Skip to content

Mijin Novel | Babi Na Talatin Da Biyu

4
(4)

<< Previous

Wata irin mummunar dokawa zuciyar shi tayi ganin Hindu zaune akan kujerun da suka saba zama, a wajen da suka saba yin zance, amman bashi bane akan kujerar, wani ne zaune a inda ya saba zama, yana magana da Hindu, har tana mishi dariyar nan tata da yake ji a ko ina na jikin shi. Dakyar ya iya yin parking saboda ko gani bayayi sosai, yasan yana da kishi na fitar hankali, ba tun yanzun ba, akan ta yasan kishin shi ya wuce duk yanda kalamai zasu fassara, dan nan take zazzabi mai zafi ya saukar mishi, ko murfin motar bai rufe ba daya fita.

Karasawa yayi inda suke yana addu’a kar ya nuna ma Hindu yanda akwai wasu daga cikin halayen shi da ba zasu taba canzuwa ba. Tsaye yayi a kansu yana mayar da numfashi kamar wanda ya sha gudu

“Hindu waye wannan?”

Ya bukata yana kare mishi kallo, kafin ya tsayar da idanuwan shi da suke cike da tsantsar rikici a cikin nata. Idan zata saurari wasu ma baiga dalilin da zata kula irin mutumin da yake zaunen nan ba, in ba kawai so take zuciyar shi ta buga ta tarwatse ba. Duk da a shekaru bayajin zai girmi mutumin, idan ma bai fi Hamzan ba to zasu zo daya. Numfashi Hindu ta sauke tana dauke idanuwanta daga cikin na shi

“Bello ga Baban su Suhana.”

Ta fadi tana kallon mutumin da ta kira Bello, kafin ta kalli Hamza da fuskar shi har tayi wani ja saboda kishi tace,

“Hamza ga Bello, shine wanda zan aura.”

Bude baki yayi da nufin yin magana, yaji wani yawu ya sarqe shi, yana fara tari babu kakkautawa, sosai yake kokawa da numfashin shi, ko bai sarqe ba, maganganun Hindu barazana ne da rayuwar shi. Murmushi Bello yayi.

“Bari in barku kuyi magana. Zamuyi waya ko?”

Kai Hindu ta jinjina mishi, kafin ya mike, Hamza da har lokacin tari yake ya samu dakyar yana furta.

“Kar… Karka kirata wallahi.”

Murmushin dai Bello ya sakeyi, Hamza na bin shi da wani irin mugun kallo harya karasa ya hau machine din shi da Samari sukafi yiwa lakabi da roba-roba yana ficewa daga gidan. A nutse Hindu take kallon Hamza da tarin shi ya tsagaita.

“Ka zauna…”

Wani irin kallo yake binta da shi, tabbas ta sami tabin hankali idan tana tunanin zai dora mazaunan shi inda Bello ya tashi.

“Ba zan zauna ba, Hindu kasheni kike so kiyi? Bana baki hakuri ba? Ya kike so inyi? Titi kike so in bi ina taro mutane dan su tayani baki hakuri ko meye?”

Ya karasa maganar idanuwan shi har sun sake launi saboda bacin rai.

“Sau nawa zance maka na hakura? Sau nawa kake so in fada maka komai ya wuce a wajena?”

Hindu ta fadi a gajiye, dan tagaji da shi, tagaji da nacin shi. Ba wai babu masu sonta bane ba, har mamakin yanda ake Mazan da suke mata tayin aure suke gane ita din bazawara ce takeyi wasu lokuttan, tunda shigarta sam bata nuna bata da aure ba. Amman sai taji zuciyarta na dokawa, a tare dasu take hango Hamza, wani lokaci har a yanayin tsayuwa, agogon da suke sanye da shi, tsadaddiyar mota ko wayoyi, sai take ganin kamar su din ma ba zasu banbanta da shi ta fannin halaye ba. Tana bautar kasa suka hadu da Bello, shima gida yazo wajen Baba, sai daga baya tasan likitan dabbobi ne, aikin da yake a karkashin Baba kamar abinda ake kira da side job ne a turance.

Har sukayi musayar lamba tana mamakin kanta, tana jinjina cewar da hannunta ta dauki lamba ta bawa Bello, saboda takowanne fanni shi din ba kalar mijin da ta taba hangowa kanta saurare bane ba. Baya matsa mata da yawan zuwa, sai ta hada satika biyu ma bata gan shi ba. Tun maganar farko ya sanar mata yana da mata da yara har guda biyu. Kusan zata ce abinda ya fara burgeta da Bello shine kusancin da yake da shi da iyalan shi. Yanda baya gajiya da bata labarin Arifa da Khalid, tasan kalar abin, tasan irin farin cikin, dan itama duk wanda zai saurari labarin su Suhana idan zata wuni tana bayarwa abin fada baya kare mata.

Soyayyar da kowanne yake yiwa yaran shi ta fara saka shakuwa a tsakanin su, kafin a hankali, cikin watanni shidda take fahimtar kyawawan halayen Bello, tana kuma mamakin yanda da duk rana yake samun waje a rayuwar ta. Bata san inda tafiyar su zata kai ba, Bello baya mata gaggawa, tasan niyyar shi, ya bata dukkan lokacin da take bukata dan ta yanke hukunci, kuma yana nuna mata ba zai riketa da laifi ba a kowanne irin decision ta yanke.

“Idan alakar mu bata wuce abokantaka ba haka Allah ya kadarta Hindu…”

Ya fada mata da take ce mishi tana jin wani iri kar tazo bata aure shi ba, dan sam bata shiryama aure yanzun ba, tafi so ta yaye yaranta, duk da yanzun ma ba damuwa sukayi ba sosai, Suhana ce da fitinarta daman. Amman alamu sun nuna Amna zata yaye kanta ko bata cireta ba. Kuma akwai tarin abubuwan da take hangowa, bai fito ya fada mata ba, maganar bata hadasu kai tsaye ba, da dabara Bello yake nuna mata zai rike mata yaranta, abinda ko auren shi tayi ba zai taba yiwuwa ba. Su Baba ma ba zasu bari ba tasani, balle kuma Hamza da take da tabbacin za ai yakin duniya kafin yabar yaran shi suyi agolanci a gidan wani.

Har ranta bawai ta raina samun Bello ba, amman ba zai iya rike su ba. Yanzun a tsorace take da halin maza, tabon guda daya take da shi, amman ya firgitata da sauran ma, alkawurran Bello iya kunnuwanta suke tsayawa, batama bari sun karasa zuciyarta ba ballantana yai disappointing dinta. Daga auren Hamza ta daina daga burinta akan komai na lamarin duniya, bata saka rai ba ballantana ya dameta idan bata samu ba, yaune karo na farko da ta furta shi zata aura, dan ta huta da nacin Hamza, amman zuciyar ta cike take da tsoron kalaman da tayi din

“Idan kin hakura me yasa ba zamu koma auren mu ba? Me yasa ba zaki taimaka mun yaran mu su rayu tare da mu biyu ba? Ki kalli irin mazan da kike kulawa Hindu, da gaske baki hakura ba”

Numfashi ta sauke mai nauyin gaske, ya katse mata tunanin da takeyi

“Nace ka zauna kaki”

Kai ya girgiza mata

“Ni bazan zauna inda ya tashi ba.”

Yai maganar kamannin shi da Suhana na fitowa sosai, duk da ba magana takeyi ba ita, amman abu da yawa zatayi da fuska sai Hindu taga kamar shine a gabanta, sai dai yanzun tana tunanin shi batare da komai ba, yana fado mata a rai bataji ciwo a kirjinta ba sam, da gaske komai ya wuce mata, tabon ne kadai shaidar da take da shi na abubuwan da suka faru. Mikewa tayi daga kan tata kujerar tana tura ma Hamza, taja wadda Bello ya tashi da nufin ta zauna, cikin zafin nama ya fisge kujerar daga hannunta

“Saboda baki da hankali ke saiki zauna? Inda ya tashi? Inda wani kato da ba muharramin ki ba ya zauna kema zaki zauna?”

Har ranta bataso dariya ta kubce mata ba, kawai ta taho ne batasan ya zatayi ta tsayar da ita ba, saboda dariya Hamzan ya bata sosai, zama yayi a kujerar yana kallon Hindu da take mishi dariya kamar akwai wani abin nishadi a maganar da yayi, kafin itama ta gyara kujerarta tana komawa ta zauna

“Na zama mahaukaci ko? Duk hakan bai isheki ba, shisa kike magana da Bello.”

Yanda ya kara fadar Bellon ya sata yin murmushi, karfin halin shi ba zai daina bata mamaki ba, muryar shi ya saukar sosai saboda yanda kirjin shi yake zafi.

“Dan Allah karki kara kula shi, nace zan rike ki da kyau, ba zan sake ba. Wallahi rabona da wata mace tun ranar da kika bar gidana…Allah ne shaida ina duk kokarin da zan iya, kiyi hakuri dan Allah…”

Kai take girgiza mishi saboda yanda ya saukar da murya sai taji wani irin tausayin shi ya cika mata zuciya.

“Idan baki duba halin da nake ciki ba, ki duba su Amna, nayiwa Anna magana tace ba zasu baki hakuri ba, tace sai dai in baki hakuri da kaina… Ni kuma kinki ki saurare ni.”

Kirjin shi kamar ana hura wuta a ciki haka yake ji.

“Ba haka bane ba.”

Hindu ta fadi, bayason abinda yakeji a muryarta sam.

“Nace maka kom…”

Kasa karasawa tayi ganin Hamza ya sauka daga kan kujerar da yake, bai damu da farin yadi bane a jikin shi ya saka gwiwoyin shi a kasa yana kallon ta da idanuwan shi da yake nuna mata alamar kuka zai iyayi kowanne lokaci.

“Inalillahi…. Hamza menene haka? Dan Allah ka tashi… Ka tashi kar wani ya fito.”

Cewar Hindu cikin tashin hankali, shekara daya da kusan rabi da suka wuce, Hamza a durkushe a gabanta yana bata hakuri abune da take mafarki, ido rufe harma a bude. Abune da zata so dauka ta dora a Instagram dan duniya taga kalar mijin da take aure, mijine da zai iya saka gwiwoyin shi a kasa ya bata hakuri, ba kamar mazaje yan gargajiya da girman kai zai yanasu ko da furta kalaman ne balle kuma har su tsugunna. Yanzun kuwa abin tsoro ya bata, ko kadan bai burgeta ba, saboda ji takeyi yana son amfani da duk wata hanya wajen tursasa zuciyarta ta koma auren shi, auren shi da yaki fahimtar ya gama fita daga kanta tas.

“Dan Allah ka tashi…”

Ta fadi, amman kai Hamza ya girgiza mata, kome zai dauke shi, indai zata hakura zaiyi, idan ma ca tayi ya kwanta zai kwanta. Koma meye dan karta sake kula Bello, zuciyar shi ba zata iya dauka ba.

“Kice kin hakura, kice zaki bani wata damar Hindu, ko baki koma yanzun ba a sake daura auren mu, wallahi zan jiraki komin tsayin lokacin da zaki dauka har sai kin yarda da na canza, abune mai wahala a wajena, amman zan jure, zan jure komai banda rabani da ke…”

Hamza yake fadi yana wani irin fitar da numfashi kamar zai shide mata.

“Ni me laifi ne, na yarda, dan Allah karkiyi mun wannan horon, karki horani ta hanyar rabani dake…”

Hawayene cike da idanuwanta, ba zata jure ganin shi haka ba, wannan bashi bane Hamzan da ta sani.

“Ki sake bani dama, ba zanyi wasa da ita ba.”

Kai take girgiza mishi, hawayenta na zubowa, sunayi kamar sun wanke mishi cikin idanuwanta ne yana ganin abinda takeji tar a cikin su.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Ya iya furtawa, kujerar daya sauka daga kai ya dafa yana mikewa da kyar ya koma ya zauna saboda nauyin da jikin shi yayi, da gaske zazzabi yakeyi, dan iskar yammaci likis data kada shi yanzun har cikin ranshi yajita, tsikar jikin shi na mikewa

“Hindu da gaske ba zaki koma ba? Da gaske kin daina so na?”

Kai ta daga mishi a hankali, yanayin na fitowa daga zuciyarta, wasu hawayen da tayi saurin gogewa suna zubo mata, batajin komai a tare da shi sai tsoro, sai tsoron komawa a auren shi duk yanda alamu suke nuna mata ya canza.

“Dan Allah kice mun ban rasaki kenan ba…”

Hamza ya fadi da nauyin da zuciyar shi tayi a muryar shi, yanajin kamar an watsa mishi ruwan kankara, idan ita soyayyar da tayi mishi zata iya bacewa shi yanzun yake jin tata, yanzun yake jin wani irin sonta kamar zai mutu idan tabar shi, kai ya jinjina.

“Ok… Kece kadai kika daina sona, ni ina son ki, zai ishe mu, zan zauna da ke ko bakya son wallahi, dan Allah ki zauna dani tunda ni ina son ki.”

Hawayen ta sake sharewa da gefen yatsunta.

“Hamza…”

Ta kira muryarta na karyewa, tana so ya dawo hayyacin shi ya yarda da kaddarar su ko da ba haka zuciyar shi take so ba, amman kai yake girgiza mata, bayaso ya yarda ta subuce mishi kenan, bayaso tace ba zata koma ma auren shi ba, wa zata aura to? Hasaso ta da Bello kadai na barazana da bugun zuciyar shi, mutuwa zaiyi tabbas idan ta auri wani, idan ya zauna da sanin tana rayuwa da wani da bashi ba, da gaske mutuwa zaiyi, kishinta ne zai fara kashe shi in har zafin son da yake mata bai kashe shi ba yanzun

“Zaki bani yara na, wallahi ba zaki tafar mun gidan wani da yara ba.”

Hamza ya fadi cike da neman rikici, so yake ya tsoratata ko zata hakura ta dawo mishi, tunda yasan yanda take son su Suhana kamar ranta, idan tasan ba dashi kadai zabinta zai rabata ba har su watakila ta dawo hayyacinta, tagane komama auren shine kawai zabin da ya fiye mata, muryarta a karye, wasu hawayen na sake zubo mata tace.

“Na sani, bance zanje ko ina da su ba daman.”

Cikin sabon tashin hankali Hamza yake kallonta, dan bayajin tana cikin hankalinta, abinda yayi mata yai muni har hakane da ta kasa yafe mishi.

“Ki aureni ki koreni cikin dare to, ki rama ko zaki hakura…’

Mikewa tayi da dan murmushi duk da kukan da takeyi, saboda har an fara kiraye-kirayen sallar Magriba. Bai kirata ba, da idanuwa yake binta harta bace mishi, ta falon Mama tabi, sai da ta taka cikin falon sannan kafafuwanta suka zabi suki daukarta, dan a tsakiyar kitchen din ta zauna tana sakin wani irin gunjin kuka da ya fito tun daga ruhinta, batama san Mama tana cikin ba saida ta taji ta kamata, a jikin Mama ta kwanta tana kuka kamar ranta zai fita

“Hindu me ya faru?”

Mama take tambaya cikin tashin hankali, da kyar Hindu ta iya dago da kanta, tana saka hannuwanta tana goge fuskarta, da kyar take jan numfashi.

“Nasan zan bashi yaran shi, na sani Mama, tun ranar da nasan ba zan koma gidan shi ba nasani… Amman zuciyata ciwo take, zuciyata kamar zata fashe Mamaa…”

Hindu ta karasa idanuwanta cike taf da hawaye.

“Oh Allah na…”

Mama ta furta tausayin Hindun na cika mata zuciya, tana tausaya musu su duka.

“Da kinyi hakuri kin koma dakin ki Hindu, ko dan yaran da kinyi hakuri.”

Kallon Mama take da bayananne tsoro, hawayenta na zuba, duk yanda zata so yi musu bayanin emotional abuse din da ta jure a gidan Hamza ba zasu gane ba, haukane kawai ba tayi ba, da kasar waje suke ta tabbata zata dauki wasu shekaru tana ganin likitan kwakwalwa saboda abinda ta hadiya a gidan Hamza, ko bata sami miji ba sai Hamza zata hakura ta karashe rayuwarta a haka.

“Mama ba zan iya ba, wallahi bashi su Suhana bai kai tunanin zama da shi firgici ba.”

Kai kawai Mama ta jinjina mata, domin ita uwa ce, ta fahimci Hindu, abinda zaisa uwa hakura da rayuwa da yaranta ba kadan bane ba, ba komai daya faru a zaman su da Hamza ta fada musu ba, iya abinda suka sani ne, sai wanda suka fahimta daga yanda ta dage ba zata koma gidan shi ba.

“Allah yasa hakan shine alkhairin ku, Allah yai miki canji kinji ko? Kiyi hakuri… Kiyi hakuri.”

Mama take fadi tana kama hannun Hindun da ta mike. Kan kujera ta mayar da ita, da kanta ta dibo ruwa ta bata tasha, sannan ta mike.

“Ki bari ki natsu, kinga Antynki ko bata nuna ba zaki sakata cikin damuwa.”

Kai Hindu ta jinjina.

“Sallah zanyi Mama.”

Ta furta tana wucewa bandakin da yake cikin falon. Gara tayi sallar Magriba ko addu’a tayi watakila ta samu saukin abinda takeji, in tama yi karatun Qur’ani zuciyarta zatayi sanyi.

*****

A daddafe ya samu yai sallar Magriba, yasan Allah ne kawai ya kai shi gidan su lafiya. A karo na farko a rayuwar shi da yaji yana bukatar Anna fiye da kowanne lokaci, saboda ciwon da zuciyar shi takeyi. Yana shiga gida bai sameta a falo ba, dakinta ya wuce, tana zaune akan darduma inda tayi sallar Magriba, yanda ya shiga babu ko sallama yai mata tsaye a kai yasa ta fadin,

“Lafiya? Me ya faru?”

Kai Hamza ya girgiza, kirjin shi kamar zai bude gida biyu zuciyar shi ta fado.

“Kai mun magana…”

Anna ta fadi, dan wuyanta harya fara gajiya, ta daga shi tana kallon fuskar Hamzan da yake tsaye har lokacin. Tsugunnawa ya yi.

“Kirjina ciwo yake Ann… Zuciyata na ciwo. Anna mutuwa zanyi.”

Ya karasa maganar yana wani irin sauke numfashi, cikin tashin hankali Anna take kallon shi.

“Wai me yake faruwa.”

Ya kai wasu dakika yana kokawa da numfashin shi kafin da kyar ya iya furta

“Ba zata dawo ba… Anna zata auri wani wai.”

Ya karasa maganar yanajin hawaye cike taf a idanuwan shi, sauki yake nema da baisan ta inda zai fara samun shi ba. Cike da tausayin dan nata Anna tace.

“Kayi hakuri Hamza, haka taku kaddarar ta zo.”

Dan daga mata kafadu yayi, a karo na farko yana kasa fahimtar kaddara.

“Nayi laifi nasani Anna, me yasa ba zata yafe mun ba, me zan cewa su Suhana idan suka nemi dalilin da yasa bana tare da Maman su?”

Wani irin kallo Anna takeyi mishi da yake kara karyar mishi da zuciya, batasan me zatace mishi ba, bata da abinda zata fada mishi ya samu saukin koma meye yake ji

“Kayi hakuri…”

Kai ya girgiza ma Anna, wasu irin hawaye masu zafin gaske na zubar mishi. Kallon shi dai takeyi kaddarar shi na dawainiya da ita, yau danta ne da ko lokacin kuruciyar shi sai kayi da gaske zakaga hawaye a idanuwan shi, shine zaune a gabanta yana kuka da idanuwan shi saboda mace, ita kam da Hindu zata saurareta yau da taje da kanta ta roketa tayi hakuri, ta dawo su karasa rayuwar su tare, duk da tasan Appa ba zai bari ba, ta gwada mishi maganar yace ba zasu shiga ba, su kyale yarinyar tunda ita kadai tasan abinda ta hadiya a zama dashi.

Sosai ya zauna kan kafet din yana dora kan shi a kafafuwan Anna, kuka yake yau kamar karamin yaro, yafi mintina sha biyar kafin ya dago da idanuwan shi da suka rine yana furta.

“Yarana zan karba…”

Kai ta jinjina mishi, ita ma ba zata bari jikokinta su zauna a wani gida ba, sai dai in Hindun bata tashi yin wani auren ba, amman in dai aure zatayi zasu karbesu, a dinga kai mata su tana gani. Tunda dai zuri’a ta hada, zumunci ba zai yanke ba. Mikewa Hamza yayi yana shiga bandaki ya bude famfo yana tarar ruwa a tafukan hannuwan shi ya wanke fuskar shi da su, dago kai yayi yana kallon fuskar shi ta cikin mudubin bandakin. A karo na biyu da ya zubar da hawayen shi kan Hindu, yau kam ya hakura.

“Idan nan kaddara ta kawo mu shikenan Hindu, na hakura, watakila karshen kaddarar mu ya hada da yanda soyayyar ki zatayi ajalina.”

Yai maganar a zuciyar shi yana fitowa, ganin ko sallama baiyi mata ba yana shirin ficewa daga dakin yasa Anna fadin,

“Ina kuma zakaje? Ba zaka tsaya kaci abincin dare ba.”

Ko juyawa baiyi ba ya girgiza mata kai yana ficewa, kallon shi tayi, a ranta tana mishi addu’ar tsari harya karasa gida lafiya. Dan taga bashi da nutsuwar kirki a tare da shi. Yana fita daga gidan ya shiga mota gidan Fodio ya nufa. Ya shiga ciki da sallama, bawai gida bane ba zai iya wucewa ba, kawai bayason zama shi kadai ne a irin wannan yanayin da zuciyar shi take ciki, temptation din ya sha wani abu zai dame shi, shekara daya da barin shi, ba zai warware abinda yasha matukar wahala da bari ba saboda bacin ran kwana daya.

Yana kallon yanda Fodio yake fama, da taimakon asibiti da komai sai yayi kwanaki baya bacci da dare, sai dai da rana ya dan samu ko na awa biyu, suna kallon shi kullum yana kokawa da depression din da yake zuwa tattare da insomnia, amman bai karaya ba, shiriyar da ta zo mishi mai karfi ce, kuma sosai yake karawa Hamza kwarin gwiwa. Yanzun ma shi kadai ya samu zaune yana danne-danne da waya, ga tv a kunne, dan raba idanuwan shi da wayar Fodio yayi suna gaisawa da Hamzan daya sami kujera ya zauna

“Ba zata dawo ba…”

Ya furta a hankali, yana saka Fodio ajiye wayar tashi hadi da kallon shi.

“Da gaske?”

Kai Hamza ya jinjina mishi, sosai kirjin shi yake zafi.

“Fodio na hakura…kawai ina tunanin abinda zan cewa su Amna ne.”

Numfashi Fodio ya sauke, maganar batai mishi dadi ba, sai dai ba kowanne shafi da kaddara ta bude maka bane yake maka dadin fuskanta, duk da wasu lokuttan yanda shafin zai kare idan ka nutsu sai kaga shine mafi alkhairi da abinda kai din kaso da farko.

“Ka fada musu gaskiya idan sun tambaya…”

Kallon shi Hamza yake cike da rashin fahimta.

“Ka fada musu kaddarar da ta hadaka da Maman su itace ta sake sakawa zaman ku ba mai nisa bane ba…ka tabbata baka basu dalilin yin dana sanin fitowa daga jikin ka ba, zasu fahimta…”

Kai Hamza ya jinjina mishi, watakila soyayyar Hindu ba zatayi ajalin shi ba, watakila ya samu karfin zuciyar jurewa kaddarar su.

“Allah Ka bani aron rayuwa mai tsayi da albarka tare da yarana. Allah Ka fini sanin dalilin rabani da Mamansu, Allah ka bani juriya.”

Hamza ya fadi a zuciyar shi yana lumshe idanuwan shi, yana karbar ciwon da zuciyar shi takeyi dan ba zai iya guje mishi ba, idan jinya zai kwanta gara ya fara tun da wuri ko zai samu ya warke, amman tunanin Hindu da wani ko da ba Bello bane zuciyar shi na tafasa.

“Katon kai gare shi…”

Ya furta batare daya bude idanuwan shi ba.

“Waye da katon kai?”

Fodio ya bukata cikin rashin fahimta, yana saka Hamza bude idanuwan shi.

“Wallahi Fodio in ka gan shi kamar mai tallar doya… Shine Hindu take cemun zata aure shi.”

Wata irin dariya Fodio ya kwashe da ita duk da Hamzan ya bashi tausayi.

“Kishi ne yake damun ka ba wani abu ba.”

Cewar Fodio, kai Hamza ya girgiza mishi.

“Allah mummuna ne, ko ba komai idan na tuna na fishi kyau zai dinga mun dadi.”

Dariya kawai Fodio yakeyi, surutan Hamza ko da gaskiya tattare suke da zafin kishi, idan hakan zai sama mishi sauki Fodio din zai biye mishi, a ranshi dai addu’ar zabin alkhairi yake ma su Hamzan, duk yanda suka so suga zaman Hamza da Hindu ya gyaru sun hada da addu’ar alkhairi, har sadaka yayi, sosai suke musu addu’a shi da su AbdulHafiz. Yana kuma da yakinin yanda zaman nasu ya kare shine alkhairi. Tunda suna numfashi, yanzun kaddara ta fara bude musu shafuka mabanbanta…!

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×