Skip to content

Mijin Novel | Babi Na Ashirin Da Biyar

3.7
(3)

Karanta Babi Na Ashirin Da Hudu.

Shi kan shi wanda yake koya mata tukin yayi mamakin yanda ta iya cikin yan kwanaki, saboda bata zaton ta taba mayar da hankalinta akan wani abu irin haka. Ko Hamza yaji dadin yanda ta iya tukin, da yake kudi ne suke aiki, harya gama hada mata duk wani abu da take bukata, an bata lasisin tukinta.

“Banda kudin sai miki sabuwar mota yanzun Hindu, mu fita kiga cikin nawa ki dauki daya, banda Corolla din.”

Ita kam ranta kal, bakar ta dauka kirar BMW 330i, saboda tun ranar daya fara zuwa da motar wajenta ta bala’in tafiya da ita, gata kal-kal babu inda wani abu ya sameta, shima Hamzan ita yayi niyyar bata, dan tafi sauran motocin shi haske, kuma bata koyi shekara da siye ba, bama sosai yake hawanta ba. Ya dai bari ta zabane da kanta. Ko baccin kirki bata samu ba ranar daya bata motar, ya kuma tabbatar mata da mallakinta ce, duk yanda take sonyi da ita zata iya. Ranar farko da ta koma makaranta da motarta ta koma, taji dadin yanda tayi parking ta fito, duk ga wasu cikin yan ajinsu suna ta kallonta, an ga ta zama Hajiya.

Danma Hamza bai fara mata zancen zuwa Hajji ba har yanzun, zata san yanda tayi ta sako maganar cikin hirar su, ta keta hazo itama, ta dawo manne da hakorin makkanta, inda duk zata shiga ana kiran Hajiya Hindu. Tunanin kawai na sakata nishadi na daban. Sai dai ba nan gizo ke sakar ba, cikin watanta na biyu a gidan Hamza, taje makaranta da safe, ana tsakiya da daukar darasi wani dan ajinsu da yazo a makare ya ratsa ta gefenta yana wucewa, kamshin turaren shi na cika mata kofofin hanci. Lokaci daya taji komai ya hargitse mata har jiri-jiri take ji.

Cikin tashin hankali, ko excuse bata iya dauka wajen Malamin ba, ta mike tana fita da saurin gaske, da kyar takai bakin kwalbatin da take gaban ajin, kafin ta tsugunna tana fara kelaya amai kamar zata fitar da hanjin cikinta. Hawwa ce ta fito tana taimaka mata, har ruwa ita ta siyo mata, ta kuskure bakinta, ta wanke fuskarta tana kuma samu ta sha, bata mike daga wajen ba sai da wani irin zazzabi mai zafin gaske daya lullubeta. Dole ta tarkata jakarta tana nufar gida.

“Anya Hindu zaki iya tuki kuwa? Dakin bari na sauke ki, sai in hau Napep in dawo”

Hauwa tace cike da damuwa a muryarta. Ita dince dai taki, aikam a jigace ta shiga gida, a bandakin baki na cikin falon taci birki saboda wani sabon amai daya sake taso mata, amman kakari kawai takeyi a wahalce tunda duk wani abu da yake cikinta ta gama fito da shi, anan kan kafet ta kwanta, tana rashin lafiya. Ba zata iya kirga yawan lokutta da ta kwanta asibiti ba, amman zata rantse bata taba ciwo irin wannan daya kamata farat daya haka ba. Jinta take kamar ba’a duniyar take ba, kamar ta shiga wata irin duniya da bata taba tunanin akwai irinta a rashin lafiya ba. Ko numfashin kirki bata iyawa, ga amai da takeji yana taso mata har lokacin.

Ta kai mintina talatin anan kwance, idanuwanta a lumshe, amman sam ba bacci takeyi ba, ganin kamar mutuwa zatayi idan bata samu taimako ba, ya dan bata karfin gwiwar mikewa, taja jiki tana janyo jakarta data cillo tsakiyar dakin tun shigowarta, wayarta ta dauko daga ciki, tana samu dakyar ta kira lambar Hamza, da bugun farko ya daga da fadin,

“Har kun fito ko bai zo ba yau din ma?”

Muryarta can kasa tace,

“Ya zo…”

Kafin ta samu furta wani abin, daga dayan bangaren Hamza ya rigata.

“Hindu? Lafiya? Me ya faru? Ya naji muryarki haka?”

Dan gyara kwanciyar tayi.

“Bani da lafiya, na dawo gida ne ma.”

Tana jin yai magana cikin yaren da bata fahimta ba kafin yace,

“Ina zuwa kinji, yanzun zan zo.”

Bai jira amsarta ba ya kashe wayar. Mai musu aiki sau daya take zuwa, da tayi share-share sai dan wanke-wanke da bama kullum suke da shi ba, sai in Hindun tayi girki, sauran tarkacen da sukaci, Hamza kance in tazo a fito mata dashi ko ansa a fridge ta tafi dashi, kuma Hindu ta dinga bata kudin mota, ko dubu daya ne. Yanayin kyautar shi na mata dadi, ko yau da zata fita dubu goma ya bata, a cewar shi ko zata bukaci siyan wani abu a makaranta, ko takardu ba saita kira shi ba, kuma akwai kudi a account dinta. Baba ma satin daya fita taga ya tura mata dubu goma, tasan kuma na makaranta. Shisa Baba yake daban a duniyar ta. Sanin tana karkashin kulawar Hamza yanxun bai hana shi sauke nauyin da yake tunanin har yanzun yana kan shi na hidimar makarantarta ba.

Bata san iya lokacin da ta dauka ba, dan bacci ya fara daukarta taki muryar Hamza daya dago ta yana tana fuskarta, wuyanta da duk wani waje da hannun shi zai iya sauka a jikinta da zaiji yanayin zazzabin daya rufeta.

“Wanne irin zazzabi ne wannan?”

Ya fadi cikin tashin hankali, shi sam bayason yaga wani bashi da lafiya. Hankalin shi yakan tashi, musamman yanda yaga duk ta langabe mishi, zuciyar shi banda dokawa cike da tsoro babu abinda takeyi.

“Hindu… Hindu.”

Yake kira yana mikar da ita zaune, shi ya mike tsaye ya kamata, tana tashi da kyar saboda wani irin jiri da taji yana shirin dibarta, ga amai daya taho mata, da sauri ta kwace hannunta daga rikon da yayi mata tana rugawa bandakin, amman babu abinda ya fito sai wahala, Hamza yayi tsaye a kanta yana mata sannu, shiya taimaka mata ta mike, suna fitowa ya zaunar da ita, da kan shi ya zame mata abayar da take jikinta, ya shiga dakinta ya dauko mata hijab, yana kamawa ya saka mata.

“Ta shi muje asibiti.”

Yanda take jinta motsin kirki ma da kyar takeyin shi.

“Dan Allah kabari in kara hutawa.”

Ta fadi kamar zata fashe miki da kuka, kan shi yake girgiza mata.

“Kalli yanda kike fa, kina cemun in tsaya ki huta. Ki tashi wallahi mu tafi asibiti…”

Hamza ya karasa yana kamo hannuwanta duka biyun ya mikar da ita tsaye, amman gani yake kamar zata bata mishi lokaci, sakin hannuwan nata yayi yana dan rankwafawa ya sungumeta ya sabata a kafadar shi kamar bai dauki komai ba, bata da lafiya amman bai hanata jin wani abu ya motsa a zuciyarta ba. Da tasan rashin lafiya ce zata sa Hamza ya dauketa haka, da ko ta karyace tayi tuntuni, luf tayi a kafadar shi har suka karasa bakin motar shi daya samu ya ajiyeta, yana amfani da hannun shi daya ya riketa gam, kamar yana tsoron inya saketa zata iya faduwa, gaban motar ya bude mata, sai daya taimaka mata ta shiga, ya rufe, tukunna ya zagaya ya shiga. 44 Nigerian Reference Hospital da akafi sani da 44 NARHK ya nufa kan shi tsaye, Anna da duka yan gidan nasu nan suke zuwa yanzun in dai basu da lafiya.

Ya yarda da aikin su da kuma yanayin kulawar su, duk da tsadar da mutane suke kira asibitin na da shi. Amman yana da halin, kuma wani kyale-kyale ma yake kashe kudin shi a kai, ballantana neman lafiya. Suna shiga kuwa ana zuwa aka taimaka ma Hindun, sannan ya fara maganar bude mata nata katin, sosai aka shiga bata taimakon gaggawa, dan yanda suka ga ta galabaita har sun bata daki ma, an daura mata ruwa ko zata samu karfi a jikinta, ruwan da takeji kamar yana sake takalo mata ciwon da take jine. Hamza ya zauna tare da ita, da yake an dibi su jini ayi gwaji, har fitsari suka sa tayi a wata yar roba, bayan jerin tambayoyin da sukayi ta mata.

Dan lokacin da results din suka fito bacci takeyi, Hamza ne zaune yana danna wayar shi. Har ofishin likitan ya bishi, inda aka tabbatar mishi da Hindu na da shigar cikine. Tashin farko ba zai ce ga asalin yanda yaji saukar maganar ba, dan daga ofishin yana fitowa, Hindu ya fara leqawa, yaga baccin takeyi. Tukunna ya fita yana shiga motar shi, masallacin farko daya samu ya tsaya ya gabatar da sallar azahar da yaji ana kira, sannan ya sami wani karamin restaurant, ya zauna. Dankali da kwai sai kaza yace a kawo mishi, su hado mishi da coke. Abincin yakeci ba dan yana gane kan shi ba, bama yunwa yakeji ba, jikin shine ya bashi cewar lokacin da zaici abinci yayi.

Wani irin sama-sama yake jin shi, kan shi kamar an dora dutse saboda nauyin da yayi mishi. Aure gare shi, matar shi ce dauke da cikin shi. Yau shine mace take dauke da cikin shi, baisan me ya kamata yaji ba, amman tsoro na daya daga cikin abinda yakeji, tsoron da bai tabaji ba tunda yake a rayuwar shi.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un”

Ya furta yana ajiye cokalin cikin plate din shi, fuskar shi ya dafe da hannuwan shi biyu yana sauke numfashi, kafin ya budeta yanajin yanda zuciyar shi take bugawa har cikin kunnuwan shi. Ko da yake hango kan shi da mata, ba zaice ya hango shi da yaro ba, bai hango wannan dawainiyar ba dan baisan ta inda zai fara ba.

“Kana zaman ka lafiya ka janyowa kan ka wannan bala’in Hamza, kana zaman ka.”

Shine abinda zuciyar shi take furtawa tana kara maimaita mishi. Mikewa yayi yana ajiye dubu biyu akan tebirin duk da abinda yaci dubu dayane da dari biyu. Sannan ya fice, motar shi ya shiga yana komawa asibitin, amman inda yayi parking nan yayi zaune cikin motar, yana kasa fitowa, ko ina jikin shi kyarma yakeyi saboda tashin hankali. Wayar shi ya zaro daga aljihun shaddar da yake sanye da ita, yana lalubo wayar Fodio ya kira, AbdulHafiz zai janyo mishi wasu ayoyi na yanda cikin jikin Hindu kyauta ce da Allah yake zabar bayinsa wanda zai ba, da sauran wa’azikan da basu yake bukata ba a halin yanzun. Wanda zai fahimci tsoro da firgicin shi yake so

“Hey…”

Fodio ya fadi ta dayan bangaren.

“Ciki take da Fodio. Bansan me zanyi ba wallahi, I’m fucking terrified.”

Hamza ya karasa muryar shi na rawa.

“Shit…. Da gaske?”

Fodio ya tambaya, Hamza najin tsoron da yake muryar shi shima

“Abinda nake fadi kenan, kaima ka tsorata ballantana ni, muna asibiti tun dazun. Ina cikin mota a zaune. Fodio ban shirya ba, wallahi ban shirya ba.”

Wani irin zagi Fodio yayi mishi da yasa shi fadin,

“Fodio”

Cike da mamaki.

“Ka jini ai, dan ubanka me kake nufi da baka shirya ba? Kana da hankali kuwa Hamza? Ita ka dai kabari a cikin asibitin bayan an fada muku? Ita kadai kabari ka fito?”

Kai Hamza yake girgiza mishi.

“Bacci takeyi sanda na fito.”

Ya furta a raunane, yanajin Fodio ya sauke numfashi.

“Kasan me yasa ban taba tunanin aure ba? Saboda ba zan dauko yarinyar mutane ban shirya daukar nauyin ta ba. Ka jini Hamza, sai da na fada maka karkayi, nace maka wahala ce a cikin shi, na fada maka aure bana kowa bane ba shisa ba’a tilasta shi bama.”

Runtsa idanuwan shi Hamza yayi yana sake bude su.

“Inda baka shirya haihuwa ba, kafi kowa sanin yanda zaka kauce ma samun cikinta, bakayi ba. Me yasa kake mun magana kamar baka taba hango cewar zata dauke shi ba? You step the fuck up kayi abinda ya kamata…”

Maganganun Fodio din yake ji har kasan zuciyarshi, yasan ya fahimci tsoron shi, amman ya manta asalin waye Fodio, ya manta in akazo maganar daukar nauyi ta fannin aure da kula da iyali, suna da ra’ayin da yasha banban da Fodio. Tsoron su ba kala daya bane ba.

“Karka bani kunya Hamza.”

Fodio ya karasa yana kashe wayar, numfashi Hamza yake fitarwa yanajin kamar iskar cikin motar bata kai mishi inda ya kamata. Hakan yasa shi fitowa babu shiri yana jingina a jikin motar.

“Ko da wata rana zan taba aure bazan haihu ba, yara ne karshen abinda zan kawo a duniyar nan. Ba zan mutu in barsu su wahala kamar yanda aka mutu aka barni ba, kudin duk da zan tara musu in babu kulawa aikin banza ce…”

Maganganun Fodio suka dawo mishi.

“Me yasa zaka auri yarinya kasan baka shirya kula da ita ba? Ina fada muku aure bana kowa bane kuna dariya kamar wasa ne magana ta.”

Fodio din ya fada wata rana da Abdallah ke basu labarin wani mutum a unguwar su da yayi aure bashi da tsayayyar sana’a, karshe sai sakin matar yayi saboda ya kasa riketa. Sosai halayen su da yawa suka banbanta da na Fodio. Ko ranar farko daya fara ganin shi da kwalbar giya tsayawa yayi yana kallon shi.

“Mene ne? Ka daina kallona kamar baka shan wani abu kaima.”

Kai Fodio ya girgiza mishi.

“Idan yau zan samu bacci batare da taimakon komai ba zan daina sha. Kai kasan me ya fara sakani shan wani abu tun daga farko, kana da zabi Hamza, kana zagaye da mutanen da zasuyi komai saboda kai, in ba zaka iya dainawa saboda kan ka ba, ka duba Anna, ka duba me zataji in ta sani ka daina”

Shiru yayi wa Fodio din a wancen lokacin.

“Ni ba AbdulHafiz bane ba Hamza, ba zan iya jure tunasar da kai kullum ba, na fada maka abinda ban samu wanda ya fada mun ba lokacin da nake da damar bari. Zabin duk da kayi bayan wannan naka ne.”

Kuma daga ranar bai sake mishi magana akan shan wani abu ba, ko kiran shi yayi ya biya ya sai mishi zaiyi. In kanata tare da Fodio, shawarar duk da zai baka ka bude kunnuwanka ka saurara, saboda ba zai sake maimaita maka ba, ko da kanka ka bukata ba zai maimaita ba. Kallon ka kawai zaiyi yaci gaba da abinda yake. Ajiyar zuciya mai nauyin gaske ya sauke yana takawa ya shiga cikin asibitin, yana nufar dakin da Hindu take, a zaune ya sameta, ruwan da aka saka mata harya kare, tana murza hannunta. Yau kawai duk tayi wani irin zuru-zuru.

“Kanki babu dankwali.”

Ya fadi wani irin kishi na tsirga mishi, wani katon banza ya shigo ya ganar mishi mata da kai a bude. Shisa bai bari ta cire hijabinta ba tunda ba dogo bane har kasa

“Yanzun na cire hijab din zanyi fitsari.”

Ta amsa shi da dan murmushi a fuskarta, kai ya jinjina mata yana shiga dakin sosai, ya kama hannun da take murzawa ya dago shi, yana shafa inda yayi alamun fasawar allura, harya dan kumbura.

“Sannu…”

Ya furta yana kamata ta mike, har kofar bandakin ta shiga, fitsari tayi ta kara wanko fuskarta tana fitowa.

“Wai zasu sallameni ne fa, ance kana ina.”

Kai Hamza ya jinjina yana fadin,

“Ina zuwa.”

Tunda yasan yanda duk tsarin asibitin yake, ya kai mintina sha biyar kafin ya dawo yana, da yar leda a dayan hannun shi, ya kama nata hannun yana fadin

“Muje…”

Kallon shi take yi, ko takalma babu a kafafuwanta, saboda sungumarta yayi da zasu fito.

“…You step the fuck up kayi abinda ya kamata.”

Muryar Fodio ta dawo mishi, dan murza goshin shi yayi yana sauke numfashi a hankali, kafin ya zare takalman da suke kafafuwan shi yana tsugunnawa ya tura su saitin nata kafafuwan, kallon shi takeyi, zuciyarta na wata irin dokawa. Kafin ta daga kafafuwanta ta saka takalman, ya kama hannunta yana janta, bin shi take tana kallon yanda yake taka cikin asibitin suna nufar hanyar fita, babu takalma a kafafuwan shi. Kallon shi takeyi kamar har abada ba zai taba bata mata rai ba, kamar ko satin daya wuce basuyi tashin hankali da shi akan Mansy ba. Wani lokacin yana mata kamar yana da iska in ya juye haka.

****

Duk fadan da Hamza yayi da tace ya sai mata soyayyar doya ta bakin titi da taga wata mata nata soyawa, yayi parking din ya fita ya siya. Haka kawai taji doyar tayi mata, yawunta har tsinkewa yakeyi, tun a motar ta faraci, har suka karasa gida tana samu waje ta zauna. Kamar jira aman daya taso mata yake yi ta karasa cinye doyar, gabaki daya saida ta dawo. Shi kan shi Hamzan hankalin shi yayi bala’in tashi, da kan shi ya taimaka mata ta watsa ruwa, ya dauko mata kayan da zata saka, sai rawar sanyi takeyi duk da ruwan mai zafine tayi wanka da shi, rigarta ya kama yana taimaka mata dan ta saka.

“Me yake damuna haka? Naji sauki fa kafin mu fito daga asibitin, me suka ce ya sameni?”

Take tambayar shi.

“Ba abinda ya sameki, ciki kike da Hindu.”

Maganar shi ta sauke cikin kunnuwan shi da wani irin yanayi.

“Ciki?”

Ta tambaya da murmushi a fuskarta, kai ya daga mata yana juyata, ya zage mata zif din rigar. Hannunta takai saman cikinta, tana lumshe idanuwanta, hadi da jero kalmomin godiya ga Allah da wannan kyautar da yayi mata, kyautar da tasan mata da yawa na raba dare suna addu’ar samu. Kwanciya tayi, ya ja bargo ya rufa mata, idanuwanta kawai ta lumshe. Bashi yake rashin lafiyar ba, amman a gajiye yake jin shi sosai, maganin da kala biyu ne kawai ya ajiye gefe yana fita. Robar ruwa ya dauko mata, yazo ya ballo magungunan yana tsugunnawa.

“Ta shi ki sha”

Batayi musu ba ta mike, ta karbi maganin ta sha tukunna ta koma ta kwanta. Shi nan ya zauna kan kafet din yana jin wata irin gajiya na saukar mishi. Wayar shi ya dauko da yaga bacci ya dauketa yana kiran Auta, bugun farko ta daga

“Yayaa”

Ta fadi,

“Auta kina ina?”

Ya tambaya.

“Yanzun na fito daga makaranta, ina kan komawa gida. Ya naji muryarka can kasa?”

Numfashi Hamza ya sauke

“Hindu bata jin dadi, ko zaki zo ki zauna da ita. I promise ba wani aiki zakiyi ba. Kawai kar a barta ita kadai, akwai abinda zanyi a wajen aiki.”

Ya karasa, dan yaga Arafat nata kiran shi, tunda AbdulHafiz kadai yasan ya fito, shima bai fada mishi dalili ba, bai kuma tambaya ba.

“Okay, bari in siya abu sai in taho.”

Kai Hamza ya jinjina.

“Na gode.”

Ya fadi yana sauke wayar daga kunnen shi. Zama yayi har saida yaga Auta na kiran wayar shi, yasan ta karaso ne kuma, ba zata shigo ba. Ta tsaya a falo tana kiran shi, mikewa yayi ya leka kai, ya ganta a zaune kuwa tana warware mayafin da yake nade da kanta

“Nagaji wallahi.”

Kai kawai Hamza ya girgiza, lalacinta bashi da na biyu, yana da tabbacin babu abinda tayi duk yau banda shiryawa ta fita makaranta.

“Bacci takeyi, in ta tashi da wani abin ki kirani.”

Kai ta jinjina mishi.

“Ka fadama Anna ina nan, kaine kace in zo. Kaji.”

Wannan karin shiya jinjina mata kai yana ficewa. Yasan tana so tazo gidan nashi, amman Anna tace me zata zo tayi, har karar Anna ta kawo mishi, ta hada su biyun ta zage. Da gasken babu abinda zatayi, kawai tana so tazo ne, itama tace taje gidan Yayanta, kamar yanda sauran kawayenta suke fadi. Anan falon tayi zamanta tana kunna TV, ta tsayar da channel din a MBC 2 da suka saka film din Step Sisters, ta kalla yafi a kirga, kawai bata gajiya da film dinne. Ice cream din data biya ta siya ta fara sha hankalinta a kwance tana kallon, dan sosai ta kwaso tarkacen ciye-ciyen da Anna kance suna tafiya a banza tunda ko yar kiba basa sakata.

Babi Na Ashirin Da Shida

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×