Shekara daya bayan gama diploma dinta, ta sake samun gurbin karatu na HND anan Polytechnic din ta Kaduna, duk da Baba yaso ta gwada Direct Entry anan KASU, amman sam makarantar ta gama fita daga ranta, haka kawai take son cigaba dayin Poly din saboda tana sakata jin wani kusanci na daban da Hamza. Ita kanta zuwa yanzun tasan inda a kasar wajene idan Hamza zai kai kararta tsaf za’a kamata da laifin bibiya, wato stalking a turance, a shekara daya da wani abu duk wani hoto da Hamza zai saka akan idanuwanta, tana liking ta kuma yi mishi comment a shafin shi na Instagram, dan ta tabbatar Hamza ko dan wasan film ne ko kwallon kafa, yanda take bibiyar shi yaci ace ya kula da ita, ko da sau dayane ya tanka.
Amman ko inda take Hamza bai taba kallo ba, har haushin kanta take ji wasu lokuttan idan ta gama yi mishi dogon sharhi musamman akan gine-ginen da yakan dora. Ranar da taga ya dawo Najeriya ji tayi kamar an mata albishir da kujerar Hajji, kamar Hamzan zai kulata saboda suna jaha daya, kuma taga dan Kaduna ne daga yanayin wajajen cin abincin da suke hotuna a ciki shida abokan shi. Amman ko like bai taba dannawa akan comments dinta ba. Ta kuma kasa daina yi saboda yanda yake bala’in burgeta.
Zuwa yanzun Samari takeyi kala-kala, ta kasa tsayar da hankalinta akan guda daya, dukkan su saita sami abinda ta kushe a jikin su, duk nasiha da Anty take zaunar da ita tana mata, ta kunnen dama take shiga ta fita ta haggu, daman ita kadai ta rage a gidan da take mata magana akan maganar tsayar da Saurayi daya, Baba kam da Anty ta gwada yi mishi zancen, ca yayi
‘Ki kyale yarinyar nan dan Allah, duka Hindatun nawa take da kikabi kika dami kanki akan ta? Ba karatu takeyi bane wai? Ko kin manta shi auren nan lokaci yake dashi?’
Daga ranar kuwa Anty bata kara daga mishi zancen ba, amman yana damunta matuka, tana kuma addu’a akai. Ita kanta Hindu abin na damunta, yanda har yanzun ta kasa tsayar da hankalinta akan saurayi daya, ta kasa samun wanda zai kwanta mata. Ba sosai take hawa manhajar WhatsApp ba, balle kuma facebook da take dauka sai gidadawa suke yinshi yanzun. Dimples ta koya mata zaman Twitter ba kadan ba. Da yake ita Dimples can tafi ganewa, ko kace ka mata magana a whatsapp bata amsa ba zata ce maka
‘Baka dubani a Twitter bane ba.’
Itama Hindun tunda tagane kan Twitter tasan cewa nan din wata duniya ce ta daban, ta hada duk wasu manyan gayu da kake tunani, babu kuma karya kamar yanda akanyi a Instagram. Akwai manyan yaran da suke burgeta sosai a Twitter, yaran attajirai ne daga yanayin shigarsu da motocin da zaka gansu a ciki, duk da kyawun su bai kai mata inda take so ba. Takan shiga wasu lokuttan a dama da ita, kusan tafi Dimples shige-shige a Twitter, ita Dimples idan ma bata sanka a gaske ba, ba zata taba sakar maka fuska har kuyi wata hira ba, ko kabita ma, ba zata amsa gayyatarka ba.
Kalar hotunan da Hindu take sakawa a Twitter yasa take da tarin Mabiya, duk da shigace ta mutunci a jikinta, duk da abaya, sosai ake mata kallan Babbar yarinya. Watan nan daya kama aure akeyi kaca-kaca a twitter, sai kaga matan sunce daga mazan sun tura musu DM wato sako ta inda su kadai zasu iya gani, su kuma suka amsa shikenan soyayya ta ƙullu tsakanin su, yanzun gashi har dunyi aure. Kuma sai taga mazan sun haɗu, ga kuɗi suna dashi, inta duba shafin su sai ta samu basu da wasu mabiyan kirki kuma basa saka hoto ko ɗaya. Abin na matuƙar burge Hindu, ita duk wanda suke mata DM tarkace ne.
Haka kawai saita fara ji a jikinta kamar itama mijinta zai fito daga Twitter ne,tunda taɗan rage burin nata, tanajin kamar ko gajerene indai yana da kuɗi sosai wataƙila ta haƙura taga abinda Allah zaiyi. Lokaci ɗaya ta fara ganin Musbey da suke following ɗin juna yana kwaso mata shafin wani Jalil idan yayi retweet ɗin posting ɗin Jalil ɗin da yake siyar da kayan sawa na maza wato kaftan. Daga yanayin kayan zaka fahimci irin kuɗin da yake dasu, duba shi tayi taga mabiyan shi kaɗan, ko data duba hotunan shi duk tallar kayane da suka ji sirfanin hannu da alamu suka nuna zaiyi tsada matuƙa. Saita tsinci kanta da following ɗin shi kafin ta sauka daga kan Twitter ɗin.
***** *****
“Usztaz kasan dai ya kamata kayi aure ko?”
Abokin sa Adam yace mishi.
“Wai meyasa kuke ce mishi Usztaz ne? Bafa ustazu bane, rashin kaya ne kawai ke ɗawainiya dashi.”
Aliyu yai maganar yana takaicin Ustaz din da ake kiran Jalil dashi, saboda ko kusa bai hada hanya da Ustazai ba. Jalil wanda aka fi sani da Ustaz baice komai ba, maganar mutane bata damunsa. Ba yau bane rana ta farko da mutane da abokan sa suke mishi maganar aure. Amma ta ina zai iya aure tunda ba shida sana’ar kirki. A shekaru arba’in da biyu sana’ar aikin hannu yakeyi. Yana saƙa design a riguna. Shima shagon ba nashi bane. Na wani wan mahaifinsa ne wanda ya gaji da ganin sa yana zaman banza.
“Haka kurum kuyita ce mishi Ustazu kamar abin arziki, daga namiji yana saka manyan kaya shikenan ya zama na kirki?”
Aliyu ya cigaba da sababi. Da Adam da Aliyu yan biyu ne yan shekaru ashirin da bakwai. Sabbin zuwa ne a shagon kuma jininsu ya haɗu dana Jalil, saidai idan ka fita kace mishi Jalil babu wanda zai sani. Anfi saninsa da Ustaz wanda ba’a san inda ya ɗauko laƙabin ba. Shi Jalil yana san gayu amman bashida hanyar da zaiyi, haka ya haƙura abinshi. Tunda yake jikinsa bai taɓa marhaba da English wears ba, toh saidai na haihuwa. Tun tashin shi ya saba saka kwabɗa kwabɗan yadi ko mai kwabo kwabo. Duka kayansa sunyi mishi girma. Gashi bala’in siriri baida faɗin kirji. Yana yanayi da ɗan shekara talatin da biyu yasa yake yarintar sa babu kama hannun yaro. Dan Jalil irin mutanen nan ne da sun girma basu san sun girma ba. Gashi idan yana tafiya saboda girman kayan shi da rashin kiba sai yayi maka kamada tuta.
Cima zaune ne na bugun jarida. Yan kuɗaɗen sa dayake samu baya komai dasu sai siyan data domin yaga kyawawan mata sannan kuma idan an dace ya samu wanda zata aure shi a yadda yake. Yanada NCE wanda yayi a FCE Zaria inda ya karanta English and Literature. Wannan ɗan turancin ne yake ma yan mata bagu dashi. A manhajan Twitter yaji labarin cewa akwai wasu manyan yaran attajirai, tun lokacin ma ta Web yake shiga, bashi da wayar da take sauke application, sai dai yana cikin mutanen da ake ma laqabi da Low-key a Twitter. Baya shiga duk wani rikici ko drama da za’ayi, kawai dai idan abu yayi mishi, sai yayi liking ko retweet, mabiyan shima basu da yawa, amman akwai wanda ake ganin girman su a Twitter da suke bin shi, sosai Jalil ya iya kama girman shi a Twitter ba kamar a fili ba.
Kasancewar Ustaz Jalil a Twitter yasa shi kara wayewa ta fannin da baka tunani, duk da rashin gayun na nan, kafin Twitter yaji yanda ake fadin fararen kaya girma ne, daga lokacin ko dan yadi zai siya sai ya siyi fari, naya saka wani kaya face fari, kuma idan aka ce farin kaya bawai ana nufin farin da mutane suka sani ba. Duk sun koɗe sunyi dariya ta wajen wuyan. Gashi yanada wani farin half cover wanda ya koma kalar madara. Ya saba idan manyan mutane sun kawo ɗinki saiya ɗauki hoton kayan ya wallafa, sannan yace shagon sa ne yanzu yaran ciki sukayi mishi aikin.
***** *****
Zata ce kusan sati biyu da tayi following ɗin Jalil amman baiyi follow back ba, hakan ya sakata tunani barkatai, sai taita ganin kamar ita ce take bin arziƙi shikuma yana ƙinta. Hindu bata taɓa mashi magana ba, tunda dai duk matan da takeji dun sami mijin aure a Twitter duk mazan ne suke fara musu magana, amma tana kallon duk wani rubutun da zaiyi, ya kuma iya turanci ba kaɗan ba. Yanayin sa yana burgeta. Babu ruwan shi. Saidai ya watsa hotunan da yaran shagon sa suka yi kamar yanda yake cewa ya tafi.
Akwai wani kwarjini dayake mata na rashin dalili, bawai ta taɓa ganinsa bane tunda yana cikin mutanen da ko kadan basa saka hoton su,amma kuma yana bala’in birgeta. Wata Isha datayi aure kwanaki tace mijinta a twitter suka haɗu kuma baida followers sosai. Watau attajiran ba’a sansu ba. Gashi kuma mijin Isha ya haɗu cikakken namiji, Allah bai rage shi da komai ba ta fannin halitta. Hindu ta kasa gane dalilin daya sa take ganin cewa Jalil yana cikin wannan sashen. Kuma idan wannan manyan kayan dayake wallafawa daga shagon sa ne. Toh ai kakanta ya yanke saƙa. Dan kullum da kalar wanda zai saka.
Yau haka kawai ta tsinci kanta da yin liking ɗin hoton kayan da ya saka. Ko wayar bats ajiye ba taga yayi following ɗinta, wani irin murmushi taji ya ƙwace mata.
Shi kuma Jalil ana shi ɓangaren dan ƙarfin hali su Adam suna mashi magana ko jinsu baya yi dan sam sai yau ya kula da Hindu tayi following ɗin shi,satin ba’a sami wani aikin kirki ba, yanata lallaɓa data din shi karta ƙare da wuri,shisa baiyi wasu shige-dhigen rashin dalili ba sai yanzun da yaga tayi liking hotunan daya saka, nan take yai follow back yana shiga profile ɗinta. Bin hotunan Hindu yayi yana kallo, ta bala’in birge shi. Bawai aurenta yakeso yayi ba, kawai dai ko gaisuwa su rinƙa yi ana mutunci. Tunda shi kanshi yasan bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane.
Sallama yayi mata, abin kuma yayi mugun bata mamaki. Kamar yasan yanzu tayi tunanin ko ita tayi mishi sallamar, Har ga Allah nan take Hindu ta fara hasaso yanda bikinta da Jalil zai kasan ce, tasan shine zai zamo uban yaranta. Batayi jan aji ba ta amsa.
“Wohoho… Maraba garsarshe!”
Jalil yace da ƙarfin tsiya. Yana saka Aliyu ɗagowa cikin ƙunar rai.
“Ya dai Ustaz meye haka muna aiki kana mana ihu, kamar wani ƙaramin yaro.”
Dama cikin tagwayen yafi zafin kai. Kuma bayason yanda Ustaz bashida kamun kai.
Kallonsa Ustaz yayi yana dariya, saiya kara masa wayan a fuska.
“Kalli abinda ya faru, nayi kamu jama’a.”
Yace sannan ya miƙe ya soma taka rawa. Irin rawar nan da Ibro keyi da kafa ɗaya bayan yaci ɗammara. Haka yayita ji yana zufa, Aliyu haushi ya gama ƙume shi.
“Ai ba nan gizo ke saƙar ba, yanzu me wannan yarinyar zatayi dakai? Jibe ka fa. Rigar ka kwara ɗaya, gashi duk ta koɗe bata kama omo.”
Aliyu yai maganar, Adam da sauran yan shagon na bushewa da dariya.
Bai kula suba, ya koma gefe ya soma chatting da Hindu gadan gadan. Sai ya zamana a duka satin babu abinda Jalil yake banda hira da Hindu da ta saki jiki ta biye mishi, duk yanda Dimples tayi mata kashedi tabi a hankali, sai ta bagarar da zancen Dimples din na cewar a low-key Twitter tabbas akwai attajiran masu kudi, akwai kuma attajiran amman tantiran yan duniya masu bin mata, kuma zai iya yiwuwa akwai yan yankar kai ma, tunda yanar gizo yanzun ta zama abinda ta zama. Sai Hindu ta alakanta maganar Dimples da rashin son mutanen ta, in da mutane zasu biye mata sam zata wuce su wuce kamar ba daga jinsi daya suka fito ba.
Ko kadan bata da yarda, zaku shekara tare da ita kafin ta sakar maka fuska, kullum girarta a sama take, bata shiga harkar kowa, ba kuma zataki kowa karya shiga harkarta ba, shisa sai ta daina mata zancen Jalil din, duk da tana so ta tambayi Dimples ko zata iya cema Jalil ya turo mata da hoton shi kar a karayin ta Elias, amman kuma nan ba 2go bane ba, Twitter ne, bata taba ganin wata ta fito tace ta hadu da gurgu ba, kuma tana ganin suna ma juna bangajiyar ziyara da kuma godiya a tsakanin su. Ga ajin Jalil din ya burgeta, har lokacin ko lambar wayarta bai karba ba.
Wata safiyar asabar da ta kasance bata da aikin makaranta sosai, ta kuma tambayi Anty Dimples zata zo suje gidan Maman Amrah Yayar Dimples din batajin dadi zata dubo ta, sanin kusancin da ke tsakanin Hindu da Dimples shisa Anty ta amince da kashedin kar Hindun ta kai dare. Ranar kuma tayi dai-dai da lokacin da Jalil ya bukaci yana son ganinta su gaisa. Nan ta shaida mishi cewa bata gida yau zasu fita ita da Kawarta. Ya tambayi unguwar tace mishi wajen Lagos Street ne, kafin wani lokaci Jalil ya amsata da cewa shima zaiyi ta area din sai su hadu ‘Briefly’ su gaisa, yanda yai amfani da kalmar a gayance ya kara burge Hindu.
Sosai taji daɗin wannan maganar, a cikin rana ɗaya tayi babban kamu. Watau Jalil shiru shirun twitter zai ziyarce ta. Kwalliya ta fesa sosai, data karbi jikin ta, tasan cewa harga Allah tayi azkar da kyau. Kuma dama Allah yana tare da mai hakuri. Wulakanci da Hamza yake ta mata ne, da kuma kalar tarkacen Samarin da tayi yau Allah zai wanke mata duk wani bakin ciki da ta kwasa. Tunani kala kala ya rinƙa rikito mata. Ita bata san gajeren namiji kamar an kifa kwando. Fata takeyi kada Jalil ya zamto gajere. Sai kuma ta tuna cewa yanzu kai ya soma wayewa, tsawonka shine aljihun ka. Idan dai yanada kuɗin sa kawai zata aure shine ne amma bazata taɓa barin ƙawayenta suga mijinta ba.
Zata ce mashi bata san snatching, kafin ayi mata dariya ace taci baya. Haka tayita tunani kala kala tana kokarin ta kawo kamannin Jalil wanda take kyautata zaton shine zai zama mijinta. Da wannan tunanin Dimples ta sameta, suka yi ma Anty sallama suka fice, a hanya ne take ba Dimples labari.
“Ba zaki rufama kanki asiri da mazan Twitter ba ko Hindu? Bakiji me nace miki ba.”
Kai Hindu take girgiza ma Dimples.
“Wallahi ina ji a jikina Dee.”
Ta kirata kamar yanda take ce mata tana dorawa da.
“Ki yarda dani, zuciyata ba ko yaushe take mun karya ba, ina da good feelings akan Jalil. Ina jin kamar shine zai zama mijin da zan aura.”
Wani irin kallo Dimples takeyi mata, su duka sunsan halinta, ba akan komai take magana ba, amman idan taji bata yarda da abuba to karshe sai abin nan ya zamana baizo musu da dadi ba
“Hmmm…”
Kawai ta furta suna cigaba da takawa zuwa titi inda zasu hau adai-daita sahu da zata kaisu gidan Maman Amrah.
***** *****
“Nifa inada abin yi, ku ce ma Kawu na fita.”
Jalil yace tareda miƙewa. Su Adam kallonsa sukayi sai suka cigaba da hirarrakin su. Gida ya koma yana cire kayan jikinsa, wankewa yayi sosai da omo dan yayi haske clean ya saka. Daman ya siyo bula domin ya ƙara ma dan yadin da yake matukar ji dashi armashi. Dayake yadin mai laushi ne kuma ana iska nanda nan ya bushe. Aikam saiya goge da kyau yana mishi karin guga na mutunci.
Takalmin sa wanda ya ɓare ya soma dariya ya ɗauko, yana saka gam da baya rabuwa dashi dan yan liqe-liqe, nan ya gyara tareda gogewa fes. Yanayin Hindu bai mashi kamar wadda zatayi wulakanci ba. Kuma ai ba santa yace yanayi ba, idan sun haɗu bayan yau zai soma binta da kalamai wanda zai sa ta soshi. Bai taɓa budurwan kirki ba, ya dai saba cema yan talla yana sansu saboda su rinka bar masa kaya kyauta. Musamman masu doughnut ko gyada. Su kuma idan suka gane halinsa su zage shi tas suyi gaba.
Karfe huɗu Hindu ta bashi damar ya ziyarce ta, inda ta faɗi yanada ɗan nisa da inda yake. Maimakon ya hau mashin sai Ustaz yace bari yaje da ƙafa tunda akwai sauran lokaci, yan kudin Machine din yayi amfani dasu ya kara siyan data. Inda yake gani babu nisa saida ya kwashi fiye da awa ɗaya yana takawa. Ga rana ana barbaɗawa ranar kamar zai soye. Duk zufa yakeyi ta ko’ina hammatar rigarshi duk tayi dabbara-dabbara da wajen wuyan sa musamman tunda kayan akwai bula.
Ya isa inda ta faɗa mishi sai nishi yakeyi zufa tana karyo mishi. Sai yayi mata text ta twitter ta fito gashi. Hindu kuwa har nuna ma Dimples tayi tana wani murmushi dan taga kalar ajin da Jalil yake dashi, mikewa Dimples tayi batare da tace komai ba ta dauki mayafinta, daman Kimono ta dora akan riga da wandon da yake jikinta, sukace ma Maman Amrah zasu ga wani a waje, yanzun zasu dawo.
Jalil yana cikin jira ta fito sai gari ya juye hadari ya haɗu, anan iska ta ɗauke mishi hular da ta Kawu ce ta aro ta kuwa cilla cikin unguwa. Haka yayita bi yana.
“Wait! Wait!!”
shi kaɗai kamar mahaukaci. Dan ya san halin Kawu tunda ya hana shi taba mishi kaya, Hular bata tsaya ba saida ta shiga cikin wata muguwar kwata. Haka ya saka hannu ya tsamo ta. Nan yayi dama dama da hannunsa. Zare ido yayi ya soma dube-dube. Sam baisan nan ne kofar gidan Maman Amrah ba, dama Dimples ta hana Hindu bashi asalin address din tace mata kada ta bashi asalin address ɗin, koda baiyi masu ba zasu iya yi mishi fuska kamar basu bane.
Nan su Hindu suka fito suka ganshi tsaye kamar mahaukaci sai zufa yakeyi ga kaya duk datti, balle kuma kayan sunyi mugun koɗewa. Bai gane Hindu ba tunda hotuna kan bambamta. Balle ita da tafi kyau a fili fiye da hoto. Saiya ƙarasa wajensu yayinda suka fito domin su taimaka mashi da ruwa ya dauraye hannun shi harma da bakar leda ya samu ya saka hular kar Hindu ta fito tagan shi.
Yana isa wajen su, bayan yayi sallama yana ajiyar zuciya saboda gudun dayayi. Dimples na watsa mishi wani irin kallo daya saka shi shan jinin jikin shi, a daburce ya soma magana.
“Dan Allah kuyi haƙuri, ruwa zaku taimaka mun dashi in wanke hulata data fada kwata…”
Ran Hindu yayi mugun ɓaci saboda bata ƙaunar rainin wayau, kar mutumin nan ya ja mata bad luck, batason wani akasi da zai faru kafin taga Jalil, Dimples ce ta riƙe mata hannu domin su saurare shi, bata son mutane, amman kuma hakan baisa tana da wulakanci ba, musamman taga zai girmesu nesa ba kusa ba, ganin haka yasa Jalil murmusawa cikin yanayin da duk idan yayi a mudubi yakan ga yayi matukar kyau.
“Dan Allah ruwan zaku taimaka mun sai yar bakar leda in saka hulata…”
Yai maganar yana dorawa da
“Nazo wajen wata abin begena ne Hindu shine hulata ta faɗa kwata”
Da yake Allah yayi mishi surutu na rashin dalili
“Me?”
Dimples ta tambaya tana son taji ko kunnuwanta yaji ‘Hindun’ da Jalil ya furta. Yana dan fadada murmushin shi ya sake maimaitawa
“Hindu, ko kinsanta ne?
Wannan karin Hindu da take jin jiri na shirin kwasarta ce tace,
“Jalil?”
Muryarta cike da matukar shakku, dago idanuwa Jalil yayi yana karema Hindu kallo, sai yanzun da ta kira sunan shi tukunna ya ganeta, yanda take kallon shi ya tabbatar mishi da kiris take jira ta kwada mishi mari.
“Kan uban can”
Cewar Hindu tana dorawa da wata ashariya da bata tabayin irinta ba, kafin ta sake wani motsi Jalil ya ari takalman kare ya yanki Hanya da wani irin gudu cikin yadin shi da yake kwasar iska yana hura shi kamar zai tashi sama. Cikinta Dimples ta rike saboda da dariyar da take tattaruwa kafin ta fito fili da wani irin yanayi da yasa Hindu taji idanuwanta sun cika taf da hawaye.
‘Wannan wacce irin rayuwa ce.’
Ta tambayi kanta, me yasa na rana daya abinda yake karbar mutane ita bazai karbeta ba? Me yasa duk wani abin arziqi da idan wasu matan sukayi dangane da samun Mijin aure na gari ita idan ta kwatanta sai yazo mata a baibai? Wacce irin rashin sa’a ce take bibiyar rayuwarta har haka?
,🤣🤣🤣🤣