Skip to content

Mijin Novel | Babi Na Ashirin Da Shida

4.3
(4)

Karanta Babi Na Asirin Da Biyar.

Duniyar tayi mishi tsaye waje daya, kallo daya za kai mishi kasan baya cikin kwanciyar hankali, damuwar da take tare da zuciyar shi shimfide take kan fuskar shi.

“Me yake damun ka?”

AbdulHafiz ya tambaye shi, kai kawai ya iya girgiza mishi yana fadin

“Babu komai.”

Ya kuma ji dadin yanda bai matsa mishi da tambaya ba, saboda bashi da wata amsa tsayayya da zai iya baiwa AbdulHafiz din. A watanni biyun nan cikin Hindu ba karamin wahala yake bata ba, bata kwana biyu ba’a kara mata ruwa ba. Gara cikin satin nan yaga ta fara warware wa, watannin nan sune masu tsayi a rayuwar shi tunda ya mallaki hankalin shi da yayi su batare da mace ba. Shisa a satin nan har cikin idanuwan Hindu yake ganin yanda ko kusa da ita ya zauna a tsorace take da shi. Wuni yake bulbulawa cikin shi giyar da yakejin tana dakushe mishi abinda yake ji.

Abu daya Hindu ta kula da shi yanzun, in har yana gida, yana manne da wayar shi, ita kanta ba dadin take ji ba, sati daya kenan da take samu taci abinci ya zauna, duk tayi wata irin rama. Duk abin Anty sai da suka zo suka duba ta, Baba kuwa zuwan shi hudu, duk idan ya dawo aiki yakan biyo ya dubata, duk da sau daya ta samu ya shigo cikin gidan harya zauna ya sha ruwa. Sauran a tsaitsaye suke gaisawa, ya bata tarin siyayyar kayan ciye-ciyen da take lodawa a fridge, wanda zasu lalace ta baiwa mai aikinta, tunda ita ba iyaci takeyi ba.

Yau ta rasa abinda zatayi, da Dimples tace zata shigo ta saka mata films, saboda zataje gidan su Biebee da bikinta sauran satika uku, suna kan hidimar da ake ta faman yi babu Hindun saboda laulayin da take fama da shi, ta kuma kira cewar ba zata sami shigowa ba, dan wajen aiki basu barta tashi da wuri kamar yanda tayi tsammani ba. Tata wayar ta dauka, yanzun ta zama yar kallo a twitter saboda bakin kishi irin na Hamza, da tayi tweet ma idan ya hau yaga maza sun yi magana baya ce mata komai, sai dai ta nemi tweet din ta rasa, ya goge.

Tasan duk inda yake yana gab da dawowa yanzun tunda har anyi sallar magriba. A nan inda ta idar da tata sallar take zaune tana danna wayar. Fita tayi daga nata account din tana shiga na Hamza da taga tarin Notification, ga kuma sakonni da yawa ta DM. Shiga tayi duk yanda zuciyarta take fada mata karta yi hakan, karta jama kanta abinda zai daga mata hankali, amman kuma wani bangare na zuciyar yana fada mata ta duba, tasan Mansy na nan tana bi mata miji, tana kuwa shiga, sakon farko nata ne

“Shegiya mai tallar taba”

Ta furta a fili, wani tukukin bakin ciki na danne ta, shiga tayi tana ja ta koma daga farkon hirar da tayi mishi magana, tana duba lokaci, jiyane ma, karfe biyu na dare, saboda ita batasan darajar ‘ya mace ba. Karfe biyu zata fara yi mata magana da miji, amsar Hamzan tagani, farko hira ce sukeyi mai tsafta, kafin Mansy din ta fara mishi wata magana da ta canza gabaki daya akalar hirar tasu, jikin Hindu babu inda baya bari saboda munin abinda ta kasa daina karantawa.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Ta furta ganin yanda Mansy take cewa Hamzan ya duba whatsapp din shi ta tura mishi hotunan da video din da ko ita da yake mijinta batajin zata taba iya tura mishi su, ko dan tsoron kar wayar tashi ta fadi, ko a sace da irin wannan abubuwan a ciki da ya kamata ace idanuwan shine kawai zasu gani. Kife wayar tayi, ko ina jikinta bari yake saboda tashin hankali. Ga hawayen da suke cike da idanuwanta sunma ki zubowa saboda zafin da zuciyarta takeyi, daukar wayar tayi tana fara rubutu.

“Dan uban babanki duk hotunan da kika tura mishi suna wayata, da screenshot din wannan hirar gabaki daya. Idan bakiyi blocking din shi, kin daina mishi magana ba sainayi posting hirar nan da duka hotunan har da videos din a TL kowa yaga karuwancin da kike bin mazan mutane kina yi. Wawiya, jaka, ballagaza da batasan inda yake mata ciwo ba, tsohuwar banza kawai.”

Sai taji zuciyarta tayi mata dan sanyi, da ace zata ga Mansy din ido da ido ta kamata ta jibga kamar ganga sai tafi hucewa, sau biyu tana sake sallar isha’i saboda ta farkon bata da tabbacin ga abinda ta karanta a ciki saboda tashin hankali, tana sallar tana kukan wannan jarabtar da take ciki, batasan ranar da Hamza zai bar zuciyarta ta samu hutun kirki ba. Ta dauka yanzun cikin jikinta yasa shi ya nutsu, duk tunanin da takeyi ya daina shan koma meye taga yasha a daren ta na farko a gidan, saboda bata kara ganin shi cikin maye irin wannan ba. Addu’ar da ta dukufa tana mishi ta karbu ta wannan fannin.

Duk da ta fara dora laifin wannan abin da taga sunyi da Mansy a kanta, watakila da ace bata nuna mishi gazawarta a satin nan bayan hakurin da yayi da ita na watanni biyu ba da bai komawa Mansy ba, da abinda ya faru bai faru ba. Tana sallame sallama sallah yana bankado dakin kamar zai karya kofar hadi da fadin

“Hindu!”

Yana hanyar dawowa, kan shi yayi bala’in nauyi saboda abinda yasha mai karfine, kuma babu wani abincin kirki a cikin shi, so yake yana shigowa gida ya watsa ruwa ya kwanta tunda yayi isha’i. Ya kusa gidan ma yaga kiran Mansy, harya yanke bai daga ba, sake kira tayi bai daga ba. Ganin tayi mishi kira na uku yasa shi dagawa, dan ya tabbata akwai dalili me karfi da yasa take kiran shi, kukan da yaji tanayi ne yasa shi sauka daga titi yana yin parking gefe, yanda kan shi yayi nauyi ba zai samu nutsuwar yin tuki da amsa wayar a lokaci daya ba.

“Ki natsu kimun magana Mansy, bana gane me kike fadi, me ya faru? Me akai miki?”

Ya karasa tambayar da fulatanci, itama da shi take mishi Magana.

“Matarka, matarka taga hirar mu jiya, ka duba whatsapp kaga me tace mun. Hamzy ka rufamun asiri ka bata hakuri karta doramun hotuna a TLl, in dai kaine na hakura wallahi…”

Cike da rashin fahimtar abinda take fadi yace

“Bangane ba…”

Amman kuka takeyi sosai, abinda bai taba gani ko jin tayi ba tunda yasan ta da shi

“Kai kasan a duniya kai kadai kake da wannan hotunan, ko na taba kasadar turawa duk iskancina saboda na yarda da kai. Wallahi ba zan yafe maka ba idan suka bazu, kayi mata Magana.”

Mansy ta karasa cike da kashedi tana kashe wayar, hakan yasa shi duba whatsapp din shi ko zai fahimci abinda take fadin, screenshot ne na sakon da Hindu ta tura mata

“What the fuck!”

Ya furta a harzuke yana sauka daga whatsapp din ya kira lambar Mansy.

“Bata da hotunanki ko daya, chats dinne kawai da ta gani. Ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru.”

Yana jin ajiyar zuciyar da take saukewa.

“Dan Allah Hamza…”

Kai yake girgizawa.

“Na fada miki karki damu, babu abinda zai faru, akwai dalilin da yasa kika yarda dani tun daga farko, ki sake yarda da nace miki babu abinda zai faru.”

Ya fadi, kafin tace wani abu ya kashe wayar, Allah ne kawai ya karasa kawo shi gidan lafiya saboda yanda yake fisgar motar. Bai aiki Hindu duba mishi chats ba, baiga dalilin da zaisa tayi abinda tayi ba, saboda bata da wata alaka da Mansy, da shi take da, shikuma shine yake da alaka da Mansy, shi ya kamata ta zaga ba ita ba. Idan mutuncin shi yake bukatar ya zube zaiyi da kan shi ba saita yi mishi ba.

“Me kike tunanin kinyi?”

Ya tambaya yana kallonta, itama kallon nashi takeyi cike da tsantsar mamaki.

“Me kake tunanin nayi?”

Ware idanuwan shi yayi yana wani murmushin takaici mai sauti.

“Ki amsa mun tambayata, akan me zaki tura mata wannan sakon? Me tai miki da zaki zageta?”

Mikewa Hindu tayi tana son saka idanuwanta cikin na Hamza, tana son ganin da gaske ne maganganun da yake fada mata

“Idan da kunya a idanuwan ka zaka tsareni da wannan tambayar dan na zagi karuwar ka?”

Ta furta, kalmar karuwar shin na fitowa daga wani lungu na zuciyarta da yake mata ciwo na gaske.

“Kin taba ganin alamar kunya a idanuwa na?”

Ya tambaya yana hade space din da ya rage a tsakanin su yana tsareta da idanuwan nashi.

“Karuwa ta ce, shisa nake tambayar dalilin da zaisa ki zageta tunda baki da alaka da ita, ni ya kamata ki zaga ba ita ba inda kina da hankali.”

Wata irin dariya taji ta kubce mata mai hade da wani sautin kuka, duk abinda yake faruwa, duk fadan da sukayi akan sauran yan matan shi, musamman Mansy da ta zame mishi wani bala’i da Hindu ta rasa ta inda zata fara tarbar shi, yaune karo na farko da take jin dana sani na tasowa daga dan yatsar kafarta yana tattarowa daga dukkan gabbanta kafin ya samu wajen zama a kirjinta.

“Kaine babban marar hankali wallahi, da kana da hankali ba zaka tsareni kana fadamun wannan maganganun akan wata ballagaza ba, kaine babban mahaukaci Hamza.”

Da mamaki yake kallonta, a tsayin rayuwar shi banda AbdulHafiz babu wanda ya taba kallon shi ya kira shi da marar hankali cikin raini haka.

“Ni kike kira mahaukaci?”

Ya tambaya, kai ta daga mishi tana saka hannuwa ta goge fuskarta da wasu hawayen bakin cikin suka sake zubowa.

“Na kiraka mahaukaci, wallahi yaune na fara tir da mugun halin ka Hamza, na dauka zaka canza, na dauka zan iya canza ka, meye a jikin Mansy da ni bani da shi? Me take maka da ni ban iya ba?”

Tayi mishi tambayar da ta dade tana yiwa kanta, yau ta bari ta fito fili saboda da gaske a tsorace take, tsoro bana wasa ba da halin Hamzan, a karo na farko tanajin kamar bata isa ta canza shi ba, kamar shi din baya son canzawa, in kuma baya son canzawa ita bata isa ta canza shi ba.

“Ka fadamun abinda take dashi da bani da shi, ka fadamun me kake nema a jikin ballagazar nan!”

Juyawa yayi da nufin fita yabar mata dakin, saboda sosai kalamanta suke kara harzuka shi, musamman da yakejin tana gab da fada mishi tayi dana sanin auren shi, idan shi bai gaya mata yayi nata ba, ba zai jira ta fara fada mishi ba.

“Ina zaka je? Ka amsa ni inji, ka fadamun abinda yake jikin karuwar taka da bani da shi.”

Juyowa yayi, muryar shi can kasan makoshi yace,

“Idan ba zaki iya karanta chats dina kiyi kukan ki ke kadai ba, karki sake shigar mun. Karki sake mun makamancin abinda kikai mun yau, wallahi zan baki mamaki, baki sanni ba har yanzun.”

Sosai take kallon shi tana sake sa bayan hannunta ta goge fuskarta.

“Wallahi idan yanzun na sake hawa saina zagi uban uwar Mansy, kana jina, saina zageta, akanta ne kake fadin zaka bani mamaki. Allah ya baka iko….na zageta, Hamza na zageta ka…”

Bata karasa ba saboda marin daya dauketa da shi, wata irin walkiya na giftawa ta cikin idanuwanta, da gaske ne, littafi bai mata karya wajen rubuta kalar marin nan ba, ta runtsa idanuwanta tana bude su yafi sau hudu dan ta tabbatar da kwayar idonta bata fado ba. Kafin ta dafe kuncin, ta nemi hawaye ma ta rasa dan azaba.

“Na fada miki zan baki mamaki kinki yarda ko?”

Ya furta da wata irin murya dashi kanshi ta sauka kunnuwan shi da wani yanayi, jikin shi har bari yake saboda bacin rai, ya dauka Auta ce mace daya a rayuwar shi da zai taba dagama hannu. Saboda bai hango Hindu zata tunzura shi haka ba, zata saka shi jin son ya jibgeta har saiya daina jin nauyin da kanshi yayi.

“Mar… Mari, ni ka mara? Akan Mansy ka mareni?”

Tsaki yaja mai sauti, yana wucewa hadi da jan kofar da karfi, kafafuwanta da taji suna rawa suka sakata zama, amman jikinta bari yake, dole ta kwanta, tanajin hawayen da suke bin gefen fuskarta, ga kirjinta da yayi nauyi kamar zai bude, mutanen da suka taba marinta basu da yawa a rayuwarta, ta kuma manta ranar da hakan ta faru. Mijin da take karkashin inuwar aure da shi, ko a mugun mafarki bata taba hango zai daga mata hannu ba, ko da hakan ta faru ba’a kan karuwar shi ba. Ba akan ballagazar da ko kira ta ‘ya mace ba zata nuna mata ba, ballantana kuma daraja.

Ta sha jin labarai na cin mutunci irin na da namiji, amman nata ne mafi muni da taci karo da shi a tsayin rayuwarta, yau ita Hindu, ita Hamza ya daga hannun shi ya dauke da mari saboda karuwa…!

*****

“Ban gane yace zai saka ranar da za’a kwashi kaya ba, sai ku ka taho kukuma?”

Baba yake fadi ranshi a matukar bace yana kallon Muhsin da Huzaifa.

“Baba bana so in biye mishine ni, saboda kar ayi abinda za’aji kunya ko da sauran zama.”

Huzaifa ya fadi a tausashe.

“Wanne sauran zama? Shi da wanene zasuyi sauran zaman?”

Shiru su Huzaifa sukayi, cikinsu babu wanda baisan halin Baba ba idan ranshi ya baci.

“Ya kore muku ‘yar uwa cikin dare da tsohon ciki har kuyi tunanin akwai sauran zama a tsakanin su. Halan bakwa kishin ta ne?”

Kai Huzaifa ya girgiza, yana shirin magana Muhsin yadan zungure shi alamar yayi shiru, tsaki Baba yaja.

“Ku koma ku kwasomun kayan yarinya dan banason su kara kwana a gidan wannan marar mutuncin.”

Muhsin ne ya fara mikewa yana ma Huzaifa ido, shima ya mike suka fice daga falon.

“Kasan halin Baba babu abinda zai saurara yanda ran shi ya baci, kuma Hindu aka taba, ni wajen aiki zan wuce, zuwa anjima watakila ya huce yanda zai iya fahimtar mu.”

Kai Huzaifa ya jinjina.

“Allah dai ya rufa asiri. Ni naso inga Hindun ma wallahi.”

Dan murmushi Muhsin yayi.

“Ka rufawa kanka asiri ka wuce, anjima ka dawo kaganta. Yanzun wallahi Baba kaniyar mu zaici.”

Shi Huzaifa ma sam ya kasa yin ko da murmushin ne saboda takaici. Shi kan shi idan za’abi shawarar shi za’a hakura da maganar Hindu ta koma gidan Hamzan nan. Tare da Muhsin din suka fice daga gidan, da shawarar duk idan kowa ya dawo daga neman halal dinshi zasu sake dawowa suyi ma Baba magana ko zai fahimci abinda suke son ya fahimta din.

Cikin gidan kuwa, Anty najin duk abinda yake faruwa, idan ta gwada yiwa Baba magana ita kanta ranta ne zai kara baci fiye da yanda ya baci yanzun. Shisa ta nufi dakin Asma tana samun Hindu a kwance ta zubawa bango idanuwa, sai taji tausayin ta ya cika zuciyarta.

“Hindu…”

Ta kira da wani irin yanayi a muryarta, tana saka Hindun tashi da kyar ta jingina bayanta da gadon, karasawa Anty tayi tana shiga cikin dakin sosai. Ta zauna gefen gadon.

“Hindu ke kadai kikasan meya hadaki da mijinki, kamar yanda ke kadai zaki taushi zuciyar Babanku yayi hakuri abi komai a hankali…”

Tunda Anty ta fara magana taji idanuwanta sun ciko da hawaye.

“Anty ki kyale shi kawai, ni ba zan taba komawa gidanshi ba, wallahi nagaji, tunda na fito na fito kenan da yardar Allah.”

Ta karasa maganar tanajin wani zogi da ba sabo bane a zuciyarta. Karfin tahowa gida ne bata da shi daman tun watanni biyun da suka wuce, da tuni ta kamo hanya ta gudo daga gidan auren daya zame mata kangin da bata tana hangowa ba, daga auren mijin da kowa zau kira da kyakkyawa amman a idanuwanta sai da ya juye ya koma kamar dodo. Ba auren Hamza kawai take son gujewa ba, gabaki daya kalmar aurene bata son ji.

“Hindatu…”

Anty ta kira da wani irin yanayi a muryarta, kai Hindu take girgiza mata, tana wani irin gunjin kuka me sauti.

“Anty karkice inyi hakuri, ya rigada ya sakeni, komawa ba zabi bane ko da ina so…”

Hindu ta karashe, ballantana tunda ta shigo gidan takejin tana shakar wata irin iska mai sanyi da ta kwana biyu bata shaki irinta ba. Ya saukake musu auren daya zame musu karfen kafa. Da kan shi ya sauke aurenta daya kira da kaddara .

“Kaddarar aurenki ce kaddara ta farko da nayi dana sanin ta Hindu a duk kaddarorin da suke cikin rayuwata.”

Ko kadan baya dana sanin kaddarar bin mata, kaddarar shaye-shaye sai ita, sai aurenta. Hamza ya gama cire mata duk wani kyale-kyale na aure da take tunani, taso MIJIN NOVEL, a sujjadarta ta roki MIJIN NOVEL, sai dai bata roka da kalar halayyar shi ba, har a zuciyarta idan ta hasaso, kudin, kyawun da soyayyar kawai take gani. Ta dauka ita kadai ta isa ta rike auren su, bata dauka aure ya wuce duk wannan ba. Hamza ya bude idanuwan ta, ya wanke tunaninta tas, ya dasa mata neman asalin dalilin da yasa aka saka aure a cikin jerin ibadu.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Anty ta fadi, wani irin daci na zauna mata a zuciya, kalmar saki abuce mai muni a duniyar ma’aurata komin karfin dalilin yin hakan kuwa. Ko labarin saki taji sai zuciyarta ta tsinke, yanzun da labarin ya fito daga bangaren ta, daya faru akan ‘yarta ji take zuciyarta ta matse a cikin kirjinta tana wani irin ciwo.

“Allah Kai Kadai Kasan me Ka boye a cikin wannan lamarin. Allah Ka bamu juriyar cinye dukkan jarabtar da ka tsara mana.”

Anty take fadi a cikin ranta, kafin ta dora da,

“Alhamdulillah ala kulli halin.”

Tana cigaba da maimatawa, hannu Hindu tasa tana share hawayenta.

“Ya sakeni Anty…”

Ta sake fadi, kalaman na zauna mata, ba kukan rabuwa da Hamza take yi ba, kukan tarin abubuwan da ta hadiya a karkashin auren shi da tunanin zata iya gujema kawowa inda take yanzun. Kamota Anty tayi, a karo na farko da hakan ya faru, gyara zamanta tayi tana kwanciya ta dora kanta a cinyar Antyn, kuka take kamar zuciyarta zata fito, kuka take yau da take samun lallashin da ta dade bata samu kalar shi ba, kuka tayi har baccin wahala yai gaba da ita…!

Babi Na Ashrin Da Bakwai

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×