Skip to content
Part 6 of 33 in the Series Mijin Novel by Lubna Sufyan

Zufa take da bata da alaka da zafin gari tana girgiza ma wayarta kai, dan bata ga dalilin da zatayi mata abinda tayi mata ba, ya kamata ta tabbatar da abinda take tunanin idanuwanta sun gani. Ga Asma bata da waya balle ta dauki tata, da dare baiyi ba tabbas bangaren Mama zataje ta karbo wayar Khadee.

“Dan Allah…. Dan girman Allah ku kawo wuta. Ku taimaki rayuwata.”

Take fadi kamar wadda ta sami tabin hankali, har a kasusuwan jikinta take son tabbatar da fuskar da tagani a jikin Hamza take, fuskar da ta sami waje tana zaunawa a zuciyarta. Lumshe idanuwanta tayi tana ganin nashi da ruwan kasane mai cizawa sosai, duk da kalace da ake samu a tattare da yan Nigeria, yankan idanuwan nashi abin daukar hankaline, shisa take so su taimaketa su kawo wuta, taga idanuwanta ne ko da gaske labban Hamza ne wani irin ruwan hoda da ba kasafai ake ganin su ba, ko a fina-finan kasashen ketare. Gashin kan shine bata kula ba, saboda askin shi buzz cut ne kamar, akwai hular rigar da take jikin shi.

Tsaki taja tana juya kwanciya, ba karamar cutarta yan Nepa sukai ba, duk kalar zagin da yazo ranta shi take auna musu, caji ta jona tana kunna socket din, da sun kawo ba saita tashi ba, ta lumshe idanuwanta, fuskar Hamza na dawo mata kamar yana tare da ita, kafin barawon bacci ya dauketa. Duk da haka a daren bata san adadin farkawar da tayi ba, tana ganin basu kawo wuta ba har lokacin, sai ta sake komawa bacci, a haka har aka kira sallar asuba, Asma ta tasheta, saboda ba wani wadataccen bacci ta samu ba, ta dai godewa Allah bata da lakca sai sha daya, dakyar ta idar da sallah, zata fara Azkar suka kawo wuta, dan casbin hannunta tayi cilli dashi gefe tana nufar wayarta kamar zata kifa

“Ikon Allah….”

Asma ta furta, ko inda take Hindu bata kalla ba, wayarta take kokarin kunnawa, amman taki kamawa, dan tsayawa tayi tana kallon wayar har tayi 1% tukunna ta kunna tana cire mukullin sirrin da yake rufe da wayar. Data dinta a kunne take amman wayar bata gama loading ba, ji take kamar tayi me dan zumudi. Tana samu wayar ta fara loading ta shiga Instagram tana komawa shafin Hamza, sai da ta fara danna ‘Follow’ tukunna ta bude profile din shi, yanda na Facebook yake haka wannan din yake shima. Hoton farko da taci karo dashi da dare ta fara budewa, tana jin bugun zuciyarta a cikin kunnuwanta. Tafukan hannunta har wata zufa suke.

Duk da ma’abota lafazi kance zuciya ita take ganin kyawu ba idanuwa ba, zata rantse tunda take kalle-kallen fina-finai bata taba ganin wanda yai mata kyawun Hamza ba, kamar komai nashi shiya zaba, daga hancin shi, idanuwan shi, girar shi da take a cike, da kasumbar da take kwance a fuskar shi data kara mishi wani kyau naban mamaki.

“Oh Allah na”

Hindu ta fadi zuciyarta cike da shauki, dakyar ta iya danna Back tana fita daga cikin wannan hoton. Wani hoton takai tana ganin su shida abokan shi, rigar shi wannan karin babu hula, amman mai dogon hannu ce, gabaki daya abokan shi sun hadu iya haduwa, babu wanda ba zata iya aure ba indai suna da kudi, kyawun su yayi mata, amman a hoton zaka gane yanda kyawun Hamza ya bambanta dana sauran. Yayi tagging din abokan a kasan hoton, bubbude tags din tayi tana following su duka hudun. Fodio, Arafat, AbdulHafiz, sai kuma Abdallah.

Sannan ta dawo kan hotunan Hamza tana cigaba da dubawa, idanuwanta na tsayawa kan wani hoto shida wata mata mai matukar kyawu. Ya rubuta ‘Ann❤’. Duk da sunyi kama dashi sai taga kamar tayi yarinta data haifi Hamzan, watakila babbar Yayar shi ce. Fita tayi tana shiga wani da ya saka ‘Barka da Sallah’ jikin shi sanye da farar shadda kal, har hular kanshi fara ce, kasa hakuri tayi ta zare wayar daga cajin tana share ‘low battery’ din data rubuta, da zumbuleliyar hijabin sallarta ta fice daga dakin zuwa bangaren Mama, tana shigewa dakin su Khadija ta sameta zaune da Qur’ani a hannunta.

“Khadee kinga Hamza kuwa? Tafdin… Kinga Hamza”

Ta karashe maganar tana mikama Khadee wayar, data karba tana rikewa sai da takai karshen ayar da take karantawa, tukunna ta dago ido tana kallon Hindu da take numfarfashi kamar taga wani waliyyi, magana zatai ma Hindun ta dago wayar tana kallon hoton da yake kai.

“Allahu Akbar….Allah mai halitta.”

Ta fadi cike da jinjina Girma na Ubangiji da yake wanzar da halitta kala-kala a tsakanin yan adam, wasu kagansu munana, wasu tsaka-tsakiya, wasu masu kyau, wasu kuwa kyawunsu kamar ba mutane ba, kamar sun fito daga jinsin aljanu, Hamza na cikin kalar wannan mutanen

“Hmm… Kibari kawai, wallahi na kasa yarda cewar shi dinne.”

Cewar Hindu, Khadee na dorawa da.

“Sai kace aljani, Ikon Allah kenan….”

Wayar Hindu ta karba

“Bari kiga sauran abokan shi ma.”

Tana komawa baya ta kai kan hoton Hamza da abokan nashi tana nunawa Khadee

“Jiba rashin adalci, shi yana da kyau duk saiya kwashe masu kyau yake abokai dasu, jiba wannan bakin… Inalillahi… Duk yafi su kyau harda Hamzan.”

Leqa kai Hindu tayi

“AbdulHafiz ne”

Nata kan Khadee ta daga tana kallon Hindu cike da mamakin yanda akayi ta san shi

“Duk na duba sunayen sune, kuma wallahi baifi Hamza kyau ba, tafdin, dan dai yana da dogon hanci shima.”

Sake dubawa Khadee tayi

“Kai mun handle din shi ingani, kin san Allah yafi Hamza kyau, hasken fata kawai zai nuna mishi.”

Da sauri Hindu ta nemo sunan AbdulHafiz din suna shiga hotunan shi, na farkon da yayi murmushi har dimple din dake gefen fuskar shi ya loba ciki kamar ka saka dan yatsa.

“Haba Hajiyata… Kiga gaye iya gaye… Haske fa Hamza zai nuna mishi.”

Wayarta Hindu ta fisge

“Ban wayata ni, ke baki san kyau ba sam, ni karki batamun rai dan Allah.”

Ta karasa maganar tana mikewa ta fice daga dakin, murmushi Khadee tayi kawai. Hindu taki yarda ne, amman AbdulHafiz duk yafi sauran kyau, amman dai-dai wani karkataccen wani, hankalinta ta mayar kan Qur’anin da take karantawa, dan shi yafiye mata alkhairi da maganar kyawun mutanen da basu san da zaman su ba, Khalifanta bashi da kyau kamarsu tasani, ba zatayi karya ba, amman shi dinne zabinta, kuma shidin take fatan ya zama alkhairinta.

Hindu kuwa daki ta koma ta mayar da cajinta dan wayar ta samu sosai. Tasan halin yan Nepa, sam basu da wata daraja. Zasu iya dauke wutar duk da basu kwana da ita ba. Bandaki ta shiga ta watsa ruwa dan karta fara bacci ta farka a makare. Tana shafa mai ta kwanta. Tun tanajin motsin Asma da ita karfe bakwai da wani abu na safe za’a kaisu makaranta harta daina ji, bacci ya saceta, wani irin bacci cike da hargitsatsen mafarkin Hamza, da bayan ta tashi duk yanda taso ta tuna me ya faru a mafarkin ta kasa.

Kiran Hauwa tagani har biyu, sai kuma text din data bude.

‘Ke kinji Arc Aboje ba zaizo ba, ya bada handout dai, ki karbar mun in kin shiga school dan Allah. Idan baki shiga ba kuma shikenan’

Numfashi ta sauke, taji dadin rashin zuwan da Malamin nasu ba zaiyi ba. Amman dai ko wajen sha biyu zata shiga ta karbar musu Handout din, gara ta kwana a hannunta sai tafi samin natsuwa. Ita bama sosai take printing ko photocopy ba, tunda Huzaifa na da shagon da akeyi irin abubuwan nan, sai dai ta aro na wani a aji, sai ta bashi yayo mata, yanzun ma duk da yana kwana gida ba sosai take ganin shi ba, tunda aka saka mishi ranar biki yake wahalar gani, dan lokacin da baya wajen aiki tasan yana can zance. Duk wasu sun kwace musu Yayye suna gani, haka Muhsin ma da haduwa da yarinyar da maganar auren duka kasa da wata hudu, abin ya jima yana bata mamaki.

Ko dan itama in dai wanda take burine ta samu bataga jiran da zata tsaya yi ba. Da wannan tunanin ta koma Instagram tana shiga shafin Hamza. Ya saka sabon hoto yana wajen cin abinci, daga kasan hoton cikin harshen turanci ya rubuta.

‘I can’t wait to be home’

Haka kawai sai taji zuciyarta ta kumbura ta cika fam, ba zai zauna acan kamar yanda duk wanda ya ketare daga Nigeria sukeyi ba, da alama Hamza na sha’awar dawowa gida Najeriya, hakan kuma yayi mata dadi da bata da dalilin shi. Hoton tayi liking ta shiga comment din tana ganin matan da suke ta cewa yayi kyau, kuma yayin, jar riga ce a jikin shi mai dogon hannu, da hula kamar ta sanyi itama ja, yadan turata baya, gashin kan shi ya fito, kunnuwan shi a rufe ruf da hular, sai dai kana ganin farin zaren earpiece din da alamu suka nuna yana manne cikin kunnuwan shi.

“Shegu mayu”

Ta tsinci kanta da furtawa, a gefe daya tana jin dadin yanda Hamzan ko like bai danna akan comments din nasu ba ballantana ya kula su. Tana fitowa daga comments din tayi refreshing taga ya saka sabon hoto na wani gini, da alama shi yayi, bayan tayi liking sai tayi comment da hotunan zuciya har guda uku, dan duk yanda taso ta fadi wani abu daban ta kasa, ta rasa abinda ya kamata ta fadi da sauran mayun matan da suke ta mishi magana basu riga da sun fada ba. Ganin haka kawai comments din nasu yana neman bata mata rai yasa ta tashi tana some shirin fita makaranta.

Tana gama shiryawa tsaf, ta dora baya akan kayanta tana yafa mayafin abayar saman kanta, yar jaka ta dauka ta saka wayarta a ciki, tana da kudi, tunda Baba na sati daya yake bata ta rike a hannunta, wani lokacin kuma yana kara mata kafin satin ya kare. Sai da ta shiga dakin Anty dan tayi mata sallama ta samu tana bacci, fitowa tayi taja mata kofar a hankali ta wuce makaranta. Handout din daya kaita kawai ta karba, da yake batai breakfast ba, yunwa takeji har wani jiri-jiri takeyi, karasawa tayi restaurant din su Elizabeth da yake nan cikin makaranta, taci doya da kwai da plantain. Sannan taji tadan samu nutsuwa.

Ganin azahar har tayi yasa ta biya masallaci tayi sallah, tukunna ta fita daga makarantar zuwa gida. Tana shiga da sallama ta sami Anty zaune a falo

“Sannu da gida.”

Ta fadi, Antyn na amsawa da

“Yawwa… Yau da wuri?”

Kai Hindu ta jinjina mata

“Ai bamuyi komai bama, Handout kawai na karbo”

Ta karasa maganar tana wucewa dakin su dan tasan da wahala Antyn ta sake cewa komai. Kayan jikinta ta rage, ta zauna kan gado tana zaro wayarta daga jaka, kiran Huzaifa tagani dayasa ta tunanin ko lafiya, dan haka ta danna tana bin kiran, yana dagawa da sallama.

“Yaa naga kiranka ne, ina dawowa daga makaranta wayar na cikin jaka.”

Dan jim yayi kafin ya amsa da

“Nabar miki sako a whataapp, ki duba.”

Ya kashe wayar, da mamaki a fuskarta ta kunna data. Sakkonin ta bari suka gama shigowa tukunna ta bude na Huzaifa din tana soma karantawa:

‘Akwai abokina Kamal, shagon shi kusa da nawa yake, ya taba zuwa gida, amman ba lallai ki gane shi ba. Tunda yaganki ya matsamun sosai, nayi miki magana ne yanzun saboda na yarda da hankali da nutsuwar shi. Duk da nasan shi wajen shekara hudu, sai da na kara bincike a kan shi kafin na yarda in hada ku. Bance sai kinso shi ba, amman ki bashi dama dan Allah. Zai zo anjima da yamma.’

Sake karanta sakon tayi tana dakuna fuska, duk da yaune karo na farko da wata magana data danganci Samari ta taba hadata da Huzaifan, watakila shisa taji zancen yazo mata daga sama. A wani bangaren kuma tana jin Kamal din bai mata ba tun kafin tagan shi, saboda tana da yakinin ko kafar Hamza bai kamo ba, ita kuma yanzun a zuciyarta Hamza yayi mata setting din wani standard da ba zata dinga auna duk wani namiji da zai kalleta da sunan soyayya.

‘Allah ya kaimu’

Ta amsa Huzaifan da taga yazo online

‘Nagode Kanwata. Allah ya tabbatar mana da alkhairi.’

Sauka tayi kawai, ba zatace Amin a abinda bata gani ba, babu wani alkhairi ita idan ba ganin shi tayi ba. Tashi tayi ta fito tana fadama Anty zatayi bako da yamma

“Daga ina? Waye shi?”

Anty ta tambaya tana tsare Hindun da idanuwa

“Bansan shi ba nima, abokin Yaa Huzaifa ne, yanzun yake fadamun.”

Kai Anty ta jinjina, fuskarta na saki da alamun yarda, tasan sukan taba kishin su a tsakaninta da Mama, amman babu ayar tambaya a kaunar da ke tsakanin yaran, Huzaifa ba zai taba aminta da yazo wajen Hindatun ba sai idan ya yarda da tarbiyar shi. Yanzun Hindun ce matsalarta, dan haka fafur duk yanda Anty taso ta da Musa kai tsaye tace bata son shi guntu ne. Tana kula da yanayin ‘yartata, zuwa yanzun kuma addu’a take mata babu dare babu rana, Allah yai mata zabin alkhairi ya tsayar da hankalinta akan mutum daya, tagaji da dauka da saukewar da Hindu takeyiwa Samari, zata so tayiwa Baba maganar amman zai goyi bayan Hindu ne, tunda bata laifi a idanuwan shi.

“Ki bashi dama Hindu, karki duba wani kyawu na halitta, ina fada miki bashi yake rike aure ba”

Kai kawai Hindu ta jinjina ma Anty tana wucewa ta koma daki,bawai dan maganar ta shigeta ba, kyawu kam shine ginshiqin komai a wajenta, ita kanta Antyn Baba ta zabo, kuma bashida muni. Babu dalilin da zaisa ta saurari mummuna, shisa ma take addu’a babu gajiyawa. Kyakkyawa, fari, dogo, mai kudi na fitar hankali. Ba zata zo tana kwana a duhu ba, ko ta fito tana kikiniyar shiga kitchen, gara tasan aure tayi, taga banbanci daban dana gidansu, tana daki a dafo a kawo mata. Ba zataki ta auri mijin daya iya girki bama, tana bacci ya tasheta ya hada musu breakfast yanda akeyi a littafin Hausa. Ai soyayya dabance, in batajin shi har bayan zuciyarta babu abinda zaisa ta aure shi.

***** *****

Karfe biyar taga kira da bakuwar lamba, dagawa tayi tana karawa a kunnenta

“Assalamu alaikum…”

Muryar shi ta daki kunnenta da wani irin sanyi da yasata gyara zama tana amsa mishi sallamar

“Kamal ne, ya kike?”

Sosai muryar shi tayi mata dadi, da dan murmushi a fuskarta tace

“Alhamdulillah. Ina wuni”

Amsawa yayi yana dorawa da

“Afuwan, kinganni sai yanzun. Ina cikin gidan ku.”

Mikewa tayi

“Gani nan fitowa”

Ta fadi tana neman Hijab din data fito da ita, ta Asma ce ma, ita ba ma’abociyar saka hijabi bace, lokaci zuwa lokaci takan saka, bata dasu da yawa ma, tafi saka abaya, yanzun da zamani yazo saita dora Kimono wasu lokuttan. Bata dai san dalilin da yasa ta zabi hijabin ba yau. Ruwan toka ce da ta haskata ba kadan ba, fita tayi zuwa falo tana zira takalmanta da suke kofar daki, tana fita ta kitchen din gidan ta zagaya, dan akwai hanya ba saita bi ta falon Mama ba, daga nesa ta fara hango shi kan machine roba-roba a zaune.

“Tafdin…Machine…”

Hindu ta fadi tana tabe baki, lallai zata sallame shi ya koma inda ya fito, karasawa tayi tana mishi sallama hadi da kare mishi kallo cikin raini, bataga dalilin da zaisa shi zuwa mata da jallabiya da hula tashi da kwakwa kamar sabon ladani ba, ga wani gemu da zata iya kirgawa tsai-tsaye kamar dole akace saiya ajiye gashin da yaki bashi hadin kai. Murmushi yayi hakoran shi na bayyana, guda daya ya karye, bashida muni, amman sam baiyi mata ba. Duk da jallabiya ce a jikin shi tana iya gane siririne ba kadan ba. Duk yanda tayi kokarin ganin tayi mishi fara’a ko dan Huzaifa saita kasa.

Dan gaisawa sukayi, Kamal duk yanajin wani iri, shi yana zaune akan Machine ita tana tsaye, hakan yasa ya sauko daga kan Machine din shima ya tsaya, duk da yaga kujeru irin na robar nan a cikin gidan, amman Hindu batayi mishi tayin zama ba, yana ganin kamar baiyi mata ba daga yanayin fuskarta, ko kuma dan zuwan farko ne shisa, shi yake ta kokarin janta da yar hira, amman sai amsa shi take da

“Umm…”

Ko

“Ai kam”

Duk jinshi yake a takure, Hindu kuwa daya sauke daga Machine din taga hannuwan shi kamar bulala, dogone babu laifi, amman bazai kai Hamza tsayi ba, sai dai sam batason ganin namiji siriri haka, ita da take son dirarren namiji da zai dauketa bai sauke numfashi ba, faffadan kirji da zata kwanta luf kamar jaririya a kirjin mahaifiyarta. Ina zata kai irin Kamal, bai cire rigar shi ba, amman tasan babu komai a kirjin shi banda kasusuwan da intayi bacci akai zata tashi da tambarin da kasusuwan shi zasu bar mata a kunci kamar bagobura.

Ganin da Kamal yayi ya rasa gane kan Hindu, ga yamma na karayi yasa yai mata sallama da fadin

“Zamu yi waya”

Shima kai ta jinjina mishi, tana kallo yaja jak din Machine din shi da bata tsaya ya tayar ba ta juya tana nufar cikin gida, badan Huzaifa yace mata yana da shago kusa da nashi ba, in a hanya tagan shi zatace Malamin Islamiyya ne, ko kuma irin matasan nan masu jan baqi a wajen tafisir. Yanzun ma tanaji a jikinta robobi yake siyarwa a shagon…!

<< Mijin Novel 5Mijin Novel 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×