Skip to content

Mijin Novel | Babi Na Ashirin Da Takwas

5
(3)

Karanta Babi Na Ashirin Da Bakwai.

Jin shi yake kamar an watsa mishi ruwan kankara, sanda ya koma gidan Fodio a falo ya sami AbdulHafiz. Tun fitar Hamzan suna tare da Fodio, panadol yasa Arafat ya dauko ya bashi. Da kan shi ya shiga kitchen ya hada mishi ruwan shayi mai kauri ya bashi ya sha, suka fito suka bar mishi dakin. Sai bayan sun dawo sallar azahar ne ma ya leqa ya ga yana kwance, sake janyo mishi kofar yayi ya dawo falo ya zauna. Addu’ar neman Rahma yake ma Ashir da ko jana’izar shi ba zasu samu suje ba, zai so suje din, amman Fodio bashida wannan nutsuwar.

Arafat ya fita ya samo musu abinda zasu ci, hakan na nashi damar kiran Nabila, da maganar farko da yayi yasa ta fadin.

“Me ya sameka? Me ya faru?”

Kai yadan girgiza.

“Bani bane ba, Fodio ne…”

Duk da ajiyar zuciyar da tayi, bai hana wata damuwar bayyana a muryarta ba sai da ya ce mata rasuwa aka mishi, abokin shine ya rasu tukunna yaji ta nutsu.

“Kaci wani abu?”

Kai ya girgiza kamar tana ganin shi.

“Kaci wani abu dan Allah, karka zauna da yunwa.”

Kan ya sake jinjina mata, yasan ta fishi rashin son magana, lokutta da dama yakanyi shiru ne dan yaji tata maganar.

“Ke ma kici wani abu, na kira ne inji muryar ki.”

Ko bai ganta ba yasan murmushi tayi.

“Ka kular mun da kanka. Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya. Ina ma Fodio gaisuwa.”

Sallama sukayi, ya sauke wayar daga kunnen shi kenan Hamza ya shigo. Kujerar da take kallon ta AbdulHafiz din ya zauna yana dafe kan shi.

“Me kayi?”

AbdulHafiz ya tambaya, yana sa Hamza dagowa ya kalle shi, hadi da dan girgiza kai.

“Ba zan sake tambayar ka ba, bana cikin yanayin Hamza, damuwar ku ba za taimun illa ba…”

AbdulHafiz ya karasa maganar yanajin shi a gajiye.

“Bazan dinga neman damuwa a fuskar ku kamar kananun yara ba, kana jina, wallahi ba zan sake tambaya ba Hamza…”

Ran shi yake ji a bace, ba tun yanzun yake ganin damuwa a fuskar Hamzan ba, ya tambaye shi yafi a kirga yana ce mishi ba komai, nauyi ya mishi yawa. Lokutta da dama yanajin kamar ya girmi shekarun shi, ko a gidansu bashi bane babba, amman matsalar kowa da shi yake rabawa, ga kuma ta su Hamza. Sosai ya gaji har cikin kasusuwan jikij shi.

“Duk wani kokari nayi, nayi Hamza…”

Dan babu yanda za’ayi ka taimaki mutumin da bayason taimakonka, ko ya kake son yin hakan kuwa. Ba wai magana bace Hamza bayason yi, ba kuma fada mishi bane ba zai iya ba, asali ya tara abubuwa da yawa da ya kamata ya fada mishi baiyi ba. Bai saba daukar laifukan shi ba, yanzun da hakan ya zame mishi dole, baisan ya zaiyi ba, ko ta ina zai fara.

“Nayi kuskure…”

Ya furta da wani nisantaccen yanayi a muryar shi.

“Ba jiya bane kawai.”

Ya sake fadi, daga randa ya fara dagama Hindu hannu ne farkon kuskuren shi, a ranar kuma yaji a jikin shi yayi kuskure, dan ko idanuwa bayason hadawa da AbdulHafiz, satin da yaje gida sai yake ganin kamar Anna zata gane abinda yayi, musamman da yaga Appa, kamar zai gane ya samu rauni a matsayin shi na namiji tunda ya dagawa matar auren shi hannu. Sai dai me, tsintar kan shi yayi da kasa dainawa, ko cikin da yake jikinta baya dubawa, karamar gardama da wahalar gaske su karasa bai daga mata hannu ba.

“Karka sake dukana, dan Allah karka sake dukana Hamza, idan zamuyi fadan mu muyi, amman ka daina dukana, zan tafi gidan mu.”

Muryar Hindu ta dawo mishi wani lokaci bayan ya hankade ta tayi wata irin faduwa, har taso samun matsala saboda cikin jikinta, tsoron da yaji bayan sun dawo asibiti, ya dauka zaisa ya bari. Sai da ya sake, sosai wasu lokuttan yake binta da idanuwa yana neman dalilin da yasa take mishi uzuri, yana rokonta da ta taimaka mishi, ko barin shine tayi ko zai dawo hayyacin shi, ya rasa abinda yake damun shi haka. Sosai yake daga kwalba fiye da da, cikin son rage damuwar da ta zame mishi abokiya. Kwata-kwata bashi da farin ciki. 

Inda wani yace mishi zai kai tsayin lokacin nan da mace daya zai karyata. Amman ko rage zafi ya fita yi da wata yarinya sai maganganun AbdulHafiz sun bishi inda duk ya shiga, wasu lokuttan kamar mai aiki da aljanu, yana dakin hotel din text din tunasarwar AbdulHafiz zai shigo mishi ya kashe duk wani abu daya shiga dakin da shi. Mansy ce kawai ta san yanda take tana samar mishi natsuwa ko da baya tare da ita.

Hakan yasa shi duk ya watsar da sauran matan, da ita kawai yakan yi chat yanzun, yana kuma kokarin ganin hirar tasu ta tsaya iya whatsapp din shi, yana gogewa duk idan sun gama, in ba tsautsayi da rabon suyi tashin hankali da Hindu ya gifta ba, ta dauki wayar tagani. Yau ma kamar kullum, uzurinta ta kawo mishi kamar yanda take yi duk satin nan, sai tace mishi bayanta kamar zai bude.

Hakuri take hada shi da shi, hakurin da baisan yanda zai fara yin shi ba, tunda bai saba ba, bar mata dakin yayi tunda ya riketa a jikin shima sai faman hakuri take bashi. Bayason suyi tashin hankali shisa ya hau sama yana wucewa ya dauko kwalbar giyar shi, ya bude ya ajiye, ya mike ya dauko kofin daya zuba kankaru a ciki ya dawo ya bulbula. Kirane ya shigo wayar shi, yana dubawa yaga Mansy ce ya daga.

“Hamzy… An shigo gidana… An shigo gidana yanzun.”

Ta karasa tana wani irin kuka kamar zata shide.

“Hey…kina ina yanzun?”

Ya tambaya yana mikewa tsaye, amman kukan da takeyi ta kasa magana, hakan yasa shi yi mata magana cikin fulatanci.

“Basu tabaki ba ko?”

Da kyar ta iya amsa shi da.

“Eh…kudi kawai suka dauka da gold, sai su TV…bansan iya abinda suka dauka ba.”

Kofin shi ya dauka yana karasa kwankwadewa

“Ki kulle dakin da kike ciki…bari in zo.”

Yanajin kukan da take yi har lokacin.

“Dan Allah ka zo… Bansan wazan kira ba, kai kadai… Kai kadai ka…”

Kai yake jinjina wa.

“Shhh…. Gani nan zuwa yanzun.”

Ya karasa yana kashe wayar, ya duba agogo yaga karfe sha biyu saura. Mukullan mota ya dauka, kan shi ya danyi nauyi saboda vodka ya sha, tana da karfi, amman zai iya tuqi. Ficewa yayi daga gidan ya dauki mota, kan shi tsaye gidan Mansy ya karasa, ya sha mata magana kan ta sami ko maigadi ne, saboda yanayin shirun unguwar su, amman taqi ji. Aikam tana jin muryar shi ta bude kofar ta fada jikin shi. Riketa yayi sosai yana dan jijjigata a jikin shi.

“Ba zan iya kwana a gidan nan ba, ka kaini wani waje… Dan Allah ka kaini wani waje.”

Dan har ranta ta dauka mutuwarta ce tazo yau, yanayin su da makamai har su biyar ya firgitata, tazo rufe gida kenan suka afko mata. Kamata yayi suna fita daga gidan zuwa wajen motar shi, sai lokacin ya kula da tata motar ma bata gidan, kuma yasan su suka dauka. Inda zai nufa da ita yake tunani, yanda take a firgice ko hotel ya kaita yasan ba zata zauna ita kadai ba, shikuma ba zai iya kwana tare da ita ba saboda Hindu ita kadai ce a gida, ga tsohon ciki.

“Dan Allah karka barni ni kadai, yau kawai karka barni ni kadai, kana da mata nasani…”

Ta karasa cikin kuka. Kai ya jinjina mata yana nufar gidan shi kai tsaye, akwai dakuna da yawa inda zata kwana, yau kawai. Zuwa gobe sai acan yanda za’ayi. Ko ba komai kawar shi ce. Haka suka karasa gidan, yayi niyyar saiya fara kaita inda zata kwanta, sannan ya shiga wajen Hindu, in batayi bacci ba yasan yanda zaiyi ya fada mata Mansy zata kwana a gidan yanda ba zasuyi rikici ba. Amman sai hakan bai yiwu ba, saboda suna shiga tana saukowa daga sama.

Haka kawai bayan yabar dakinta take ganin kamar zai je yayi waya da Mansy, batasan ya haihuwa take ba tunda bata tabayi ba. Amman har a kasusuwan jikinta takejin tana gab da sauke abinda yake cikinta, duk da asibiti sunce mata tana da sauran satika uku, ko sama da haka, amman yanda bayanta yake amsawa kawai yana karyata likitocin. Amman Hamza yaki fahimta, kamar ranta zaibar jikinta haka takeji duk idan ya kasance tare da ita. Yanda ya fita a fusace har kwalla tayi, jarabar shi ta isheta, har auren ma ya fita a ranta, a hankali komai ma take tsintar kanta da jin baya ranta.

Musamman yanzun da take jin kafarta daya a duniya, daya a lahira, wasu kyale-kyale ne karshen abinda yake ranta, inda wani yace bata fara hauka akan siyayyar kayan baby ba zata karyata. Amman Hamza da yayi mata maganar ca tayi yaba Anna din da ta fara mishi zancen suyi duk abinda ya kamata, ita kam ba zata iya ba, so take kawai taga ta haihu lafiya. Duk da sun yanke hukunci basa son sanin meye zasu haifa din, gara yazo musu a ba zata.

Har bandaki ta duba shi bata gan shi ba, dakyar take saukowa daga benen, da hijab din da ta saka bayan ta daura alwala da nufin yin ko raka’a biyu ce ta nafila bayan fitar tashi, saita kasa samun nutsuwa shisa ta fito ta duba shi. Sai gashi ya shigo, da wata mace manne a jikin shi, ko dankwali babu a kanta, asalima rigar jikinta ko gwiwarta bata karasa ba, ita kanta Hindu daga inda take tana ganin duk wata halitta ta jikinta.

Harta karasa saukowa daga benen abin na mata kamar a mafarki, saboda tasan duk abin Hamza ko da wasa bai taba shigo mata da wata mace gida ba, yanzun ma yana kokarin boye mata abinda yake faruwa da wannan fannin na rayuwar shi. Ko giyar shi da tagane bai daina sha ba, ya sha yau bata tunanin zata gaya mishi ya shigo mata da wata mace cikin gida haka. Ta kasa yarda harta karasa gab dasu ta tsaya, tana karewa Mansy da ta boye bayan Hamza kallo.

Dariya Hindu tayi me sauti tasan mafarki ne daman, saboda Mansy tafi tsana duk a cikin matan da yake bi, shisa ta kasance macen da mafarkinta ya hango mata a tare da Hamza.

“I can explain, ba abinda kike tunani bane ba.”

Hamza ya fadi yana kallon Hindun, har ranshi ba abinda yasan take tunani bane ba.

“An shigar mata gidane, bata da inda zataje, kwana kawai zatayi da safe sai tasan ya zatayi. Nasan zaki fahimta.”

Kallon shi Hindu tayi, tana saka hannu ta taba kirjin shi, taga yana nan dai, itama kanta ta mintsina taga da gaske na mafarki bane ba, wani irin ashar ne ya kubce mata, sam batasan duk zagin da takeji tana adana shi bane sai bayan ta auri Hamza, Mansy da ta kara shigewa bayan Hamza ta mika hannu ta fisgo.

“Dan ubanki da nace ki kyalemun miji baki jini ba ko?”

Hindu ta karasa maganar wani irin kishi na lullube mata idanuwa, dan batasan lokacin da ta daga hannu tana shararawa Mansy mari ba, ko kadan bataji nauyin cikinta ba, niyyar fara jibgar Mansy din takeyi kamar ganga, dakyar Hamza ya banbare Mansyn da ta koma gefe tana rawar jiki, ita iya tashin hankalin da ta gani yau ya isheta, maruka tasha sunfi goma a hannun barayin nan, dan daya sai da yaso keta mata haddi, ogan nasu ya tsawatar mishi, tasan haushin hakan yasa shi shimfida mata wasu marukan.

“Hindu… Hindu…”

Hamza yake fadi, yasan ta iya rigima saboda ba karamar mace bace zata iya kallon idanuwan shi ta biyema tashin hankalin shi, amman ko dukanta yayi bakinta baya mutuwa, kuma saita fada mishi duk wani abu da tayi niyyar fada ko zai kasheta. A girman jiki Mansy ta fita, amman idan zai barsu, duk da cikin jikin Hindu dukan tsiya zatayiwa Mansy yasani.

“Ta fitar mun daga gida…dan ubanki ki fitar mun daga gida kafin in karairayaki.”

Kamata Hamza yake yi tana zillewa, in bata jibgi Mansy ba sam ba zata ji dadi ba, ko kuka ta kasa, haka Hamza yake janta harya samu ya shigar da ita daki.

“Ina ki ke so taje? Bakiji nace miki barayi sun shigar mata gida ba?”

Kallon shi tayi.

“Idan baka fitar mun da ita daga gida ba ku biyun zaku ga tashin hankalin da baku taba gani ba.”

Idanuwan shi ya runtsa, kan shi yayi nauyi sosai, kuma ranshi ya fara baci.

“Bafa gidanki bane ba, ina da damar da zan kawo wanda duk naga dama…bana son yin rigima dake. Zata kwana da safe zata tafi.”

Dariya Hindu ta kwashe da ita da bata da alaka da nishadi ko kadan.

“Wallahi ba zata kwanar mun a gida ba, ka kawo kowa banda karuwar ka.”

Kai yake girgiza mata.

“Ki bari, karki sake…”

Ya karasa yana fita daga dakin, ta kuwa bi bayan shi, kitchen ta wuce bata sami wani abu a kusa ba, saboda ta manta ranar karshe da tayi girki, tukwane ne kawai a kusa, guda biyu ta dauko, tana fitowa daga inda take ta fara cillawa Mansy.

“Dan ubanki ba zaki fitar mun daga gida ba ko?”

Dayar tukunyar ta sake dagawa tana nufar ta, da gudu kuwa ta fice daga gidan, Hamza ya tare Hindun yana kokarin karbar tukunyar da take hannunta, dakyar ya kwace, bata nutsu ba duk maganar da yake mata, haukan da takeyi mishi saika dauka tana da aljanu, sai da ya kwashe ta da mari tukunna ta fara dawowa hayyacinta.

“Ki kiyayeni Hindu, wallahi ki kiyayeni.”

Ya furta yana ficewa daga gidan, a harabar ya samu Mansy tana kuka kamar ranta zai fita.

“Kabani mota in samu ko hotel ne, matarka zata kasheni Hamza.”

Dan dafe kai yayi, yana komawa cikin gidan ya haura sama, kudi ya dibo da baisan yawan su ba da mukullin dayar motar shi yana komawa ya bata sannan ya dawo cikin gidan.

“Na fada maka ba zata kwanar mun gida ba.”

Kallonta yake yana tunanin abinda yasa take kiran gidan shi da nata.

“Wallahi idan nayi niyya ke baki isa ba Hindu, gidana ne idan ma karuwar zan kawo gidana ne.”

Kallon shi takeyi tanajin yanda auren shi ya kawo mata iya wuya.

“Sai dai ke kibar mata gidan idan ba zaki iya zama ba.”

Kai take jinjinawa wasu hawaye na zubar mata.

“Ka bani hujja kaga idan ban tafi gidan mu, ka sakeni kagani…”

Ran shi yayi matuqa wajen baci, yagaji da auren ta, ya gaji da yanda take nuna mishi saboda ya aureta bai isa yayi abinda yake so ba.

“Kaddarar auren ki ce kaddara ta farko da nayi dana sanin ta Hindu a duk kaddarorin da suke cikin rayuwata.”

Sai lokacin hawayenta suka zubo jin yanda kalaman suka fito daga zuciyar shi.

“Baka ga kaddarar neman mata ba, baka ga kaddarar shan giya ba sai ta aurena? Na tsaneka Hamza, nayi dana sanin da ban saurari Yayana ba na aureka wallahi.”

Kai ya jinjina mata.

“Da kin fadamun tuntuni ai, dana saukaka mana duka damuwar mu kinyi gaba.”

Hannu tasa tana share hawayen fuskarta,

“Yanzun ma bai baci ba Hamza…ka bani takardata kaga idan ban bar maka gidan ka ba.”

Yanda yakeji idan ya kara minti daya a wajen rufeta zaiyi da duka. Sama yahau ya samo takarda ya sakko, har lokacin tana nan tsaye tana zubar da hawaye, jinta take da gaske kamar a mafarki, tana kallon shin yana rubutu, harya gama ya ninke yana fadin.

“Gashi nan, ki fita kibar mun gida.”

Sosai take kallon Hamza saboda ta tabbatar ba kunnuwanta kadai suke jin alamar ruwan sama ba, hakan yasa ta dan kalli window din dakin.

“oh karki damu…”

Ya furta yana wucewa kitchen din dakin, wata bakar leda ya samu ya kulle takardar a ciki yana janyo hannunta ya mika mata.

“Sai ki fitar mun daga gida, ba zata jiqe ba, kina da abinda zaki nuna musu in kinje”

Kuka take zuwa yanzun, badan sakin yana mata ciwo ba, sai dan ganin da gaske Hamza janta yake zai fitar da ita daga cikin gidan ana ruwan sama, da tsakar daren nan.

“Duka biyun ka karasa?”

Ta bukata tana kokarin kwace hannunta daya rike yana janta kamar zai karyata, tana son tuna mishi bata manta da sakin farko da su kadai suka san da shi ba.

“Koma nawa nayi ba dawowa zakiyi ba…”

Ya karasa maganar yanajin iskar ‘yan cin da yake shaka, kawai so yake ta fitar mishi daga gida, duk inda zataje taje. Da ta fara tirjewa sosai tana fadin,

“Takalmina, ban dauki wayata ba Hamza… Ka bari in dauki takalmana…”

Wani irin mari ya kwasheta da shi sai da komai ya tsaya mata na wasu dakika, dan harya jata ya fita da ita, taja jin yanda yake ma maigadi kashedi amman wani irin sama-sama take jinta. Kamar yanda yake jin shi sama-sama, yanda yake jin shi kamar a mafarki yake, duk maganar da yake da yanda sabon tashin hankali yake ziyartar shi gani yake kamar zai koma gida ya gan Hindu.

Sai da yaga AbdulHafiz ya mike tukunna yace,

“AbdulHafiz…”

Amman baiko nuna alamar yaji ba ballantana ya kalle shi, wayar shi da take gefe ya dauka ya saka a aljihu, yana daukar hular shi,

“AbdulHafiz…”

Hamza ya sake kira cikin wani sabon tashin hankali, bai kamata yabarshi shi kadai ba. Ba zai yiwu ya gama bude mishi ciwukan shi yayi kamar hakan ba komai bane ba. Wucewa AbdulHafiz din yayi, yana cin karo da Arafat a bakin kofa.

“Muje…”

AbdulHafiz din ya fadi yana sa Arafat kallon shi cike da rashin fahimta.

“Ka wuce muje, kaima ba zaka so ka zauna da shi ba in kasan me yayi, ka wuce kawai Arafat.”

Kai kawai Arafat ya jinjina yana wucewa suka fice daga gidan gabaki daya. Suna barin Hamza nan sake da baki, a karo na farko a rayuwar shi da yasan tabbas yayi babban kuskure, in har AbdulHafiz zaiki sauraren shi haka, da gaske yayi kuskuren da baisan ta ina zai fara gyarawa ba.

Babi Na Ashirin Da Tara

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×