Skip to content
Part 52 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Tayi murmushi ta ce share hawayenki ki wattsake babu wani abinda zai je ya yi har ya kusa da kusan-kusan abinda yayi miki, ko yake yi miki a yanzu. Na ce Gambo kenan, ta ce eh ai gaskiya ce kawai mai ita kuma yana iya yiwa kanshi hukunci.

Shi mutum bai cin zamaninshi ya hana wani cin nashi zamanin, ai kin ci naki Maman Umamatu kina a kai tunda me akai da maza? Don haka itama barta ta ci irin nata saboda naki zamanin babu tsawo ya kuma yi karko mai kyau.

Amma menene? Me zai je yayi sabo? Wane da ne jemage bai gani ba? Ai sai na ranar mutuwarsa ke ce fa aka bashi ke yana da shekaru talatin kina da shatara, kin san muhimmancin shekaru talatin wurin da namiji kuwa shekaru ne na kammala cikar halittarsa.

Shekaru ne na ganiyar karfi, shekaru ne na abubuwa masu yawa da ba zai yiwu in yi ta lissafo miki su ba, sannan a wancan lokacin bai da wani nauyi kece ke kadai, bai da wani uzuri sai naki, bai da wata bukata sai taki, bai da wani abinda yake so sai ke gaba daya lokacinshi naki ne, gabadaya hidimarsa taki ce.

Ba yanzu da ya riga ya gama mallakar hankalinshi nauyin Jama’a da kuma abubuwa masu yawa suka hau kanshi ban da haka kina ma da wasu darajojin a wurinshi ke kadai ce zai yi surukata da uwarki irin surukutar da yake yi dani ba zai sake yiwa uwar wata hakan ba.

Saboda ya riga ya girma sannan ban da wadannan duka sai kuma ki ka yi sa’a ki ka zama kece ki ka zamo mishi uwar Umamatu, ki ka sake zuwa ki ka haifan mishi Baba Yahya.

Ko wadannan biyun kawai ki ka tsaya akai ai kinsan kin haifi abin da yake so, to balle gasu Zainab, ga Khadija ga Fatima, don haka kar ki yarda ki mance ni’ imomin da aka yi miki kije kina sa ido kan abin da bai taka kara ya karya ba.

Kullum ki tasa al’amarin ya’yanki a gaba kar ki zalunci dan kowa balle sakaiya ta taba miki yayanki, nayi maza na ce to Gambo.

Kullum kalaman Gambo suna kwantar min da hankali su sanyaya min zuciyata su kara min son ya’yana da ganin darajar su, ba wai son ‘ya’ya irin na rashin kwaba ba, a’a son ‘ya’ya irin na hakura da abinda ka ke so ko yin abin da baka so saboda su saboda rayuwarsu ta gaba ta inganta.

Kalaman Innata ne suka kara sanya ni na yarda na gane na kara hakuri na kara kyautatawa mijinam, ita kuwa matarshi na maida ita tanfar yar uwa bani da wata ita balle in je ina sha’awar zaluntarta, musamman kuma da yake nafi kowa sanin mijin nawa Dr. Ado Sulaiman zai yi min kawaici ya ji kunyata ne ya kuma yi ta girmamani kan abin da yaga ina yi na adalci, amma ba zai taba yarda da zalunci ba.

Rannan da daddare muna hira da Gambo a waya saboda hirar tamu ta zama ka’ida yanzu kullum sai mun yi, na ce mata ai dazu na fita Gambo.

Tayi maza ta tambaye ni, ina ki ka je? Na ce robar nan naje na cire, Gambo tayi dariya ta ce kishi dai ya motsa kenan, na ce ba kishi ba ne Gambo, na dai gaji ne kawai, ta ce ai shi din ne dai.

Na numfasa na ce mata ni wanne yafi ne cikin biyun nan Gambo? Tunda ke su duka biyun kin san yadda suke kin zo kin samu an kuma zo an same ki?

Tayi murmushyi ta ce, ni kam a wurina ai dace ne kawai.

Tunda ita rayuwar gaba dayanta sa’a ne, na tuna mata da kalaman Mama a da cewar da take yi ‘ya’yanta ba za suje gidan kowa ba zuwa za’ayi á same su, tayi dariya ta ce ba gashi ba, kuma da aka zo aka same sun sai aka kore su saboda sun kasa yin hakuri? Na ce haka ne, ta ce ai babu mai cin ribar rayuwa sai yayi hakuri, na sake cewa haka ne.

Mama tayi ta zuba ido tana kasa kunne ko zata ji wata rigima ta tashi tsakanina da Ado, shiru babu wata matsala, saboda yana matukar jin kunyata da ganin girmana a dalilin na yarda da shawarar da ya bani na in dan yi mishi kawaici da kuma kara.

Sai kuma hankalinta yayi matukar tashi ta rinka fadin maganganu wannan aure da aka yi ai ba aure ba ne an kawo ‘yar mutane an ajiye a gida ana cutar ta.

Rannan ina daga falona na ganta ta fito kan keken guragunta, tana tura tayoyinshi da hannunta kofar dakin amarya taie ta tsaya saboda ba za ta iya tura shi yı shiga ba. Ni yarinyar nan ana baki abinci kuwa?

Ban ji abinda Bilkisu ta ce mata ba na dai ga kawai ta gyada kai ta ce au to, ta juya ta tafi. Ban san yadda aka yi ba, daga tsayuwar bakin kofa tayi magana sai kuma abu ya dawo in ta zo bakin kofar ta tsaya sai ta kira Balkin ta tura ta su shiga ciki.

Ni kam ko a jikina saboda da na gaya wa Gambo ma abin da Maman take yi dariya tayi ta ce ai babu abu mai dadi a rayuwa irin ka rayu kana addini kana kuma yarda da kaddara na ce haka ne Gambo.

Rannan sai kawai aka yi kacibis tsakanin Mama da Ado a dakin amarya, shi zai shiga ita kuma za ta fito ina jin shi yana fadin a’a-a’a Mama, ai kin ji sauki tunda ki ka iya fitowa daga dakin ki ki ka zo har nan ai shi kenan magana ta kare.

Mama tayi maza ta ce, a’a wane sauki? In ban da karfin hali don in zo in duba wannan yarinyar abincin da ake bata ne nake ganin kamar ba ya isanta, ya ce eh wannan duk ai alamar samun lafiyarki ce tunda gashi har kina iya shiga harkar da ba taki ba ce.

Don haka sai ki shirya za ki koma dakinki, Mama ta soma kuka tana bashi hakuri, ya ce a’a ai ba za ki kasa zaman lafiya a naki gidan ki zo nima ki bata min nawa ba.

Dama kwanaki an kira ni a gidan su aka yi min wasu maganganun da nayi zaton da hannunkii a ciki, tun a lokacin na gaya wa Mallam Haruna cewar ni ban saba da irin wadannan maganganun ba. Ban iya yin irin wannan surutun ba na kuma gayawa ita Balkin cewar in aka sake kirana a gidansu kan wasu maganganun da ban san da su ba zata koma gidansu. To ashe ke ce Mama, don haka zan kira Baba an jima in gaya mishi yasa ayi miki fentin dakinki ga ki nan zuwa, ai ba rabuwa kuka yi ba.

Na dai kyale ki a nan din ne kawai don na gane ba kya son zaman can din amma ba zai zama dalilin da kuma za ki nemi kulla min fitina a cikin iyalina ba.

Mama tayi kuka har ta gaji ta bai wa Ado hakuri har taji babu dadi ya ce a’a Mama ki koma dakinki kawai ita mace ai bata da wani wurin da ya fiye mata dakin mijinta daraja in kina da matsala kawai ga sabuwar waya nan na saya miki ki kira ni ki gaya min, nima kullum zan rinka kiranki muna gaisawa.

A haka Ado ya kammala mata shiri ya kuma sani wai ni da yara muyi mata rakiya na ce mishi to, muka je muka kwana muka dawo. Sai bayan dawowar nawa ne naji labarin wa duk wanda yazo sai ta gaya mishi cewar ni nasa Ado ya kore ta.

Bayan kuma ita din ita ce tayi sanadin aurena da shi, amma a yau na shiga tsakaninta da dan uwanta na raba su.

Ni kam tunda nayi sa’a Mama ta yi wa dan uwanta abinda ya tattara ta ya maida ita inda dama mazauninta yake, sai naji sakat na samu sa’ ida, na gane ashe ba kishiya ce ma babbar matsalata ba a rayuwa Mamace to na rabu da ita shi kenan zance ya kare.

*****

Shekaru biyar ne yau tunda Dr. Ado Sulaiman ya yi min amaryarshi ta farko Hajiya Bilkisu bayan ita ya kara bayan wannan ma ya sake karawa.

Don saukin ma su din basu zauna ba can ta bare musu suka watse, kenan in ana sabawa to na saba a yanzu ma naji yana cewa da wata akan hanya.

Duk da har yanzu na kasa daina kishin mijin nawa, ban cika jin zafin shi sosai ba, saboda ya riga ya samu daukaka mafi yawancin aurenshi na baya-bayan ba shi yake nema ba, yana zaman zaman shi ne kawai za ki ji an ce Dr. ga wata tsuleliya an baka.

Shi kuwa sai ya ce wai mutumin kirki baya maida hannun kyauta baya, don haka nake yi mishi sassauci mai yawa.

Amma wai duk da hakan da nake yi in sun fitan sai ka ji su da iyayensu dama Mama suna ta yada zance cewar wai din ni nake hana shi zama da amaren nashi saboda fin karfin da nayi mishi.

Iyakar sa’ar da nayi ita ce ni dashi da akwai fahimtar juna mai yawa a tsakaninmu, a duk lokacin da ya ji ana yada irin wadannan maganganun zaunar dani yake yi ya rarrashe ni.

Rabu da su Humairah, toshe kunnuwanki kawai kiyi kamar ba ki ji su ba, ni kam ai nasan kaina na kuma san ki nasan kishi mai tsananin zafi da na fuskanta a wurinki, ai wanda ki ka nuna ne akan auren Bilkisu.

To ba gashi kin yi mata adalcin da ku ke zaune lafiya tana kuma ganin girmanki ba? Surukuta ce irin ta iyayensu ban saba da ita ba surukuta irin ta zamani wace babu kawaici ko kara a cikinta.

Kuma babu kunya balle nuna sanin ya kamata, na riga na saba da surukuta irin Gambo wacce komai suruki yayi wa ‘yarta ba za ta daga ido ta kala ba, sai dai in shi da kanshi ya yi tunani.

Kunyar kanshi ya kama shi kullum tsakaninta da yarta nuni ne na alheri bi mijinki, kyautata mishi, kiyi mishi biyayya, saboda girman hakkinshi da yake kanki yawa ne da shi.

Bisa wannan dalilin ne yasa har yanzu dai ni da Bilkisun mu biyun ne dai a gidan na Dr. ‘ya’yanta biyu dukan su maza, Sulaimañ da Adam. Nima na kara daya da kyar bayan nasha kafirar wahalar da na kubuta da kyar saboda matsalar da na samu da mahaifar tawa.

A dalilin kakaba robar nasara da nàyi don haka ina da mai sunan Babana Sirajo wanda Sulaiman ya girma da shekara daya shima ya girmi Adam da shekara daya. To har yanzu dai itama uwar tasu shuru ban sani ba ko itama ta yarda da hikimar ta maigidan ne na bin tsarin iyali don a samu wadataccen lokacin kulawa da juna.

A wannan lokacin gaba daya ‘yanmatan gidan nawa su Umamatu, Nusaiba, Hindatu da Aisha suna dakunan mazajensu har da rabo a tsakani saboda Ado yayi musu auren ne da sha bakwai-bakwaj.

Sai dai har yanzu suna can suna ci gaba da karatunsu a Jami’o’i daban-daban, shima kuma mai daukan nauyin, shima Baba Yahya yana kasar Malesia ya tafi karatun digirin shi na farko kan aikin zane.

Sai su Zainab, Khadija da Fatima sune suke Makarantar secondary ta Marigayiya Hajiya Maryam Babangida, don haka a gidan a yanzu Sulaiman ne kawai sai Sirajo da Adam.

Wadanda guda biyun farkon Sulaiman da Sirajo a wurina suke duk inda zani kuma tare dasu nake zuwa, Adam ne a wurin uwarshi.

Gonata tayi matukar bunkasa, don’ haka a yanzu a shekarun da nake da su guda arba’in mafi yawañcin al’amurana da lokutana da farin cikina kan tafi ne kan abin da ya shafi ‘ya’yana, ‘yan uwana, iyayèna, gonata, hidimomina, .kwalliyata, karatuna da har yanzu ban daina ba, da wasu abubuwan da suka danginci hakan.

Aure-auren da Ado ya tsunduma yi a shekarun bayan nan sun kara fahimtar dani cewar a shekarun mace na girmanta tana bukatar farin cikin abubuwa da yawa da nasarorinsu kafin tata nasarar ta tabbata.

Babba daga ciki kuwa shi ne nasarar ‘ya’yana ta kintsuwarsu, su kama hanya ta zama mutanen kirki, wannan shi ne gaba da komai a wurinta, sabanin lokacin kuruciyarta da zaman lafiyarta da mijinta kawai ke gamsar da ita har kullum rayuwar Mama kan zame min darasi saboda masu hikima.

Sai suka ce wanda duk bai hankalta ya lura da abinda ya samu wani ya zamo mishi darasi ba, to wani zai lura da abinda shi zai same shi ya hankalta dashi ya koyi darasin rayuwa.

Rugujewar rayuwar Mama ta rasa farin ciki, kwata-kwata mijinta ya subuce mata, gidan da take gadara dashi ya fi karfinta ya faru ne a dalilin rugujewar al’amarin ya’yanta har a yau kuma a haka take a zaman hakuri a zaman babu yadda za’ ayi tunda har yanzu ita da Babana dai gasu nan ne kàwai har yanzu babu wanda yasan inda babu yake.

Har yanzun su Anti Sha’awa basu wuce zawarci ba, tunda tayi aure yáfi a kirga, Suwaiba sai kwanan nan ta samu wani Dattijo ya aure ta bayan ‘bukin su Umamatu daga Giyade matanshi uku ita ce ta hudu.

Tana can Giyade a gidan kauye ga iyali wannan dalili yasa ban taba yarda na sa kaina cikin ‘damuwar aure-auren Ado ba, balle in rinka daga ido ina ganin abinda yake yi da ‘yan kananan matanshi, har in je ina neman in takurawa wani ko Wata.

Da na daga ido ni’imomin da aka yi min nake kalla in tuna rayuwata da ta mahaifiyata a lokacin kuruciyata, rayuwar rashin yanci, Kaskanci, wulakanci, rayuwar da uwarmu zaune kawai take tanfar ba matar gida ba ce.

Mu ma ‘ya’yanta ba a dauke mu wasu ‘ya’ya ba, sai gashi a yau duk ya wuce, ina tuna wannan sai in yi ta yiwa Ubangiji godiya, in na ga ma kamar Ado zai yi wani bare-baren da zai bata min ko ya daga min hankali a kan wata.

Tattara shi nake yi in sa shi a gefe bana Kallon abin da yake sai shi da kanshi yaga kamar abin nashi zai wuce makadi da rawa sai ka ganshi yayi maza ya dawo yana fadin ni me nayi wa yarinyar nan ne nake ganin kamar sha min kamshi take yi tana wani shasshare ni?

Ya rinka lallami kenan da kalamai masu dadi, na fa je wajen Gambo tana gaishe ki ko Umamatu ta ce kaza, don ya nemo dalilin da hira zai yi nisa, sannan a hakan sai in ji itama matar gidan da ake ganin zaman lafiyar tamu tana korafin ai ba shi da wani zance sai nata in ma labari ya zauna zai, baki to ba ki sanin yanda ake yi sai kiji labarin ya koma nata da iyayenta ko da ‘ya’yanta.

A haka sai na kara fahimtar cewar shi dai namiji mai mata biyu ko uku a tsakani kawai yake, bai cika samun gwaninta mai dorewa wurin guda daya ba, in dai har akan adalcin ya tsaya ba karkata yayi ba.

Don haka yana da kyau wata tafi wata hakuri, da kuma dan saurara mishi don a samu saukin al’amura kan haka na sake yankewa kaina hukuncin kara hakuri da mijin nawa a kowane lokaci a kuma kowane hali.

Rannan mun ziyarci kasar Malesia ni da shi don kaiwa Baba Yahya ziyara, mun ziyarce shi, a makaranta ya kuma biyo mu masaukinmu don yi mana hira suna zaune shi Babanshi kan kujera guda daya irin zaman da suka saba yi tun yana dan yaro dan karami.

Ado yana rungume da kafadar shi yayin da shi kuma ya kwanto da nashi kan kafadar Baban a haka suke hirarsu, ni kam ina can a gefe kan wata kujerar ni kadai kallonsu kawai nake ina tunani gaba daya Baba Yahya ya sauya ya zama tanfar ba shi ba.

Ga wanda yayi shekaru bai ganshi ba, zai yi wuya a yau ya ganshi ya gane shi. Gaba daya ya zube kibar tashi babu ita, tebar shi ta zama kamar ba a taba yin ta ya zama wani -dan dogon saurayi dan sirirn wankan tarwada, kamanannin nashi na yanzu sun fi kama da kamannin Kawu Ado a farkon zuwanshi gidanmu.

Hira sosai suka yi da Babanshi tattaunawa suka yi tayi kan karatun nashi da kuma bambancin nomanmu na kasashen Africa da kuma na kasashen da suka samu ci gaban zamani, tunda shima Baba Yahya aikin gonar yazo karantawa.

Sai da yaga dare ya fara nisa sannan yayi mana sallama da nufin komawa cikin makaranta in da yake zaune.

Ado ya mike ya tsaya yana kallona bari in raka shi cikin makarantar in dawo na ce mishi to a dawo lafiya.

Ba mu baro kasar Malesia ba sai da muka kai ziyara wasu manyan gonaki da Baba Yahya ya ba shi shawarar ziyara saboda itama Malesia tana cikin kasashe da Gwamnatocinsu ke bayar da muhimmanci kan aikin gona.

Mun dawo gida babu dadewa muka nufi Bakori saboda saukan ruwan saman da aka samu da ya gamsar da noma na soma shukan wannan shekara.

Wata sabuwar gonar Ado ya bude a can ta noman masara zalla wacce ba zai yiwu in tsaya kwatanta girmanta ba, a bisa tsarin da aka shirya kuma za a rinka noma masarar ne sau biyu maimakon sau daya.

Ina tsaye tare da ‘ya’yana Sulaiman da Sirajo muna kallon aikin da ake yi Sirajo ya wage baki da karfi yana hamma. Na kalli Sulaiman da ke rike da hannun Bala na ce mishi dubi irin hammar da kaninka ke yi saboda baka koya mishi ladabin hamma ba.

Yayi maza ya kalli Sirajo ya ce mishi, kai ba haka ake yi ba in zaka yi hamma rufe baki ake yi don kar shedan la’ananne ya shiga bakin in da hannun dama zaka rufe sai kasa tafin hannu in kuma da hannun hagu ne sai kasa bayan hannu.

Ado ya Zubaida yaron ido yana kallonshi cikin murmushi yayin da Bala ke kallon shi yana fadin ashe Babangidan Malami ne, da kuwa har naji Umahumah tana fadin wai zata zo ta kwashe ku a gaban Goggo don ta lura shagwabarku tayi yawa saboda wai ba irin tarbiyar da aka yi mata ake yi muku ba.

Ado ya kyalkyale da dariya ni kam cikin zuciyata tunani nake yi na ranar da Ado ya kawo min Bala da Hamza a matsayin ‘yan almajiraina gaskiyar da Bala ya riki Ado da ita, tayi dalilin da ya so shi ya sanya shi karatun boko.

Bayan yayi haddar Alkur’ani har daga baya ma ya bashi diyarshi Umamatu bayan ga mutane da yawa ‘ya’yan manya shi kam Ado ya ce ai babu wani babban da ya fiye mishi Bala tunda makarancin Alkur’ani ne kuma mai gaskiya ne.

A zuciyata na sake fadin babu abin da tafi yawa babba a lokacin da yake zaune da na kasa dashi illa adalci don bai san abin da gòbe zata haifar ba.

Kallon Baban na sakeyi cikin natsuwa na ce mishi Bala, yayi maza ya amsa cikin natsuwa da nuna ladabi ya ce min na’am, na ce mishi yanzu a irin wannan aikin da kuke yi a gonakinku kuna da wani-shiri da kuke yi na taimakon kananan manomna?

Cikin ladabi Bala ya ce min ba wannan ne asalin taimakon da kananan manoma ke bukata ba Goggo saboda injinan da muke amfani da su wajen yin kaftu, kunya da shuka injina ne da suke karawa manomi kashe kudade masu yawa a gonarshi saboda suna tono kasa tun daga can cikinta. Ita kuma kasar wannan da muke takawa tafi kowacce kasa danko da kuma sinadarin da amfani ke bukata, shi karamin manomi yafi bukatar shanun garma, muna kuma bada su bisa farashi mai rangwame har ma mu daga kafa muyi lamuni matukar mun san za’a biya mu muna bada taki bisa farashin da Gwamnati take bayarwa.

Haka nan da akwai kungiya da gonarmu ke jagoranta da take karbanwa kananan manoma rancen da babu ruwa a ciki.

Ado ya galla min harara alamar nuna takaicin shi a zahiri ya ce kai ke ka surukutarki ba irin ta Gambo ba ce jeka wurin aikinka kaga abinda suke yi ka ji Engineer Bala yayi min sallama ya tafi.

Yana barin wurin na kallo Ado na ce mishi tausayin kananan manoma nake ji Dr. jaruman manoma irin su, Baba Tanimu wadanda jaruntakar rayuwarsu ke faraway kan gona guda daya babu wani ci gaban da suke samu.

Ado ya ce ch, Humairah ai kin san duk wani abinda ilimi zai yi aiki a cikinshi to kuwa za ki tarar da banbanci mai yawa tsakaninshi da abin da karfi ne kawai jagoranshi.

Na ce to in kuwa haka ne Kawu ai yana da kyau kuyi ta janyo hankalin masu ilimin mu na arewacin kasar nan da su dawo su tsunduma sosai cikin harkar noma tunda nikam a wurina banga sana’ar da ta fita riba ba, musamman a wannan lokacin da u Jama’ar arewa ke cikin halin da muke ciki.

Muke fuskantar abinda muke fuskanta, muke kuma ganin abinda muke gani, gaba daya arewarmu ta zama tanfar ba ita ce arewar da iyayenmu ke bamu labarinta ba ita da shugabanninta.

A yau mun zama komai na koma baya namu ne rashin kishin kai namu ne, rashin aikin yi ma namu, talauci ma nau, rashin ilimima namu, rashin mafadi ma namu rashin hadin kai namu, rashin tsaro ma namu, rashin zaman lafiya…

Ado ya katse ni ta hanyar fadin komai haka ne Humaira, sannan da za’a kama aikin gonan gadan-gadan fa da kin ga anyi magana mafi yawancin matsalolin namu kamar talauci da rashin aikin yi wadannan guda biyun kuma in da za ayi maganinsu.

To da sun isa su zama sanadin da za’a sau saukin fitintinu da tashin-tashina, musamman ma da yake ita arewa ai ta taba yi an gani, an taba yin lokacin da kasar nan gaba dayanta ta dogara kacokan kan tattalin arzikin da ake samu a arewa wanda Noma ne.

Cikin natsuwa na ce haka fa aka ce kawai Kawu ya dan yi tsaki nuna alamar tsananin damuwarshi da bacin ranshi kan sakacin damu da kanmu ne muka yi wa kanmu da kuma saki na dafen da muka yarda aka yi mana kafin ya sake sakin ajiyar zuciya mai karfi.

Sannan ya ce Ubangiji dai yana kallon komai yana kuma sane da komai ya kuma san dalilin da komai yake faruwa, mu kuma yasan gare shi muka dogara gare shin kuma muke neman taimako muna rokonshi ya taimake mu ya sanya mana sauki cikin wadannan al’amura da suka addabe mu suka addabi yankinmu na arewa.

Ya dawo mana da zaman lafiya da duk wani abinda muka rasa albarkar Alkur’anin da muka yi Imani da shi muke kuma karanta shi kullum. Nayi maza na ce amin Kawu.

*****

A gida a zaune nake ni kadai cikin falona saboda yara suna makaranta, Bilkisu tana nata wurin yayin da maigidan ya nufi Abuja tare da sabuwar amaryarshi mai shekaru sha bakwai, tunani nake yi kan shekaru ashirin da daya na rayuwar aure na da Ado, auren da ya sha gwagwarmaya da kwaramniya iri-iri.

Ya fuskanci matsaloli tun daga na iyaye har kawo kan dangi da abokan zama kafin ya tsunduma, cikin matsalar kishi ko in ce kishiyoyi.

Wadannan matsalolin da kwaramniyar duka basa iya sani in rufe in mance alheri, jarumtaka da tsayuwar mijin nawa a kaina balle ina daukarshi ina jefa shi cikin mazan da ake cewa wai su din ba ‘yan goyo ba ne.

A’a, ni kam nawa mijin da na goya shi ban ga komai ba sai alheri har ma nake ganin tanfar da dai ace shi din shi kadai halinshi kan gamsar har ya iya wanke laifuffukan da sauran yan uwanshi kan yi wa sauran mata, to da sai in ce wa ‘yan uwan nawa mata cewar ai babu wani goyo mai dadi irin goya NAMIJI.

Don kuwa shi namijin ba kowa ba ne face wani cikakken mutum kammalalle, jarumi mai fuskantar kowane irin al’amari da karfin zuciyarshi, mai iya Juyawa daga wani mataki ya koma wani ba tare da yana waiwaye ba.

Mai tarar kowane irin wahala da jaruntakarshi don ya zamo kariya ga na kasa da shi mai sanin ya kamata wanda kuma yake iya saka alheri da alheri.

Ni kam a wurina wannan shi ne namiji.

Allahumma la sahala illa maja’altahu sahalan,

wa’anta taj’alul hazana izah shi ‘ita sahalan.”

Na gode.

Hafsat Chindo Sodangi.

17/1/2013

160

<< Mijin Ta Ce 51

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×