Kamar yanda Zahra Tabi'u, marubuciyar Mai Tafiya, cikin alkalamin ta a rubutun Farin wata:
"Kowane labarin duniya yana da tushe. Kowanne yana da mafari. Me ke nan? Wani abu da ya faru har ya zama sanadin wanzuwar jirkitattun al'amura."
Labarin Hindu ya fara a shekarar 2012 a lokacin tana aji biyar a sakandire. Tun bayan haihuwar ta, tun ranar da Baba ya dora idabuwan shi a kanta tana a cikin shawul, aka mika mishi ita dan yayi mata hudu ba, Anty zatace taga wani yanayi a fuskar shi da bata taba gani ba a game da sauran. . .