayin fuskar budurwar shi ko tana kishi.
Dariya Fodio yayi yana girgiza kai, lokacin da yayi dai-dai da canjin daya bayyana a fuskar Ashir din yana dakatawa da rawar da yake hadi da dan dakuna fuska yana dafe kirjin shi.
“Ashir?”
Fodio ya kira, amman sautin kidan da yake tashi bai bar muryar shi ta karasa fuskar Ashir din ba, kafin Fodio yai wani yunkuri har Ashir din ya yanke jiki ya fadi. Yanayin da yasa hankulan mutane da yawa komawa kan shi. Kafin wani lokaci gabaki daya hall din ya hargitse. Fodio ba zaice ga asalin abinda ya faru ba saboda tashin hankalin, abinda zai iya tunawa shine kalaman wani da baisan wanene ba yana fadin,
“Wannan ai ya rasu fa.”
Kalaman da suka gigita gabaki daya rayuwar shi, suka jefashi cikin wani irin firgici marar misaltuwa, wanda bashi kadai ba, dan da yawa mutane har an fara gudu ana fita daga hall din, cikin wannan tururuwar fitar ya tsinci kanshi da binsu, ya manta sam da mota yazo wajen, a haka ya samu ya fita daga hotel din zuwa titi ya fara tafiya, sai da ya karasa gidan man farko da yake hanyar tukunna ya iya tsayawa yana dan tsugunnawa cikin son neman numfashin shi da yake kokarin kwacewa.
Jikin shi babu inda baya rawa, ko da tunanin ya ciro wayar shi ya kira kowa ya fara samu yazo mishi, sau hudu tana subucewa ta fadi daga hannun na shi. Sai da ya tsugunna tukunna ya samu ya kira Arafat, muryar shi ma bata fita sosai, kalamai yake kokarin hadawa kamar mai koyon Magana.
“In zaka iya Fodio ka turomun location din da kake.”
Arafat din ya fadi, hakan ya samu yayi, tukunna yazo ya dauke shi. Basuyi wata magana ba har suka karasa gida, kan shi tsaye daki ya shiga yana mayarwa ya rufe. Kayan jikin shi ya fara cirewa, yana wanka ya tsarkake jikin shi, ya fito ya nemi wasu kayan ya saka, zuwa lokacin har zazzabi ya rufe shi. Mutuwar bata kara gigita shi ba saida ya kwanta, tukunna wani irin tsoro ya shige shi.
“Mutuwa na binku fiye da yanda tunanin ku yake baku wallahi, ba jiran ku zatayi ba, kuna tare da ita a duk takun da zakuyi, a duk inda zaku shiga tana jiran umarni, ku dinga shiga inda ba zakuyi dana sani idan mutuwa ta riske ku ba.”
Kalaman AbdulHafiz da yake fada musu a duk rana suka dawo mishi.
“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”
Ya furta muryar shi na karyewa, da gaske AbdulHafiz yakeyi, mutuwa bata jiran kowa. Koya ya rufe idanuwan shi Ashir yake gani, yana kasa gasgata cewar a gaban idanuwan shi, a cikin hotel, da kida yana tashi mutuwa ta dirkar mishi. Ba abinda Ashir zai cewa Ubangiji Fodio yake tunani ba, shi abinda zai fada, baisan lokacin daya dirko daga kan gadon ba yana zama dirshen ya janyo kafafuwan shi, ba zai iya tuna ranar karshe da hawayen shi suka zuba ba.
Duk kuwa bakar wahalar da yasha a gidan su, tunda ya fara gane kwayoyi ma ko dukan shi sukayi da ya jefa hudu ko biyar komai yake bace mishi, amman yau kuka yake kamar karamin yaro, kuka yake yana rasa kalaman da zai amfani da su wajen neman yafiyar Ubangiji, balle kuma ta inda zai fara dan ganin ya kankare tarin zunuban da suke kan shi. Gani yake kamar ba zai tashi daga inda yake ba mutuwa shima zata dirkar mishi kamar Ashir. Haka ya kwana anan wajen, bacci ko na dakika, asuba ma anan yayita, kan shi yake ji kamar zai bude.
Har zuwa yanzun da su AbdulHafiz suka shigo, kafin suzo din yanajin kiran da Arafat ya dinga mishi, amman bayason ko da motsawa ballantana yaje ya bude kofar. Yanzun ma kallon su yakeyi.
“Inalillahi… Wai Fodio me yake faruwa ne?”
Arafat ya fadi, ganin hawayen da suka zubo mishi, yana saurin saka hannu ya goge su. Hamza ma dagowa yayi da sauri, kafin yaji cikin shi ya hargitsa da tashin hankali.
“Fodio.”
Ya fadi cike da mamakin ganin da gaske kuka yakeyi, nan wajen ya durkushe, baya kunyar kuka a gaban su, ba lallai su fahimci kalar tashin hankalin da yake ciki ba, Ashir bai mutu a gabansu ba, basu ga yanda ran shi yabar jikin shi cikin wasu yan dakika ba, su dukan su tasowa sukayi suna rasa abinda ya kamata suyi banda tsayuwa akan Fodio din.
“Ashir…. Ashir… Ya… Ya rasu.”
Fodio ya kakalo maganar dakyar, su duka ukkun kowanne da kalar salatin daya fito daga bakin shi.
“Fodio…”
Arafat ya fadi cike da tausayawa.
“A hotel… Ya rasu a hotel.”
Fodio ya karasa maganar yana tsayar da rinannun idanuwan shi akan Hamza.
“Bamu da lokacin da muke tunani… Hamza bamu da wannan lokacin.”
Kan shi Hamza ya saddar kasa, tsoron dake cikin idanuwan Fodio na taba shi ta fannonin da bai taba tunani ba, fannoni daban da yanda suke taba Fodio, dan bacin ran da yake tare da shi ya nema ya rasa, hakan na bude mishi kofar da yayi amfani da bacin ran ya rufe, hakan na ba wasu abubuwa daban ziyartar shi, kamar wanda aka dokama guduma a kai ya kalli AbdulHafiz, kafin ya furta,
“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”
Amman daga Fodio har Arafat sun dauka shima mutuwarce ta taba shi, AbdulHafiz ne kawai ya fahimci damuwar da take tattare da Hamzan bata da alaka da mutuwar Ashir. Kai Hamza ya dafe yana dan murza goshin shi, kafin ya sauke hannun hadi da furzar da iska ta bakin shi, yasan yanda yake idan ranshi ya baci, ya kuma san yanda yanke hukunci cikin fushi yake abokin tarayyar shi. Musamman idan yasha wani abu da ya kara taimakawa wajen tunzura shi.
“Hindu…”
Ya furta kasan numfashin shi, hanjin cikin shi na hautsinawa, hannun kofar da yake tsaye a kusa da ita ya kama, hakan nasa Fodio janye jikin shi ya matsa, Hamza ya bude kofar ya fice, su dukan su suna binshi da kallo kawai. Kafin Arafat ya zauna a gefen Fodio, AbdulHafiz ya zauna a dayan gefen, lallashin juna ba halayyar maza bace a yankin Najeriya, zasu zauna tare da shi har ya samu natsuwar da zai iya jinyar ciwukan shi da kan shi. Shine kawai abinda zasu iya yi mishi.
*****
Yana zaune a mota yake gwada kiran lambar Hindu, tunda yayyenta suka zo gidan shi maganar kwasar kaya ya tabbata tana gida. Yasan yanda take a wajen Babanta, duk yanda zai dauki zafi, ita din zata iya lallaba shi, tunda tasan shi, tasan yanda yake idan ran shi ya baci, daya huce shikenan zasu shirya, yanzun ma da ta hakura har safe ta dawo gidan ya huce komai zai wuce musu kamar bai faru ba. Ba wannan bane gagarumin fadan da sukayi, kuma ko wancen dinma sun shirya, babu wanda yaji sunyi, sirrin su ya zauna a tsakanin su.
Sai dai har tayi ringing ta yanke ba’a daga ba, ya sake kira har sau hudu.
“Bafa kabari ta dauki wayar ta ba.”
Wata murya ta furta kasan zuciyar shi tana saka shi dukan abin tukin da karfin gaske, kafin ya dora kan shi a jiki.
“Bamu da lokacin da muke tunani…”
Maganar Fodio ta dawo mishi da yanayin da yake fuskar shi lokacin daya furta mishi wannan kalaman. Tunasarwar AbdulHafiz ta kullum ce, amman duk idan Fodio ya bude bakin shi, saiya fadi maganganun da Hamzan zaiji sun shiga cikin fatar jikin shi suna tsikarin shi a wajaje da dama hadi da barazana da zaman lafiyar shi. Lumshe idanuwan shi yayi, kafin wani abu ya tsirga mishi, Ashir ya rasu, fuskar Ashir din yake gani da ranar karshe da suka hadu, yanda yake maganganun shi cike da buruka masu tarin yawa.
“Ba zaka gane rayuwar nan ba komai bace, sai kayi kokarin juya kwanciya bayan Allah ya mayar maka da ruhinka a gangar jikin ka, kaji kamshin kasa ya cika maka hanci, kana tunanin mafarkine, saika bude idanuwa kaga dundum, kafin mala’iku su dirar maka da tambayoyin da baka da yakinin zaka iya amsawa.”
Dagowa Hamza yayi da sauri yana bude idanuwan shi, kan shi ya girgiza ko muryar AbdulHafiz da tsoron dake muryar zasu fice mishi daga cikin kai. Da ya sami Hindu ya lallabata zata dawo, tsautsayina yasa fadansu yakai kunnuwan yan gidansu. Ta dawo ya riketa a jikin shi ko zai batar da abinda yake faruwa da shi yau. Samu yayi ya murza mukullin motar shi, kan shi tsaye gidan su Hindu ya nufa, ya dade ko bayan an bude mishi kofar yayi parking a zaune cikin motar yana rasa ta inda zai fara. Bawai yana ta’ammali da kunya bane ba, kawai baisan ta inda zai fara ba.
Fitowa yayi daga motar.
“Kuskure ne kayi Hamza, idan su basu fahimta ba ita zata fahimta. Tana son ka, zata yafe maka kamar kullum.”
Ya furta ma kanshi a hankali yana kara samun kwarin gwiwa. Gidan nasu ba bakon shi bane, tunda bashi da wanda zai aika ya kira mishi ita, kan shi tsaye ya taka har ciki hadi da yin sallama yana shiga, da yake yasan gidan, baibi ta falon Mama ba, zagayawa yayi yana shiga falon Anty kai tsaye. Ita kuwa ta amsa mishi sallamar tana karasawa cike da bayanannen mamaki a fuskarta da ma muryarta ganin Hamza ne.
“Anty ina wuni.”
Ya furta yana sadda kan shi kasa, dan haka kawai yaji yau tayi mishi kwarjinin fiye da ko yaushe.
“Lafiya kalua.”
Ta amsa tana kallon shi cike da mamaki, dan bata tsammaci ganin shi yau ba, ko dame yazo kuwa. Zuwa tayi tana wuce shi, numfashi mai nauyi ya sauke ya sami waje ya zauna, da zaiga Hindu, da zata fito komai zaizo mishi da sauki, ko Asma ma, sai ta kira mishi ita. Yana wannan tunanin yaji muryar Baba kamar daga sama yana fadin,
“Me yazo yi?”
Sai da zuciyar shi ta doka, baisan bashi da confidence ba sai ranar daya fara dora idanuwan shi akan Baba, muryar shi har rawa yaji tanayi, kuma gaishe shi kawai yaje yi wancen lokacin. Yanzun kam sai abinda Allah yayi, amman koma meye yayi laifi, wannan karin ya sani, laifin nashi ne daya bari rigimar su ta kawo gida.
“Lafiya? Me ya faru?”
Baba ya furta yana zagayowa ya tsaya yana kallon Hamzan da har karfin halin zauna mishi cikin gida ya samuyi.
“Baba ina kwana.”
Hamza ya furta yana wani irin sauke murya.
“Me ya faru?”
Baba ya sake furtawa kamar baiji gaishe shin da Hamza yayi ba. Numfashi Hamzan yaja yana saukewa.
“Ni mai laifine Baba, dan Allah kayi hakuri. Zuwa nayi in bada hakuri.”
Wani irin kallo Baba ya yi mishi.
“To madallah….ka tashi ka koma, kar su Muhsin su karasa gidan kuma a kulle, bana son kayan nan su kara kwana.”
Dagowa Hamza yayi yana kallon Baba cikin tashin hankalin jin maganar da yayi, abin babbane, yaga borin namiji ne.
“Babaa…”
Ya fara, Baban na dakatar da shi.
“Ka tashi ka ficemun daga gida…ba zan sake maimaitawa ba.”
Yanayin muryar Baba ya saka shi mikewa, dai-dai lokacin da suka hada idanuwa da Hindu da ta fito daga dakin Asma da nufin ta dauki ruwa, ko muryoyinsu bataji ba saboda hankalinta na wani waje daban, aikam zuciyarta tayi wata irin mummunar faduwa, ji tayi kamar taga dodo, iskar da ta fara shaka ta daban na bace mata.
“Baba me yake yi? Ni ba zan koma ba, dan Allah karku ce in koma.”
Ta karasa muryarta na karyewa.
“Hindu…”
Hamza ya fadi wani abu na matsewa a zuciyar shi ganin da gaske take furta maganganunta, har matsawa takeyi kamar zai karasa ya kamata su koma dole, kai take girgiza mishi.
“Zaka fice mun daga gida ko saika kara firgitamun yarinya?”
Sosai ya kara kallon Hindu, kafin ya juya yana ficewa daga dakin, ita kam inda ta fito ta koma da saurin gaske, badan cikin jikinta da yayi mata nauyi kamar yana shirin fitowa kowanne lokaci ba, tsaf da gudu zata karasa cikin dakin. Anty ma nata dakin ta wuce, kome zata tsaya tacewa Baba bata bakinta zatayi, batace a saurari Hamza yanzun ba, koba komai dole su kwatarwa Hindu ‘yancinta kafin su bari ta koma, amman yanda Baba ya dauki zafi idan tai mishi zancen komai ma zai iya faruwa, dan haka kai tsaye bandaki ta shiga tana daura alwala, abin yafi karfinta, ba zata wahalar da kanta ba, addu’a zatayi, tana da yakinin komai zaizo musu da sauki.