Skip to content
Part 18 of 33 in the Series Mijin Novel by Lubna Sufyan

Ta dauka lokaci zai yi mata tsaye, kalaman AbdulHafiz da Nabila bayan saka ranar su ya zauna mata daram, amman sai tasha mamaki, dan lokaci bai taba yi mata gudu irin wannan karin ba, ko dan jarabawar da suka yi da gujumniyar project din karshen zangon, duk da lokacin Hamza ya karba yayi mata tracing. Ta samu sauki, amman sam ta kasa yarda da cewa kwanaki kasa da ashirin suka rage a daura aurenta, sai take ganin komai ya cakude mata, ga Hamza sam aiki ya wani irin rike shi, komai ya bari a hannunta.

Dan Dimples da Biebee su sukayi hidimar fito da anko, sun sha wahala kafin su yanke hukuncin anko kala biyu, atamfa da za’a saka wajen Kamu, sai kuma leshi da za’a saka a wajen dinner. Wannan ma batabi ta kansu ba, nata kudin ma su taba, Ita tun sauran wata biyu bikin take duba leshina a Fabrique Castle, harma ta dauki lambar Waheedah Shu’aib Haroon da itace mai mallakin shafin, kuma da alama mutane sun yarda da kayanta, taga hotunan amare da dama da suka siyi kaya a wajenta cewar abinda suka siya shi aka aika musu da shi.

Dan ba sosai take yarda da siyayya online haka ba, amana tayi karanci a cikin mutane yanzun. Amman tabbas akwai kayayyaki daga leshi zuwa atamfofi irin wanda bako ina ake samun su ba, yanda take son komai nata ya fita daban. Anan tayiwa Waheedah magana ta tura mata kalaluwan leshina da atamfofi, Hamza ya tayata zabe, tunda shima duk shaddojin daya siya tare suka zabi wanda zai dace da kayan da zata saka. Babu yanda Anty batayi da ita ba kan a siyi kayan anan Kaduna, itama tasan mutane, amman Hindu taki.

“Anty harfa nayi magana da Baba, yama bani kudi.”

Cewar Hindu, dan Baba ya kirata yaji ita dame-dame ta zaba, ta kuma nuna mishi, da Antyn tayi mishi magana ca yayi,

“Ki kyale yarinya da zabinta dan Allah, ke abinda zaki so ba lallai ya yi mata ba, kuma kinsan kayansu na zamani.”

Shi sa Anty ta koma gefe ta saka musu ido, kiri-kiri Baba yake nuna yanda Hindu tafi mishi kowa a gidan, har saida Antyn ta dinga jin babu dadi, tunda da Hindu da Khadee za’a yi bikinsu lokaci daya. Amman kai tsaye Baba yake kiran Hindu yana tambayarta zabinta akan abubuwa da dama, ko da Khadee take nuna hakan ba komai bane, Anty tasan Mama ba zata ji dadi ba, kawai dai in akace Baba da Hindu ne, babu wanda ya isa yace wani abu. Shi sa kowa ya dauki ido ya saka musu.

Yanzun ma Hindu na daki a zaune ta shiga Instagram, wani biki ta fara cin karo da shi, ita yanzun gabaki daya bikin AbdulHafiz ya dakushe mata kyallin duk wasu bukukuwa da take cin karo da su, badan bata taba ganin bikin da yafi nasu AbdulHafiz ba, tunda Allah yayita da bin shafukan manyan mutane, amman nasun ne anyi shi cike da natsuwa, ga kuma irin kalar shigar da sukayi. Akwai kudi dan kudi, amman sarautar da take tattare da shagalin bikin na daya daga cikin abinda ya qawatar sosai da sosai.

Kuma lokacin dan rashin tausayi, duk da a Kaduna yake da zama da matar shi, amman sai su Hamza suka bashi sati biyu, tunda aiki suke a Kano lokacin, shi yake kular musu da sauran ayyukan su na nan Kaduna, shida Abdallah. Ita Hindu sai take ganin sati biyu yayi kadan, dan tana so idan nasu yazo a basu fiye da haka. Tasan yanda Hamza yake rawar kafa a kanta, ko wata daya aka basu wuni zaiyi cikin gida, yanda zata zuba sangartarta, tafiya ma a cikin gidan ba sosai zata dingayi ba, sai dai ya dauketa. A ganinta idan mata basu more wannan damar da Allah ya basu ta lokacin amarci ba, ai an gama sha dasu, indan Hamza ne yanayin soyayyar su ma, harsu tara yara ba zata wuce sunguma a wajen shi ba.

Murmushi tayi ita kadai tana dan sadda kai cike da kunyar kalar tunanin da sake-saken da take yawan tsintar kanta a ciki tun bayan da aka tsayar da lokacin auren su, balle kuma yanzun da abu ya matso kusa, sosai take hasashen yanda rayuwar auren nasu zata kasance. Ta gama da maganar dinki, Doka plaza takai, da aka lissafa mata kudin dinkunan gabaki daya sai da taji kanta ya sara, dan har kasan ranta take tausayin Baba, balle taga kudin da yake kashewa, tun daga kayan kallo dana kitchen, komai aka shigo da shi gidan guda biyu ake siyowa.

Ranar tana shigowa gida sunayin waya da Hamza, yake tambayar me tayi ranar, ta fada mishi takai dinki, sukai hirar, sai gashi ya turo mata kudin dinkin, taji dadi har ranta. Idan baba ya bata kudin dinki, ko nawane sai tayi maganar kwalliya dasu, taga yanda abin zai kasance. Ta dai ajiye lambar Nadine da Meemie Beauty, amman ranar Kamu dai zataje colors of Meena da yake safaha plaza anan kwato road, tayi gyaran kai, wankin kafa sai kuma suyi mata kwalliyar fitar bikin ranar acan. Khadee tayi musu booking din mai kunshi da zatazo tayi musu har gida.

Shiga tayi tana duba masu yin cake din biki, dan Hamza yayi mata maganar jiya, amman shi ba wasu abubuwa yakeyi da yawa ba, dinner ce kawai da zasuyi, kuma Fodio da shi kadai take da lambar wayar shi duk a cikin abokan Hamzan, da bikin ya gabato.

“Nikam kaina na ciwo, haka biki yake da wahala daman? Kuyi magana da Fodio ni dai, nagaji wallahi.”

Hamza ya fadi ranar da suke maganar wanda zai musu hotuna a wajen bikin. Yanzun ma alamar shigowar sako tagani ta whatsapp, tana budewa taga Fodio dinne ya yi mata sallama, ya tura mata wasu hotuna da ta bude, wajen event ne har guda uku. Yana dorawa da.

“Ki zabi daya.”

Zabar kuwa tayi, inda yafi kowanne yi mata kyau a cikin hotunan, tana hasaso yanda zasu kawatu sosai, har saukowa daga gado tayi tana tashi tsaye, dan sosai wajen yayi mata kyau.

“Castle event center, daman nima duk yafi mun kyau.”

Ai bata ma ba Fodio amsa ba, ta sauka daga Whatsapp din tana shiga Instagram dan ta duba su, wani irin tsalle tayi ganin sosai yanda wajen ya kawatu, tana da tabbacin zaiyi tsada sosai da sosai. Dan Big city events center ma nawa aka ce musu, dan anan zasuyi kamun bikin, da yake wajen babu laifi shima ya kawatu, da wuri sukayi booking, kar a fara gaya musu labaran da zasu karya musu zuciya. Murmushi kawai take yi ita kadai, a tsayen Asma ta shigo dakin ta sameta.

“Ke zo kiga inda za’ayi dinner din bikina.”

Tace ma Asma cike da farin ciki, da gudu Asma ta karasa tana karbar wayar daga hannun Hindu.

“Inalillahi…. Kai… Wallahi wajen nan ya yi mugun kyau, amman da tsada ko?”

Kai kawai Hindu take dagama Asma, murmushi take har kumatunta sun fara mata ciwo, amman ta kasa dainawa saboda tsantsar nishadin da take ciki, wayarta ta soma ruri, kafin tayi wani yunkuri Asma ta daga, muryar Hamza na dukan kunnenta da fadin.

“Babe…”

Cike da gajiyar da yake tattare da ita, dariya Asma tayi,

“Ba ita bace ba.”

Shima dariyar yayi, tun bayan saka ranar su da Hindu sukayi wata irin shakuwa da Asma din, dan Hindu batajin a gidan akwai mai yin Hamza bayan ita, sai Asma, takance yana da kirki sosai, haka kawai zai turo ma Hindu kati yace taba Asma, tayi sub ta duba assignment, ko zuwa yayi wajenta yakan taho da kayan ciye-ciye yace a bata, sosai in kana tare da shi zaka fahimci yanda hannun shi yake a bude kamar ganyen magarya, ba kamar samarin yanzun ba da Dimples kance.

“Ki godema Allah Hamza na yi miki kyauta, yanda samari suke kamar kwalta, sam basa banbaruwa.”

Godiyar Allah kullum a cikinta take dan ta sami cikar burinta, addu’arta bata fadi a banza ba, jinkirin da ya sameta yazo da alkhairi.

“Asma, ina Babyna?”

Hamza ya fadi, dariya Asma ta karayi, kafin tace wani abu Hindu ya fisge wayar tana kai mata dukan data kauce tana fita daga dakin, dan har lokacin dariya takeyi.

“Hello…”

Hindu ta fadi, tana jin yanda Hamza ya sauke numfashi .

“Nagaji sosai, Fodio yake cemun kun zabi wajen da za’ayi dinner ko?”

Kai ta daga.

“Eh yanzun ya turomun, sannu da gajiya, su AbdulHafiz ba zasu kyalemun kai kadan huta ba ko?”

Numfashin ya sake sauke mata cikin kunne.

“Kibarsu, kuma wai zamu shiga Kano gobe, gashi yanzun suna so su kara jana mu fita, ni zan watsa ruwane inyi Magriba inzo wajen ki.”

Zama Hindu tayi, jin kafafuwanta sun fara gajiya.

“Dan Allah zaka zo? Karka sakamun rai fa.”

Yar dariya ya yi.

“Jibi yanda kike magana kamar da gaske kinyi kewata, bayan nine nace zanzo.”

Itama dariyar ta yi.

“Da gaske ina kewar ka, bana so ince yaushe zan ganka dan kar in kara takura ka.”

Tunda tasan aikin da ya ke fama dashi.

“Sau nawa zan fada miki duk aikin da nake yi idan da gaske kina son ganina zan ajiye in zo? Sai dai in bana garin.”

Murmushinta ya fadada, tanajin yanda soyayyar shi take kara cika mata kirji.

“Sauran ‘yan kwanaki dai, duk mu huta da wannan wahalar.”

Ya fadi, yar dariya tayi a kunyace.

“Ba zaki daina mun wannan kunya-kunyar da kika san bana so ba ko?”

Tasan yanda yake a gajiye, rigima zai iya yi mata, tana kuma cikin farin ciki, sam batason abinda zaija suyi rikici.

“Ka tashi ka watsa ruwan, yamma na karayi, nima alwala zanyi.”

Zata rantse kai ya girgiza mata.

“Ni um um, ban gama jin muryarki ba.”

Mikewa ta yi.

“Yi hakuri, kai da zaka zo muyi hira ma, tashi ka watsa ruwa dan Allah, ka ji.”

Shiru ya yi na yan dakika kafin taji ya sauke numfashi me nauyi.

“Baka tashi ba fa.”

Ta fadi.

“Yanzun zan tashi ai.”

Yayi maganar yana karasawa da hamma.

“Bacci ko?”

Ta bukata muryarta na sauka kasa, cike da kulawa.

“Ummm, bari dai inyi wankan.

Ya karasa maganar yana kashe wayar, kan gado ta cillata, itama tana shiga bandaki.

*****

Zuwa yanzun Hindu gani take yi kamar da ta tashi da safe dare yake sakeyi ta kwanta, saboda yanda lokacin yake yi mata sauri. Gidansu Biebee taso shiga, amman suna wajen suna, zaifi mata sauki akan zuwa unguwar su Dimples, amman babu yanda zatayi, dole can din ta tafi, saboda za’a kawo lefen su, gidan ma akwai wasu cikin ‘yan uwansu, tacewa Anty a can zata kwana, idan ta kira Hamza tsaf zaije ya dauketa ya mayar da ita gida. Ko Baba Abba ma Yayan Dimples idan yana gida, dare kuma yayi tasan zai taimaka ya sauketa. Tunda taje suka gaisa da Mama tana dakin Dimples suna zuba labari, tana kwance akan gado, ita kuma Dimples din tana kan keken dinkinta.

“Dee rashin mutuncin ki bashi da na biyu, jibi rigar da kike dinkawa kan ki.”

Idanuwa Dimples ta juya mata tana cigaba da abinda take yi kafin tace,

“Kinfi kowa sanin ban koyi dinki dan kowa ba sai kaina, kuma nama tsani abin yanzun wallahi, sam baya raina. Su Mama ma sun cire rai, tela suka samu suna kai dinkin su.”

Dariya Hindu tayi, tasan halin Dimples, tunda Mama ce ba zata ce mata ba zata dinka ba kai tsaye, amman ayi watanni ko yankawa batayi ba, Mama kuma irin mutanen nan ne da basa son a ja musu rai, tunda ta gwada sau biyu, bata kara bata dinki ba.

“Allah ya shiryeki wallahi, amman ke banza ce, da kudin da zaki samu Allah kadai yasan yawan su.”

Dankwalin da Dimples ta karasa lafewa ta jefa kan gado tana fadin,

“Naji…yanzun zamuyi wata maganar mai muhimmanci ko baki gaji da bata bakin ki ba?”

Sosai Hindu take dariya, kafin ta daga wayarta da Hamza ya kira.

“Nifa ina inda kika ce, ki fito, tun dazun nake kiran wayarki ban samu ba.”

Mikewa tayi tana fadin,

“Dee bari inga Hamza.”

Kai Dimples ta daga mata.

“Ki gaishe da shi.”

Wucewa Hindu tayi, tasan Dimples, ko catayi ta fito su gaisa ba zataje ba, haka ma zatace.

“Bana son shegen gulma, kibarni.”

Shisa batayi asarar maganarta ba, fita tayi tana kuwa ganin motar shi da yayi parking a gefe. Karasawa tayi ta bude tana shiga, ya jingina sosai da jikin motar, ya juyo da kanshi yana sauke mata idanuwan shi da take ganin sun sake launi, takan ga hakan wasu lokutta, sai yace mata bacci ne da gajiya. Murmushi tayi mishi, yana sake shagwabe mata fuska.

“Gajiya?”

Ta tambaya, ya daga mata kan shi da yakejin yayi wani irin nauyi, kuma yasan abinda yasha ne, da bacci zai kwanta yayi, kawai yaji yana son ganinta. Shisa ya kara bulbula ma cikin shi vodka, ko zai samu ta dishe mishi abinda yake ji, yanzun sosai take mishi rigima idan ya nemi ko hannunta ne ya rike, kuma ran shi na baci ba kadan ba, shisa yake kokarin ganin yayi controlling din kan shi, kamar yanda tace ne.

“Saurin me kake yi?”

Kuma AbdulHafiz yace mishi,

“Idan kana son ta, da gaske idan kana son ta, ba zaka tayata tara zunubi ba, ba zaka nemi wasa da kwanciyar kabarin ta ba.”

Kuma tunda aurenta zaiyi, zai jira, yana azabtuwa da hakan ne fiye da yanda ita da AbdulHafiz zasu taba fahimta, ba wasa yake so yayi da kwanciyar kabarinta ba, dan shima na shi yana kan layi, ita dince take barazana da nutsuwar shi.

“Ya kike?”

Ya tambaya muryar shi a dishe.

“Ni ina lafiya, kai zan tambaya ya kake… Ka karbo dinkin?”

Kai ya daga mata, yanda itama take zaune cikin kujerar ta kwantar da kanta na saka shi sauke numfashi.

“Kinsan kina da kyau ko?”

Yar dariya ta yi.

“Kai baka ganin naka kyan? Dan wanda na samu shine baka gajiya da magana a kai.”

Numfashi ya sauke, idan zai kwana yana mata bayani ba zata taba gane abinda yake nufi ba, ko magana take yi sai yaji tsikar jikin shi na mikewa, wani irin kyau take mishi na ban mamaki, jin yayi shiru, ga wani irin kallo da yake mata yasa ta fadin,

“Ya turo hulu nan?”

Wayar shi da take ajiye cikin gaban motar ya mika hannu ya dauko, cireta ya yi daga mukulli yana shiga WhatsApp din shi, ya kai kan inda yayi saving lambar mai hular, ya mika mata, shiga tayi tana dubawa, gabaki daya sunyi kyau, kuma zasu shiga da kayanshi.

“Dubu arba’in da takwas?”

Ta fadi tana ware idanuwanta, ganin kudin daya daga cikin hulunan, amman dai daga zanen ma ta fita sosai, tana dai jinjina kudin, sai taga sauran ma suna da tsada sosai, guda daya ce dubu sha biyar. Fita tayi daga kan lambar mai hulunan, tana ganin wadda take saman tashi da akayi saving da 1. Anyi sako, baima bude ba

“Naga alert din. Na gode.”

Tagani, batasan me ya kaita ba, kawai ta tsinci kanta da bude sakon, haka kawai taji tana son sanin kudin menene ya tura, kuma waye ya tura ma, chat din ma baiyi tsayi ba, sama tayi tana fara ganin na farko daya tura

“Hi”

Kafin a amsa shi, zuciyarta tayi wata irin dokawa

“Sunan hotel da kuma kudinki.”

Ta karanta, tana ganin yarinyar ta turo kawunan mamaki da kuma alamar tambaya

“Karki bata mun lokaci. Ba zan maimaita tambayata ba.”

Anfi awa biyu a tsakani kafin ta turo.

“Assa pyramid hotel. 100k”

Wannan karin shiya tura mata kawunan mamaki.

“100k? Sake turomun hoton ki ingani.”

Tasan ya kamata ta daina karantawa, amman ta kasa dainawa, duk da zuciyarta na mata barazanar tarwatsewa a cikin kirjinta saboda zafin da takeyi, hotunan ta shiga, yarinyar da wahala idan musulma ce, dan kanta yasha kitson gashin doki, kuma riga da wandone a jikinta da suke bayyana duk wata halitta da take da ita.

“Meye abin 100k anan? 15k idan zaki iya.

Sai da ta duba mintinan da suke tsakani kafin yarinyar ta amince, zuwa lokacin idanuwan Hindu cike suke taf da hawaye. Tana karasa karanta hirar da lokacin da suka saka zasu hadun, kuma jiya ne, baizo yaganta ba. Ya samu lokacin da zai hadu da wata a hotel, har ranta ta dauka ya daina, saboda bata ganin maganar shi dasu a twitter, har Mansy tun bayan saka musu rana bata ganinta, ta dauka sun rabu itama, yanzun kuwa ya dawo mata da shakku da kokwanto, ga wani zafi da kirjinta yake yi. Hamza na kallonta, yana kallon yanda hannuwanta suke rawa, yasan wani daga cikin chat din shi ta shiga.

Gudun ruwanta ya tsaya kallo, dagowa tayi tana kallon shi da hawayenta da sai lokacin ya samu damar zubowa, dagowa yayi daga jikin kujerar motar yana mika hannu ya fisge wayar shi, ya duba yaga abinda ta karanta, dan bata fita daga kai ba, fita yayi, ya saka wayar a key, ya mayar da ita inda ya dauko.

“Hulunan sunyi kyau?”

Ya bukata, yana saka Hindu kai hannuwa ta goge fuskarta.

“Huluna sunyi kyau? Shine abinda zaka ce mun? Hamza karka raina mun hankali, wallahi karka nuna mun kamar baka san abinda ya faru ba.”

Hindu ta fadi a masife, kallonta yake yi a kasalance.

“Me ki ke so ince miki?”

Yanayin yanda ya ke very calm, yana kallonta kamar baiga wani abin tashin hankali cikin abinda tagani dinba na kara tunzurata.

“Wow…. Da gaske? Da gaske baka san abinda zaka ce mun ba?”

Komawa ya yi cikin kujerar ya kwanta, yana karkato jikinshi ya zuba mata idanuwa.

“Hula na baki kigani, me yasa zaki bude mun wani abin daban? Na aike ki? Nace ki duba? Me kike so ince miki bayan ban saki duba mun waya ba?”

Hannu takai zata bude motar ta fita, yayi saurin rufe murafun motar gabaki daya.

“Ke kin isa ki fita kibar mun mota Hindu?”

Cikin idanuwa take kallon shi, kirjinta kamar zai bude.

“Ka bude mun mota in fita, bana son ganin ka.”

Wani irin kallo yake mata, dan yaga alamar nata rikicin wasa ne, bai aiketa ba, baice ta duba mishi waya ba, yana mamakin mata, idan kinsan ba zaki iya jurewa ba me yasa zaki duba tun daga farko?

“Wallahi zan baka mamaki, ka bude mun mota.”

Hindu ta fadi, dan yanda takeji komai zai iya faruwa, gara ya bude mata motar ta fita tayi kukanta ko zata samu saukin tukukin bakin cikin da take ji.

“Karki mun fada, karki fara cewa zaki mun fada. Ya kike so inyi? Hauka? Kince in daina tabaki, duk kokarin da nake yi ba kya gani?”

Sosai take kallon shi, mamaki da takaici duk sun hadar mata waje daya.

“Dan nace ka daina tabani shisa kake bin wasu matan? Abinda ka fada ya maka kama da uzuri? Ya maka kama da dalilin da zai saka yin abinda ka yi?”

Ta karasa maganar tana kokarin mayar da hawayen da suke cike taf da idanuwanta, cike da rikici shima yake kallonta yanzun.

“Idan ban bisu ba zaki bani?”

Sake jinjina murfin motar tayi dan ta fita, bata son ganin shi, ko kadan bata son ganin shi, amman a rufe yake, hannu ta mika da nufin ta dauki mukullin motar da yake jiki, ya damke hannunta yana saka dayan na shi ya cire mukullin motar ya saka a aljihun jeans din da yake jikin shi, sannan ya saki hannunta yana tsare ta da idanuwa.

“Karki gwada hakuri, kinga yanzun ke kika sa na tabaki, ki bari ki huce sai in bude miki ki fita. Ba zaki koma gidan mutane a haka ace na miki wani abu ba.”

Fuskarta ta rufe da hannuwanta, wasu hawaye masu dumi na zubo mata.

“Babe ki bari, ki daina kukan nan, kina sa ina jin ina son in rikeki in lallasheki, kuma ba kya so, ki daina kure hakurina, yanzun inbi wasu kice zaki ji haushi.”

Sosai yasan yana bin mata tun kafin su hadu, amman bashi da wannan jarabar haka sai bayan ya hadu da ita, rashin samunta yasa shi son kashe wutar da take kunna mishi da duk macen da ta tari gaban shi, amman a daddafe yake lallaba rayuwar shi, ita dince taki fahimtar shi, taki gane halin da yake ciki, gyara zaman shi yayi cikin motar, yana sauraren sautin kukanta, harta dago fuskarta, ruwan da yake cikin motar ya dauka ya bude yana mika mata, harar shi tayi da idanuwanta da sukayi ja.

“Yi hakuri, ki sha ruwa to dan Allah.”

Karba tayi tana shan ruwan, ya duba agogon shi, shidda harda arba’in.

“Are you calm? Kice mun idan na tafi ba zaki sake yin kuka ba.”

Shiru tayi ta kyale shi tana kauda kanta gefe, har lokacin kirjinta kamar an zuba garwashin wuta take ji.

“Babe… Kinsan a gajiye nake, kaina na ciwo wallahi, karki karamun, karki mun fushi. Ba laifina bane ba, bansan ya zanyi bane ba.”

Ya fadi yana wani irin sauke murya da ya kashe mata jiki, kallon shi tayi.

“Bana so, zuciyata na ciwo wallahi, dan Allah ka daina.”

Ta karasa maganar muryarta na karyewa, kai ya jinjina mata yana hade hannuwanshi waje daya.

“Karki mun fushi to, kinji.”

Kai ta jinjina mishi, tasan idan har tana so ta canza shi, dole sai tayi kokarin fahimtar shi.

“Na gode… Kinsan ina sonki ko?”

Kai ta sake daga mishi, kuma soyayyar nan da yake mata ita zatayi amfani da ita wajen kokarin canza shi, mukullin ya dauko daga aljihun shi yana bude mata murfin motar

“Baki ce kina sona ba.”

Ya fadi yana daga mata gira, murfin motar kawai ta bude tana ficewa, yau ba zai sami wannan na tunda laifi ya yi mata.

<< Mijin Novel 17Mijin Novel 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.