Skip to content
Part 29 of 33 in the Series Mijin Novel by Lubna Sufyan

Da wani ya tambaye shi me yayi a cikin kwana biyu ba zai iya fadi ba, ko da kudi za’a saka mishi kuwa. Ko masallaci baije ba a kwana biyun, tunda ya hau sama bai sakko ba, kwalaben giyar shi ma dibowa yayi ya ajiye gefen gado, daya mika hannu dauka zaiyi. Ranar farko yana dawowa gida ya sami su Muhsin a kofar gida, bai tsaya gardama da su ba yace su shigo su kwashe kayan, ya sanar musu kayan duk da suke a kasan na Hindu ne, sannan ya hau sama ya shige dakin shi, kwalaben giya ya dauka ya samu waje ya zauna, sai da ya daina gane abinda yake faruwa, bai sauran salloli ba sai cikin dare. Gabaki daya ya daina gane kan rayuwar. Jin shi yake kamar an kama kafafuwan shi an daga su sama an jirkice shi.

Dan snacks din da yake dashi a saman ne kawai abinda yake a cikin shi. Ko yau ma daya mike zaiyi alwalar Magriba saida ya koma ya zauna na wasu dakika saboda jirin da ya kwashe shi da bashida alaka da giya sam, tunda bai sha ba duk ranar. Badan sallah ba, motsi ma ba zaiyi ba. Wayar shi na falon kan kujera tun shekaranjiyar, idan an kirama bai sani ba, balle kuma ko da caji a jiki ko babu.

Yana samu yayi sallar ishai ya koma ya kwanta, ko kwan dakin da yake ji cikin idanuwan shi bai iya tashi ya kashe ba. Duk tsaftar Hamza a kwanaki biyun nan jikin shi banda ruwan alwala baiga wani ruwa ba, kayama amai da yayi ne ya jikasu garin wanke fuska shisa ya sake wasu. Kallo daya za kai mishi idan kagan shi kasan baya tare da natsuwa sam, dan rigar da wandon basu hadu ba, haka yasa kayan shi.

Kamar cikin kunnuwan shi yake jin ana sallama, sake runtsa idanuwan shi yayi yana shigar da kanshi cikin filo. Sosai yake jin sallamar na kara kusantowa kafin a fara kwankwasa kofar dakin da yake ciki.

“Yayaa”

Yaji muryar Auta, kafin ta Abid da cikin yaren shuwa yake fadin.

“Yayaa…ko dai basa nan?”

Da shakku a cikin muryar shi, suna zaune a gida kawai shi da Auta suka yanke hukuncin fita siyan shawarma, Anna ma sai da tace suyi order a kawo musu gida, sukaqi saboda yawon suke so. A hanyar su ta dawowa ne sukayi shawarar su biyo gidan Hamzan tunda kwana biyu basu gan shi ba. Suna da tabbacin aiki ne ya rike shi, idan bai kira su ba, yakan yi musu zuwan bazata makaranta ya duba su.

“Wanne irin basa nan, kana ganin wayar shi a kan kujera? Ni jikina na mun wani iri. Kuma falon kasa tas an kwashe kaya fa”

Auta ta fadi, kafin ta murza hannun kofar tana turawa.

“Yayaa”

Abid ya kira cikin tashin hankali, su biyun suna turereniya wajen shiga cikin dakin, amman ko dagowa Hamza baiyi ba, basu tabbatar yana da rai ba saida suka hau kan gadon, Abid na kama shi ya juyo da shi,

“Ka kyaleni Abid”

Ya furta yana kwace jikin shi, ko motsi bayason yi. Shiru yake bukata har sai ya samu dai-daito koya yake.

“Wanne irin in kyaleka? Me yake faruwa? Me ya sameka?”

Abid yake tambaya cikin tashin hankali, dan ba zai tuna ranar karshe da yaga Hamza kwance yana wani ciwo ba tun tasowar su. Baisan ko da yabar kasar ba. Auta ce da ta taba jikin Hamzan tana jin shi kamar wuta tace,

“Zazzabi ne ma a jikin shi.”

Kama Hamzan ya sake yi yana dago shi, yama ki bude idanuwan shi.

“Yaya ka tashi mu kaika asibiti, baka da lafiya zaka zauna a gida. Ina Anty Hindun zata barka haka?”

Kai Hamza ya girgiza mishi yana bude idanuwan shi da yakeji sunyi nauyi, jin sunan Hindu na saka tsikar jikin shi tashi, hannun shi daya yasa yana ture na Abid.

“Na ce ka kyaleni bakaji ba ko?”

Kallon juna Abid da Auta sukayi, cikin su babu wanda baisan kafiya irin ta Hamza ba, sauka daga gadon Abid yayi, mutane kance Hamza dogo ne, tsayayyen namiji, amman wanda duk zaiga Abid din saiya dauka shine Yayan Hamza, saboda a tsayi da girman jiki ya fishi. Akanyi mamaki ko da Hausa yayi akaji alamar fulatanci daya zauna a harshen shi, mutane na da yardar cewa fulani na da dan jiki, mafi yawancin su kuma basa girma.

Sai su dinga yi kamar Abid dinne bafullatani na farko daya karya al’adar su ta fitowa a siraran mutane.

“Zaka iya tashi da kanka Yaya… Ko zan dauke ka. Wanda duk ka zaba shi zai faru”

Abid yai maganar yana kallon Auta.

“Ki kira Ann”

Kai kawai ta daga mishi tana sauka daga kan gado itama, dan wayarta na cikin mota tabari, duk a zaton su ‘yan mintina zasuyi su wuce gida.

“In dauke ka din kenan?”

Kallon shi Hamza yayi, baya cikin yanayin da zai iya yin wata gardama, dan haka ya mike, jirin da yake gani bai hanashi ture hannun Abid daya mika mishi cikin son ya taimaka mishi ba. A haka suka sauka kasa. Abid ne ya dauki wayar Hamzan yana sakawa a aljihu, a wajen suka hadu da Auta.

“Babu asibitin da zanje, mu tafi gida kawai.”

Ya furta yana bude bayan motar ya shiga. Cikin kasa da mintina da suka dauke shi ya fito daga cikin gidan ya shiga motar ya riga ya yanke hukunci daya, ya daina boyewa abinda yake faruwa, fadansu ya riga da ya kai gidan su Hindu, ko zata dawo mishi dole maganar ta kai nasu gidan. Da Anna taji me yake faruwa daga bakin wani cikin manyan Hindu, gara taji daga bakin shi. Ko ba komai ita ba zata bar shi kamar yanda AbdulHafiz yayi mishi ba.

Duk a cikin abinda ya faru daga kwana uku zuwa yau, babu abinda yake mishi ciwo har kasan zuciyar shi irin yanda AbdulHafiz ya tashi tsam bayan ya gama bude mishi ciwukan shi, yanda ya mike yana barin shi kamar yana tsoron idan jinin da ciwukan da ya bude mishi suka taba shi wata cuta zata kama shi. Sosai abin yayi mishi ciwo na gaske, sai da suka hada idanuwa da Arafat kafin shima ya zabi bin AbdulHafiz batare da yama san meya faru ba.

Har suka karasa gida wannan tunanin yakeyi a ran shi. Auta ce tayi sallama, dan a falo ta sami Anna a tsaye, tun bayan da ta kira ta fada mata Hamzan bashi da lafiya, gashi suna gidan shi ma, ta kasa samun natsuwa sam, itama ta sake kiran Autar, tace gasu nan ma zasuyo gidan. Hatta Appa ta fada mishi, shima yana falon a zaune, idan yace mata ta zauna ma ba zata zauna ba, shisa bai bata bakin shi ba.

Appa ya dauka ciwon ba zai wuce zazzabi ba sai da ya kalli yanayin Hamzan kamar wanda ya sami tabin hankali na wucin gadi, ga gashin da yake fuskar shi duk ya cukurkude saboda rashin gyara. Waje ya samu a daya daga cikin kujerun falon yana zama, ba sai wani ya fadama Abid da Auta abinda suke gani ba, sun san koma meye yake damun Hamzan ya girmi rashin lafiya. Dan haka kowa ya wuce dakin shi batare da sunce komai ba.

“Hamza…”

Appa ya kira, dan Anna ma ta rasa abinda zata ce saboda tashin hankali, tunani takeyi barkatai a lokaci daya tana son hasaso abinda ya sami danta haka.

“Appa ban kyauta muku ba.”

Hamza ya fadi idanuwan shi kafe a jikin bango, yaki yarda ya kalli fuskokin su, jin yanda kafafuwan Anna suke rawa yasa ta samun waje gefen Appa ta zauna, numfashi Hamza ya sauke mai nauyin gaske, yana sauke idanuwan shi akan su Anna.

“Na saki Hindu.”

Ya furta yana jin wani irin shiru daya biyo bayan maganar da ya yi.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Shine abinda Anna ta fadi, Appa na dorawa da,

“Subhanallah, saki da tsohon ciki Hamza? Me ya faru haka?”

Dan daga kafadun shi Hamza yayi, baisan ta inda zai fara ba, baisan me zai ce musu batare da halayen shi daya dauki shekaru yana boye musu sun fito fili ba.

“Bansan me zance ba Appa, kawai nasan ba laifinta bane ba…har sun kwashe kayan su.”

Ya karasa maganar yana gyara zaman shi a cikin kujera. Yanayin shi yasa Appa fadin,

“Yanzun aini gidan ya kamata inje…”

Saboda koma meya faru yanayin Hamzan ya nuna idan fada ya rufe shi da shi babu abinda zai fahimta. Tun ranar da abin ya faru ya kamata ace sun sani, baisan wanne kallo iyayen Hindu suke musu ba, ballantana ga tsohon ciki, haihuwa yau ko gobe, ace ya sakar musu yarinya.

“Ai bakai kadai ba, harni ya kamata mu tafi.”

Anna ta fadi tana daukar mayafinta da ta fito da shi da nufin ta bi bayan su asibiti. Ganin Hamza ya kara gyara zama yasa Appa fadin.

“Kaima kasan ai ba zama zakayi ba ko?”

Numfashi yaja yana saukewa, bashi da wani zabi. Haka ya mike yana bin bayan Appa, sannan Anna ta furta,

“Abid mun fita.”

Cikin yaren shuwa, tana jin ya amsa mata tukunna itama tasa kai suna ficewa daga gida. Appa ne yaja motar suka nufi hanyar Barnawa da zata sada su da gidan su Hindu.

*****

Wani irin bacci takeyi a kwana biyun nan kamar wadda ta tara gajiya mai yawan gaske. Tun da aka kwaso kayanta sai take jinta wani irin sama-sama, ga ciwon baya da take fama da shi da bata furtawa kowa komai a kai ba, asibiti ma da taje batayi musu magana akai ba. Tana jin yanda tai wata irin saduda da lamurran duniyar gabaki daya. Ko da wayarta da aka kawo mata, drawer ta ja ta jefata a ciki. Batasan karya ta fadama kanta na cewar Hamza da auren shi sun fita daga ranta ba sai da taji zuciyarta na mata wani irin ciwo bayan kwaso kayan.

Amman ta mikama Allah lamurranta, hawaye ma a kwanakin nan sun kaurace mata. So take kawai ta juye abinda yake cikinta ko zata rage wani nauyin. Gashi yan gidan kowa yana kokarin ganin murmushi a fuskarta, musamman Asma da ko kwanciya ta juya sai taji ta tambayeta ko lafiyarta. Daren jiya ma sai da tace.

“Asma lafiyata kalau fa, kiyi bacci kin ji ko?”

Anty kanta tana iya lekasu fiye da sau biyar kafin wayewar gari. Yau ma ganin yanda duk idan ta wuce suna binta da ido kamar mai shirin breaking a kowanne lokaci sai ta koma tana tausaya ma damuwar da suke ciki. Shisa tana idar da isha’i bata kwanta kamar yanda takanyi ba, ta fito falo ta zauna ayi hirar da ita, suna kallon shirin “Kwana Casa’in” a tashar Arewa24.

“Ni fa Mal. Alin nan bala’in kunnani yake yi.”

Asma ta fadi, Jafar na jinjina kai.

“Ai wawane, yanda yakeyi kamar yana da kyau shine abinda yafi batamun rai.”

Dan murmushi Hindu ta yi.

“Kuji ikon Allah fa, celebrity ne fa.”

Wani irin tsaki Jafar yaja.

“Kuyita rage mishi dai kunji.”

Cewar Anty da take zaune a gefe, da yake girkinta ne ranar. Mikewa ma take shirin yi ta shiga bangaren Baba, sai gashi ya shigo falon.

“Me ake kallo haka?”

Hindu da murmushinta ya fito daga zuciyarta yanzun ta riga kowa amsa shi.

“Baba…”

Ta furta cike da kaunar da take yi mishi.

“Hindu… Kinci abinci?”

Baba ya tambaya. Ta bude baki zata amsa shi, sallamar su Anna ta katse ta, sai da taji zuciyarta tayi wani irin dokawa kamar zata fito waje saboda wani irin firgici da ta tsinci kanta a ciki, har suka gaisa da Anty, aka basu wajen zama, sam bataji ba, hankalinta na kan Hamza da yake tsaye a gefe kamar magen da aka tsoma a ruwan sanyi. Kanshi sadde yake a kasa, lokacin da Anty tadan taba Hindu ne ta kula da har su Anna sun zauna, Asma da Jafar ma bata ga barin su falon ba.

“Ina wunin ku.”

Hindun ta iya furtawa muryarta na karyewa.

“Lafiya kalau Hindatu, sannu kinji.”

Appa yai maganar kamar yana neman wata Hausa da ta dace yayi amfani da ita, Anna kuwa duk kunya ta gama rufeta, tama kasa cewa komai, wani irin shiru na ziyartar falon, kafin Appa ya fara Magana.

“Wallahi Alhaji Aminu mu bamu san abinda yake faruwa ba sam sai yau din nan, yana zuwa ya same mu da maganar muna tahowa.”

Kai Baba ya jinjina.

“Haba bakomai, ai zance ya rigada ya kare ma. Har an kwaso kaya.”

Kallon Hamza da ya kara sunkuyar da kan shi Appa yayi, kafin ya mayar da hankalin shi kan Baba.

“Subhanallah…”

Sai dai bai samu damar furta wani abu ba, Baba ya riga shi.

“Da ya fada muku ya saketa, ya gaya muku cikin dare ya korota waje? Ana tafka ruwan sama?”

Wannan karin Anna ce ta kalli Hamzan cike da bayanannen mamaki a fuskar ta, so take ya kalleta, so take ya karyata mata abinda Baba ya fada, dan tasan yaronta mai tausayi ne, Hamzan ta ko mace mai ciki yagani tsakiyar dare ana tafka ruwa zai tsaya ya taimaka mata, dan ta ba zai aikata wannan halin da zata alaqanta shi da na marassa tunani da tausayi ba, dan bata taba jin ko yan unguwa sun mishi shaidar zalunci ba.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Appa ya fadi yanajin lamarin yafi karfin shi, da Baba yace an kwaso kaya sai da ranshi ya sosu da rashin neman su da baiyi ba dan ai kokarin sulhunta lamarin. Yanzun kuma da yaji dalili, sai yaga sunyi mishi matukar kokari da suka ma basu wajen zama.

“Bana so duk mu bata lokacin juna, aurene kaddara ta hada, yanzun kuma ta raba. Sai muyi musu addu’a Allah yasa hakan shine alkhairin su, ba zance zumunci zai kare ba saboda rabon da yake jikinta…aure kam in shaa Allah karshen shi kenan.”

Baba ya karasa maganar da dukkan zuciyar shi, dan yaga takardar sakin, kuma a rubuce saki daya ne Hamza ya yi. Hindu tasan ya gani, saboda Anty ta fada mata, su duka basu san saki biyu bane ba, har yanzun akwai kome a tsakanin su da Hamza, komen da ko a mugun mafarki bata fatan ya faru da ita balle kuma a gaske.

“Baba dan Allah kayi hakuri, nayi kuskure nasani, amman kayi hakuri.”

Hamza ya fadi zuciyar shi na wani irin radadi, ganin kallon da Baba yayi mishi yasa shi kallon Hindu.

“Hindu ki bashi hakuri, kinsanni, ke kinsan abinda su basu sani ba a kaina. Ba zan sake ba, wallahi ba zan sake ba… Ki basu hakuri.”

Ya karasa maganar yana takowa ya shigo tsakiyar falon ya tsugunna a gabanta batare daya damu da su Anna da suke zaune ba, ballantana kuma su Baba. Baya jin akwai macen da zata zauna da shi da halayyar shi kamar Hindu, baima san yanda yake son ta ba sai yanzun da yake ganin da gaske raba shi za’ayi da ita, da gaske sukeyi ba zasu hakura ba.

“Ba zamu bar juna ba, duk abinda zai faru ba zamu bar juna ba, zaki zauna da ni har in canza, zakiyi hakuri dani har in canza…”

Hamza yake furtawa yana sauke idanuwan shi cikin na Hindu da suke cike taf da hawaye.

“Kome zai faru ba zan barka ba, na yafe maka kuskuren ka na baya, zanyi kokari in yafe maka kuskuren ka na gaba.”

Hindu ta karasa mishi hawaye na zubar mata, wannan shine alkawarin da sukai ma juna bayan ya sake ta, lokacin da yaga da gaske ta janyo akwati tana hada kayanta, hakurin daya bata a ranar tayi tunanin shikenan, ta dauka wani abu ba zai taba sake shiga tsakanin su daya danganci shan giyar shi ko Mansy ba. Shisa ta tayashi suka binne rigimar, babu wanda yaji ko yagani. Hannuwanta duka biyun ta saka tana goge fuskarta, wasu hawayen ne suke sake zubowa kamar an bude famfo.

“Wannan alkawarina ne, nayi kokarin cikawa, ka manta naka?”

Wani abu da yaji ya tokare mishi makoshi yake kokarin hadiyewa.

“Zaka canza, ba zaka sake dukana ba, ba zaka sake shan wani abu ba, matsalar mata ba zata sake zama dalilin rigima a tsakanin mu ba…”

A rayuwar shi ya lissafa abubuwa da dama da zasu saka shi kuka, amman bai hasaso mace bace ba, ko bayan da ya auri Hindu bai dauka rana irin ta yau da hawayen shi zasu zuba a kanta zaizo ba, sai yanzun da yaji idanuwan shi sun cika taf da hawaye.

“Zan dora alhakin auren ka akan kaddara, amman yi maka uzuri a lokutta da dama kuskurena ne, ba zan sake maimaitawa ba, Hamza bazan sake maimaita wannan kuskuren ba.”

Kai yake girgiza mata, idan yai magana gunjin kukan da ta karashe zancenta da shi zaiyi shima, fuskar shi ya dafe da hannuwa biyu. Daga Anty da take zaune, Baba, Anna har Appa jikin su ya gama yin sanyi. Kaddarar yaran nasu ce take taba su har kasan zukatansu, bude baki Hindu tayi zata roke shi daya tashi daga tsugunnan da yayi a gabanta, ya daina zubar mata da hawaye karya sa zuciyarta ta karaya, kar ya yaudareta kamar yanda ya saba, wani irin ciwo daya tsirga mata har ranta tayi zaton kashin bayanta ne ya karye.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…. Baba baya na… Bayana ya karye Baba…”

Hindu ta furta cike da wani irin rauni da yasa Anna da tafi kusa da ita kamata, saboda ta kula da abinda yake bin kafafuwan Hindun, tasan nakuda ce ta taho mata gabaki daya, ita da Anty suka kamata, banda salati babu abinda yake fita daga bakinta har suka samu suka karasa mota. Anna ce take tambayar Hamza asibitin da Hindu take zuwa, kafin su duka su dunguma zuwa asibitin.

<< Mijin Novel 28Mijin Novel 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×