Dan baccin da ta samu bai shige awa biyu ba, sai taji kamar tana rufe idanuwanta ne aka kira asuba ta sake bude su, cikin yan dakika zuciyarta tai wani irin tsalle daya tuna mata akwai abinda ya faru da ita a daren jiya, kafin tai wata irin mikewa daga kan gado tana daukar wayarta, dan ko addu’ar tashi bacci ma batayi ba. Duk da daukar wayar da sassafe haka dabi’arta ce, Dimples kan ce,
‘Daga tashi da safe sai ka janyo waya, baka duba ko zaka iya magana ba, ka taka kafafuwan ka kaji ko suna nan lafiya ba, ka dauki waya. Baka ma godema Allah daya dawo maka da ranka ba, tsabagen rashin hankali. Sai ranka ka gama latsa wayar kayi ka mike ka kasa tukunna zaka dawo hayyacin ka.’
Kuma maganar Dimples din tayi tasiri a ranta ba kadan ba, wasu lokuttan da tazo daukar wayar ta tuna sai ta ajiye ta fara yin addu’ar tashi, wata rana har alawala ma sai tayi indai da wuta, in babune zatai amfani da fitilar wayar. Amman yau baiyi amfani ba, dan so take ta tabbatar da cewa da gaske ne tayi magana da Hamzy. Tayi magana da Hamza Abu Abbas, Instagram din ta koma tana bin gabaki daya hirar hadi dayin wani murmushin nishadi, kafin ta tashi har Asma ta rigata mikewa ta shige bandaki, zaune itama Hindun ta tashi tana tunanin dalilin da zatayi amfani dashi wajen sake yiwa Hamza magana.
Mikewa tayi tanayi shiga bandaki, ganin lokaci ya kure yasa tai alwala ta fito tana gabatar da sallah, tadan yi karatun Qur’ani, ta gabatar da azkar din safe, tana kuma bin shi da addu’arta, ta yau da kullum. Wannan karin tana ji har a ranta tamkar addu’ar ta gama amsuwa. Sai da tayi wanka ta shafa mai, sannan ta sake kwanciya tana komawa wani baccin sanin cewa sai karfe goma da rabi take da lacka a safiyar. Sanda ta tashin ma goma tayi, fuskarta ta wanke, tana gyarawa ta sake kaya tayima Anty sallama ta fita, ko yunwa ma bataji, in sun fito sha biyu da rabi sunje restaurant ita da Hauwa.
Tana fita harabar gidan tana cin karo da Musa daya fito daga motar shi, yana sata jan karamin tsaki, duk da taji Mama na fadama Anty an saka bikin shi, bai hana mata haushin shi da take ji ba, manyan kayane a jikin shi ruwan omo, yana rike da hular kayan a hannun shi, ga kan yasha aski sal, sai taga yayi mata kama da dan ta’adda saboda kasumbar daya tara ya kuma salle kai tas, dan dai bata jin akwai gajeru kamar shi a cikin su, saura kiris taji ya cire mata son da takema kasumba a fuskar maza, tahowa yayi bigil-bigil, gajartar da askin na haduwa su saka shi yi mata tamkar kwalbar roll on.
“Hindu…”
Ya kira yana mata murmushin da yasa ta kara tamke fuskarta tana furta
“Sannun ka”
Ta rabashi ta wuce karma ya kara samun damar da zai mata wata magana da sanyin safiyar nan, ita bama kullum take son yawan haduwa da gajerun mutane tunda sassafe ba haka, Musa kuwa kai ya girgiza, ance zuciya bata da kashi, kuma masoyi baya laifi, shikam ya yarda da haka, dan har yanzun da sa ranar shi amman yana jinta har ran shi. Soyayyar da yake mata ba karama bace, haka dai Allah ya kadarta ba zai sameta ba, ya kuma rungumi kaddarar shi da hannuwa biyu. Tunda yanzun in ba wani dalili mai karfi bama, baya zuwa gidan sam-sam.
Da ta isa makaranta taji haushi sosai jin cewa Malamin ya fasa zuwa, ta kuma san ganin Musa da tayine ya shafa mata rashin sa’ar nan, Hauwa ta kira tana fada mata
“Taf… Kinga saurin da nake, kice inyi zamana.”
Kai Hindu ta girgiza.
“Banza kizo dan Allah… Ni banajin komawa gida ma sam.”
Tana jin dariyar da Hauwa ta yi.
“Ashe in zo, bacci zan koma wallahi, kinji kaina yanda yayi nauyi.”
Ita kanta Hindun da tasan ba zaizo ba kwanciyarta zatayi tai baccinta, ko ma ta kara rage assignment din da yake gabanta.
“Ai shikenan, bari in koma kawai. Sai munyi magana, ki gaishe da Anty.”
Tana sauke wayar daga kunnenta bayan Hauwa din ta amsa. Kamar yanda tace mata, gidan kuwa ta koma, sai dai batayi sauri ba, dan bata son komawa ta sake haduwa da Musa, kar ya kara shafa mata wata rashin sa’ar Hamza yaki kulata. Da ta shiga gidan ma a falo ta cire abayar dake jikinta tana ajiyewa da jakar, ta shiga kitchen. Dankali ta fere ta soya ta dauko ta fito, kayanta ta tattara tana shigewa daki dasu. Kan tabirin zanenta ta dora plate din dankalin ta linke abayar sosai ta mayar da ita inda ta fiddo da dan mayafin nata. Sannan ta dauki plate din da wayarta tana komawa kan gado.
Twitter ta leqa ta samu ana cece kuce kan maganar yawan sakin aure, mata na ba maza laifin, su kuma suna kin karba. Ta sauka ta koma Instagram tana shiga shafikan kwalliya, a nutse take duddubawa sosai, dan ita bakowacce mai kwalliya bace zata taba mata fuska idan bikinta ya tashi. Dinki kan shi tana da telolin da take hari, tasan duk yanda Baba yake sonta, bashi da kudin da zai mata kalar bikin da take mafarki, amman tare da hamshaqin mijin da zata samu, abin bazai wahala ba sam. Tunda tana da yakinin zai bata wadatattun kudi da zata gudanar da hidindimunta a cikin tsanaki.
Dabara ce ta fado mata a rai, tana sakata ajiye plate din dankalin a gefe tana mikewa, zanikan da tayi daren ta dauko, ta warware su tana dauka hoto daya bayan daya, guda shidda ne daman ta gama, sannan ta bude Instagram dinta. Sallama ta fara yima Hamza sannan ta tura mishi hadi da dorawa da.
‘Bansan ko nayi dai-dai ba.’
Sannan ta ajiye wayar tana nannade zanen ta mayar inda ta fito dasu kafin ta koma kan gadon tana addu’ar Allah yasa kar Hamza yaki yi mata magana, ko da kalma dayace ya fada mata zataji dadi.
***** *****
Da sallama ya shiga gida, Anna na zaune ta nade kafafuwanta akan kujera, ta amsa mishi, amman ko inda yake bata kalla ba, murmushi yayi, yasan bata kaunar yanda yake kwana a wani waje ba gida ba, duk da Appa ya goya mishi baya da fadin,
‘Namiji ne shi, kuma ya kai munzalin da zai fita ya nema har wata kasar ma,’
Abin baima Anna dadi ba kwata-kwata. Tafi son yaje ya dawo gida ya kwana. Wani lokacin sai ta kira shi ta zage shi tukunna yake dawowa gida.
“Ann”
Hamza ya furta yana zagayawa ya zauna gefenta. Hararshi tayi, tana saka shi yin dariya,
“Haba mana Ann… Aikine fa ya rikeni,”
Ya fadi da harshen Hausa, duk da yasan Ann din ba zatayi mishi Hausa ba, kwata-kwata bata musu Hausa, asalin yaren kasarta take musu, larabci ne gurbatacce, duk da shi Hamza yanajin larabcin na kwarai, yana kuma yima kannen shi cikin kokarin ganin nasu ya gyaru kamar na shi. Kishin abinda Anna din takeyi yasa ta karfi da yaji Appa ma ya daina musu hausa yake yara musu fulatanci, sai suka taso suna jin yarikan duka biyu, ita kuma Anna a tsakaninta da Appa suna fahimtar kome zasu fadama juna da yarukan su, amman kowa bayayin na kowa.
“Hmm, ka kyauta dai, in kasa kafa ka fita daga gidan nan sai an ganka,”
Dariyar ya sakeyi dan bayason maganar tayi nisa.
“Ina Auta? Bakowa gidan? Appa fa?”
Kai ta jinjina mishi.
“Auta na makaranta, su Abid sun dawo sun kara fita.”
Sake gyara zaman shi Hamza yayi.
“Me kika dafa? Yunwa nake ji Allah.”
Mikewa Anna tayi batare da tace mishi komai ba, ta shiga kitchen din tana zubo mishi dambun shinkafa da yaji kayan hadi ta dawo ta kawo mishi.
“Shisa nake son ki Anna.”
Hamza ya fadi yana karbar plate din daga hannunta, hira suke kadan-kadan harya gama cin abincin. Da kanshi ya kai plate din kitchen ya fito yana wucewa dakin shi, samun shi yayi a gyare tsaf, ya kuma san aikin Auta ne, bayan ya sai musu gidan da suke ciki, yaso ya daukar musu mai aiki, saboda babu kalar wahalar da su Anna basu sha ba kafin rayuwa ta kawosu inda suke yanzun, idan dubu daya yake da ita, dari takwas daga cikinta a kansu take karewa, yana kokarin kyautata musu da dukkan wani abu daya mallaka. Ba wani dangi gare su ba, garama Appa akanta, sune komai nata, da wahala ta saka mishi doka ya tsallake.
Ita kanta tana alfahari da Hamza, tun yana karami kalar kwakwalwar da yake da ita yasa takeji a jikinta dan nata zai iya zama wani, yanzun kuma gashi zatonta ya tabbata. Shisa take da buri akan Hamza, bakowacce kalar mata bace zata bari ya aura, sai yar manyan mutane da suka san mutunci, wadda ba zata shiga tsakaninta da danta ba, dan yanzun rayuwa ta canza, mutane babu Allah a ransu. Sai ka samu iyaye da yaran su, kayi kokarin rabasu dashi, ta karfi da yaji ka fara adawa da kyautatawar da yake musu, saboda rashin tsoron Allah.
Shiga yayi yana karasawa kan gadon shi ya kwanta, tun jiya yake tunanin Hindu batare da wani dalili ba, kawai ta samu waje a cikin kanshi ta manne, kaf duk wani hoto da ta saka sai da ya duba, da yanayin yanda take magana da mutane daya bata mishi rai haka kawai. Dan har yau da safe sai da ya sake dubawa yaga tana hirar film da wani kato, shisa mata suke kamar hula a wajen shi, sai ya zaba ya darje, in ya dora na wani lokaci ya cire ya ajiye, yawancin duk matan daya taba mu’amala dasu, su suke kawo kan su wajen shi, da bakin shi bai taba neman mace ba, baima taba nuna ta mishi ba ko da ta mishi din.
Duka halin su daya, idan ba kyawun shi suka biyo ba, to kudin da sukaga yana da shi ne, garama Hindu yaga ita maganar Architecture tayi. Shisa shima baya kasa a gwiwa wajen amfani da wannan damar da suka bashi, in dai zasu mori juna to shikenan, daya gama yayi gaba abin shi, da wahalar gaske ya koma ma mace sau biyu. Har iskanci Fodio yake mishi, cewar yana tsoron attachment. Kuma da gaskene, duk wani abu da zai takura shi baya kaunar shi. Abdallah ne ya kula ya kasa gajiya da yi musu nasiha akan mata shi da Fodio, AbdulHafiz ya dauki idanuwa ya saka musu yanzun.
Basa dai hirar a gaban shi ne, tun ranar da yayi musu hauka sosai yafi sati hudu ko waya bata hadasu ba, sai suke taka tsantsan da yanda suke hirar mata, daman shi da Fodio ne kadai. Kusan Hamza zaice yanda matan suke yawan kawo mishi kansu ne ya fara jan ra’ayin shi, tun yana ND kuma wasu cikin abokan karatun shi da suke kwana studio tare suka koya mishi fara shaye-shaye. Tun yana mamakin yanda bacci baya kamasu har suka sanar dashi wiwi ce, a indomie suke dafawa, ko su zuba a shayi, in zaka kwana idanka kyam, ga yanda yake jin kwakwalwar shi har wani kaifin tunani take karawa.
Sai kuma ya samu Fodio ma yana dan sha, duk da shisa ce abinda yafi bulbula ma cikin shi, Arafat ma na shan shisa. Hamza zuwa club ya fara koya mishi daga kwalba, sai kuma yaga kan shi na rike wuta, bata bugar da shi kamar yanda yake ganin tana yiwa sauran mutane. AbdulHafiz kan ce,
‘Kana cutar da kanka Hamza, akwai kuskuren da kakeyi a cikin sallarka, shisa bata hana maka aikata wannan abubuwan… Wallahi ka gyara kafin lokaci ya kure maka.’
Nasihar kanbi ta kunnen shi na dama ta wuce a ta haggu ne, abinda yasani kawai shine komai yana da lokacin shi, idan lokacin barin yayi zai bari. Kuma azumin litinin da alhamis baya wuce shi sam, in ba rashin lafiya ba, safiyar yau saboda yasan zai zo gida, bai niyyar shan wani abu ba, amman hirar Hindu da wannan ‘katon banzan’ kamar yanda ya fadi ta saka shi kunna wiwi, hakan kuma yasa shi yin fada da AbdulHafiz da bayason jin warin ta, shisa bayason damuwa ko kadan, haka kawai daga ganin hoton yarinya kamar jaraba ta manne mishi a kai.
Shisa har wajen sha daya tukunna yayi wanka ya fito. Yanzun ma tsintar kanshi yayi da komawa Instagram, yana duba hotonta da yake na karshe da ta saka, dan yatsa yasa yana shafa kan fuskarta, na rana daya idan ya sameta ma yayi mishi, zai cireta daga kan shi kwata-kwata. Yana da wannan yakinin, sakkonni ya shiga yana ganin sunanta a sama alamar ta mishi magana.
“Sai yanzun zakiyi mun magana?”
Ya fadi a fili kamar tana jin shi, tun da ya tashi yake dubawa, baisan me zaice mata ba, shi daya fara mata magana, kuma bai saba yima mace magana ba sam, bude sakonnin yayi yana shiga hotunan, badan abinda tayi din ba dai-dai bane a zanen, akwai dai gyara da yawa, kuma layikan basuyi mishi yanda yake so ba. Sallamarta ya amsa sannan ya ce,
‘Akwai gyara kam, bazan iya dogon typing ba. Zan kiraki.’
Sai da ya tura yai tunanin bashi da lambarta balle ya kirata din, baima san dalilin da zaisa yace mata haka din ba, kawai zuciyar shi ce ta darsa mishi son jin muryarta, ko zatayi dai-dai da kalar fuskarta. Sauka zaiyi daga Instagram din yaga alamar tana rubutu.
‘Da gaske? Like da gaske zaka kirani?’
Kafin ya amsa yaga alamar ta sake cigaba da rubutun.
‘Kaifa zaka kirani, dan Allah karka ce mun wasa kake mun.’
Dariya yayi mai sauti, yana fara rubutu.
‘Ki ajiye lambarki kafin in canza ra’ayina.’
Bai taba ganin saurin rubutu kamar yanda ta turo lambar ba, kwafa yayi yana saving da Hindu. Sannan ya danna kira, ta daga yayi mata sallamar da ta amsa shi yana jin farin cikin da yake tattare da muryarta hadi da wani irin excitement da duk basu hana muryar sauka cikin kunnen shi da wani sauti na daban ba, bai tambayi ya take ba, ko ya makaranta, kawai abinda yake so ta gyara a jikin zanen ya fada mata, ko godiyarta bai jira ba ya kashe wayar shi, dan yana ganin kamar duk sakokin da yake kara magana da ita, da yanda take sake manne mishi a kai, da yanda zuciyar shi ke kara kwadaituwa da ita.