Prologue
“Wai baku gama ba har yanzun?”
Hamza ya fadi yana daurama Amna takalminta. Fitowa Sadiya tayi daga cikin dakin da Suhana da ta turo bakinta tana gab da fashewa da kuka, ko zip din rigar jikinta ba’a zage ba.
“Ban gane me take cewa ba, nayi maganar duniya tayi shiru ta kyaleni.”
Sadiya ta furta cike da neman taimakon Hamzan, wani lokaci har tunani takeyi anya Suhana bata wuce shekara shidda ba, saboda attitude din yarinyar ya wuce shekarunta, tana sane da bakomai Sadiya take ganewa da fulatanci ba, shekara daya kenan da yaran suka dawo hannunta, shekara ta uku kuma da aurensu da Hamza, tasan ba shi kadai ba, harta Annar shi sun barta ne su gwada hankalinta kafin su yarda ta rike su Suhana. Yanzun ma rabin rayuwar da kwata a wajen Anna sukeyi.
Yau weekend din karshen wata, sabon shine ya sauke su wajen Hindu duk karshen wata, acan suke mata hutun karshen mako.
“Kina so in zane jikin ki ko Suhana? Me kike so kuma?”
Bakin da ake cewa irin nashi ne, sai dai shikam yasan baya turo shi haka kullum.
“Ni farar riga nake so…kalar na Amna.”
Kai ya girgiza, su kadai yake da har yanzun, Sadiya tun barin da tayi har yanzun shiru, Allah bai kawo musu wani rabon ba. Amman baya hana shi zane su, akwai kananun rashin kirkin da ba zai dauka ba, ko Sadiya yana mata fadan yanda take sangartasu, yasan yanzun ma fadan shi take tsoro shisa bata sake ma Suhana rigar ba, zama dasu yasa tana jin fulatanci sosai sosai, kawai mayarwa ne bata iyawa har yanzun.
“Ki dauko takalmanki. Idan na sake magana babu inda zaku je.”
Yana kallon hawayen da takeyi sanda ta wuce tana komawa sama. Numfashi Sadiya ta sauke.
“Ke ma baki shirya ba ko? So kuke sai kaina yayi ciwo.”
Dariya tayi tana bin bayan Suhana, Amna ce kawai bata saka shi surutu, ita maganarta ma sai kayi da gaske zakaji, sunfi fada akan ya mata magana tana ji tayi shiru ta kyale shi, fiye da tayi laifi. Karya yake idan yace rayuwa ta kawo shi wannan matakin cikin sauki, ya wahala, yayi jinyar rashin Hindu kamar ba zaiyi rai ba. Sai da ya dauki shekaru biyu ko mace baya daga idanuwa ya kalla, a sujjada Anna ta dinga mishi addu’a kafin ya fara sauraren maganar auren da take yi mishi.
Ranar da tace yaje wajen Sadiya, yar kawarta bai musa ba. Yayi mamaki bayan yaje kofar gidan yaga ita ce ta fito.
“Saad…”
Ya kira da sunanta da yasanta da shi, sun hadu a manhajar BBM tun lokacin blackberry, ita ce mace ta farko daya sani data ke da group a farkon WhatsApp cike taf da mutane duk Ire-iren Hamza, ita kadai admin a cikin su. Ya taya Saad tun a lokacin, saiya kula da duk badalarta a screen ta tsaya, sosai ya karanci tsoronta da yai mata tayin haduwa da shi. Shi kan shi ya girgiza daya ga hotonta, yarinya ce karama a lokacin, daya matsa mata da tambaya ta fada mishi WAEC tayi a lokacin.
Fada yayi mata kamar kanwar shi, basa bin kananun yara, basa bin yaran da basuyi hankalin sanin abinda zabukan su zasuyi musu ba tuntuni. Tayi blocking din shine, bai kuma kara bi ta kanta ba, dariya ya kwashe da ita bayan ta fito ba dan yana cikin nishadi ba. Yasan karya yakeyi yai wa Ayar Allah wayau. Dan rana daya ya wayi gari cewar ya tuba ya daina bin yaran mutane baya nufin kuskuren shi ba zai biyo shi ba. Yasan duk sujjadar shi yana kare sauran addu’ar shi da nemar ma yaran shi kariya, da neman canjin kaddarar laifukan shi su tsaya iya shi.
Idan hakan na nufin auren macen da take da tarihi irin nashi zai hakura, sosai yaga kokarin Fodio na auren Mansy da yayi. Ashe shima bai wuce wannan din ba, kan gwiwoyinta Sadiya ta tsugunna tana rokon daya rufa mata asiri, yace batai mishi ba amman karya fadi dalili.
“Ki tashi kawai, mu duka ba zamu guje ma laifukanmu ba, ni zan aureki, idan ma ban aureki ba wata dai zan aura…”
Yai maganar a gajiye, kuma a yau inda yake zai godewa Allah da zabin da yayi, a duk rana Sadiya na kokarin ganin ta faranta mishi, tana kokarin cike gurbin abinda bata bashi a darenta na farko tare da shi ba wajen gujema bacin ran shi. Daya daina bin mata, ya daina shan wani abu, sauran halayen shi suna nan, ya kula babu inda zuciyar shi da saurin fushi ya tafi, kawai Sadiya ta iya hakuri da shi, tana kokarin tausasa nata harshen idan shi nashi yana tashi.
Da yawan lokutta yasan inda ta biye mishi daya daga mata hannu, daya daketa duk bayan alkawarin da yayiwa kan shi, amman bata biye mishi, tana da hakurin da Hindu bata da shi ta wannan fannin, zai karya idan yace yana jinta a ranshi har kasan zuciyar shi kamar yanda yaji Hindu bayan ya rasata. Amman Sadiya ce abokiyar rayuwar shi yanzun, baya dana sanin aurenta ko na minti daya, a aljanna ma yana so ya fara ganinta a jerin matan da zai samu, shisa yake kokarin rike hannunta su nufi hanyar a duniyar su ta wajen kokarin kyautata zaman su da ibadar su.
“Mun gama…”
Ta furta tana rike da hannun Suhana da sai lokacin ya kula da sun fito, tare suka fita suna nufar mota, har kofar gidan Hindu da yake nan Hayin Rigasa ya karasa yana tsayawa a bakin kofa, Sadiya ta fita da kanta tana bude ma su Suhana bayan motar, itama tsaye tayi sai da taga sun kwankwasa an bude musu gidan, ko da wasa bai juya kan shi da nufin kallon kofar gidan ko zaiga Hindu ba. Ta riga ta zama wani bangare daya bari can wani waje mai nisa, ba kowa bace ita yanzun a wajen shi sai Ummansu Suhana. Sai da Sadiya ta dawo motar ta rufe tukunna yaja su. Gidan AbdulHafiz zasu je da matar shi tayi haihuwa ta biyu, zai sauke Sadiya wajen sunan.
*****
Tunda ta tashi da safe take duba agogo dan aiki ya rincabe mata yau. Ga Bello ba shayi yake sha da safe ba, dole sai ta dafa mishi wani abu, cefane ne ta markada tasa a fridge, wutar unguwar ta lalace. Karamin generator ne da ita, shikuma ba daukar fridge din yakeyi ba. Da kyar ta lallaba shi yaci indomie da kwai yana mata mita ba zai rike mishi ciki ba.
“Kai da abincin nan yana nuna wa a jikin ka da yanzun kofofin gidannan sun maka kadan.”
Dariya ya yi.
“Ni har wani cin abinci nake.”
Kai ta girgiza mishi tana fadin.
“Baka ci kam.”
Ya dai fita, tare suka wuce da Yusuf, yaronta daya da ta haifa tare da Bello. Da yake yana da gidan ruwa bayan aikin da yake, kuma zata ce suna samun rufin asiri ba kadan ba da gidan ruwan na shi. Da Bello irin mazan da suka dogara da albashin sune da sun sha wahala. Amman suna zaune cikin rufin asiri, a shekaru hudu da auren su yanzun har yar mota yana da ita, duk da bata kai ta Hindu tsada ba. Ko da tata ta fara bata matsala sosai yan kudinta data tara ta cika ta dauki wata tana lallaba kayanta.
Tunda Bello ba shida sa ido, bai damu da albashin da take samu ba, da yake ta samu aikin lakcarin a poly tana daukar yan aji daya. Tana jin dadin aikin matuka tunda babu takura sosai. Ba zatace tana da matsala da kishiyarta ba, sai tayi wata shidda bata sakata a ido ba inba da wani dalili ba, gidansu daban, unguwannin da suke ma haka, dan ita tana Kabala, Hindun kuwa tana Rigasa. Yusuf ne ma yakan yi har sati biyu a can gidan, hakan yake kara tabbatar mata da cewar matar Bello wato Amina bata da matsala ko kadan, da tana nuna ma Yusuf din wani abu ko a fuska ba zai dinga nacin zuwa gidan ba sam.
Alkhairi ta roka, sai Allah ya jeho mata Bello a cikin rayuwarta, karya take idan tace bashi da tashi matsalar, amman wannan abune da yake a cikin kowacce rayuwar aure, itama tasan ko rashin hakurinta da saurin daga harshe aka barta bakowanne namiji bane zai iya dauka. Amman da yake akwai kyakkyawar fahimta a tsakanin su da Bello, kuma auren sukayi dan su zauna, auren sukayi dan zallar ibadar da take ciki hankalin su a kwance yake.
Har abincin rana ta samu ta kammala, duk da ba girkinta bane, tasan dai zai dawo ya dubata kamar yanda yakan yi ko da ba girkin wata a cikin su bane ba. Amman saboda ta samu wadataccen lokacin zama da su Suhana ne, tasan Hamza ma ya mata halacci da yake kawo mata su duk karshen watan duniya inba sunyi tafiya ba. Ko Anna takan kirata wani lokacin su gaisa, ana zumunci sama-sama da take da tabbacin saboda yara ne. Tanajin an kwankwasa tasan sune, taje ta bude, ba wani Babban gida bane ba, dan flat ne mai dakuna uku, kitchen sai dan karamin store, ita a gidan haya ma ta fara zama da Bello, kafin a hankali ya gina wannan din da suke ciki yanzun, ko shekara basu hada ba.
Sosai take zaune da yaran a falo suna hira da Suhana, Amna na kwance a jikinta tunda surutu ba damunta yayi ba, dariya takeyi cike da nishadi, a haka Bello ya shigo ya same su.
“Ai tunda nake jin dariyarki nasan ke da su Suhana ne.”
Da gudu Suhana ta karasa inda Bellon ya ke.
“Abban Yusuf.”
Ta kira kamar yanda take ce mishi, gara Amna tana cewa Abban kawai, Hindu tayi tayi da Suhana, amman Abban Yusuf yaki barin bakinta, harta kyaleta tunda taga Bellon bai damu ba. Yarinya kamar tana taya Babanta kishin Bellon.
“Suhana…ya kike?”
Amsa shi tayi da yaren fulatanci, tana dorawa da.
“Ina Yusuf?”
Tana kallon fuskar shi.
“Yana dayan gidan su.”
Bello ya fadi yana karasawa inda Hindu take ya zauna a gefen ta.
“Gaskiya yau akwai rana… Kinji dana tunkarota.”
Dariya tayi.
“Sai da nace ka dauki motata da zaka fita ai.”
Rausayar da kai yayi.
“Na dauka zai gyaramun tawa kafin inje ne wallahi, da naga inata kiran shi bai daga ba.”
Kai kawai ta girgiza, gaddamar shi bata sallah, ko da ba’a gyara din ba in bai niyyar dauka ba tasan ba zai dauka ba, shisa ba akan komai bakinta yake surutu ba, mikewa ya yi.
“Zan duba kine daman, bari in wuce nikam… Kije ki dauko Yusuf daga islamiyya anjima zan kawo shi, kinsan ba zai zauna ba in yaji su Suhana sunzo.”
Kai ta jinjina mishi tana zame Amra daga jikinta ta mike, har bakin kofa ta raka shi.
“Gidan har ya fara mun shiru.”
Ta fadi, murmushi yayi.
“Kaji neman magana ko? Ke da ga yaranki kina magana kamar zakiyi kewata.”
Dariya tayi kawai, tana mishi sallama ya fice ta mayar da gidan ta rufe. Kalma daya take da ita idan aka tambayeta me ta samu a gidan Bello banda Yusuf, idan mutane suna tunanin tayi kuskuren kin komawa auren Hamza saboda a komai yafi Bello, shine,
“Kwanciyar hankali.”
Abinda bata sani ba a zaman aure sai da ta auri Bello, hankalinta a kwance yake, suna cikin rufin asiri, ci da sha, suttura ta mutunci batafi karfin su ba, wauta tayi da take tunanin samun MIJIN NOVEL, soyayyar mazajen ciki da wadda take tafiya a rayuwar yau da kullum suna da banbanci mai nisan gaske. Tana ganin soyayyarta a tare da kalar kulawar da Bello yake bata, a lokuttan da zata bude baki tace wani abu na mata ciwo, ko da farcen yatsanta ne, saboda hankalin shi baya kwanciya sai yaji ta samu sauki, soyayyar shi na cikin yanda yake zuwa gidansu duk juma’ar duniya ya gaishe da iyayenta har yai musu alkhairi duk da bashi da wadatar tsohon mijinta da mutane suke tunani.
Tana ganin yanda yake sonta a aikace batare daya furta ba, tana kuma ganin banbanci kulawar da taso samu da wadda ta samu yanzun. Ko kadan bata tsoron sauran shafukan da kaddara zata bude mata, me kyau ko akasin hakan, tare da Bello rike da hannunta tana da yakinin wuce komai, mijinta zai tayata raba ranakunta marassa dadi, kamar yanda yake raba na farin cikinta da ita. Bata da bakin furta komai sai
“Alhamdulillah.”
Kalmar karshe da ta furta, kalmar kuma da zan amfani da ita wajen rufe wannan tafiyar da Allah ya kawo karshenta.
*****
Na gode da karamcinku, Na gode da kaunarku, Na gode da uzurrrukan da kukayi mun a cikin tafiyar nan.
Ina muku fatan alkhairi a duk inda rayuwa zata kai ku gabaki daya.
Naso su koma aurensu da Hamza tunda yayi tuban gaskia. Hindu kingane mijin novel duk mafarki neko? Mungode Allah ya biya
Na dade ban karanta super realistic fiction irin wannan ba wlhy kin iya rubutu mai dauke hankalin mutum, felt like i was in the book myself, darussa da dama Alhamdulillah a littafin, Mungode da wannan koyin. I learnt how dogon buri can be dangerous, learnt hakuri sosai na da kyau, Zina da shaye shaye ya na da illa sosai. Allah ya sa mu fi karfin zuqatan mu ya shirye mu shirin addinin musulunci. Ameen ameen