Skip to content

Mijin Novel | Babi Na Uku

5
(4)

<< Previous

Kamar yanda Zahra Tabi’u, marubuciyar Mai Tafiya, cikin alkalamin ta a rubutun Farin wata:

“Kowane labarin duniya yana da tushe. Kowanne yana da mafari. Me ke nan? Wani abu da ya faru har ya zama sanadin wanzuwar jirkitattun  al’amura.”

Labarin Hindu ya fara a shekarar 2012 a lokacin tana aji biyar a sakandire. Tun bayan haihuwar ta, tun ranar da Baba ya dora idabuwan shi a kanta tana a cikin shawul, aka mika mishi ita dan yayi mata hudu ba, Anty zatace taga wani yanayi a fuskar shi da bata taba gani ba a game da sauran yaran nashi, ba wanda ta haifa tare dashi ba kawai, har wanda suka haifa da abokiyar zamanta, dan tana wajen duk yawanci sanda ake bashi yaran yayi musu huduba. A lokacin da yake rike da Hindu zaka iya rantsewa ita ce yarinya ta farko da Allah ya nufe shi da samu bayan tsayin shekaru, kuma a lokacin yana da yara bakwai kafin ita. Ya kuma kara samun yara hudu bayan ita din, jimlar yara goma sha biyu da Allah ya albarkace shi da samu.

Amman ya riketa a jikin shi ko bayan daya gama yi mata huduba, daga ranar kuma har zuwa yanzun zaka gane yanda wajen Hindu daban yake a zuciyar Baba. Akwai dalilin da yasa Malamai da yawa suka karkata ra’ayin su da kafa hujjoji masu karfi akan cewa iyaye su boye yaron da yafi soyuwa a ransu, karsu nuna a fili saboda hakan zai iya saka kishi a zukatan sauran yan uwan su, idan da kaddarar shaidan ya darsa musu wani tunani zasu iya cutar da juna ma. Sai dai a gidan Baba hakan bai faru ba, saboda bokon shi ta rinjayi ilimin addinin shi ba kadan ba. Duk yanda Anty taso ta nusar dashi akan yanda yake nuna kaunar Hindu karara sai ya nuna mata bacin ran shi, ya nuna mata shi duka yaran shi yana kaunar su.

Da dukkan gaskiyar shi yakan yi maganar, yana kaunar yaran shi, zai iya komai a kan su, yana kula dasu, yana kare musu duk wani hakki har wanda bai rataya a wuyan shi ba indai zasuyi farin ciki. Da iyayen su mata basa tsaye akan tarbiyar su, tabbas da yaran gidan Baba zasu taso cikin wata irin sangarta taban mamaki, dan shi in ba Hindu aka taba ba, baisan ya kwabi yaro ba, wannan itace kalar fahimtar da Baba yayiwa kaunar yara. Ita kanta Hindu tana girma tana kara fahimtar yanda ita dince raunin Baba, ko da ana so a roke shi abinda ba ayi tunanin zaiyi ba, ita din ake turawa, da ta shagwabe fuska tace

“Babana”

Kamar yanda take kiran shi, ko wacce bukata zata furta bayan kiran sunan nashi, dai-dai kun ranaku ne yake iya ce mata a’a shima badan zuciyar shi taso hakan ba. Ba zaka ce babu kishin kalar kaunar da Baba yake ma Hindu a tsakanin yan uwanta ba, dan lokutta da dama a fuskokin su zaka gani. Sai dai su kansu akwai wata irin kauna da shakuwar zaman yau da gobe hadi da karfin jini ta saka musu akan junan su, shisa kishin kaunar da Baba yake mata din baya damun su na tsayin lokaci, zasu nuna a lokacin da hakan ya faru, ita kuma tayi musu dariya dan har ranta take jin Baban nata, idan kaunar shi a gareta daban ce, tana da yakinin kaunar da take mishi daban ce da ta sauran yan uwan ta.

Bawai dan Anty bata da halaye masu nagarta ba, ba kuma dan batajin mahafiyarta har karkashin zuciyarta ba, haka kawai ta taso da son zama kamar Baba, ta taka matakin karatu kamar shi, taso yaranta kamar yanda Baba yake son su, dukkan rayuwarta tana kwatanta ta akan son zama kamar mahaifin nata.

Yau tun da akaje daukosu daga makarantar su ta Zamani College dake nan garin Kaduna, Hindu take jin ranta kal, farin ciki takeyi tunda satin ya kama, bawai dan kasancewar yau din ranar alhamis ba, ranakun da take matukar so fiye da kowanne a cikin satika shine Alhamis da juma’a, dan babu islamiyya, zata samu tayi kallo yanda ranta yake so. Musamman idan Allah ya dora ta akan Yaa Zaid ya ara mata kwanfutar shi kirar laptop tayi kallon a ciki. Akwai faifan cd din data siya har biyu, daya fina-finan indiya ne da baka raba rayuwarta da kallon su, dayan kuma korea ne da bata jima da fara kallon fina-finansu ba, ta kuma sami sunyi dai-dai da ra’ayinta.

Zuwa yanzun tana da tabbas duk kudaden da zata samu wajen siyo su zasu kare. Tana son soyayya, tun bata kai haka ba take hasaso kalar mijin da take so, ballantana yanzun da take kan ganiyar shekarun yan matancin ta. Duk da kullum saita canza ma mijin da take ra,ayi siffa ko launi a cikin kanta, amman dai a kowanne yanayi, kyakkyawa ne na kwatance. Sai dai alhamis din yau ba murnar kallo bace kawai a ranta, harda murnar Baba zai cika mata alkawarin wayar da yayi mata. Kusan duk kawayenta a makarantar boko suna da wayoyin hannu, shekarar da tazo ana yayin Nokia daga kan Express zuwa C2 da kuma X2 da take tashe tsakanin yan mata, samari harma da masu aure, idan kuma akazo wayoyin Nokia na symbian series da bakowanne bama yasan darajarsu balle yagane dadin amfanin da suke dashi da yanda a lokacin suka shallake ma duk wani samfuri na wayar hannu da kamfanin Nokia suka kaddamar.

Saboda haka dai-dai kun mutane ne suke da ita. Ita kam Hindu ba wannan tunanin bane a ranta, waya take so ta mallaka kawai. Yanda yan ajin su ke hirar manhajar sada zumunta ta 2go bata so a barta a baya. Dan haka ta addabi baba cewar suna duba aikin gida da za’a basu a makaranta a wayar ta google. Kuma yana da kyau ace ta mallaki tata saboda jarabawar da karshe da zata shirya su shiga aji shidda da take gabato musu. Kuma ta fada mishi idan ya hado mata da memory card har karatun Qur’ani kamalalle za’a tura mata, zata dinga kunnawa tana sauraro saboda haddar da sukeyi a islamiya. Duk da Baba yaso sai Hindun ta gama sakandire, dan shine tsarin shi ga matan na rike waya.

Mazan kuwa kusan yanzun da wayar ta yawaita duk ya siya musu, har Khalil da Junior suna da yan Nokia dinsu kananu. Ita ce mace Babba a gidan tunda Amna da Asma’u yanzun suke tasowa, wayar hannu ita ce karshen abinda yake ran su. Sosai Khadija take mata yanga da Nokia Express dinta, tana kara kwadaita mata son wayar, kawarta Zainab da duka suke kira da Biebee, makociyar su ce, tare suka taso tun yarinta, duk da ba makarantar bokon su daya ba, amman islamiya daya suke zuwa, itama satin daya wuce Babanta ya sai mata X2 yar yayi.

Naci da rokon da ta dinga yiwa Baba ne yasa shi amincewa. Yace har sim da memory duk zai hado mata dashi, ran alhamis yace mata, tana kuma lissafe da ranakun. Yau a sama take jinta tana yawo kan gajimaren farin ciki. Har fina-finai ma sai ta dinga bayarwa ana tura mata a memory dinta, kallo zata dinga yi a nutse babu takura, bamai zuwa falo yai mata iko da rimat. Sosai take cikin nishadin da ko fuskarta kagani saika fahimta. Suna shiga gida kai tsaye bangaren su ta wuce tana shigewa dakin su ita da Asma. Kai tsaye bandaki ta wuce dan babu wutar lantarki, ga wani irin zafi da taji ya saukar mata, ruwa ta watsa tunda tayi sallah a makaranta, tana fitowa ta saka riga da zani na Atamfa tukunna ta fice daga dakin zuwa kitchen dan ta zuba abinci.

Duk da batajin yunwa, cikinta a cike take jin shi da murna, tuwon shinkafa ne da miyar taushe da tasha lawashin albasa tana ta zuba kamshi, ga wadataccen naman rago da ya kara taimaka mata wajen yin kyau. Rabin malamala ta zuba tana saka miya a kai ta dauka ta fito falo ta zauna, bata nemi Anty ba dan tasan bacci take a irin wannan lokacin, ko da zata tashi sai zuwa la’asar. Asma kuma tana da tabbacin tana bangaren Mama. Ta fara cin abincin kenan Khadija da suke kira da Khadee ta shigo falon, duk da yanda suke furta nasu sunan a gayance Kha din daban sai Dee din da take fitowa a gajarce D, in wasu suka kira sai suna gyara musu da cewar ba haka bane ba.

“Banza ashe kin dawo, yau Baba zai kawo miki wayarki ko?”

Khadee ta fadi tana samun waje kan kujerar da Hindu take ta zauna, kai Hindun ta daga mata dan ta cika bakinta da tuwo, hadiyewa tayi kafin tace

“Eh yau yace in shaa Allah… Zaki tura mun 2go”

Dan karamin tsaki Khadee taja

“Ke ba zakiyi addu’a ba ya siyo miki mai yin WhatsApp, yanzun shi ake yayi ba wani 2go ba”

Dan turo baki Hindu tayi, duk da yanayin ya zame mata jiki, fuskarta kusan ko da yaushe a shagwabe take, da harda muryarta kafin tsokanar yan makaranta yasa tayi kokarin gyarawa, amman duk da haka, magana kawai zatayi ka fahimci tsantsar sangarta a tattare da ita

“Ni dai ina son 2go”

Ta fadi, dan kuwa shi yan ajinsu suke labari kullum, suna hirar rooms, Nigeria room1, Kaduna room1, da Comedy room1. Duk da shi Comedy room din monitan ajinsu taji yana maganar shi, akwai masu account biyu ma a ajin, da garin Kaduna da kuma garin Kano, dan ance sosai ake buga dirama a BUK room1. Tama ji kawarta Yasmin na fadin zata bude, dan rannan wasu yan Kano su B2 sun shigo Kaduna room din sunyi fadan turanci da akafi sani da brawl da su Curious su Zeegee, dan daga baya fadan ya koma BUK room, taso ta kalli yanda aka kare.

Labarai irin wannan su suke kara kwadaita ma Hindu 2go din, ita whatsapp din bawani burgeta yake ba, dan taji Khadija tace yafi rashin hayaniya. Saima kana da lambar mutum tukunna zaka gan shi. A kunnuwan Hindu hakan ba abu bane da zaiyi mata dadi, tunda duk kawayenta sunfi yin 2go, bata da waya amman duk wata dirama da za’ayi suna bata labari, da yanda suke fadar turancin samarin Kaduna room1 tasan dole akwai hadaddu a cikin su. Zata je itama a gabza da ita, a santa a Kaduna room1 dan duk wanda yai mata ba barin shi zatayi ba, da alama Yasmin yar kallo take zama dan ta cika tsoro, takan ce mata tana gudun tayi turanci su Qwaro ko Curious suja mata layi alamar batayi dai-dai ba.

“Ke kika sani, meye a 2go banda hayaniya, da shirme, kowa sai yace zai turo maka friend request, aita maka shirmen banza da wofi”

Cewar Khadee dan sam bata san hayaniya, duk gidan ita da Zaid sun fita daban. Gara ita Khadee ma ana hira da ita idan taso, Zaid kuwa zuciyar shi a wuya take kullum, da wahala ayi hirar mintina goma bai watsama wani zagi ba, dan zaka fadi wani abin da bai mishi ba sam-sam. Kusan a yayyen maza yan gidan sunfi shakkar shi, yana musu dariya, amman hakan baya hana shi hukunta su idan bukatar hakan ta taso. Karasa cinye tuwon ta Hindu tayi ta dauke plate din takai kitchen ta wanko hannunta, dai-dai lokacin da suka kawo wutar da ta sakata wani ihun murna tana fitowa daga kitchen din da gudu.

“Allah ya sambada muku albarka yan nepa.”

Yar dariya Khadee tayi.

“Kafin anjima ki tsine musu in sun dauke ba.”

Kayan kallon dakin Hindu ta kunna tana dauko remote ta dawo ta zauna, kafin su gama kawowa tace ma Khadee.

“Anya akwai wanda suka fi yan Nepa shan tsinuwa a kasar nan?”

Kai Khadee ta girgiza mata.

“Bayin Allah, ko yan sanda basu kaisu shan zagi ba, duk in suka kawo wuta suka dauke fa sai kinji an zage su, ko kwana nawa wutar zatayi.”

Dariya sukayi su biyun, suna mayar da hankalin su kan tv din, Hindu na canza channel din zuwa ta indiya sun saka film din Ishq, duk da ta kalla, tana son film din har lokacin, saboda soyayyar da aka shimfida a cikin shi, ita ta saka Ajay ya kara burgeta matuqa, daman yanayin miskilancin shi ya mata, haka take son namiji karya cika dariya ta rashin dalili, abu kadan ya bude hakora cike da rashin aji. Kallon sukeyi suna dan taba hira kan film din, kafin a kira sallar la’asar data tashe su, Khadee na wucewa bangaren su, ita kuma Hindu tayi daki abinta.

*****

Da yake sun saba cin abincin dare tare da Baba, yamma nayi suka tattaru bangaren Mama kasancewar ranar ta fada girkinta. Su biyar ne a dakin. Huzaifa, Khadee, Jafar, Hindatu sai Junior da ya shigo da sallama yana zama gefen jafar da ya lafe cikin kujera mai mazaunin mutum biyu da wayar shi makale a kunne, da alama ya gama nutsuwa cikin wayar da yakeyi, banda murmushi babu abinda yakeyi, muryar shi ma can kasa, Junior din ma da yake kusa dashi ba zaice ga abinda yake fada ba.

Muhsin ne ya fito daga bangaren su, da sai daga baya aka gina musu, boys quarters din da yake bayan gidan ne Baba ya rushe aka sake ginin ya hade bangaren da cikin gida, a ra’ayin shi bai yarda shi yana cikin gida yara dan maza ne suna can wani bangare kofa ta raba su ba, duk da a ko ina suke cikin gidan ba zai hana abinda Allah ya kadarta samun su ba. Amman zasu iya fita yawon rashin dalili sukai dare a waje bazai sani ba, ba lallai maigadi ya fada mishi ba. Idan anan ciki suke, dole zai san karfe nawa suka dawo, in fitar dare ce zasuyi sai da sanin shi, hakan yafi mishi kwanciyar hankali.

Kallon Jafar yayi da yake ta zabga murmushi tukunna ya kalli Huzaifa yana fadin

“Shi kuma wannan me yake yi?”

Cike da rashin kulawa Huzaifa yace

“Waya”

Girgiza kai Muhsin yayi dan yana da tabbacin da budurwa Jafar din yake waya, rigimar yaran na bashi mamaki, idan yana da yarinya kamar su Jafar na zuwa wajenta, da kan shi zai fito yace ya turo manya. Yasan daga nan bazai sake ganin shi ba, yara basu da ko sisi wai soyayya.

“Jafar da muryarka na sauka haka kake mana hayagaga.”

Cewar Muhsin din cikin jimami, dariya Huzaifa yayi,

“Me yasa zai kashe maka murya?”

Dan rausayar da kai Muhsin din yayi yana samun kujera ya zauna.

“Hakane kuma…”

Ganin zasu dame shi yasa Jafar mikewa har lokacin da wayar a kunnen shi dan yabar musu falon, yana kan fadin,

“Jiya ko baccin kirki banyi ba ina tunanin ki.”

Suna cin karo da Mama da tayi karaf tace,

“Kaji shegiyar karya, ba ina jin Babanku harya dawo masallaci ba yana faman tashin ka…”

Da gudu Jafar din ya wuce dan yasan Mama zata ballo mishi aiki, gabaki dayan su dariya suke, Mama kam kai take jinjinawa.

“Haka kuke samun yan mata kuyita gillara musu karya, sai kiji yaro yana fadin ya kasa cin abinci, bayan ya share faranti biyu yana neman kari.”

Sosai Huzaifa yake dariya.

“Mama banda ni fa.”

Hararar shi ta yi.

“Kai din? Allah dai ya shiryaku kawai.”

Ta karasa maganar tana shigewa kitchen ta dauki kofi ta koma daki abinta. Hira suke dan tabawa kafin ayi kiran sallar magriba, mazan su wuce masallaci, su Hindu duk anan bangaren Mama sukai sallah. Kafin Baba ya shigo da sallamar da suka amsa su dukan su, dan sauran mazan ma sun dawo sanin Baban na gab da shigowa, murmushi ne najin dadin ganin yaran nashi bayyane a fuskar shi da take cike da dattako, kasumbar da furfura ta fara fitowa ta kara mishi wani kwarjini naban mamaki, kallo daya zakaiwa Baba kasan dan boko ne, ga gayu ya samu wajen zama tattare dashi. Yakan saka manya da kananun kaya duk randa ra’ayin hakan ya motsa mishi.

Su duka sukayi mishi sannu da zuwa, ya amsa yana dorawa da.

“Hindu”

Murmushi Hindu take ganin ledar dake hannun Baban, cike da shagwarta ta amsa,

“Babana”

Karamin tsaki Zaid ya yi.

“Wai Baba na, kamar ke kadai kike da Baban”

Shagwabe fuska Hindu tayi sosai, dan Zaid ne shiya hanata furta wani abin, ko a gaban Baba ne zai iya kwadeta sai dai yayi mishi fada, ledar hannun shi Baba ya mika mata yana dorawa da

“Ga alkawarin ki.”

Cikin hanzari ta mike tasa hannuwa biyu tana karba hadi dayin wani ihun murya tana rungume Baban kamar zata karya shi.

“Nagode Baba na, Allah ya kara arziqi ya kare mana kai.”

Wani karamin tsakin Zaid yaja yana takaicin yanda Hindu ke abubuwa kamar wata yar shekara hudu, ita kuwa bata ma bi takan shi ba, Baba ya gama mata komai yau. Nan Baba yabar su yana shigewa ciki, Muhsin ya kalli Hindu da fadin,

“Zo muga wayar Yar Baban ta.”

Kamar yanda yakan kirata in yanajin tsokana, da sauri ta karasa wajen shi.

“Babban Yaya ai kaine ma zaka bude min daga kwalin.”

Hadi da mika mishi ledar, ya karba ta fito da Nokia C2 dal a kwalinta. Murmushi yakeyi, da gaske Hindun yar Baban ta ce, dan ko shi wayar hannun shi bata kai tsadar wannan ba, shiya bude ya saka mata sim din da memory ya mika mata. Murna fal ranta, inda Huzaifa yake ta karasa

“Yaa Huzaifa kaga”

Karba yayi, wayar ta mishi kyau yana fadin

“Ma shaa Allah, aikam idan na fita zan siyo miki kati. Sai a kiyaye banda abinda bai kamata ba, nasan ban isa in hanaki chatting ba, ki dai saka Allah a duk wani abu da zakiyi da wayar nan Hindu…”

Huzaifa ya fadi yana kallon sauran kafin ya dora da.

“Ku dukan ku ma, wayar nan da kuke rainawa zata iya halakar da ku Wallahi, kuyi chatting dinku, bashida wani aibu in dai kuka tsarkake zuciyar ku, duk da hanya ce ta shagala da ta same mu, yana dauke hankali sosai daga muhimman abubuwa, dan Allah ku kula”

Kai Hindu ta jinjina mishi, nasihar tashi na zauna mata.

“In shaa Allah Yaya.”

Wayar ya mika mata, ta karasa tana nuna ma sauran, kafin ta wuce bangaren su ta nuna ma Anty, fadan da Huzaifa yayi mata shi Anty ta sake maya mata. Caji ta saka tana komawa suka ci abincin dare, ko da akayi isha’i anan sukayi. Baba yace jikin shi ya mishi nauyi a gajiye yake, Junior yaja musu sallah, shine ustazun gidan, ya kusan hada haddar shi ta Qur’ani, yaro ne da kallo daya zakai mishi ka fahimci nutsuwar da take tattare dashi da annurin fuskar shi wanda hasken karatun Qur’ani ne kawai yake zaunar dashi.

Huzaifa ana idar da sallah ya fita, baifi mintina sha biyar ba ya dawo, ya mika ma Hindu katin dari biyu, sosai tayi mishi godiya tana jan hannun Khadee suka nufi bangaren su

“Dan Allah kizo ki turamun…”

Hindu ta fadi, nan suka zauna suka kunna wayar, Khadee ta tayata suka saita komai. Tukunna ta fice daga dakin, kan gado Hindu ta koma, tana jin ranta kal, ta siyi go credits daman, shiga 2go din tayi tana fara saka user name din duka kawayenta tayi adding dinsu. Biebee ta fara ansa mata tana turo sakon

“Kawata kin shigo gari, kice Baba ya miki komai yau”

Dariya Hindu tayi a bayyane suna fara hira da Biebee din. Kafin ta shiga Kaduna room1 din, yar kallo ta zama saboda tayi magana tafi sha biyar babu wanda ya kalli ko inda take, abin daya kona mata rai sosai. Dawowa private tayi tana fadama Biebee data turo mata kawunan dariya

“Banza baki ga star dinki a Novice take ba, waye zai kula ki? Haka zaki ci gaba da dagewa har adan fara ganin ki”

Jikinta Hindu taji yadan yi sanyi da maganar Biebee din, da tayi mata sallama dan tace bacci take ji zata kwanta. Fita daga room din Khadee zatayi taga an turo mata friend request. Da kamar ba zata amsaba ganin Elias aka rubuta a jiki. Sai kuma ta amsa, sannan ta fita daga room din. Sallama yayi mata da tasa ta duba profile din shi, zuciyarta na dokawa saboda ganin hoton nashi, ya hadu iya haduwa, bashi da hasken fata, amman yana da kyau, ga kasumba luf-luf kwance a fuskar shi, yasha shadda ruwan kasa da hula. Da alama a zaune yake da mota a bayan shi, sosai yayi ma Hindu kyau.

Sallamar shi ta amsa suna gaisawa, yake ce mata sunanta yayi mishi dadi da harshen hausa, dan tunda suka fara hirar da turanci suke yi.

“Kana jin Hausa daman?”

Ta tambaya, tana saka shi turo mata dariya.

“Sunana Illiyas Abdallah. Bahaushe ne ni, ko dan kinga Elias, haka abokai suke kirana.”

Dakuna fuska Hindu tayi, sam sunan nashi bai mata ba, dan ita tafi son sunan yan gayu. Meye wani Iliya?

“Yayi kyau, sai da safe.”

Ta fadi tana sauka daga kan 2go din batare da ta jira amsar shi ba, WhatsApp din da bata bude ba, ta shiga ta saka lambarta tana yin register. Tukunna ta sauka da kudirin da taje makaranta da safe zata amshi lambobin yan ajin su, itama su san ta faso gari yanzun. Danne-danne ta shiga yi na son ganin komai na wayar. Da Asma ta shigo dakin dakyar ta bata wayar tagani na wasu yan mintina. Har wajen sha daya na dare tayi kuri tana danna waya. Jin motsin Anty yasa ta tura wayar karkashin pilo zuciyarta nayin tsalle har cikin makoshin ta saboda tsoro.

Dan Anty ta mata kashedi banda chatting din dare, tasan kuma tsaf zata iya dinga karbe wayar duk dare inta kula Hindun bata ji maganar da tayi mata ba, Anty na sakar musu fuska yanda ya kamata, amman suna bala’in shakkarta, bata da wasa ta fannoni da yawa. Baccin da bata shirya ba ya dauketa cike da mafarkin wayar tata.

*****

Cikin sati biyu yanayin surutun da Hindu take da kuma tsoma baki a cikin duk wani fada da zata gani yasa aka fara ganeta a Kaduna room1 harma wanda ake ji dasu a group din kanyi mata magana, zuwa lokacin request take samu kaca-kaca. Takan amsa wasu, wasu kuma bata amsawa, tunda wanda take so suyi mata request din su Curious ne da su Rugi, amman taqi samu, dan ance mata Rugi ma zaku iya shekara kuna hira a room bai maka request ba. Gashi turancin shi na tafiya da ita.

Duk a tarkacen da tayi babu wanda suke magana dashi sosai kamar Elias, wata irin shakuwa sukai a satika biyu, har sun koma da hirar su ta WhatsApp, yakan kirata da daddare ta shiga bandaki ta amsa a tsorace kar Asma ta farka taji ta, tasan bakar shaida irin tata, tsaf zata kwashe ta gayawa Anty, tayi mata sanadin wayar gabaki daya. Hankalinta a tashe takanyi wayar na mintina ta kashe. Dan dai taga hotunan Elias din, ya tuttura mata, ya kuma yi mata kyau sosai, dan ya iya daukar wanka.

Cikin wata daya kuwa, kaf kawayenta babu wanda baisan labarin Elias ba, wasu suna dan ganin shi a room, amman da yake bai cika magana ba, ba wani sanin shi akayi ba. Sosai sukan yi hira, wani lokaci tana assignment suna taba hirar su. Lokaci daya Elias ya nuna ma Hindu yana so su hadu, hankalinta ya tashi, amman bata so ta nuna mishi ita din ba babbar yarinya bace kamar yanda ya dauketa. Ranar juma’a da daddare yai mata maganar, washegari Asabar tace ma Anty zata shiga gidansu Biebee dan suyi assignment din Nahwu, tunda anyi hutun kwana uku a islamiyar, daya cikin Malaman su ya rasu, sai ranar Monday za’a koma.

Anty bata hanata ba, gidansu Biebee dasu kusan an zama yan uwa, tana shiga suka gaisa da Hajiya mahaifiyar Biebee din Hindu tajata suka shiga daki

“Ke wajen ki nazo fa, Elias naso mu hadu, wallahi na rasa yanda zanyi”

Wani irin kallo Biebee takeyi mata da yasa ta fadin

“Dan Allah Bie, ki fadamun me ya kamata inyi”

Gyara zama Biebee tayi

“Me ya kamata kiyi banda ki fada mishi ba’a barinki zance a gida, sai kin gama secondary, in zai iya jira ya jira. In bazai jira ba yai gaba”

Dafe kai Hindu tayi, Biebee ba zata gane ba, matsalarta daya da ita kenan, komai a tsaye takeyin shi babu wata kwana, yanzun ma dorawa Biebee tayi da fadin

“Ni nace miki baiyi mun bama, hoton shi duka a waje daya, kuma yanayin pattern daya, me yasa ba zai turo miki hoton shi a tsaye ba? Ke ni bai mun ba”

Langabar da kai Hindu tayi

“Bie ki rufamun asiri dan girman Allah, so kike yaje room yana fada musu yarinya ce ni, ina tunanin da mu hadu wani wajen… Sai muje dake kice ma Anty zamuje dubiya… In dake ne ba zata hana ba”

Tunda Hindu ta fara magana Biebee take girgiza mata kai

“Ku hadu ina? Idan dan yankar kai ne fa? Hindu ki rufama kanki asiri”

Hannunta Hindu ta kamo tana fadin

“Bie mana…. Dan Allah kimun wannan abin daya. Ki taimaki rayuwata”

Hannunta Biebee ta fisge tana mikewa, bada ita za ayi wannan rashin hankalin ba, ko bakomai tana jin tsoro, yanzun duniyar babu gaskiya. Shisa inda duk tace zataje bata biyawa wani guri, tana tsoron kar taje wani abu ya sameta, ko babu mutuwa akwai hatsari, akwai rashin lafiya da take dirar maka babu sallama. Idan tace zataje tudun wada a gida, sai ta wuce Malali, wani abin ya faru, ko mutuwa haka iyayenta zasu kasance cikin tunanin me ya kaita malali har karshen rayuwar su. Tunani irin wannan yana hanata abubuwa da dama.

Amman Allah yayiwa Hindu wata baiwa ta samun abinda take so a wajen mutane, bai dauketa mintina talatin ta shawo kan Biebee ba, amman da sharadin inda sukace zasuje nan zasu. In yaso sai Elias din ya same su a bakin hanya su gaisa su wuce. Hakan yayi ma Hindu, hira suka dan karayi tana tashi ta wuce gida ta fadama Elias gobe zasu hadu, amman zata fada mishi ko karfe nawa da safe, sukayi hira dashi tukunna ta kwanta tana jin yanda zuciyarta take lugude, gani take kamar Anty zata shigo dakin ta dauki wayar in tayi bacci, tashi tayi zaune ta dauki wayar tana goge chats dinsu duka, ta goge kiran wayar sannan hankalinta yadan kwanta. Ta samu bacci ya kwasheta.

Next >>

How many stars will you give this story?

Click to rate it!

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Share the story on social media.

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.