Wata irin mummunar dokawa zuciyar shi tayi ganin Hindu zaune akan kujerun da suka saba zama, a wajen da suka saba yin zance, amman bashi bane akan kujerar, wani ne zaune a inda ya saba zama, yana magana da Hindu, har tana mishi dariyar nan tata da yake ji a ko ina na jikin shi. Dakyar ya iya yin parking saboda ko gani bayayi sosai, yasan yana da kishi na fitar hankali, ba tun yanzun ba, akan ta yasan kishin shi ya wuce duk yanda kalamai zasu fassara, dan nan take zazzabi mai zafi ya saukar mishi, ko murfin motar. . .